← Book details Beelal Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 13

Sashe 11

Beelal Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Page1 *BEELAL* Duk yadda yake zaga wurin ko sau aya bai bu e baki da sunan yin bara ba. Kawai zagaya wuraren yake amma ko ka an ya kasa bu e baki ya yi bara, ga yunwa bashi da karazana ko ka an, dan gani yake ma tu in keken ma kamar ba zai iya ba. Wanda Allah ya sa yana mi a masa ku i ko a bashi abinci. Tun da suka araso wajen da yake suka tsaya daga can gefe, Idrisu sai harara yake aika masa amma Beelal bai ma san suna yi ba, hankalinsa ba a kan su ba yake, ya tafi tunanin Mamarsa. Idrisun ne ya cigaba da tsayuwa a wajen shi kuma Imran ya gewaya a hankali yadda mutane ba za su lura ba ya je wajen Beelal in cikin aure fuska ya kalli Beelal in ya ce "Dalla ka wani zo ka tsaya a wuri aya kai baka yi barar ba ka tsaya sai kallon mutane kake kamar ka ga hoto" "Ina yi mana" Cewar Beelal da sai lokacin ya lura da Imran. "A gidan uban wa kake yi, ka auka duk ba ma ganinka to duk abin da kake muna hangoka, bani abin da aka samu" Ya fa a yana mi a wa Beelal in hannu. Ledar ya mi a masa tare da sanya hannu a aljihunsa ya akko ku in ya mi a masa,lissafawa ya yi, ya ga ari uku da arba'in ne sai da ya duba ya ga babu wanda ya lura da su ya ce "Wallahi ka kutsa cikin mutane ka ware murya ka yi bara ta kirki ka samo mana abubuwa, dan wannan in'innar ma sai kana danneta saboda ake fahimtar bara kake, dan na ga alama in'innar za ta sa ake kasa gane bara kake ko ro o, ko kuma wa a, murya ce gaba aya a dagule" Imran ya fa a yana yiwa Beelal wani kallo tare da mi a masa wata ledar da zai cigaba da zuba abincin in ya samu, juyawa ya yi, ya bar wajen, da kallo kawai Beelal ya bishi yana jinjina rashin tausayi da imani irin na Babansa da abokinsa su basa ma ta shi kawai ta kansu suke ya samo abincin amma sai hannu ya su e sun kar e za su je su cinye dan zalunci. Imran na arasawa inda Idrisu yake suka bar wajen suka koma asan wata bishiya kusa sa wata mota suka zauna suka cinye abincin suka sayi pure water suka sha abinsu. "Gaskiya abokina ba aramar dibara ka mana ba da ka taho mana wannan annakasun" Cewar Imran yana cilla ledar pure watern da ya gama sha, sama ya bugata da afarsa ta yi gefe guda. "Ai nake fa a maka sai da na yi dogon tunani kafin na yanke hukuncin" Idrisu ya fa a yana wani washe baki jin abokinsa ya yabe shi da abin da ya yi. "Aikuwa dai ka ceto mu daga yunwa da rashin ku i, ji fa yanzu ba ko asinmu amma mun ci mun sha har da ku in kashewa gashi za mu raba, dan ma dai na ga kamar har yanzu bai saki jikinsa ba yana ari- ari da abin da za mu samu ma ya fi haka" "Rabu da shi zai ware ne, yanzu dan farko ne amma idan ya ga dole uwar na i dole ya rage dantse ya samo mana ko dan ya ci shi ma, dan idan bai samo da yawa ba yana ji yana gani za mu cinye an wanda ya samo in" Idrisu ya fa a yana dariyar eta. "Kana lokacinka nawan" Cewar Imran yana mi awa Idrisu hannu suka tafa. Beelal kuwa ganin sun kar e abincin da ku in sai ya rasa ma ya zai yi dan yunwa yake ji kamar me gashi kuma la'asar ta yi sosai, haka ya shiga can ciki yana bin wurin sana'ar mutane yana tsayawa wani wajen a koreshi, wani wajen a tambayeshi mai zai siya, idan ya ce sadaka yake nema sai a hantareshi a ce barar ce kuma ba za kake yi da bakinka ba sai ka tsayawa mutane zo o. Hakan ne ya sanya Beelal in ya cigaba da tafiya sai dai yana bara saboda ya ga ba a bashi sadaka saboda ba ya bara dan haka babu yadda ya iya ba dan ransa ya so ba haka ya shiga fa "A taimakawa almajiri da sadaka, almajiri yana bara" Amma duk lokacin da zai ambaci sadaka sai ya ji wata walla ta kawo idanunsa saboda ya san dai ragas yake Allah bai masa nakasar da zai ke yin bara ba. Cikin iko da hikima ta ubangiji sai kawai yake ta samun sadaka, dan sai ya ga jama'a ma kamar shi ka ai suke baiwa sadakar saboda idan ya ce "A taimakawa almajiri da sadaka, almajiri yana bara" Sai kuma ya ara da cewa. "Duk wanda ya bayar domin Allah, Allah zai mayar masa fiye da abin da ya bada" Wannan hikimar d ya sanya a cikin barar tasa ita ce ta sanya mutane ko basu da niyyar bashi