Sashe 5
Beelal Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
da sauran abokananmu muka ha u muka yi shaye-shaye, amma in sha Allahu ni da shaye-shaye har abada dan kalamanki na yanzu sun shigeni har na ji cewar ina so in zama mutumin kirkin da za a yi alfahri da ni. Ina cikin tafiya sai na hango wani machine ya taho daga bayana ya samu wuri ya faka ua sauka ya tsaya kamar dai yana jiran wani abu, to bai ganni ba da yake akwai duhu, sai na uya inaso in ga mai zai aikata, duk tunanina cikin auyen zai je yin sata, zuwa can sai na hango wani mutum ya taho da yaro a sa e a kafa arsa, cikin mamaki sai nake tunanin masu satar yara ne, gabana na fa uwa ina so na fito amma ina tsoro dan ni a buge nake duk da dai ba sosai ba amma dai babu wani arfi a tare da ni, mutumin na arasowa sai na ga ashe Idrisu ne ya akko Beelal a kafa arsa dan yana zuwa wajen mai machine in suka fara magana ya ora Beelal in da ke bacci da alama ma bai san ya akkoshi ba, sai da ya ora shi a machine in ya falka. amma haka Idrisu ya tsawatarwa yaron dan dole ya yiwa bakinsa linzami ba dan ya so ba, cikin mugun gudu abokin nasa ya ja machine in suka bar wajen, ni kuma dama da na ga an garin nan ba aunar yaron kowa yake ba sai kawai na ga an samawa kowa lafiya duk da ban san ina zai kai yaron ba bare kuma da na ga Babansa ne ma duk da kowa ya san ba ya aunar yaron, sai kawai na ta e baki na fito daga mo oyata na tafi, amma ki gafarceni " Kallonsa kawai Fatima take da idanunta da ke zubar da hawaye tamkar an kunna famfo ita kan ta ba za ta ce ga irin tsananin damuwar da ta kaiwa zuciyarta farmaki ba lokaci guda, ban da wacce take ciki. Ji take tamkar a jijjigata a ce ta tashi bacci ne take komai da ya faru ba a gaske bane mafarki ne. "Dan Allah jama'a ku jijjijgani in falka daga wannan mummunan mafarkin da nake, mafarkin nan da yake kokarin rabani da wanda na fi auna duk cikin duniyar nan, shin ya mutum zai ji a lokacin da aka rabashi da wanda ya fi auna? Ya uwa take ji a lokacin da mutuwa ta rabata da anta, duk da ta san mutuwa dole ce kuma wanda ya kar i kayansa dama shi ne ya bata kuma ya fi aunar an nata fiye da yadda take aunarsa, amma a haka take jin damuwa ta mutuwar an nata shin ni kuma da wane kwatance za a kwatanta halin da nake ciki, har gwara mutuwa mutum ya ce mutuwa ce amma fa a raba uwa da anta bayan yana raye shi kuma wane irin unci zuciyar uwa za ta shiga? Shin matan aure da mazanjensu suke sakinsu su rabasu da yaransu ya suke ji a duk lokacin da suka koma gidan iyayensu , ji suke tamkar an rabasu da wani sashe na farincikin rayuwarsu, a koyaushe uwa tafi so ta kasance a tare da anta, idan har wacce ta baro yaranta a gidan mijinta za ta shiga damuwa duk da ta san inda yaran suke, to ina kuma ga wacce bata ma san inda yaronta yake ba, sannan ta san yaron yana hannun wanda baya aunarsa, dan Allah jama'a ku kwantanta yadda nake ji yanzu a cikin raina, kowa ya san Idrisu ba ya son Beelal saboda nakasar dake tare da shi, kamar yadda mutanen gari ma basa son sa basa aunar ya ra i inda suke ma, yau kuma ya auke min shi cikin talatainin dare ya gudu dashi dan Allah ku taimaka min" Fatima dake bin mutanen wurin aya bayan aya tana kuka tare da neman agaji a garesu dan ta kasa dakatar da zuciya da kuma hawayenta, babban tashin hankalinta ma shi ne ina Idrisun ya kai yaron. Kowa na wurin babu wanda za ka kalli fuskarsa ba tare da ka yi arba da hawaye sun gama wanke masa fuska ba, gaba aya wurin sun