← Book details Bana Sonshi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 25

Sashe 15

Bana Sonshi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lieutenant general ne ya mike yace"toh gaskiya kiyi sauri domin yaron nan ya fara caza Mana kai in kuma babu cigaba me zai hana mu kashe shi inda muka kashe mahaifinshi"

Senator ya mike yace*Nima dai bansan meyasa aka barshi har yanzu ba"

Hajiya saratu tace"ai a ganina komai ya zo da sauki tunda yanzu yana da iyali mu fara me barazana dasu ai duk wani me iyali zai kiyaye domin nasan ba zai so a cutar da ita ba "

Samira tace"eh yanzu nasan abinyi in ta kama zan kashe matar nashi"

Shugaba yace"ba itace target ba focus on the main target "

Haka fa sukayi ta tautanawa kafin kowa ya watse inda Suka yanke zasu halbe shi dajin da zasu inda abin zaiyi looking kakar a cerelion din yan ta'ada can be suka halbeshi babu Wanda zai zargesu

B'angaren Rahma ko bayan ta idar da sallah kwanciya tayi Amma ba bacci take ba yunwa da ta fara ji ne yasata saukowa

Ganin shi tayi zaune a falo,shiko tun tana saukowa ya zuba mata ido"

kallonshi tayi tace"zan iya samun abinci? yunwa nikeji"

Ji yayi be kyauta ba mikewa yayi zai Kama hanunta ta fisge

Tafiya ya fara sai ta bishi a baya,kicin ya nuna Mata yace"ki dafa komai kike so"

Bata tanka shi ba ta karasa gaban gas ta kunna ta d'aura tukunya

Jellouf din taliya ta dafa,bayan ta gama ta bude fridge sai ta gan water melon fitowa dashi tayi ta had'a juice sanan ta kwashe zuwa dining

Zama tayi ta fara cin abinci cikin natsuwa

Ganin bata kirashi ba yasa shi mikewa ya karasa ya zauna har zai jawo kulan ta rike

Kallonta yayi yace"ni bazan ci abinci bane?"

Wani kallo tame tace"miye hadina da kai da zan ma girki ka Kira karuwar ka ta zo ta girka maka"

Nade hanunwanshi yayi yana kallota dariya ma ta bashi toh me take nufi?

Tashi yayi ya haura sama sai gashi ya fito da jallabiya domin an fara kiran sallah magrib

Yana fita ya had'u da Abdul shima ya fito yana sauri zashi massalaci

Abdul na ganin shi yayi murmushi yace"ango Ashe ka fito "

Aayan yace"Abdul akwai matsala fa'

Abdul yace"na miye?"

Yace"muje in mun fito zan maka bayani"

Massalaci Suka Shiga sukayi sallah basu fito ba sai bayan isha'i suna fitowa Abdul yace"inajin ka,domin sauri nike na bar baby a gida

Tsaki Aayan yayi yace"Kai baka da kunya fa"

Abdul yace"kunyar me zanji matatace Kai dai fada kawai

Aayan yace"Samira ta tunkari Rahma and the worst thing da muka dawo mun sameta a gidan mu,Kuma Rahma ta ganmu muna kiss"

Abdul yace"what?kana nufin kayi kissing Samira why?"

Yace"ba kissing dinta nayi ba muna magana ne kawai sai naji ta hade bakin mu dai-dai fitkwar Rahma I don't know what to do I know yanzu tana Nan tasawa kanta damuwa"

Abdul yace"toh ai ya kamata kayi Mata bayani ka jawota jiki ka lallashe ta"

Aayan yace"toh ai raina ni zatayi"

Cikin jin haushi Abdul yace"ka ajiye maganar raini a gefe domin ita macece Mata Kuma yan sarauta ne komai kudin ka da mulki ka sai sun juya ka Kuma gaskiya in bakayi wani abu ba Ina tabbatar maka ka bude kofane na shaidanu su Shiga tsakanin ku gaskiya tama birgeni da bata nunawa Samira kofar da zata shiga ba ta nuna ko a Yaya kake Kai mijinta ne gaskiya na yaba da tarbiyanta abokina ka ajiye maganar girman Kai ka je ka rungume matar ka ka bata farin ciki in ba kana so ka rasa ta bane,mu ne fa Muka rabasu da masoyansu ai in bamu kwantar musu da hankali ba mun cika azzalumai,ni tun farko shiyasa banso idea na using Samira ba gashi yanzu she is becoming a night mare Kuma kayi kuskuren Bata free access na gidan ka "

