← Book details Bana Sonshi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 25

Sashe 9

Bana Sonshi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma tace"me za ayi dashi"

Be tanka ta ba ya fara gyrawa Rahma hijab

Su Hassan ne Suka shigo da gudu dawowarsu daga makaranta

Zama Hassan yayi Yana cire socks hussaini ko tambaya yake akan meya same anty Rahma

Socks din da Hassan ya cire shi Aayan ya d'auka yasawa Rahma

Sai a lokacin umma ta fahimci desighn dinta ne beso a gani murmushi tayi

Yace"umma muje asibiti"

Tace"ah'ah ba sai munje ba bari in d'auko ruwan sanyi domin daga jiya zuwa yau sumanta be kirguwa Kuma ruwan sanyi nike watsa Mata"

Kawo ko a ranshi cewa yake" ki tashi Rahma filina na hanun ki "

Umma na zuwa ta watsa Mata ruwan

Wani numfashi ta ja sanan ta bude idonta

Kawo yace"sannu dan girman Allah karki Kara sumewa in ba haka ba nima zan biki yau ma a gidan ku zan kwana Kar cikin dare ki sume a rasa me taimako"

Umma tace" ikon Allah ka tafi mun gode sai goben kenan"

Aayan ya harareshi ai sai kawo yace"wallahi Allah ya dibewa yaron nan albarka yanzu Dan shiga hakkin ya kakabawa yariya sharri dake sumar da ita "

Aayan yace"me akayi Mata?

Yace"ai video akayi mata da wani gardi ni na tabbata ba ummana bace"

Aayan ko a ranshi yace"Allah yasa ba jibrin bane kodai plan din da yace kenan?"

Kuka Rahma ta fashe dashi tace"Dan Allah ka daina tsineme bashi da laifin ni na San shiga tsakanin mu dashi akayi Kuma wallahi bazan tab'a yafewa ko waye keda hanun a ciki ba"

Ji yayi gabanshi ya fadi

Mikewa yayi yace"umma ni zan tafi zan turo likita a dubata "

Yana gama magana ya ja hanun kawo suna fita yace"tafi gida ya Isa haka"

Zaiyi magana ya katseshi da cewa ka tafi ko insa a Zane ka"

Yace"tuni na Kai gida"

Jibrin ya zo ya d'auke shi suna kaiwa guest house

Ya kalli jibrin yace...

Maman Nur
Share
[2/20, 8:26 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄👄
*BANA SONSHI*
💋💋💋💋💋💋
_By maman noorul_
_Hudah__

*👄💡NUR WRITER ASSOCIATION💡💋*

💡 *N W A* 💡

*Lightning and bringing smile to your world is my peority*

*NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~

🅿3⃣5⃣-3⃣6⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Kallon jibrin yayi yace"what exactly do you do da yasa aka fasa auren Rahma?"

Jibrin yayi murmushi ya tsara me kafin yace"sir it was a simple plan"

Aayan ya gyra Zama yace"Iam interested"

Jibrin cikin jin dadi ya bashi labarin komai harda nuna me video

Ji yayi jinin shi na tafiya a 360 ganin wani saman Rahma yasa ranshi mugun b'acewa

Mikewa yayi ya kaiwa jibrin wani mugun pounch kawai jini ya b'ale me

Aiko be kyalleshi ba ya dinga naushi Amma ba halin gudu

Neel down yayi,shigowar Abdul ne yasa ya kyaleshi yace"kasan abinda ka aikata kuwa?kasa mutane na Mata kallon Yar iska,you defame her above all ka kawo wani kazami ya hau jiki Rahma"

Jibrin yace"kaifa ka ce at all cost"

A fusace yace"will you shout your dirty mouth"

Abdul yace"toh me kake so yayi inda beyi haka ba da yanzu kana gadon asibiti an d'aurawa Rahma aure da wani"

Wani kallo yayiwa Abdul yace"ai da ya fad'a min dana sa abinyi"

Kallon jibrin yayi yace"yau ka koma Lagos a can zan hukunta ka"

Jibrin ya tashi ya tsara me sanan ya bar wurin

Wanene Aayan?

