← Book details Bana Sonshi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 25

Sashe 1

Bana Sonshi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[2/20, 8:20 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄👄
*BANA SONSHI*
💋💋💋💋💋💋
_By maman noorul_
_Hudah__

Dedicated to FATIMA MUSA (mummy nijar)nagode Allah ya Kara budi ya rufa Mana asiri duniya da lahira

🅿3⃣&4⃣
Bismillahir Rahmanir Rahim

Cikin mamaki tace"but jiya fa an Aiko min da flower Kuma a jikin flower an rubuta to my heartbeat Rahma Kuma nasan babu Wanda zaiyi min haka sai Kai bana son Wasa"

Hade rai amir yayi ya juya Mata baya yace"watoh har kina da wani da zai aika Miki flowers baby yaushe kika fara kula wasu"

Itadai mamaki take because this is not the first time da ake yi Mata aike Wanda a tunaninta Amir ne but ji take ta tambayeshi ne ko tayi shiru gudun kar ranshi ya b'ace"

Zuwa tayi gaban shi tace"baby wallahi babu Wanda nike kulawa kaima kasani ka yarda dani baby please "

Kallonta yayi da jajjayen idonshi ya Kama hanunta ya Kai saitin kirjinshi dake mugun bugawa yace"baby ki ji fa wallahi in kika kula wani mutuwa zanyi baby Ina kaunar ki dan Allah ki rufamin asiri karki gujeni"

Rungumeshi tayi tare da fashewa da kuka tace"wallahi my amir hakan bazai faru ba Allah ya jarrabe ni da mugun sonka please karka sa damuwa a ranka bana jin zan iya rayuwa babu Kai please karka zargeni"

Kama fuskarta yayi yana mata kallon cikin ido cikin karyewar zuciya har hawaye yakeyi yace"baby bansan meyasa wallahi hankalina ba zai kwanta ba sai na ganki a gidana"

Murmushi tayi ta Haye saman desk tace"ka ji ka da wata magana aini in ba mutuwa ba auren Kamar an gama ne saura fa sati d'aya"

Zama yayi yace"thanks aina sani Kuma in so samu ne mu mutu tare"haka fa Suka cigaba da Hira cikin nishadi

B'angaren Aayan kuwa bayan ya gama waya da jabir ya fara zirga-zirga ya kasa Zama ya kasa tsaye

Sake dialling number jibrin yayi yace"kana Ina?"

Jibrin yace"yanzu ina makaranta ne"

Yace"Ina ita Rahama?"

Ya tsosa Kai yana in Ina,tsawar da Aayan ya daka me ne yasa shi cewa"sir kayi hakuri yanzu tana office din malamin nasu ne"

Yace"ok ai nace kayi ta video movement dinta ko?ka turo min yanzu"

Jibrin yace"oga kayi hakuri na tura kawarta taje ta manna cameran a Jakarta yanzu ta kawomin Ina dubawa ne"

Yace"turomin yanzu"Yana Gama magana ya yanke wayar

Jibrin yace"nidai na gan ta kaina yanzu in ya gan sun rungume juna sai ya fasa kwakwalwata da al'shashi,but nari in tura me kawai in yi sha'hada"turame yayi

Bude laptop yayi ya bude video Yana kallo ai ji nayi yayi wurgi da laptop Yana watsi da kayar office din sai cewa yake no it can't happen not my Rahmat bazan yafe maka for hugging my Rahmat"

Kuji karfin hali

Waya ya jawo ya Kara kiran number jibrin

Yana jin ya d'aga yace"stop that weeding at all cost I repeat at all cost"

Jibrin yace"oga yanzu ya zanyi ?me zanyi dan in stopping auren?babu lokaci fa"

A fusace yace"I don't care what you do but nidai Ina son a b'ata auren"

Jibrin yace"an gama oga zan San abinyi badai ka ce ko miye ba?"

Ba tare da tunanin komai ba Aayan yace"eh komiye"

Yana gama waya da jibrin ya zauna Yana huci sai cewa yake my Rahmat hugging another man,hmm wallahi ke tawace"a haka Abdul ya shigo ya sameshi

Karasawa yayi yace"

Maman noor
Pls share
[2/20, 8:20 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄👄
*BANA SONSHI*
💋💋💋💋💋💋
_By maman noorul_
_Huda_

Wanan labarin kagagen labari ne ban shi dan cin zarafin kowa ba.

