Sashe 7
Beelal Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
abin da Allah ya hore" Cikin sauri Beelal ya waiga ya kalli mai barar aikuwa idanunsa suka sauka a kan wani matashin gurgu da ke rarrafe a asa, gwiwar afarsa ya sanya tsumma ya aure saboda rarrafen, sannan takalmansa sai ya sa ala kowane aya a hannu aya yana rarrafawa gaba aya afafunsa a lan washe suke, da sauri Beelal ya kalli keken da yake zaune a kai sai ya ga da wannan gurgun ya dace ba shi ba, sai ya ga gurgun ya fi bu atar keken ba shi ba da yake da afafunsa amma dole uwan na i ta sanya shi ya hau ba tare da ya shirya hakan ba. wallar da ta cika idanunsa ya yi arin maidata, cikin sanyin jiki ya fara tu a keken a hankali wajen mutane ya nufa amma la ansa sun i bashi ha in kai ya furta abin da yake son furtawa. Yana nan ya ga wannan gurgun ya zo ta kusa da shi ya wuce. ganij a wurin babu wanda ya baiwa gurgun sadaka sai ya cigaba da an tafiya ka an ya ara tsayawa ba tare da ya ce komai ba. "Ungo nan almajiri" Cewar wani mutum da ke su e hannu yana mi awa Beelal sauran abinci a cikin kwano. Hannu biyu Beelal ya sanya ya kar i kwanan yana mai cewa. "Allah saka da gidan aljanna" "Amin yaro" Cewar mutumin yana wanke hannunsa da pure water. "Idan ka cinye ka baiwa waccen mai siyar da abincin kwanon" Mutumin ya fa a yana nunawa Beelal wata budurwa dake siyar da abinci. "To" Beelal ya ce, ganin mutumin ya juya ya yi tafiyarsa, sai ya akko ledar da Imran ya bashi ya shiga juye abincin a ciki dan ya tabbata su Imran suna hangoshi yunwa yake ji amma babu damar ya ci saboda kar ya yi laifi haka yana ji yana gani ya kuye abincin ya ulle ledar tare da rataye ta a jikin hannun keken, kwanon ya su e tare da hannunsa ya arasa ya baiwa mai abincin kwanonta, ya auki wata buta mai ruwa da ya gani a wajen ya wanke hannunsa, ya cigaba da zagaya wurin amma har lokacin bai yi bara ba. MMN AFRA 09030283375 *BEELAL* NA MAMAN AFARAH *FCW* Book 2 Page1 *FATIMA* Tun da Babangida ya auke ta a machine in gabanta yake mugun bugawa tana jin kamar dai akwai wani abu da ke shirin faruwa dan haka sai ta kasance a cikin muguwar damuwa. Tafiya suke amma gani take kamar ma basa sauri gani take garin ya mata nisa sosai. Sunayen Allah ta fara karantowa tare da yiwa annabin rahma S.A.W salati cikin hikimar ubangiji sai ta ji hankalinta ya an kwanta ta samu nutsuwa. Suna shiga garin suka yi tambaya gidan su abokin Idrisun sai wani daga cikin mutanen da suka tambaya na majalissar ya kwatanta musu inda za su samu mutumin. Haka suka tafi wajensa, tun daga nesa suka hangoshi a wajen mai gyaran machine yana tsaye ana duba masa iska a machin insa. Sun kusa arasawa sai machine in nasu ya tsaya, da sauri Fatima ta sauka daga kan machine in dan ita dama ji take kamar ta tashi sama ta isa gareshi. Cinkin hanzari ta isa wurinsa har tana tuntu e zuciyarta tamkar ta tsaga irjinta ta fito haka take ji musamman da ta hango shi babu Idrisu bare Beelal, amma dai tana rayawa a ranta cewa ba zai rasa sanin inda suke ba tun da an sanar mata shi ne ya aukesu da daddare. Gaba aya bata cikin nutsuwarta dan haka komai ya kwance mata, sallama ma baya zo mata a ranta ba, shi ma abokin Idrisun da bai kula da zuwanta ba kawai sai ganinta ya yi a gabansa tamkar an jefo ta. Kafin ya gama tantance daga ina take, mai kuma ya kawo ta sai ji ya yi ta jefo masa tambaya. "Ina Idrisu yake???" Ita ce tambayar da ta fara jefo masa, da farko bai gane ta ba sai da ta yi masa tambayar ya gane matar Idrisun ce. A maimakon ya bata amsa sai ya fara zare ido kamar ya yiwa sarki arya, abinka da marar gaskiya ko cikin ruwa sai ya yi gumi a take a wurin sai ya fara inda-inda a maimakon ya bata amsa kai tsaye. " Na ce maka ina Idrisu yake, saboda an fa a mini kai ne ka akko shi a machine jiya da dare tare da Beelal ka fa a min ina ka kai su?" Ta jefa masa tambayar a karo na biyu. "Eh, eh, am eh haka ne" Ya fa a yana wani inda -inda. "Yana ina???" Shi ne tambayar da Fatima ta masa cikin gushewar hankali dan gaba aya a firgice take ji take kamar kawai ta sha e shi ta yi da jibgarsa ko hakan zai sa ya yi gaggawar bata amsar da take nema, sai dai a gefe aya kuma tana cike da fargabar amsar da zai bata. "Idrisu fa ya tafi