Aayan yace"

Maman Nur

Share
[2/20, 8:31 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄👄
*BANA SONSHI*
💋💋💋💋💋💋
_By maman noorul_
_Hudah__

*👄💡NUR WRITERS ASSOCIATION💡💋*

*💡N W A💡*

*Lightning and bringing smile to your world is our perority*

*NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~

Dedicated to MUM KHADY

🅿6⃣3⃣-6⃣4⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Yace"toh amma ganin haka zaiyi aiki?"

Abdul yace"ai zakayi tayi ne har sai ta sauko daga fushin da takeyi ka gan kamar ni yanzu yusra ta daina fushi "

Aayan yace"da gaske?"

Abdul yace"eh Mana domin ni bauta nike mata ba ruwana tunda ba haramun bane"

Aayan yace"ok but gaskiya bazan iya yi mata bauta ba"

Abdul yayi tsaki yace"shiyasa Kai har yanzu Kai Yaro ne mu har mun kusa wuce wurin"

Aayan yace"toh fad'a min kalmar soyyaya da zanje in fad'a Mata"

Abdul yace"nidai na tafi baby na jirana"bejira abinda zaice ba ya wuce

Aayan ya shige ciki a falo ya tarar da ita zaune tayi tagumi tana ganin shi ta mike zata haura
Sama"

Ji tayi yace" _Rahma_"cak ta tsaya amma bata juyowa ba

Yace"dawo ki zauna"

Da ta so tafiyarta ne ta barshi amma ta tuna
Nasiha ummi ta dawo ta
Zauna

Komawa yayi kujeran da ta zauna ya Kama hanunta Yana murzawa ya rasa daga Ina zai fara

Gyran murya yayi yace"Rahma me kika d'aukeni? ina son in sani"

Tace"d'an iska,mugu azzalumi,mazinac...."

Toshe Mata baki yayi yana girgiza Mata kai

Kuka ta fashe dashi tace"nidai ka mayar dani gidan mu ni bazan iya zama da fasiki ba

Kallonta yayi cikin ido yace"Rahma please look at me nayi miki Kama da fasiki?wallahi ban tab'a aikata Zina ba wallahi ki fahimceni a baibai ni ban tab'a ba

Fisge hanunta tayi tace"nidai ka sallameni *BANA* *_SONKA_* bazan zauna da kai ba

Murmushi takaici yayi yace"da a ce Zaki bani dama d'aya tak Rahma da kin gane ni ba makiyin ki bane Zaki gane ni mai kaunar ki ne"

Tashi tayi ta wuce ta barshi zaune

Shima tashi yayi ya koma dining ya bude kulan taliya ya fara ci

Su Amir ko tunda aka kawo Aneesa be shiga d'akinta kuma in ya Shiga nashi ya kulle hakan ya Kara b'ata ranta domin ta bishi ta buga Amma yaki budewa

Kiran mahaifiyarta tayi a waya ta zayyana mata komai

Anty hafsat tace"shine sai yanzu kike sanan Dani?toh karki damu yanzu zanje wurin malamina komai zai dai-daita "

Aneesa tace"toh mama and kisa ayimin maganin uwashi kin gan fa jiya har part dina ta biyoni tana min matsifa akan wai banje na gaisheta ba"

Anty hafsat tace"toh ita ce Mata akayi jaka ce ke ko ita ya aurowa ke da tun ba a Kai ko Ina ba ta fara takura ki toh dole ne in Yi maganin ta,domin auren akayi ki huta bawai ayi ta tayar Miki da hankali ba"

Aneesa tace"yauwa mama harda wanan Mara kunyar kanwar tashi Zahra ta fara raina ni"