Warning:ban yarda wani ko wata ta canja min labari ko ta wata siga ba

Banyi alkawarin typing kullum ba ranan da kuka jini shiru a min uzuri

Please ku fara daga farko Basai nayi nisa ayi ta Bina pc ba

🅿1⃣&2⃣

Niger state college of education Minna (c o e)school of vocational department of Business education

Zaune suke a babban aji suna Hira su biyar ne kowa na fadin al'barkacin bakin shi Amma banda rahma dake waya sai kashe muryar take ji nayi tace"haba sweery na fa ji kewar ka"

Kallonta sa'ida tayi tace"gaskiya Rahma kina da aiki yanzu fa sir Aamir ya bar ajin nan shine Zaki wani ce kina jin kewarshi Ina fa lura dake fa Yana koyarwa amma sai aikawa junan ku sakwani kuke da ido"

Yusura tace"ai in wa ya'nan tsunsayen tsoyayya ne sai dai ki kyalesu ni abin nasu ma ya fara b'atamin rai haba ai sai ku jira sati d'aya ya rage ayi auren"

Tashi Rahma tayi tana cigaba da waya tana murmushi tace"sweery ganinan zuwa office dinka Yan sa ido sunyi yawa "

Tabe baki yusra tayi,sadiya tace"kwaji dashi dai"

Itadai zainab kallonsu yusura tayi tace"yanzu Kuna nufin nan da sati d'aya za ayi auren Rahma da sir Aamir?"

Sadiya tace"ikon Allah kina ina muke ta planing bikin"

Zainab tace"gaskiya toh Baku kyauta min ba a ce sai yanzu na sani ai dama na dade da sanin baku d'aukeni matsayin kawar ku ba"

Murmushi yusura tayi tace"toh kema ai kinsan ba laifin mu bane tunda ai kin gan be dade da muka had'u ba kuma ke ba department din nan kike ba"

Zainab tace"toh ba komai Allah ya Sanya alkhari"

_______________
Tana shiga office dinshi ta gan Yan Mata tsaye a gaban shi da alamu laifi sukayi

Yatmusa fuska tayi tana wani irin hararanshi ta hade rai"

Murmushi Aamir yayi ya kalli Yan matan yace"you can go"fita sukayi

Kallon Rahma yayi sai yayi murmushi yace"baby Yi hakuri please ba Hira Nike dasu ba laifi sukayi

Ga mamakin na sai na gan ta fashe da kuka

Tasowa yayi yace"subhannallah baby kiyi hakuri"

Cikin kuka tace"ni bana son kana kula wasu Mata my amir "

Murmushi yayi da ya fito da kyaunshi yace"but my Rahma is not possible ya kamata ki gane ni lecturer ne Kuma Ina koyar da Mata da maza"

Zatayi magana kawai sai ya rungumota yace"it's ok bana son jin komai baby ki yarda Dani"

Murmushi tayi ta janye jikinta ta Haye saman desk din office dinshi ta fara bashi labarin inda sukayi dasu yusura"

Murmushi yayi yace"ai zasuyi ne su gaji amma ai hanta da jini ba a rabasu"

Murmushi tayi ta kalleshi tace"my amir in munyi aure zanyi ta baka kulawa zan nuna maka soyyaya sosai"

Shima murmushi yayi yace"Allah ko baby"

Tace"eh"

Yace"wallahi ji Nike Kamar in jawo kwanakin"

Tace"ai Kamar gobe ne sati d'aya ne kawai"

Yace"Allah ya nuna Mana"

Haka fa Suka cigaba da hiran su inda suke tsara inda rayuwar su zata kasance in sunyi aure abun sha'awa

****************

Zaune yake a hadadden office dinshi Yana kallon hotuna a laptop dinshi yana jin nishadi

Murmushi yayi yace"my Rahma saura wata biyu ki gama makaranta a lokacin zan bayyana kaina Ina sonki Rahma, nasan da kin ganni Zaki Soni"