Lagos da yaron nan" Wannan ita ce wata mummunar kalma da ta ziyarci kunnuwan Fatima wacce har sai da maganar ta yi amsa kuwwa a cikin kunnuwanta. Sai da jinta ya auke na wasu sakanni kafin ya dawo mata. "Ya, ya, ya" Ta rin a maimaita ya, ta ma kasa ha a kalmomin da za ta yi masa maganar da su, hakan ya yi dai dai da arasowar Babangida wurin yana tura machine in da suka zo a ka. "Ki yi ha uri dan yanzu na san sun bar Kano sun hau hanyar Lagos dan tun sassafe suka bar garin nan, a can bakin titi suka hau mota" Ya fa a yana mata nuni da bakin titin. Da ido Fatima ta bi hannun nasa da ke mata nuni da bakin titin, tun da ta ura ido a titin ta kasa auke idanunta daga wurin sai hawaye kawai da ke malala daga idanun nata.Kallon wurin take ko iftawa babu, kamar dai wanda aka ce ta yi ta kallon wurin za ta ga Beelal in ya fito. "Lagos kuma amma me yasa zai tafi da yaron Lagos? Ba tare da sanin mahaifiyarsa ba?" Babangida ya jefa masa tambayar. "Ni ma dai ban sani ba, kawai dai ya mini waya jiya ya ce in zo in akkoshi a machine, sai da na je ma na ga ashe harda yaro to ni dai bansan dalilinsa ba kuma ma da na ga ansa ne waye zai masa shamaki da ansa shi yasa ban kawo komai a kai ba" Ya fa a yana wani sussun ui da kai asa. Fatima a hankali ta shiga juyo da fuskarta daga kallon bakin titi zuwa fuskar abokin Idrisu, ta ma rasa mai za ta ce wani haushi take ji wanda da a ce yanzu za ta ga Idrisu tabbas idan ta ci kwalarsa sai dai a waceshi a hannunta in yaso hakan ya zama sanadin mutuwar wannan addararren auren nata da shi. "Kai yanzu ko da ansa ne zai akko yaro mai larura ya tafi da shi Lagos ba tare da sanin mahaifiyarsa ba? Kuma ma dai in har tafiyar tsakani da Allah ce, zai ce ka je ka aukeshi tsakiyar dare?" Babangida ya fa a yana kallonsa. "Dakata malam ba fa za ku zo kuna min wasu tambayoyi ba kamar wasu an sanda, kamar wani arawon da ya yi atuwar sata, kuma wannan tambayoyin ai ba ni ya dace ku yiwa su ba, Idrisu ya kamata ku yiwa" Ya fa a yana wani ha e rai kamar zai hau su da zagi, dan yana ganin kamar abin nasu ya zo da rainin hankali tun da dai shi ai ba shi ne ya kar zomon ba rataya aka bashi. "Au haka ma za ka ce ko, to shikenan amma ka saka kan ka a matsayin da nake, shin ya za ka ji? Ko ka saka matarka ko anwarka idan su ne wani irin abu za ka ji a cikin zuciyarka? Shin ka san ciwo da ra in da suke yiwa uwa suka a duk lokacin da ta rasa anta kuwa, ka san yadda nake ji kuwa a cikin zuciyata, amma tambayoyin da muke maka domin samun mafita su ne har ka osa da su, bayan kuma kai kan ka, ka san babu inda za mu samu amsar tambayarmu sai a wajenka, babu wanda ya san amsar tambayarmu sai kai, to babu damuwa Allah mana maganin matsalarmu" Cewar Fatima cikin kuka duk wanda ya ganta a halin da take ciki yanzu sai ya tausaya mata. Mutane har sun fara taruwa, juyawa Fatima ta yi ta kalli Babangida idanunta cike da hawaye ta ce. "Tada machine in mu tafi Babangida" Ta fa a tana sanya bayan hannunta ta goge hawayenta, shi ma Babangidan bashi da ta cewa dan gaba aya tausayin Fatima da ma Beelal in baki aya ya cika masa zuciya, haka ya tada mashine in ta hau ya ja suka tafi, shi kuma abokin Idrisu ya bisu da ido jikinsa sanyi alaw dan kalamin Fatima sun gama kashe masa jiki. Tun da suka au hanya babu wanda ya yi magana daga Fatimar har Babangidan, sai dai Fatima tun da suka fara tafiya hawaye ya kasa auracewa idanunta, saboda kawai ganin abin take tamkar almara, wai yau Beelal inta ne bai kwana a gida ba abin takaici ma wai Idrisu ne ya auke mata shi ya tafi da shi Lagos, wannan abin idan ta tuna shi yake sa ranta yake una. Ji take da a ce tana da dama da tuni ta zama tsuntsuwa ta bi bayansu, tana ta sa ar jakin nan ta sa a ta warware a hakan har suka shigo garinsu, har ofar gida Babangida ya kai ta, yana ta faman bata ha uri ita dai kai kawai take iya aga masa dan hawaye sun i yankewa idanunta, ji take har wara a ce da mutuwa Beelal in ya yi ake bata ha uri da sau i tun da dama kowa ya san mutuwa dole ce, amma yanzu kuma yana raye bata san halin da yake ciki ba wannan abu yana matu ar sanya zuciyarta damuwa. Fakyar ta iya yiwa Babangida godiya ta juya ta shige gida, dan mutane har sun fara taruwa masu son jin waf