Sashe 10
Beelal Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read
dan bawa ba ya fidda rai daga rahmar Ubangiji. Sai da ta yi tafiya mai nisa ta ji ta gaji kuma idanunta ko iftasu bata son yi saboda kar Beelal ya ace mata, ganin bata ganshi ba kuma ga yunwa da ishirwa sun dame ta dan rabonta da abinci tun daren da Idrisu zai auke Beelal da suka ci tuwo da daddare tare da Beelal in. Gashi kwanansu biyu a hanya kafin suka araso amma bata sanya komai a cikinta ba ta san dai ta sha ruwa a hanya sai kuma waji cincin da ta siya ta an ci shi ma dan ta ga tana ganin jiri saboda yunwa. Wani wurin siyar da abinci ta zo wucewa wata mata tana daga gefen wurin inda aka tanada dan wanke-wanke tana wanke-wanke, rumfar wurin kuma ga mutane nan maza da mata kowa yana sabgar gabansa wasu na cin abinci wasu suna hira. arasawa wurin Fatima ta yi bakinta auke da sallama duk da idan ka ganta ka san tana cikin damuwa sannan ga uwa uba yunwa daje tare da ita.kowa yana uzurinsa sai wani matashin saurayi ne amsa, wanda yake zaune yana cin abinci kuma wata budurwa ta kawo masa wani abu a ba ar leda da alama wani abincin ne zai tafi da shi. arasowa wurin ta yi babu wanda ya kula da ita, saurayin nan ne da ke cin abinci ya tsaya yana kallonta, ganinta gaba aya kamar a birkice take amma kuma ya ga da hankalinta ba mahaukaciya bace sai ya danganta hakan da yunwa ce ko kuma babu ma'ana talauci. Ganin haka sai ya auki abincin da yake ci ya bata dan duk tunaninsa neman taimako take, Fatima kuwa kai ta jijjiga msa alamar a'a hakan ya sanya ya ajiye plate in abincin a wajen dan dama ya gama tafiya kawai zai yi, ledarsa kawai ya auka ya fito daga rumfar, wani machine da ke fake wurin daga gefe Fatima ta ga matashin saurayin nan ya je ya tada machine in ya hau ya tafi abinsa. "Me kike so?" Wata murya da hausa bata gama ratsata ba ta jefowa Fatima tambayar. *BEELAL* NA MAMAN AFARAH *FCW* Book 2