Wayar shi ne tayi Kara ya duba murmushi yayi kafin ya d'aga yace"I know magana ne akan masoyiyata" d'agawa yayi yace"inajin ka"

Jibrin dake zufa ya had'iye wani abu me d'aci kafin yace"oga akwai matsala"

Cikin tashin hankali Aayan yace"don't tell me wani abu ya sameta"

Jibrin yace"no sir wallahi wai nan da sati d'aya za a Mata aure da wani malamin su"

Ai wani tsawa yayi yace"kana hauka ne? ya haka ta faru?for 3years nasa kayi ta binta dare da rana but dan iskanci suddenly zaka cemin zatayi aure, beta know what to do,THAT WEEDING SHOULD NOT TAKE PLACE AT ALL COST"

Jibrin yace"toh ya zanyi ba lokaci wallahi sir Ina iyakar kokarina bansan ya haka ta faru ba

Aayan yace"I don't care how you do it komai zai faru dani za ayi auren nan da sati d'aya kasan abinda zakayi I don't care and start preparing for my wedding yanzu zan Kira gida su fara shiri"Yana gama magana ya yanke wayar

Jibrin yace"nidai Allah ya had'ani da jaraba kana son budurwa girman Kai ya hana ka fad'a Mata yanzu ka zo kana hura min wuta, yanzu ya zanyi?'

B'angaren su Rahma ko sosai suke soyyaya da amir dinta

Tace"sweery nagode da flower jiya da ka Aiko min dashi

Da mamaki ya kalleta yace"wani flower?"

Tace"na jiya daka Aiko"

Yace"ni ban aiko da flower ba"

Cikin mamaki tace"

Fans sai mun had'u wanan talla ce kawai comment dinku shi zai bani karfin Yi muku typing in Kuna ba comment in cigaba da hutu🥱😴

*Coming soon*

Maman Nur
Luv all

Please share
[2/20, 8:21 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄👄
*BANA SONSHI*
💋💋💋💋💋💋
_By maman noorul_
_Hudah__

Dedicated to *Hajiya AISHA D'ANGUGUWA*

🅿5⃣&6⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Yace"mazaje ya haka?na gan ranka a b'ace ne'

D'angowa yayi yace"wallahi sai na b'atawa Rahma rai can you imagin tana hugging maza?"

Murmushi Abdul yayi yace'ni kana bani mamaki yariyar nan fa Bata San kanayi ba amma sai kayi ta d'aukan abu da zafi kai da ya kamata ka nimi hanyar lallab'ata"

Kallonshi yayi yace"wani irin in lallab'ata ita yariya ce salon ta raina ni,duk ba wanan ba yau ina cikin tashin hanki ko kasan nan da sati za a Mata aure da wani d'an iska "

Abdul yace"yanzu ya zakayi?"

Yace"wallahi sai an b'ata auren nan,domin sai na aure ta da karfin tsiya"

Abdul yace"Aayan kayi hauka ne ka kyaleta ka Nima wata kila ba matar ka bace kasan ko babu al'akhari a auren taku?"

Yace"wallahi bazan iya ba Abdul kaima ka sani bazan iya ba Ina son Rahma bazan iya rabuwa da ita ba"

Cikin tausayawa Abdul yace"kaima fa kayi shirme ai kamata tunda ka ganta ka fad'a Mata kana sonta Amma ka tsaya girman Kai yanzu gashi ka tsaya kallon ruwa kwado ya maka kafa you fuck up man"

Aayan yace"ai ita ya kamata ta nuna tana Sona sai ni zan nuna Ina sonta bazan iya ba kana so ta Raina ni ne?"

Abdul ya me wani kallon raini wayau yace"gaskiya ne ita ya kamata Aayan in ban dakai mahaukacine yaushe mace ta fara cewa tana son namiji ai namiji ne ya kamata yayi ta lallab'ata in ta gan dama ta amince"

Yace"nidai nasan da ta ganni zata soni bari ka gani"

Abdul yace"Ina ganin kanka ba d'aya bane"

Yace"nidai in zaka bani shawara ka bani ba wai kayi ta fad'a min abinda zai b'ata min rai ba"
Chapter 1 · 0% Book details