Sashe 3
Beelal Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
NA MAMAN AFRAH Book 2 *FCW* Page 5 Aminullah yana ji yana gani Imran ya kama Beelal iii ko tsayawa babu, har sai da ya dangana shi da kan arfen keken, dan wurin zaman ko katifa babu ta cire sai arfen kawai, yana zaunar shi tare da yiwa Beelal in mugun kallo. a mu tafi" Idrisu ya fa a cikin zafin rai, su duka daga Imran in har Idrisun sai muzurai suke kamar wa anda suka yiwa sarki arya. "Ban iya ba wallahi ko ta a hawa ban yi ba" Beelal ya fa a kamar zai fashe da kuka. "Banda rainin wayo ya ma za a yi ka ce wai baka iya tu a kekenku na nakasassu ba, ai sabo da ku aka eroshi dan haka yanzu ya zama dole ka tu a ko baka so" Cewar Imran yana kallon Beelal. "Bari dai ka ga arshen rainin wayo dan ya ata mana lokaci ne yasa yake ja mana rai" Cewar Idrisu yana fisgar keken da uban arfi suka fara tafiya, Imran na bin bayansu, Aminullah da ke shirin yin magana ganin sun ja keken sai ya saki baki yake bin su da kallo, yana aga hannu kamar mai neman taimako. "Ku bishi a hankali dan Allah" Cewar Aminullah cikin aga murya amma ko sauraronsa ba su yi ba. Beelal kuwa hannu biyu ya sanya ya ri e wajen tu in ganin irin gudun gangancin da Idrisu yake yi da keken ura sai tashi take. Sai da suka an yi tafiya mai an tazara Idrisu ya saki keken ba tare da ya tsayar da keken ba, da sauri Beelal ya sauke afarsa mai lafiyar ya taka asa hakan sai ya zamana kamar ya taka birki ne, dan yadda Idrisu ya saki keken da arfi ka an ya rage Beelal ya hantsila daga shi har keken. "Kai ka fara tu awa da kan ka ka ga mun baro waccan lungun da shagonmu yake mun fito cikin jama'a tun daga nan har zuwa ko ina ma na unguwar nan kasuwa ce dan haka yanzu za ka fara tu awa ka yi gaba mu kuma mu biyo ka a baya kuma kar ka nuna ma ka san mu, duk da ba lallai wani ya hango jirginmu ba, kuma ba lallai wani ya lura cewa mun sanka ba saboda babu yadda za a yi wani ya kalleka ya ha amu da kai" Cewar Idrisu yana hararar Beelal. "Ka ga duk wannan fa in wajen duk wurin ma kasuwa ce amma kar ka shiga can ciki ka je ka ata kake bararka a iya nan, ungo nan, duk wani abu na ci kake sakawa a nan kafin a samo maka robar da za kake sakawa, ku i kuma kake sakawa a acikin aljihunka idan sun taru muna gefe za mu kar a sai ka cigaba da barato wani" Imran ya fa a yana mi a masa wata ledar yaluwa mai sarsar da ya fito da ita a aljihunsa. "To" Cewar Beelal yana ha a hannayensa wuri aya ya sanya hannun biyu ya kar i ledar, dan Mamarsa ta koya masa cewa ba a kar ar abu da hannun hagu ko kuma a kar a da hannu aya sai dai duk abin da mutum zai kar a ya sanya hannu biyu tare da an rusunawa saboda hakan shi ne cikar tarbiya. "Ka taimaki kan ka" Idrisu ya fa a yana fa a murmushinsa dan har ya hango sun fara samun ku "Me zan ke cewa barar, mai zan ke fa a idan ina barar" Cewar Beelal cikin sanyin murya. "Ka ji wani rainin wayo kuma yanzu kai abin da kuke fa a ne baka sani ba, ai a gani na nakasashshe babu wanda zai koya masa yadda zai yi bara tun da dan ita aka halicceshi a nakashe" Cewar Imran yana wani yatsina fuska. "Allah ya haliccemu ne dan mu bauta masa kuma Allah ya hore min rai da lafiya da sassan jiki dai dai gwargwadon yadda zan nemi ilimi in nemi halal in ba wai in yi bara ba, Allah ba ya son ro o ma" "Inyeee to wallahi wannan darasin sai dai ko ka bari sai ranar da ka koma gun wacce ta koya maka wato mahaifiyarka ka fa a mata hakan idan da rabon zaku sake ha uwa ma kenan, idan kuna da rabon sake sanya juna a idanu dan mu wannan karatun mun da e da saninsa" Idrisu ya fa a yana hanka a keken da Beelal in ke ka. Daddagewa Beelal ya yi ya ri e kan keken, ya cije le ensa na asa da ha orinsa, ya shiga arin tu a keken cikin iko da hikimar ubangiji sai gashi ya tu a keken. an rainin wayo ashe ma ya iya ya sa kake wahalar turashi" Cewar Imran. "Rabu da shi mana in ma bai iya ba da ya ji uwar bari ai ya tu a dole ne ai ya nemo mana abin da aka kawo shi takanas domin ya yi wato bara" Idrisu ya fa a yana dariya idanunsa na hango Beelal na jan keken dakyar. "Hahahaha ai dole ne