← Book details Bana Sonshi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 25

Sashe 24

Bana Sonshi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mata mu kiyaye d'an na kowa ne balle rikon maraya yana da tarin Lada bamusan me zai Zama gobe ba

Allah yasa mu dace

Maman nur
[2/20, 8:37 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄👄
*BANA SONSHI*
💋💋💋💋💋💋
_By maman noorul_
_Hudah__

*👄💡NUR WRITERS ASSOCIATION💡💋*

*💡N W A💡*

*Lightning and bringing smile to your world is our perority*

*NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~

🅿1⃣0⃣2⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Rahma ko sabuwar soyyaya Suka bude da Aayan inda take jinjina jaraba irin nashi domin a lamuran shi babu d'aga kafa gara kawai yake kwasa

A yau ta kama jumma'a yau sunan yusura Rahma ne gaban madubi tana drying kanta da hand dryer

Tace"soja yau ka Gama bani kunya ummi da umma sai sun min fad'a za a ce ban zo da wuri ba kwana fa ya kamata inyi a nan shine sai yanzu zani"

Tasowa yayi a gado ya rungumeta ta baya ya zame towel din jikinta yace"Rahma saboda suna baki Bari na samu Hutu ba
Ki Bari in samu natsuwa Mana"juyawa tayi ta kalleshi tace"soja wani irin natsuwa Kuma bayan Wanda ka samu yanzu nifa na Lura kasheni kake son yi har yanzu zafi Nike ji a wurin ban saba ba kuma baka Bari na yanzu ni kaina a gajiye Nike ga bashin bacci"

Komawa gado yayi ya kwanta yace"shikenan ki tafi sunan"

Ajiye dryer tayi ta Haye gado ta kwanta a saman shi tace"toh gani"

Kallon kwayar idonta yayi yace"yauwa Rahma "

Nan ma fa soyyaya aka Sha da sauri Rahma ta sauka ta Shige toilet ya bi bayanta wanka sukayi suna fitowa

Ta shirya cikin Shirin alfarma shima kalal kayanta yasa ta d'auki jaka Ashe ya cika mata su da kudi

Koda suka isah sun tarar da jama'a a gidan cike

Rahma na hango ummi tayi kwalliya tayi kyau taje ta rungumeta tace"nayi kewar ki ummina"

Ummina tace"ai na ga alama ai da kun sani da kunyi zaman ku domin Banga amfanin zuwan ku a wanan lokacin ba "

Aayan ya karaso ya tsosa kai Yana murmushi

Rahma tace"Yi hakuri ummi"

Jan hanun Rahma tayi suka shige ciki

Yusura zaune a bakin gado tayi kyau cikin wani lace gashi ta Sha d'auri

Rungume juna sukayi yusura tace"sai yanzu"

Rahma tace"wallahi karkiyi fushi abubuwa ne sai a slow

Rahma ta lura da Mami dake zaune ta rungumeta tana ihu

Mami tace"Kuna Nan abinku"

Suna yayi suna an ci an Sha da yamma taro ya watse

Bayan an watse duk suka cika a falon ummmi ana hira

Umma tace"Bari in Kira ya'ta Amina "

Kiranta tayi Amina dake wasan b'uya da amir ta ji wayarta yayi Kara ta d'aga tana sheke dariya karasowa yayi yace"nine winner "

Duk Suka kalli juna domin wayar na speaker

Cikin dariya tace"umma Ina wuni?"

Umma ta kalli ummi kafin tace"da Amina Nike magana?"

Amina tace"eh nine"

Ummi tace"toh dama Kira nayi in fad'a miki nayi nazari na gano be kamata a tursasa ki a Miki auren dole ba toh yanzu mun yanke hukunci raba auren ki da amir tundabaki sonshi "ta Kare magana cikin danne dariyarta

Amina tace"ni yaushe nace bana sonsa?nidai umma ku kyaleni nafi san nan ku barni Ina son mijina"

Ummi ta kwace wayar tace"Sannu Amina shugaba marasa kunya"

Murgud'a baki tayi ta yanke waya ta ajiye amir ya kwashe da dariya yace"basu san mun jone ba"

Aayan yace"dama Ina son in sallame ku gobe zan tafi Lagos Amma Rahma anan zan barta"ji tayi gabanta ya fadi

Abdul yace"yusura ki fara had'a Kaya "

Yusura tace"toh"

Ummi tace"ko Kaine shugaban mayu sai ka barta tayi arba'in"

Mami ne ta jehowa Abdul da tambaya tace"Abdul dan Allah miye sunan mahaifiyarka?"

