← Book details Bana Sonshi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 25

Sashe 8

Bana Sonshi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fitowa tayi ta tarar da Abba zaune har kasa ta duka ta gaishe shi

Be damu da ya amsa gaisuwarta ba sai cewama yayi saura in kinje ki nuna musu baki da tarbiya sha-shasha "

Kuka ta fashe dashi tace"Abba ka bani dama in Yi maka bayani wallahi ban sanshi ba kuma *BANA SONSHI* bigeta Mata baki yayi yace"shasha-shayi mun shiru munafuka so kike ki mayar dani karamin mutum maza jeki ki gaishesu kan ranki ya b'ace Mara mutunci"

Tashi tayi ta fara tafiya tana kuka

Ko da taje falo Abdul ne kadai Dan tuni su general Suka tafi Suka barshi"

Da sallamar ta shiga falon tana kuka

Lumshe ido Abdul yayi ya budesu

Duba falon tayi sai ta gan shi kadai ne

Wani haushin shi take ji a fusace tace"malam me na tare maka a rayuwa?me nayi maka ka had'ani da iyayena?meyasa kamin sharri kana kokarin rabani da iyayena"

Ba tare da ya bata amsa ba yace"gobe bayan an d'aura aure za a kaiki barrack jibi zamu tafi kano dan haka ki had'a muhimman abinda kike so domin kina barin garin Minna baki da ranan dawowa sai in kin haihu muzo nunawa Abba yaro,and next thing ki bani size din takalmin ki da na rigar ki domin on Saturday zamuyi reception ranan lahadi Kuma mazaje sun had'a Mana party a barrac. .."

Katseshi tayi tace"dakata d'an rainin wayau ya Ina tambayar ka kana min maganar rainin hankali meyasa ka rabani da me Sona?"Kara canza topic yayi da cewa"yusra lallin ki yayi kyau duk ni nine da wanan kwaliyar?"

Kara kunnata yayi ta mike tare da fashewa da kuka tace"Allah ya isa tsakanina da kai mugu kawai azzalumi"

Murmushi gefen baki yayi daya Kara me kyau yace"ki bani size din sauri nike akwai shirye-shirye"

Tace"ban badawa munafuki allah"

Yace"toh bari in Kira Abba"

Tace"takalmin 39ne gown din Kuma 20"

Yace"good girl

Tashi yayi ya zauna kusa da ita yace"baby me kike shirya min a daren mu na farko?"

Kallonshi tayi ta janye hanunta tace"sakeni munafuki kawai"

Murmushi yayi yace"ko dai abin sirri ne sai a turaka?" Ya Kare magana da kashe mata ido

Wani haushi ne ya kamata sai ta fashe da kuka tana dire-dire

Natsuwa yayi Yana kallon shagwab'ata Kamar Yar baby

Yace"

Anty shamsiya da sis khady team soja ni Kuma team lecturer Nike😜😜😜😜in na gan dama in bawa soja in nagan dama lecturer

Maman Nur
Share
[2/20, 8:26 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄👄
*BANA SONSHI*
💋💋💋💋💋💋
_By maman noorul_
_Hudah__

Dedicated to my fans

*👄💡NUR WRITERS ASSOCIATION💡💋*

💡 *N W A💡*

Lightning and bringing smile to your world is our perority

*NUR WRITERS* ~it a beautiful~ ~world~

🅿3⃣1⃣-3⃣2⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Yace"yus ai ba sai kin fara yau ba ki hakura gobene fa sai kiyi shagwab'a a jikina hankalin ki kwance"

Hararanshi tayi tare da mikewa tace"mugu kawai"

Hanunta ya kama ta fisge tace"karka Kara tab'ani"

Yace"kina nufin in Bari sai gobe kenan muyi Mai gaba d'aya?"