Anty hafsat tace"duk ki kwantar da hankalin in Ina raye sai kinyi mulki a gidan"

Wani ihu tayi tace"ina ji dake mama"

B'angaren su Abdul ko

Maman Nur
Share
[2/20, 8:32 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄👄
*BANA SONSHI*
💋💋💋💋💋💋
_By maman noorul_
_Hudah__

*👄💡NUR WRITERS ASSOCIATION💡💋*

*💡N W A💡*

*Lightning and bringing smile to your world is our perority*

*NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~

🅿6⃣5⃣-6⃣6⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Yana shiga ya tarar da yusura zaune a falo sanye da hijabi

D'auke Kai tayi yace"baby ba Sannu da zuwa?"

Hade rai tayi murmushi yayi ya karasa inda take yace"fushi kikayi ko?"

Bata amsa ba sai ya rungumeta yace"sorry na tsaya magana ne da abokina,tashi muje mu ci abinci yau da wuri zan kwanta"

Tashi tayi shi ya bata har ta koshi

D'aukanta yayi sai bedroom sukayi wanka sanan ya kwantar da ita ga mamakinta sai ta gan ya kwanta

Tace"kaje d'akinka ka kwanta ni bazan kwanta gado d'aya da Kai ba"

Jawota yayi ya rungume yace"ai in kin gan mun raba shimfida sai dai in bana gari ko ke kinyi tafiya Amma ai so Nike mu zama hanta da jini,Ina son mu kasance babu Wanda zai iya rayuwa sai da d'an uwanshi yus Ina son ki zamto ko wani lokaci Ina ranki,yus nasan ni Mai laifine na bi hanyar da be dace ba dan in aureki amma please ya kamata kiyi min kyakyawar fahimta sonki ne ya jawo haka baby ki yafe min"
Yus saura sati d'aya mu tafi peace keeping ina son cikin kwanakin da suka rage ki bani kulawa baby kila bazan dawo a Raye ba amma Ina son kiyi tamin addu'a baby na,baby ni bani da kowa a duniya yanzu sai ke ki rufamin asiri ki soni ko kema Zaki rabu dani ne?baby in na mutu a peace keeping dan girman Allah Ina niman alfarma kiyi idda a gidana na kano kiyi tamin addu'a ko kin auri wani in kuma na barki da ciki in kin haifeshi karki Bari ya wulakanta a idon duniya karki bari a....."

Kuka me karfi yusura ta fashe dashi tace"ka Bari bana so,daman kasan zaka mutu ka rabani da Wanda zan aura?"

Murmushi jin ta damu dashi yayi yace"Yi shiru toh na daina in na tafi kiyi tamin addu'a in kina son in dawo"

Jan majina tayi tace"zanyi tayi maka addu'a "

Rungumeta yayi ya ja masu bargo bacci ya kwashesu

Aayan ne a falo Yana waya da jibrin,jibrin na rokonshi akan ya yafe me yayi laifi

Yace"jibrin what you did is unforgiveabla bazan yafe maka ba,in ba rashin hankali ba meyasa zaka je kasa ayiwa Rahma video da wani kato ita kanta kawarta zainab take ko waye? da zan ganta sai ta fuskanci hukunci,kasan irin kallon da ake Mata kuwa?ana Mata kallon Yar isakan ce fa"

Fadiwar plate din hanun Rahma ne yasashi juyawa sai ya ganta tsaye tana nunashi

Yace"oh no "

A hankali ta zube kasa ta saki kuka

Tashi yayi yace"Rahma please let me explain is not what you think please"

Mikewa Rahma tayi ta

Maman Nur

Share
[2/20, 8:32 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄👄
*BANA SONSHI*
💋💋💋💋💋💋
_By maman noorul_
_Hudah__

*👄💡NUR WRITERS ASSOCIATION💡💋*

*💡N W A💡*

*Lightning and bringing smile to your world is our perority*

*NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~

🅿6⃣7⃣-6⃣8⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Mikewa Rahma tayi ta kalleshi tace"wani laifi na tab'a maka a
rayuwa?meyasa ka zab'i ka b'arka min rigar mutunci?"
Chapter 15 · 0% Book details