← Book details Beelal Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 13

Sashe 4

Beelal Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yin addu'o in ta kamar yadda ta saba, bayan ta gama sai ta shiga gabatar da azkar in safiya, tana yi amma kuma tana jiran jin shigowar su Beelal, a haka har gari ya yi haske tangararai amma babu wanda ya shigo, so take ta tashi ta fita amma kuma bata so ta yi laifi a wajen Idrisu haka ya sanya ta ara daurewa. Zuwa can ta ji ha urinta ya are ba za ta iya cigaba da zama ba tare da ta ga Beelal ba dan haka cikin sauri ta fito daga akin gabanta na dukan uku-uku dan ta san dai matsawar masallaci suka je da Idrisu kuma suka tsaya a masallacin ko kuma a wani wajen to tabbas ba za ta fita b a wajen Idrisu duk da yana mata an faram-faram sai ya mata masifa amma haka ta daure dan ta san dai duk abin da zai mata nafila ne a kan halin da take jin zuciyarta tana ciki yanzu. Tana fitowa ta ga ofar gidan a bu e, haka ta shiga duba sawun amma abin mamaki sai take ta ganin sawun Idrisu babu na Beelal, sannan tun da ta fito daga gidan sai ta ga sawun Idrisu bai bi hanyar da masallaci yake ba, a hankali take bin sawun cikin fa uwar gaba dan tabbas sai yanzu take jin hankalinta bai kwanta da kasancewar Beelal a wajen Idrisu tana bin sawun duk da tana ha uwa da mutane jifi-jifi har da masu tambayarta ko lafiya. Amma bata da warin gwiwar amsa musu tambayarsu sai dai kawai ta gya a musu kai, ganin sawun Idrisu ya nufi hanyar fita gari a take wata mummunar fa uwar gaba ta ziyarci zuciyarta duk da ta kasa gane menene hakan ke nufi. Mmn Afrah 09030283375 *BEELAL* NA MAMAN AFARAH *FCW* Book 2 page7 Idanu Fatima ta zaro cikin tashin hankali, tun da dai ta san ita ma da ta tashi da asuba bata ga Beelal ko Idrisu ba, to kenan tun kan asuba suka fito, ko kuma ma ya aka yi bata ganin sawun Beelal sai na Idrisu kawai, wannan tambayoyin take jefawa kan ta hankali tashe, dan ita dai ta san waye anta babu yadda za a yi Beelal ya fita ko da nan da ofar gida ne bai fa a mata ba, ko da, da rana ne bare kuma dare bare ma Beelal ba ya yawo dama gidan su Hameeda ne yake zuwa amma tun da iyayenta suka mutu su kuma wanda take hannunsu wato Yayan mahaifinta da matarsa sun tsani Beelal in ya ra i Hameedar ma ban da ma uwar wahalar da suke bata kamar baiwa, bare ma yanzu ta kwana biyu bata ga Hameedar ba gashi ko gidan ta je matar gidan ta ringa ci mata fuska, kuma ba za ta bari ta ga Hameedar ba hakan ya sanya ta daina zuwa. Wani uban b irki ta ja ta tsaya ganin sawun Idrisu dai ya nufi hanyar barin gari ko lan wasa babu gashi kuma ta ma rasa wane irin tunani za ta yi ta ina za ta fara. Hawaye ne suka shiga zarya a fuskarta wani irin jiri ta ji ya fara juyawa da ita hannu ta mi a ta dafe wani maina da ke kusa da inda take tsaye. "Wai ni ke Fatima me kike dubawa a asa ne ko ku i kika jefar ne, tun da ewa kowa zai wuce ana tambayarki lafiya amma sai ki agawa mutane kai kamar wata adangaruwa, kuma lafiyar ce ta sanya yanzu kike zubar da hawaye har kina neman fa uwa sai da kika ri e maina" Cewar wani matashi da yake mata magana cikin muryar an shaye-shaye sai wani tanga i yake idanun nan jajawur. " Wayyo Allah na Beelal nake nema wallahi ban ganshi ba da na tashi" Wani uban tsaki ya ja sannan ya ce "To kuma menene dan baki ga wannan mai afa a lan washen ba, ke ba ma kya ganin irin ba in jinin da yaron nan ya jawo miki a garin nan tun da kika haifeshi amma har wani ruwan hawaye kike dan baki ganshi ba ai na zata mur... "Ba wai na fa a maka bane dan ka ci mini mutunci, kamar yadda kowacce uwa take so da aunar anta to haka ni ma nake matu aunar nawa an in ma ban fi wata uwar aunar ana ba, kuma wani ba in jini a wajen mutane bai dameni ba dan jahilci ne yake damunsu suna mantawa da cewa Allah shi ke halittar mutane shi ke yin kowa yadda ya so shi ke barin kowa a yadda ya so babu wani mahalu i da zai ja da ikon ubangiji ko ya canja halittar ubangiji ko da kuwa ta kiyashi ce bare kuma ta an adam, dan haka ina aunar Beelal ko da kuwa gaba aya mutanen duniya za su tsane ni su yamace ni, ni na san ubangijina yana so na, kuma yana sane da ni, sannan soyayar ubangiji a gareni ne yasa ya bani Beelal bayan