Cikin jin haushi ganin in ta b'ulo ta nan saiya fitota wani wuri"

Tace"nifa bana son iskanci fa ni ba a koya min iskanci a gidanmu ba'

Murmushi rainin hankali yayi yace"da ma koyawa mutum akeyi?ai ji mutum yake a jikin shi Amma in ke baki jin feelings kiyi hakuri zan koya Miki"

Tsaki tayi,sai ya buge Mata baki yace"karki Kara min tsaki bani son rainin "

Kara jan wani dogon tsaki tayi tana wani irin janshi tana turo baki tace"in bakaso sai ka fasa auren "

Murmushi yayi yace"baby sake Jan tsakin ta Miki kyau wallahi ni gaskiya a ta jamin kullum "

Cikin haushi ta fashe da kuka murmushi yayi a ranshi yace"duk abinda bana sonshi zanyi ta nuna Miki Ina so Wanda nike so Kuma in nuna Miki bana so"

Har zata fita a falo sai taji yace"ki shirya da yamma zamuje muyi hoto zanzo in d'auke ki zan zo da kayan da Zaki sa kuma babban hijab Zaki sa domin banason kowa ya gan lallin da akamin na amarci"

Tsaki tayi ba tare da ta amsa ba

Yace"yus in kikayi tsakin nan sai in ji kamar in rungume ki domin jin sonki Nike har zuciyata"

Har zatayi tsaki sai ta tuna faranta me take in tayi tsaki

Yace"ki shirya sai na zo"

Tace"babu inda zani"

Yace"toh zan fad'awa Abba"

Sai tace"karfe nawa"

Yace"karfe takwais Kuma bana son kiyi kwalliya domin banason kowa ya kalle mini ke,nafi son ki bini da kumburaren idonki in so samu ne ki wuni kina kuka domin idon su Kara tashi"

Bata kulashi ba ta shige ciki ya bita da kallo yana murmushi

Tana wucewa ya bar gidan

Bayan su general sun bar gidan direct gidan su Rahma sukayi inda suka aika yaro ayi musu sallama

Kawo da ya kwanta a taburma Yana jira ga yunwa domin umma share shi tayi

Yana ganin yaro ya fara kwalawa umma kira yace"sun iso maman Yan biyu"

Kafin ta fito ta bashi amsa har ya fita waje yayi musu izo da su shigo kafin ya dawo har umma ta shimfide taburma

Zama sukayi itadai tayi mamakin ganin malam haruna

Har kasa Aayan ya sunguna ya gaida umma ya kasa d'agowa ya kalleta itako sai murmushi take domin tana son mutum me kunya hakan yasa itama kunya ya kamata

Malam haruna yace"Ina fatan malam Musa yayi Miki bayanin komai?"

Kafin ta bada amsa kawo yace"ai tun safe Nike Nan na Mata bayani Kuma ta amince"

Gyran muryar malam yayi yace"nasan a ka'ida be kamata mu sameki ba Amma mun amsa gayyatar ki ne bisa bukatar ki na son ki gan angon toh sai mu ka duba Kuma muka gano kina da hakki akan yar'ki kuma Zaki so a ce kin San inda za a Kai yarki toh da farko dai nasan kin sanni Amma bari in Kara gabatar da kaina sunana malam haruna nine Wanda zai tsayawa Abubakar ki kwantar da hankalin ki yar'ki hanun ta gari zata shiga"

Umma duk sai taji nauyin su ga kunya ya lullubeta ga wani kallo da dattijo general ke mata Kuma ta yaba da tarbiyyar Aayan

Kawai sai tace"babu komai kawunta zaiyi komai Allah ya Sanya alkhairi "tana gama magana ta shige d'aki ta barsu

Duk sukayi murmushi kawo ya kallesu yace"yanzu za a d'aura?"

Hararanshi Aayan yayi kasa-kasa sai yace"eh na tuna sai gobe"

General yace"sai goben kenan mu had'u a massalacina"

Kawo yace"angama"

Tashi sukayi Aayan shima ya tashi

Sai general yace"yi zaman ka ka gana da amaryar taka baza ku rasa abin Fadi ba tunda abin ya zo ba shiri"

Zama Aayan yayi cikin jin kunya yayiwa su malam godiya

Bayan kawu ya dawo daga rakiya Aayan ya kalleshi yace"Ka maida musu kayansu da kudin da Suka kashe ko kuwa?"