Fada mata yayi tace"zan iya ganin hoton ta?"

Yace"Bari in dubo"

Zuwa yayi ya d'auko ai Mami na gani ta fashe da kuka tace"wanan ai Yar uwatace uwa d'aya uba d'aya yayata ce"da mamaki Suka kalleta har yusura

Tace"mahaifin mu ya hanata auren mansur lokacin muna yan mata amma ta nace har taje aka d'aura musu aure tun daga wanan ranan ya sallamata

Wani sabon murna ya Kara mamaye familyn Abdul har kukan farin ciki yayi"

Aayan ya d'auki matarshi Suka tafi gida

Haka fa rayuwa ta cigaba da tafiya inda bayan wasu shekaru abubuwa da dama sun faru ciki harda rasuwar anty hafsat aneesa ta haifi shegiyar yar'ta zuwa yanzu Rahma yaranta uku yan biyu maza ne farko sai kuma mace d'aya,yusura yara uku,sai Amina yaranta biyu

Yusura da Rahma a kano suke Zama sai dai su Abdul na zuwa lokaci lokaci

Soyayar Rahma da Aayan ba a cewa komai inda yanzu suke Shirin zuwa Paris Hutu zasu barwa umma yara Amma zasu biya wajen hamza dake karatu a lodon
Kawo ko duniya ta koya me karatun ta natsu domin yanzu ya Kare a gidan Aya domin tsiyacewa yayi da shi kanshi besan sanadi ba

Su Rahma da Aayan Abdul da yusura,Amina da Amir sai dai muce Allah ya Kara dankon soyyaya they all lived happily ever after

~The end~

Alhamdullilah inda nayi kuskure Allah ya yafe min

Na sadaukar da wanan littafin wa masoyana masu kaunata

Thanks a lot sai mun had'u a littafina na gaba Mai suna *SO MAKAHO NE* na kudine

*_SO MAKAHO* *NE_*

Ni sunana Maryam a yau zan Baku labarina na

Watoh a lokacin da muke yan matanci muna tashe da rashin kunya a lokacin duk wani magana da iyayen mu ke fada a banza ne sai dai Wanda yayi tashen tsoron Allah,lokuta da dama mun fi fifita maganar samari fiye dana iyayen mu

Ku biyo maman Nur dan jin ya nawa rayuwar ta kasance wani kuskure na aikata a rayuwa kila daga mistake dina kuyi learning lesson

A naira d'ari biyu kacal just 200 naira only dan girman Allah in kin San Zaki fitar min da littafi ki rike kudinki

*SO MAKAHO NE* littafine da ya kamata Yan Mata da matar aure su karanta iyaye da yara ya kunshi abubuwa da dama

Sai mun hade

~Maman nur~
Share
[2/20, 8:37 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄👄
*BANA SONSHI*
💋💋💋💋💋💋
_By maman noorul_
_Hudah__

*👄💡NUR WRITERS ASSOCIATION💡💋*

*💡N W A💡*

*Lightning and bringing smile to your world is our perority*

*NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~

🅿1⃣0⃣0⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Yace"iam sorry I misunderstood you wallahi kishin ki ne ya jawo hakan ki yafe min Rahman soja"

Ummi ne ta shigo da sallama tace"miye Kuma ya kawo ka?ai da Bari kayi ta mutu kowa ya huta Daman ni na gaji da ganinta hakan,Kai daga dawowa ko murna baza ka Bari jama'a suyi ba ka tada hankalin jamma'a ba tare da kayi tunanin akwai jama'a a gidan nan ba"

Tashi yayi ya rungumeta yace"ummi kiyi hakuri naji kewar ki"

Abinka da d'an da uwa balle d'an da ta ciren rai baya duniya babu kunya ta kankame d'anta tace"meya faru meyasa Muka jika shiru?"

