← Book details Bana Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 25

Sashe 7

Bana Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Katseta yayi da cewa"ah'ah babu kyau kina aibata Yar ki albarka Zaki sa mata Kuma ni ban yarda Rahma ta aikata abubuwan da ake zarginta ba sharri ne irin na yan adam"

Umma ta fashe da kuka tace"yanzu bansan Ina zan saka kaina ba in na fita kallona akeyi a gari nasan yanzu zaiyi wuya Rahma ta samu mijin aure"

Kawu ya gyra hulan shi yace"maman Yan biyu Ina raye kike fadin haka ai komai lalacewa na banzan bari Yar Yaya na ta wulakanta ba karki damu na samo Mana mafita domin inshaallah Rahma bazata kunyata a idon duniya ba"

Umma tace"yanzu ma dan gulma jama'a sai zuwa suke da sunan sun zo aikin biki wata ma har cemin take zata rufawa Rahma asiri a had'ata da d'an ta mashayi"

Kawo yace"duk ki bar wanan maganar aini nace Miki bazan Bari ta kunyata ba ko?kuma in Suka zo ki fito musu da aikin da za ayi domin inshaallah gobe za a d'aurawa Rahma aure da mijin da yafi wanan d'an iska kamar inda za ayi me aure gobe itama za ayi Mata "

Umma dai mamaki ya bata domin be tab'a nuna damuwa a al'umaransu ba hakan yasa ta fara zarginshi

Kallon tuhuma tayi me kafin tace"shi waye wanan da za a musu aure da gaggawa haka?"

Kawo yace,"dan abokina ne yana tsaye a lokacin da alhaji ya zo fadamin sun fasa auren Rahma shine ranshi ya matukar b'acewa yace"toh sai ya nuna musu ba kwantai tayi ba kuma babu abinda ya Kara b'atame rai Kamar inda Amir ke ta fadin mugayen kalamai akan Rahma harda tara Mana jama'a toh shine yace shi zai aureta a goben yanzu ma mahaifin ya bar gidan mu"

Umma ta d'anyi shiru tana tunani kafin tace"nifa bana son in kai ya'ta inda za a wulakanta ta ko a Mata gori bana son abin ya Zama kamar taimakon mu yayi dan haka a hakura kawai ko mutuwa zatayi babu aure na gommace ta tsaya gabana"

Kawu a ranshi yace"ka ji Yar bakin ciki dole in Yi da gaske"

Fashewa yayi da kuka yace"yanzu kina nufin dani da ya'yan Yan uwana ban Isa ba kenan dasu?yanzu a ce kamar ni nayi Rahma Miji Amma ki ki amincewa ai inda Kara ai kyamin Kara ko?"

Umma tace"toh a gaskiya zan amince amma sai an turomin yaron nayi me tambayoyi"

Kawo yace"yanzu kuwa"

Waya ya ciro da card din Aayan da ya gani cikin ledar kudi da Suka bashi

Kiran wayar yayi sanda yayi missed call biyar ya d'aga

Yace"kawo ne so Nike ka zo gidansu Rahma yanzu nan mahaifiyarta na son ganin ka"

Aayan dake gaban oganshi ganeral da zaiyi me walihi yace"ok ku bani minti 30 dan Allah "

Kawo yace"toh kayi a hakali duk lokacin da ka Gama ka zo zan jira ka"

Bayan ya yanke wayar yace"bani kujera zaman jira ta kamani "

Umma tace"oh Dan samun wuri mu zamu jirashi?"

Yace"kedai Yi me uzuri a rayuwa ana son mutum me yin uzuri"

Shigewa tayi ta barshi waje yace"ki Kira min Rahma"

Umma tace" Rahma bata jin dadi ta kwanta

Umma na shiga ta zauna kusa da Rahma tana shafa kitson kanta ba bacci takeyi ba jikinta ne ba dadi domin ko tashi Bata jin zata iya tunanin da kewar amir ya lullubeta gashi ta Kira wayar shi ya ki d'auka da ta Kira da wayar umma sai yace shi besan wata Rahma ba har yanzu she can't believe amir ya Mata haka,ita tasan ba haka kawai bane ji take dama mutuwa zata d'auketa ta huta

Umma cikin tausayin ta domin Rahma ta bata tausayi hakan yasa ta manta fushinta cikin tausayawa tace"Rahma ki manta duk wani abinda da ya faru a baya ki manta da amir Allah zai musaya Miki da Wanda ya fishi "

Cikin kuka tace"umma ki min rai wallahi Ina matukar son amir umma bazan iya rayuwa babu shi ba,umma mutuwa zanyi,umma nasan yana sona an Shiga tsakanin mu ne"

