← Book details Beelal Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 13

Sashe 6

Beelal Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Page 9 *KATSINA STATE* *UNGUWAR* *KAFIN SOLI* ~HAMEEDA~ Tun lokacin da Ramma wacce za ta kaita wurin aiki ta je ta taho da ita, Ramma tana kai yara an mata da yara mata gidan masu ku i su yi aikace -aikace kama daga shara wanke-wanke goge-goge raino da dai sauransu. Ta tafi da Hameeda da sauran wasu yaran a inda ta yiwa iyayen kowacce yarinya al awarin idan an biya ku in aiki za ta kawo musu sannan duk arshen wata idan aka bada ku in aikin yaran za ta kawo musu ita ma su bata kason ta. Garin Katsina ta nufa da su Hameeda su bakwai ne amma Hameeda ce arama a cikinsu. Sai da ta kai duka yaran saura Hameeda ka ai ta rage dama kuma akwai wata Hajiya da ta ce tana son yarinya arama dan haka can gidan Hajiyar suka nufa. A ofar tangamemen get an sahun ya ajiyesu Ramma ta biya shi ku insa. Tun da aka sauke su a ofar gidan Hameeda ta maida hankalinta kwacakom a kan tsararren gidan kallo kawai take tana tunanin gida ne za a kaita aiki. "Wuce mu je kin tsaya saboda auyanci kina kalle-kalle" Muryar Ramma ta katse mata tunaninta, cikin sauri ta yi gaba ri e da ledar kayanta. Sai da suka je jikin get in Ramma ta sanya hannu ta shiga wasa get in gidan, mai gadi ne ya bu ofar ganin Ramma sai ya washe baki ganin Ramma dan ya gae ta Hajiya Zulaiha matar gidan ta sanar da shi zuwanta kuma sai da ta tabbatar ta masa kwatancenta dan dama tana an zuwa gaishe da Hajiyar lokaci zuwa lokaci. Gaishe da shi Hameeda ta yi cikin ladabi ya amsa yana gaishe da Ramma suka gaisa tare da tambayar bayan saduwa. Cikin gidan suka nufa domin Hajiyar ta san da zuwansu, kuma gidna ba ba on Ramma bane, Hameeda gaba aya ta shagala da kallon cikin gidan dan sai da ta ga cikin gidan ne ma ta ga ashe dai bata ga komai a waje ba gidan ya ha u ya kuma tsaru. Ramma ce ta wani fisgi hannunta suka fara sauri sai wani hararar Hameeda take, a ofar part in Hajiya Zulaiha suka tsaya Ramma ta fito da waya ta kira Hajiyar ta sanar mata gasu a angarenta, umarni ta musu a kan su shiga, haka suka kutsa kai cikin angaren nata, tangamemen falon da ya gaji da ha uwa da kayan alatu suka shiga bakinsu auke da sallama sai dai ba kowa a falo dan haka shiga suka yi kawai tun da ta ce su shiga. A asa Hameeda ta zauna rungume da jakar ledarta, sai arewa falon kallo take tana rayawa a ranta wannan ce aljannar duniya. Ramma kuwa kan kujera ta haye are - are. Jim ka an sai ga Hajiya Zulaiha tana sakkowa daga upstairs sanye take da rigar leshi an mata inkin buba, sai sar a da ankunne na gwal sanye a jikinta, afarta cikin takalmi wanda ya yiwa afarta kyau. A hankali take sakkowa kai da ganinta ka san ku i sun samu wurin zama, Ramma ganin Hajiyar na sakkowa sai ta sauka daga kujera ra zauna a asa tana washe ha ora. aya daga cikin kujerun da suka awata falon ta samu ta zauna, da an murmushi a fuskarta take kallon kyakkyawar fuskar Hameeda a gefe aya tana ganin kamar ta yi anta a kan aikin da za ta mata, sannan kuma tana ganin wautar wasu iyayen dake aika yaransu aikatau ba tare da tabbas in a hannun waye za su yi aikin ba ko kuma wane irin zama za su yi a gidan su dai kawai burinsu a samo ku i a basu. "Hajiya barka da yamma" Cewar Ramma tana an rusunawa daga zaune da take. "Barka Ramma ya hanya" "Lafiya lau wallahi " "Saukar yaushe?" "Wallahi da azahar muka sauka to na tafi raba sauran yaran gidajen aikinsu, to wannan ita ta rage kuma ita na ga ta yi dai dai da wacce kika ce kina so" Cewar Ramma tana nuna mata Hameeda. "Ina yini" Cewar Hameeda cikin sanyin murya. "Lafiya lau, yarinya ya sunanki?" "Hameedatuwa" Ramma ta kar "Hameedatuwa kuma suna ne?" Cewar Hajiya Zulaiha tana kallon Ramma. "Eh mana" Cewar Ramma. "Ke yarinya ya sunanki" Cewar Hajiya tana kallon Hameeda. "Hameeda" Cewar Hameeda tana wasa da yatsunta na hannu. "Ma sha Allah suna mai da i" Cewar Hajiyar tana kallonsu. "To Hajiya ya kika ganta ta yi kuwa?" Cewar Ramma tana washe baki. "Haba Ramma wannan ai ta yi anta, ba za ta iya yin aikin da nake bu ata ba sai dai kawai a barta take yin goge -goge da an abubuwan da ba a rasa ba" "Hajiya antar ta kike gani, amma wannan babu abin da ba za ta iya ba saboda mari iyarta sai da ta tabbatar ta hore ta sannan ta bayar da ita aiki" "Ikon Allah, wato ma ba mahaifiyarta bace ta bayar da ita?" "Eh