Yace"ummi bayan uche ya halbeni sai yaje mota d'auko bomb kafin ya dawo sai ga wani sojan kasar ya d'aukeni ya kaini' asibiti "

Ummi tace"but meyasa ka cire bullet proof?"

Yace"ummi anfa Gama komai sanda ya Bari na Gama cire komai ya halbeni"

Ummi tace"toh a rinka kula Allah ya Kare ku"

Yace"Amin"

Tace"ka zauna da ita bari inje in gan bakin nan umman ku ma na hanya zuwa nan"

Yace"ok Allah ya kawota"

Yusura ko komawa tayi d'aki ta kwanta domin cikin ta na murd'awa ga ciwon Mara da baya

Abdul yayiwa Amir bayanin Kuma ya amince yayi godiya

Mummy ya Kira a waya ya sanar da ita canji da aka samu albarka tasa musu tace"sai kun dawo Kuma nayi murnan dawowan soja"

A gurguje mummy tasa akayiwa Amina gyra sai kuka takeyi lefen amir dama komai inda akeyiwa budurwa haka yayi mata Bata akayi umma ta bata Kaya tasa tare da magungunan emergency ta Sha kuka take Sosai domin bata sa ran zata bar gida yanzu ba

Umma na shigowa Aayan ya zo Suka gaisa tayi murna Sosai cikin zolaya tace"Ina ita Rahma take yaudai rai ya samu abinda yake so ko ganinta ba ayi "

Murmushi yayi ya shafa kanshi ya bar wurin

Komawa yayi d'akin ummi ya d'auketa a hankali ya rike drip din a baki ya kaita part dinta

Motorci d'aukan amarya sun iso Nan fa ummi da umma Suka sa Amina gaba suna ta mata fada Sosai da nasiha kuka takeyi ta kankame su tace"ni ba inda zani a barni *BANA SONSHI* umma tayi Yar dariya tace"haka kuke cewa daga baya ku ishe mutane da rashin kunya

Itama ummi ji take kamar tayi kuka amma ta daure

Bayan an tafi da Amina nakuda ya tasowa yusura gadan-gadan ummi taje ciki ta kori Abdul ta fara bata taimakon gaggawa

Cikin ikon Allah ta haifi santalelen d'anta namiji sai dai ta Sha wuya Sosai gyra ta umma tayi tayiwa jariri wanka sai a sanan Abdul ya shigo da Aayan duk suna murna

D'aukan yaron Abdul yayi ya me addu'a da abinda ya dace sanan ya mikawa Aayan yace"ga takwaran ka little Aayan "

Da farin ciki ya amshe shi yace"really?"

Abdul yace"yes"

Ummi ta shigo tace"mashaallah bazan taba manta wanan juma'a ba"

Umma tace"ai Allah shine abin godiya"

Kiran su Abba akayi aka sanar musu Mami ko ji tayi kamar tayi tsalle ta zo ta gan yar'ta nan fa maganar haihuwa da dawowan Aayan ya zaga ko Ina

Yusura ko bacci takeyi

Komawa Aayan yayi ya kwanta a gefen Rahma shima yayi bacci

Rahma bata farka ba sai cikin dare sosai misalin karfe 2:am

A hankali ta bude idonta tana kokarin tashi sai taji yace"Ina zuwa?"

Kuka ta fashe dashi tace"soja wallahi ni banyi komai ba ko fita banyi a gidanan ba kayi hakuri karka sakeni bazan iya rayuwa babu Kai ba na tuba "

Ji tayi ya hade bakinsu yana tsosa sun dade a haka yace"ni zan baki hakuri girgiza me Kai tayi tace"bakamin komai ba soja"

Kunna bedside lamp yayi yace"Bari in kawo Miki abinci na samu labarin baki cin abinci"

Har zai fita tace"ka jirani muje tare"

Dawowa yayi ya d'agota tasa takalmi Suka fita

A dining ya ajiyeta yace"Bari in zubo abinci "

Tace"muje tare"

Murmushi yayi yace" zauna ki jirani inshaallah bazan kara barinki ba"

Tashi tayi da gudu taje ta rungume shi tace"ji Nike kamar mafalki"
Chapter 24 · 0% Book details