Kawo ya fara in Ina Aayan yace"amsa nike jira"

Kawo yace"ai kasan asara ce a maidamusu ai su Suka ce basu son auren bamu ba dan haka komai ya Zama namu"

Aayan ya kalleshi daga sama zuwa kasa silipas ne kafanshi ga uban kaushi da pasau ga shaddan Nan yayi bakin kirin

Tsaki yayi yace"shiyasa baka cigaba duk cutar mutane da kakeyi baka arziki,yanzu dai ka maida musu kayansu domin ni ba matsiyaci bane kuma karka Bari in samu labarin baka maida musu ba"

Yace"toh yallabai Amma maganar filin tana nan ko?"

Wani kallon Aayan yayi me sai ya natsu yace"Bari in kira maka ita Ramatu bacci take zazzabi na damun ta ne"

D'akin ya shiga Kamar an koroshi umma ta harareshi

Ganin Rahma zaune ta jigina da bango tana hawaye

Hamdala yayi yace"ummana ki saka hijabi ki fito ana jiran ki"domin Rahman sunan mahaifiyarsu gareta

Umma tace"tashi kije kinji Rahmatu na"

Itadai Bata fahimci meke faruwa ba mikewa tayi jiri na d'ibarta umma ta sa Mata hijabi

Ganin tana tafiya a hankali yasa kawu cewa"ummana ko in d'auke ki ne"har ya karasa

Umma tace"ah'ah ya haka?"

Yace"wai da in taimaka mata"

Itadai umma harya isheta Allah Allah take ya bar Mata gida

Rahma na ganin uku-uku ta isa gaban Aayan ta zauna

Kawo ya zo ya zauna kusa da ita ya sata a tsakiya

Wani kallo Aayan yayi me sai kawai yace"da wai kasawa zanyi in tsare kar tace Bata sonka kasan ummana akwai kafiya"

Umma data fito d'aukar wani kwanu kawai ta gan kawu zauna

Tace" wai ya haka?"

Yace"kamar ya?"

Tace"toh ai na gan ka wani samu wuri ka zauna da sirikin ka ko da Kai za ayi zancen?"

Yace"yanzu zan tashi"

Rahma ko tunda kawo ya anbaci aure ta fara harhad'a kalaman su har da umma tace"siriki"

A fili tace"wai meke faruwa ne?"

Kawo yace"ai shine mijin da Zaki aura ki rabu da wanan d'an isakan"

Shidai Aayan beyi magana ba amma a ranshi cewa yake ita Bata gaisuwa ne watoh dan raini so take in gaisheta"

Maganar Rahma ne ya dawo dashi duniyar tunanin shi da yaji tace"aure kuma?me Kuma ya samu my Aamir kuyi hakuri wallahi ni nasan gobe my Aamir zaizo nasan yasan halina bazai tab'a yarda da wanan videon ba"

Kawo yace"wanan yariyar da bakin ciki take"shiko Aayan ranshi ne ya mugun b'aci a ranshi yace"kamar ni a ce dan rainin hankali tana maganar wani a gabana"

Umma tace"watoh Rahma ban Isa ba?bana hanaki kiran sunan shi ba?"

Ai ji sukayi ta gangara jikin Aayan summamiya

Umma tace"subhannallah"

Kawo yayi maza zai d'agota sai ya ji hanun maza ya

Please yau ku min afuwa wallahi aikine yamin yawa kwanan nan sai kuyi hakuri da inda posting zaiyi ta zuwa muku Amma zan kokarta a min uzuri please

Maman Nur

Share
[2/20, 8:26 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄👄
*BANA SONSHI*
💋💋💋💋💋💋
_By maman noorul_
_Hudah__

Dedicated to ummu Yasmeen novel group

*👄💡NUR WRITERS ASSOCIATION💡💋*

💡 *N W A💡*

*Lightning and bringing smile to your world is our perority*

*NUR ~WRITERS* ~it a beautiful~ world~

🅿3⃣3⃣-3⃣4⃣
Bismillahir Rahmanir Rahim

Rike me hanun yayi gam da yasa kawo sake tusa domin tusar sub'uce me yayi

Umma cikin b'acin rai domin yau kawo ya Gama ba da ita

Tace"wallahi anji kunya a ce a gaban siriki ake Banka tusa"

Yace"da kin ji rabin abinda na ji ke har kashi zakiyi "hanun maza fa naji

Umma zatayi magana sai Aayan yace"umma dan Allah in akwai socks kusa a bani"
Chapter 8 · 0% Book details