a sha man amarya ko da ta i" Imran ya fa * AUYEN MAZARI* ~FATIMA~ Cikin bacci ta fara jiyo ana kiran sallar asuba, dan haka a hankali ta bu e idanunta tana yamutsa fuska alamar mai bacci. Hannu ta kai gefenta domin ta o Beelal sai ta ji baya nan, hakan ya sanya ta auka ko ya gangara gefe guda ne da yake har lokacin akwai sauran duhu haske bai riga da ya fara fitowa ba. Hannu ta kai inda take ajiye fitilar ta touchlight ta auko, kunnawa ta yi ta haska amma abin mamaki haske na gauraye akib sai ta ga wayam babu Beelal a inda yake kwance, bata kawo komai a ranta ba hakan ya sanya ta yi zaton ko fitsari ya fita duk da ta yi mamakin fitarsa fitsarin ba tare da ya tasheta ta raka shi ba ko kuma ya kar i fitila ba. Sai kawai ta danganta hakan da kawaici da sanin ya kamata irin na Beelal ta tabbata wata ila dan ya ga tana bacci ya i tashin ta ya gwammace ya fita fitsarin a duhu. Sai lokacin ta shiga karanto addu'ar tashi daga bacci (Alhamdulillahil lazi ahyana ba'adama amatana wa ilaihin nushur) Sannan ta mi e ta fito daga akin ganin shimfi ar Idrisu ba ya kwance sai ta yi mamaki kar dai tashi ya yi dan zuwa ya yi jam'i a masallaci mutumin da ko ka an ibada bata dame shi ba shi dama jam'i ma ba zuwa yake ba a gida yake sallarsa shi ma ba a kan lokacin ba. Hamdala ta shiga yi tana ganin dama kwana biyun nan da ya yi da dawo wa ya canja mata gaba aya ba kamar yadda ta saba ganinshi ba, ashe dai canjin har na ibada. Addu'a ta shiga yi a kan Allah ya ara shiryar da shi ya gane gaskiya ya daina zaluntarsu ita da Beelal. Tun tana tsaye tana jiran fitowar Beelal daga bayi har dai ta fara haska fitilar daga inda take tana haska bayin tana karka a fitilar tare da kiran sunan Beelal in dan yanzu ta fara danganta shiga bayin nasa da kashi, dan tana ganin jimawar tashi ta zarce fitsari. "Beelal ka kula ka fito mana mu yi sallar kar lokaci ya ure, kuma ma ka je ka shiga bayi babu fitila ai da ka tashe ni na baka fitilar" Ta fa a da arfi yadda zai ji. Jin shiru sai kawai ta an ji gabanta ya fa i amma bata kawo komai a ranta ba. Takalmi ta sanya ta nufi bayin cikin aurewar kai dan ta san dai Beelal ko gyaran murya da ya mata, amma kuma shirun da ta ji sai ta fara tunani ko dai zamewa ya yi a bayin ya fa i, wannan tunanin sai ya sanya gabanta mummunan bugawa a nan take sai ta ara sauri dan zuwa ta ga mai ke wakana. Addu'ar shiga bayi ta ( Allahumma inni a'uzu bika minal kubisi wal kaba'isi) Da mugun sauri ta afka bayin abin da ya ara sanya gabanta fa uwa ganin bayin wayam babu alamar wani bil adama a ciki. Idanu ta zaro tana wala kiran sunan Beelal in tare da ara haske bayin wai ko idanunta ne basu gani dai dai ba amma sai ta ara gani babu ma wata alamar an shiga bayin, dan ko igon ruwa ma babu. "To ko dai Beelal da Babansa suka tafi masallacin?" Wani angare na zuciyarta ya jefa mata tambayar. "To kuma indai tare suka tafi masallaci to a ina suka yi alwala, tun da dai babu alamar ruwa ma ya ta a bayin sannan ga butoci nan a cike kamar yadda na ajiye" Ta sake baiwa kanta amsa. "Amma kuma Baban Beelal ba ya son ko ka an Beelal ya ra e shi to ta yaya zai tafi da shi masallaci?" "Kika sani ko ya canja ra'ayi, tun da dao kin ga tun da ya dawo ya sakar da fuska ba kamar da ba, kuma kika sani ko a masallacin za su yi alwalar" Wata zuciyar ta raya mata hakan. Wata ajiyar zuciya ta sauke jin wannan tunanin sai ta an ji hankalinta ya kwanta. A haka ta daure ta yi tsarki ta gabatar da alwala duk da ba wai hankalinta ya kwanta bane dan ta san Idrisu ko ka an ba ya aunar Beelal in dai ba ra'a yi ya canja ba duk da cewa wanda ya ce ba ya yi da kai to kuwa ba ya yi da kai in ne har abada, duk wanda ya ce ba ya aunarka to ba ya aunarka in ko da ya dawo daga baya ya ce yana sonka to tabbas ba lallai ya kasance so na gaskiya ba so na ha a ba. Shi yasa ma manzo S.A.W ya ce idan za ka so mutum to kada ka zurfafa son sa domin wata rana zai iya zama ma iyinka idan za ka i mutum kar ka zurfafa insa domin shi ma zai iya zama masoyinka. Allah ha amu da ma su son mu da gaskiya amin. A haka ta gabatar da salla tare da