Major general Abubakar mohammed jabir Amma ana kiran shi da Aayan Yana domin sunan kakarshi ne dashi d'an ne ga marigayi late general Mohammed jabir da mahaifiyarshi dr Maryam su asalin Yan garin kano ne hausawa ne

Su biyu iyayen su Suka Haifa dashi da kanwarshi Amina

Aayan a kano aka haifesu inda tun Yana da karanci shekaru mahaifin shi ya turashi N D A watoh Nigeria defence academy tun yana karami yake samun horo me sanani

Aayan Yana da mugun girman Kai Kuma miskili ne na ajin farko shi a rayuwar shi ya tsani raink Amma Kuma shi Yana da rainin wayau da wuya ka gan Yana da dariya sai dai in su biyu ne da ummishi ko da babban aminin shi Abdul Wanda shima ba kullum yake ganin dariyar shi ba ga shegen miskilancin tsiya wanan dalilin na cikin abinda ya hanashi aure domin a ganin shi macece zata ce tana sonshi Amma yafi karfin yayi ta bin mace shiyasa in yayi budurwa Wanda su din ke nuna suna sanshi in sun gaji sai su rabu domin be Basu kulawa ko kiran su beyi

Tun suna kanana Suka kulla abota da abokin shi Abdullahi mansur (Abdul )Wanda tun abdul na karami yake da sha'awar aikin soja amma da yike rayuwar yanzu in Kai ba kowa bane makaranta ma gagaran talaka yakeyi domin shi Abdul iyayen shi ba masu Hali bane kuma maraya ne domin a wajen haihuwarshi mahaifiyarshi ta bar duniya ya taso ne cikin ukuba da matsifar kishiyar uwa Wanda kwata-kwata bata sonshi a gidan ta mayar dashi jaki Kuma mahaifin shi be isah yayi magana ba kasan cewar sai inda akayi dashi

Ba karamin wahala ya Sha ba gidansu Aayan kawai yake zuwa ya ji sauki a lokacin da Aayan ya tafi NDA duniya tame mugun zafi shima Aayan haka bejin dadin makaranta a daddafe yayi shekara d'aya a shekara na biyu ne ya tursasawa Abba shi ya tsayawa Abdul shima ya shigo makaranta

Kowa a makaranta yasan da abotansu duk da Aayan yayi senioring dinshi da one year
Sai dai sun mayar da hankali sosai a karatu suna abinda ya dace

Cikin ikon allah Aayan ya fara graduating inda ya fito da second lieutenant

Aayan jami'i ne Mai hazaka da sanin aikinshi shekara na zagayo Abdul yayi graduating duk a Lagos aka tura su aiki basa rabuwa da juna sai dai hallayensu ya bambanta domin shi Abdul Yana da fara'a shi Kuma Aayan babu dariya a tsarin shi

Ganin yau abdul ya Zama wani abu yasa ladidi fara shishshige me karshe ma sai ya fita harkarsu ya bar gidan mahaifinshi sai dai duk wata Yana aika musu kayan abinci ana cikin haka ne sai Allah yayiwa abbanshi rasuwa

Mutuwar ya girgiza shi domin baba ne kawai ya rageme a duniya besan Yan uwan ummashi ba kuma Yan uwan abbana shi a kauye suke"

A haka rayuwa ta cigaba da ta tafiya inda cikin ikon Allah Suka Kai wani matsayin babba a aikin soja

Sai dai kuma wata rana aka samu gawar general abban Aayan a office an bindige shi saboda ya kasance mutum ne me son gaskiya hakan yasa na gaba dashi dama kasa dashi Suka tsaneshi domin ya hanasu musgunawa talakawa kuma ya hana ayi ta kashe su

ana hakane wasu kungiyan Yan ta'ada da Suka adabi al'uma masu suna *Alkibila* Suka nimi ya had'a hanun dasu Amma yaki Kuma sai ya fara bincike akan kungiyar a b'oye har ya gano shugaban Wanda be tab'a tunanin Yana da hanun a kashe dumbin jama'a ta hanyar sa musu bomb Amma a zahiri mutane na ganin shi mutumin arziki