ba ita bace mahaifiyarta ta rasu ita da mahaifin suka ci maganin era a abu shi ne silar barinsu duniya, ita wannan matar Yayan Babanta ce" "Ayya marainiya ce ashe?" "Eh wallahi" Hameeda tun da suka fara maganar iyayenta, hawaye ya gama wanke mata fuska, sosai rayuwarta da mahaifanta ta dawo mata da Yayanta Beelal amma mutuwa ta mata yankan auna, gashi Beelal in ma an rabata da shi, Allah sarki maraici. Jaraba Ramma ta fara mata wai daga zuwan su ta fara kuka saboda ita kuka ba ya mata wahala, sai da Hajiya Zulaiha ta ce ta yaleta ai kuka dole ne kuma wajibi ga duk wanda ya rasa iyaye tabbas ya yi kuka. Abinci Hajiyar ta sanya aka gabatar musu Hameeda dai bata ci ba amma Ramma ta zage ta ci ta oshi duk da sun ci abinci a wasu gidajen da ta je kai sauran yaran amma a nan in ma dai bata tsallake tayi ba. Sai da ta ci ta yi nata sannan Hajiya ta kawo ku i dubu goma ta bata ku in aikin Hameeda na watan da za ta fara sannan ta bata dubu biyar nata da atamfofi guda biyu, haka ta yiwa Hajiyargodiya tare da sallama ta tafi tana murna, da yake tana da ar uwa a cikin Katsinar to a can take zaune sai dai ar Mai mazari ce tana zuwa lokaci- lokaci. Tun da ta tafi Hajiya ta sanya wata dattijuwa mai mata aiki mai suna Baba Ramatu ta tafi da ita sashensu na an aiki. Baba Ramatu a akinta ma ta ce Hameeda ta zauna saboda ganin antar ta bata ce ta je akin sauran ma'aikatan ba kuma tana ganim ta yi anta a ce ta zauna a akinta da ban Sosai Hameeda ta ji da in zama a wajen dattijuwar saboda yadda take bata kulawa da nuna tausayi a gareta. Bayan sallar magariba Hameeda Hajiya ta bata plates daga kicin ta kai kan dinning, da sallama ta shigo falon da aran TV a cika shi, tana shigowa ba tare da ta tsaya komai ba ta nufi kan dinning in za ta ajiye plates in. "Ke! Bakya ganin mutane ne ko baki iya gaishe da mutane ba" Cewar wani matashi da ke zaune a kan kujera ya jingina bayansa a jikin kujerar afarsa aya kan aya yana danna waya ba tare da ya ago ya koda kalleta ba. Da sauri ta baro dinning area in ta taho har gabansa ta zubar da gwiwoyinta a asa ta ce. "Barka da dare" A fusace ya aga hannu zai wanke ta da mari Hajiya da fitowarta daga kicin kenan idanunta suka sauka a kan su cikin hanzari ta ce. "Kar ka kuskura ka dake ta musty shin me ma wannan aramar yarinyar ta maka da zaka aga hannu ka dage arfinka za ka duketa?" Ta fa a tana arasowa wajensu. Jim e hannun nasa ya yi wanda zai yi marin da shi ya naushi iska yana wani kumbura baki, tare da aikawa Hameeda wata uwar harara. "Hameeda me kika masa?" Cewar Hajiya tana kallon Hameeda da ke dafe da kuncinta dan tun da ya ago hannu zai mareta ta sanya hanu ta dafe kumatunta, duk da cewa mari duka da duk wasu u ubobi babu wanda bata fuskancesu ba a hannun matar wan mahaifinta. *BEELAL* Tun da ya fara tu a keken nan sai ya ji gaba aya tausayin kansa ya kama shi, tabbas ana shiga damuwa idan aka rasa iyaye kamar yadda ya ga Hameeda ta shiga uncin rayuwa tun daga lokacin da iyayenta suka rasu. Sai dai shi gashi iyayensa a raye amma ya zama tamkar maraya marar uwa da uba. Duk da cewa babu sanin mahaifiyarsa, kuma babu hannunta a tahowarsa amma dai ga mahaifinsa nan da saninsa kuma da sanya hannunsa kai shi ne ma ummul aba isin shigarsa wannan halin. Haka ya cigaba da tu a tsohon keken nan gashi babu katifa ko wani tsumma a wajen zaman, ga duk tsatsar jiki sai zuba take jajawur da ita, hawaye gaba aya ya gama wanke masa fuska a lokacin da ya tuno irin halin da Mamarsa za ta shiga ta kuma kasance a duk lokaci da ta gane ba ya nan, sannan ya san da ace ta san yana nan yana bara to da kuwa ya san ko ta halin a ba za ta bari haka ta kasance ba. Hannu ya sanya ya goge hawayensa saboda ganin ya zo cikin mutane. Haka ya arasa wani waje inda mutane ke ta siye da siyarwa ya tsaya daga gefe kusa da wani maina, yana tunanin ta ina zai fara bara. Bayansa ya waiwaya inda su Idrisu suke, aikuwa dama kamar jira suke suka fara wani aga masa hannu suna masa alama da ya fara bara, kansa ya auke daga kallonsu, zuciyarsa na masa una wai yau shi ne zai yi bara ba wai kuma dan ya fi arfin hakan ba sai dan wadatar zuci da suke da ita shi da mahaifiyarsa duk rintsi basa yin bara duk halin da za su shiga kuwa. Yana cikin tunanin abin da zai ke cewa in zai fara barar ya jiyo waji sautin wani almajiri yana cewa. "A bani ta annabi, a taimaka min da sadaka da
Chapter 6 · 0% Book details