ya hana miliyoyin mutane haihuwa ni kuma ya bani dan haka ina da a gode masa a bisa ni'imarsa gareni" Ta ora da cewa "Wallahi da a ce mutane za su san waye Beelal wace irin baiwa Allah ya yiwa yaron ta fili da ta oye, baiwar walwar da ba kowa yake da ita ba, Beelal Allah ya halicceshi da nakasa amma kuma ya bashi inbin baiwar da mararsa nakasa basu da ita ga kyan zuciya. Ni na kasa gane kan mutane na kasa gane kansu bare afarsu an adam da bashi da ikon canja mutum amma yana adawa da yadda aka halicceshi, shin sai yaushe ne mutane za su farga, sai yaushe ne za su farka daga baccin da suka yi mai nauyi su gane cewa Allah dai aya ne kuma bashi da abokin tarayya a komai shi ke halitta kowa kuma babu wani wanda ya isa ya canja dan haka kowa ya godewa Allah a yadda ya halicce shi ba wai a tsaya kai da fata sai an samu wanda za a tsangwama dan kawai Allah ya masa halittar da ya so, shin jiki da fata da asusuwan da za a maida su cikin asa menene na damuwa da su? Komai daren da ewa mutuwa ce za ta auki kowa kuma cikin asa za a sanya kowa duk kyau da tsarin halittar mutum, fari ne ko ba i ne, asa ce makomarsa, duk mulki da sarautar mutum bashi da makomar da ta wuce cikin asa dan haka babu abin da ya dace da kowa face yin biyayya da bin dokokin ubangiji da yin ibadah da an da kai domin samun rabauta da kuma samun sakamako mai kyau domin bautar Allah ita ce gaba da komai auracewa shirka da manyan zunubai su ne abin gudu. Sa awa Allah ba shi ne abin yi ba ga wanda bashi da tabbacin ara second aya a koyaushe a duniyarsa,mutane su bar kiwon mutane an uwansu su maida hankali da abin da ke gabansu, shi ne ya fi dacewa da kowa ba wai lura da rayuwar wasu ko yamatarsu dan wata halittarsu ba" Fatima ta kai arshen maganar tana kuka sosai, lokacin har mutane maza da mata sun taru yara da manya duk suna sauraron abin da take fa a kowa sai jijjiga kai yake alamar tausayawa da kuma da na sani a kan abubuwan da ake musu a gari ita da anta, basu da damar su ra i mutane, basu da damar su sake, su yi rayuwa irin yadda kowa ke yi, anta bashi da halin ya shiga cikin yara ya yi wasa, bashi da damar ya je makarantar boko ko ta arabiya sai an rakoshi har gida ana tsokanarsa, kuma ba dan ya yi komai ba sai dai suna yi ne a kan abu aya kawai wato NAKASAR da ke tare da shi nakasar da bashi ya yi kansa ba, Allah ne ya yi shi, nakasar da ita kanta wacce ta haifeshi a haka ta ga ta haifeshi amma aka auki gaba aya laifin aka ora a kansu, ita da ta haifa da shi wanda aka haifa, hatta wanda suka ha u suka haifi an bai barta ba wato uban an shi ma yamatarsa yake, to shin ina suke so Fatima da Beelal su sanya ransu?. "Dan Allah Aunty Fati ki yi ha uri ki bar kukan nan wallahi wa annan kalaman naki sun sanya na ji gaba aya duniyar ta ishe ni, sun sanya na ji nadama a kan duk wata yamatar wata halittar ubangiji koda kuwa masu nakasar da ta fi ta kowa abin yama kama daga kuturu makaho da dai wasu masu nakasa kowacce iri ce, tabbas yau kin zama madubi da kika haska mini abubuwa da dama da suka shige mini duhu" Cewar wannan matashin mashayin yana share hawayen fuskarsa. "Ba komai kar ka damu ni zan bi sawun nan domin zuwa in ga inda Idrisu yake ko Allah zai sa in ga Beelal a tare da shi in samu sassauci duk da na ga ban ga sawun takalmi ko afar Beelal ba amma na tabbata Beelal ba zai fita daga gida ba tare da sani na ba. Dole zan bi sawun Idrisu dan na san tabbas akwai lauje cikin na "Zan fa a miki inda Idrisu yake kuma ina tabbatar miki suna tare da Beelal sabodanna gansu da idanuna a daren jiya su... "Dan Allah yana ina ka fa a mini dan girman Allah" Cewar Fatima cikin tashin hankali dan jin ya ce suna tare kuma tun daren jiya sai ta ji hankalinta ya yi mummunan tashi. " A daren jiya bayan dare ya tsala, duk da bansan ko arfe nawa ba amma na san tsakiyar dare ne, na dawo daga yawo wurin wani abokina da ke auyen sama da mu, to tare muke da abokin nawa ya akko ni a machine amma dama tun daga can yace ba zai kai ni har cikin garin nan ba, tun da dare ya yi zai ajiye ni a bakin bari in araso shi ma ya koma dan yana tsoron Babansa ya san baya gida, dan ba a san ya fito ba ta katanga ya etara ya fito muka je mu
Chapter 4 · 0% Book details