Wanan kungiya ya tara manyan kasa Kama daga minister senators da Yan kasuwa yan siyasa jami'an tsoro da sauransu

Tun wanan ranan Aayan ya d'aura d'anmara Kuma ya Sha al'washi sai ya kunyarta da duk wani Wanda keda hanun a kisar abbanshi sai yasa ya fuskanci hukunci Kuma sai ya tarwasa kungiyar *Al'qibila* yanzu wanan shine babban burin mazajen nan biyu Wanda yanzu Aayan ya Kai major general shikuma Abdul brigadier general

Aayan fari ne sol Yana da kwarjini sab'anin Amir dake da baby face shima Abdul farine Amma be Kai Aayan ba Domin farin Aayan har jaja yakeyi

Aayan Yana da skekara arba'in shikuma Abdul Talatin da Tara

Wanan kenan sauran bayani sai Nan gaba

*Cigaban labari*

Please ignore any errors
Maman Nur

Share
[2/20, 8:26 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄👄
*BANA SONSHI*
💋💋💋💋💋💋
_By maman noorul_
_Hudah__

*👄💡NUR WRITER ASSOCIATION💋💡*

*💡N W A💡*

*Lightning and bringing smile to your world is our peority*

*NUR WRITERS* ~it a beautiful~ ~world~

Dedicated to zainab Hassan Ina jin dadin comment dinki

🅿3⃣7⃣&3⃣8⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Bayan jibri ya bar gidan Abdul ya kalli Aayan yace"yanzu miye abinyi domin mu kanmu musan masu laifine mun zalunce matan nan me zamuyi dan goge lafin mu"

Aayan yace"wani laifin?ai babu ko wani laifin da nayi everything is fair in love and war,Kuma bazan Bari yar tasisiyar yariya ta raina ni ba kuma ai itama tayi laifi kuma zan hukunta ta na kiran sunan wani yaro a gabana"

Abdul yace"lallaima ka duke ta ka Hanata kuka niko kulawa zan bawa yus dina har sai ta fara Sona da kanta tunda nasan ni me laifine"

Tabe baki Aayan yayi yace"Ashe zaka jawowa kanka raini ni ba wani lallab'ata da zanyi casa juna zamuyi daga baya mu shirya most important thing na aureta"

Abdul yace"nidai ba ruwana in tayi tsami kowa nashi ta fishe shi"

Da misalin karfe 8:pm Abdul ya fita direct gidan su yusura yayi Walid ne yayi me izo daya shigo ciki gidan falon Abba ya kaishi suka gaisa

Walid ya shiga cikin dan Kiran yusura

Yusura ne zaune bakin madubi ta tsara kwaliya tayi masifar kyau fashe jikinta tayi da tulera

Tace"aini abinda baka so shi zanyi tayi Kuma wallahi babu wani hijabi da zansa haka zan bishi dan ni ba umurnin shi zanbi ba "

Gylen abayanta ta d'auka tayi rolling

Walid ne ya shigo d'akin yace"kizo Yana jiran ki"

Kallonshi tayi tace"Yaya yanzu ka kyauta kenan?a matsayinka na yayanah ka bari a ka had'a baki da kai akamin sharri?kai ka Kara d'aurewa wanan munafukin gidi ya min sharri Kaine ka ce ka ganni ina rokonshi harda auwal"

Walid yace"ke yimin shiru ya min alkawarin zai kaini kasar waje"

Yusura tace" yanzu saboda kasar waje za a had'a baki da kai a cuceni?"

Wucewa yayi ya Barta da takaici kasancewar shi Yaya a gareta babu sallama ta sameshi a falon abba

Karasawa tayi cikin hade rai ta zauna

D'angowa yayi ya kalleta dariya na niman sub'ace me ganin tayi kwaliyya watoh dan ta b'ata ranshi tayi Bata san abinda yake so ba kenan

Gimtse dariyar shi yayi yace"baby ba gaisuwa ne?"

Tace"eh babu"

Murmushi yayi yace"ai nasan kunya kikeji domin na gan kunyar a kwayar idonki yus ashe bana ce karkiyi kwalliya ba"
Chapter 9 · 0% Book details