sadakar sai su bashi, shi kuma wannan hikimar maganar ya koya ne a wajen Mamarsa, saboda idan suna da ishashshen abin da za su ci, kuma sai almajiri ya yi bara to tana kiran almajirin ne ta bashi ko da a cikin wanda za ta ci ne, idan Beelal in ya ce "Mama ya kika bayar da abincin da za ki ci kika bar an ka an?" Sai ta ce masa "Beela ai duk wanda ya bayar domin Allah to Allah zai mayar masa fiye da abin da ya bada, ka ga kenan idan na bai wa almajiri sai Allah mu ma ya ara kawo mana ta wata hanyar da bamu yi zato ba" Wannan abin da take fa a masa ne yasa yake saka hikimar maganar tata cikin barar tashi sai gashi kuma hakan ya sanya yana samun sadaka, lallai abin da uwa za ta koya wa anta ba iya lokacin zai musu amfani ba har da bayan wasu lokutan ma dan yanzu gashi Beelal ya yi amfani da abin da ya koya daga mahaifiyarsa ya samu hanyar samun bara cikin sau i.Tabbas tarbiya ba aramin makami bane mai kyau da uwa take bai wa anta wanda wannan makamin zai amfane su duniya da lahira, mahaifya ta gari idan ta bai wa anta tarbiya mai kyau ha a tana jifan tsuntsu ne da dutse biyu, tarbiyar za ta amfane su duniya ne da kuma lahira. Sai da ya ji an fara kiran sallar magriba ya fara tu o keken yana fitowa daga cikin jama'a, yana ta kallon yadda mata inyamurai ke akko aton baho ko daro a kansu cike da kaya, tabbas ya jinjina musu dan ya san hausawan mu ba za su yi haka ba. Yana fitowa ya hangi wurin da ya ga su Imran suna tsaye amma basa wurin hakan ya sanya ya rin a kutsa mutane ya samu ya fito ya samu gefe guda, cikin abincin da ya samu, ya sanya hannu ya fara ci, sai da ya an ci amma ba sosai ba dan yana tsoron kar ya ci ya oshi su gane ya ci su masa wani abun. Ledar ya ulle ya rataye ta a jikin hannun keken nasa, masallacin da ke kusa wanda ya ji ana kiran sallah ya nufa yana zuwa ya ajiye keken a gefe guda, aikuwa sai da ya faki idanun mutane ya tashi tsaye daga kan keken gudun kar a ganshi da afarsa a ce ya hau keken guragu mutane ba a iya musu duk da ma dai akwai nakasa a jikinsa amma ba wacce zai hau keken guragu ba. Wajen famfuna ya nufa ya yi alwala ya shiga masallacin sai da ya yi sallar la'asar dan bai yi sallah ba amma Idrisu bai damu da ya ce ya yi sallah ba ko abincin da zai sanya a cikinsa, ko dan shi ma Idrisun sallar ba damunsu ta yi ba. Ya idar da sallar kenan sai aka tada sallar magriba dan dama wa'azi aka gama a masallacin shi ne kuma za a yi sallah. Bayan an idar da sallar ya yi addu'arsa sai ya fito ya arasa wajen keken, idanun mutanen dai ya faka ya hau keken ya baro cikin masallacin, yana fitowa kwa ya hango Idrisu da Imran sai sintiri suke a wajen suna nemansa, hangoshi da suka yi, ya fito daga masallacin cikin hanzari suka nufo shi suna wani zare "Kai gurgun mage ina ka tafi ka sa sai duba ka muke a wajen nan?" Idrisu ya jefa masa tambayar yana kallon ledar da Beelal in ya rataye a jikin keken wacce abinci ne da yawa a ciki. "Masallaci na shiga na yi sallah, ko la'asar ban yi ba" "To sallau, wato kai ga mai sallah to mu nan ko azahar bamu yi ba" Imran ya fa a yana kallonsa. Shiru ya yi shi dai Beelal bai ce komai ba dan shi in banda larura ma babu yadda za a yi ya ha a salloli amma su gasu manya da su wai ko azahar basu yi ba kuma gashi yanzu har an yi magariba, kuma ko alamar yin niyya babu a tare da su. "Kawo ku in" Cewar Idrisu. Hannu ya sanya a aljihun nasa ya fito da duka ku in dan a farar leda ma ya sanya sannan ya sa a a ljihun. Su duka baki suka washe ganin har da ari biyu guda biyu a ciki sauran kuma canjuna ne, lissafawa ari takwas ne da naira ashirin. Hannu Imran ya sanya a cire ledar abincin ya ce. o hannunka mu san maka abincin" Hannu Beelal ya ha e duka biyun Imran ya zuba masa abincin, Idrisu naira ashirin in ta saman ku in ya mi a wa Beelal ya ce. "Kar i wannan in ka tafi hanya ko za ka siyi wani abu ka ara" Abincin hannun nasa ya cinye ya kar i ashirin "Ai dai ka ga inda muka biyo a tahowa, waccen hanyar inda da wancan motar yashin take tsaye, ka bi nan ka koma shagon namu, mu akwai inda za mu je" Cewar Imran yana kallon Beelal. "To" Kawai Beelal ya ce ya juya kan keken nasa
Chapter 11 · 0% Book details