matu ar tausaya mata irin tausayin da kaf garin babu wanda ya ta a musu, haka suke rayuwa a cikin garin tamkar wasu haure da basu da kowa da komai a cikin garin, amma sai gashi yau sanadin kalaman Fatima kowa ya ji tausayinsu ya kamashi, kalaman Fatima kalamai ne wanda akwai hikima, ilimi da kuma iya furta kalma kowacce a mazauninta an bata ha inta. Ha uri aka shiga bata wata dattijuwa ce ta kama Fatimar ta rungume ta dan ta samu sassauci, dan tabbas a duk lokacin da an adam ya tsinci kansa cikin damuwa to idan har aka rungumeshi aka lallashe shi to ko da a ce damuwar nan bata bar shi duka ba zai samu sassauci ko da ka an ne a cikin ransa. Musamman a ce wanda zai rungumi mutum ya kasance uwa ce wato mahaifiya dan ita uwa umin jikinta da ban yake haka nan soyayyarta ta zarta ta kowa ta kuma wuce a misalta ta. Fatimar kwa kamar jira take sai kawai ta kwantar da kanta a jikin matar da ta mata awanya da hannayenta a bayanta, Fatima idanu ta rufe hawaye na kai koma a fuskarta, ji take tamkar a jikin mahaifiyarta, ko Kakarta, ko Yayarta take domin su ne duk duniya suke bata mafaka a baya kafin barinsu duniya, yanzu kuma sai Yayarta Hajiya La ifa kawai wacce kuma yanzu ta yi nisa da ba za ta samu taimakon gaggawa na runguma da lallashi a gareta ba. Da a baya ko Yayarta bata nan idan tana cikin damuwa mijinta wanda ya kasance abin so da auna a gareta wato Idrisu shi yake sanyata farinciki a duk lokacin da ta shiga damuwa in Yayarta bata kusa, kafin ya juya mata baya, kafin ya sauya mata daga Idris zuwa Idrisu, kafin ya manta da so da duk wata auna da yake mata ya maye gurbin auna da iyayya, haka kuma ya yi watsi a duk wata kulawa da nauyinta da ke kansa, kafin ya canja daga fari zuwa ba irin wanda har yau bata san dalilin yin hakan ba, duk da an ce mata da dama su kan auri namiji aure irin na so da auna amma idan an je gidan daga baya komai ya kan canja, sukan rasa duk wanann abubuwan zaman ya dawo sai na ha uri da zaman ansu, amma ita nata salon da ban yake da na saura dan ita abin ya wuce misali sai dai fatan Allah kawo arshen abin. Dattijuwar nan bata cire Fatima daga jikinta ba har sai da ta ji ta an tsagaita kukanta tana sauke ajiyar zuciya, sannan kuma Fatimar ce da kanta ta ago kanta daga jikin tsohuwar tana share hawayenta, dan kuka ya zame mata jiki dan ita kullum idan har za ta tuna da damuwarta to kuwa za ta kasance ne ciki kuka, kuka kamar matar marigayi, dama kuma Beelal shi ne yake auke mata kewa da duk wata damuwa, zama da ita ne da kuma halin da suka tsinci kansu shi da ita ya sanya yaron ya zama tamkar wani babba, ya iya lafazi da kalamin da yake kwantar mata da hankali wa anda a wajenta yake koya saboda da su take amfani wajen lallashin sa da kuma koya masa zama da mutane da ha uri da rayuwa a duk halin da mutum zai tsinci kansa da i ko akasin haka. "Bari na je na bi sawu na kar o Beelal in na gane garin kusa da Kazaure ne wajen abokinsa ne zan je in gani" Ta fa a tana runtse idanunta ta bu e su ko ta ke gani sosai saboda kukan da ta yi sun kumbura suntum, har bata iya gani sosai. "Babangida akko machin ka kaita" Cewar wani mutum da ke tsaye ya fa a wa ansa, da to matashin ya amsa ya je ya akko machine in Fatima ta hau ya ja suka tafi kowa yana tsaye ana jimantawa har sai da suka daina gango machine in su Fatima sannan kowa da ya taru ya watse dan lokacin sosai rana ma ta fito wajen arfe tara saura ne. MMN AFRAH 09030283375 *BEELAL* NA MAMAN AFARAH *FCW* Book 2