A fusace umma tace"Yi min shiru inda yana sonki da be bari mahaifiyarshi ta biyo mu har gida ta ci Mana mutunci ba, inda yana sonki da ya aureki ko a wani irin hali kike,Rahma inda yana sonki da ya rufa Miki asiri koda bazai aureki ba da be tona Miki asiri ba,Rahma inda yana sonki da bai Bazai yarda a d'aura me aure gobe ba da wata dama dai Yana niman dalili ne"

Rahma ta kalli umma tace'kina nufin gobe zai aura wata"

Kafin umma ta bata amsa kawo ya shigo yace"kwarai kuwa ai yaron nan beda mutunci shi ya addasa wanan fitina baya sonki maimakon ya fito fili ya fad'a sai ya fake dake Yar iskace Ina fad'a Miki Rahmatu duka na ya rage beyi ba akan na bashi hakuri ya Bari ayi aure"karya ya sharara musu domin ko kashe kawo za ayi bezai Fadi kamanin Amir ba so d'aya ya taba ganin shi so d'aya ma da daddare

Itadai Rahma shiru tayi amma tasan ba haka kawai amir zai ki taba sai dai in shiga tsakaninsu akayi koma waye bazata yafe me ba

Lumshe ido tayi tana jin radadi a zuciyarta

Umma tace"kin ji ai sai kiyiwa kanki karantun ta natsu kema ki cireshi a zuciyar ki"

Kawo ya zauna kusa da ita Yana ja Mata kafa domin ji yake Kamar ya maidata ciki

Umma ta mike tace"sai muje waje ka jira shi ni Ina da aikin yi"

Yace"toh toh ai ko Nan zuwa Isha ne zan jira kinsa zan iyawa Rahma komai"

Tace"na ga alama

B'angaren Aamir ko

Maman nur
[2/20, 8:25 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄👄
*BANA SONSHI*
💋💋💋💋💋💋
_By maman noorul_
_Hudah__

*👄💡NUR WRITERS ASSOCIATION💡💋*

💡 *N W A* 💡

*Lightning and bringing smile to your world is our perority*

*NUR WRITERS* ~it a beautiful~ ~world~

Dedicated to my fans

🅿2⃣9⃣-3⃣0⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

B'angaren Aamir ko tunda ya shiga d'akin be fito ba domin wani mugun ciwon Kai ke damunshi ya rasa me ke me dadi ji yake kamar ya rasa wani abu kwata-kwata ya mance Rahma

Jin shiru yasa mummy binshi ta tarar dashi zaune

Tace"Aamir ya Kuma Zama a d'aki?"

Yace"wallahi mummy kaina ke mugun ciwo yanzu ma a d'aki nayi sallah

Mummy tace"Sannu "

Yace"mummy ji nikeyi a jikina Kamar na rasa wani babban abu mummy akwai Wanda ya rasu ne?"

Tace"ah'ah kayi wanka ka Sha magani ka fito yau dinner"

Be amsa ba ya kwanta abinshi

Aneesa ne ta shigo d'akin bayan fitar mummy

Ganin shi tayi zaune a falonshi cikin jallabiya ya zauna ya lumshe ido

Murmushi tayi ta karasa inda yake ta rufe me ido

Cire Mata hanun yayi yace"waye"

Murmushi tayi ta dawo gaban shi tace"nice amaryar ka"

Kallonta yayi sai Kuma ya basar ya d'auki waya ya fara latsawa

Fisge wayar tayi tana dariya kallonta yayi yace"bani wayana"

Sai tace"haba amir a ce Ina amaryar ka kayi ta basar dani haba

Kallonta yayi yace"bani wayata ni ban masan lokacin dana amince zan aure ki ba"

Murmushi tayi ta kamo fuskarshi tana kokarin hade bakin su ya wani mugun tureta ta fadi tsaki yayi ya tashi ya shige bedroom ya barta a kasa

Su Aayan ko daga barrack direct gidan su yusura suka je da ogan nasu

A falon Abba suka zauna inda suka samu tarba Mai kyau

Nan fa ogansu da abokansa biyu suka fara me bayani da bashi hakuri inda abin ya zo cikin gaggawa

General ya fad'a me dalilin da yasa auren ya zo a haka saboda bayan bikin zasu je peace keeping ne shiyasa"

Malam haruna yace"karka damu yarka a hanun na gari zata fad'a domin munyiwa abdullahi kyakyawar shaida Kuma Nima kasan ni bazan maka karya ba"

Abba dai yaji nauyin malam haruna domin mutumin kirki ne Kuma babba malami kowa yasanshi a garin Niger bazai iya Musa me ba'

Cikin jin nauyi yace"babu komai Allah ya Sanya alkhairi"

Malam yace"Amin Dan Allah Ina niman alfarma ka bari a d'aura massalaci na"

Abba yace"babu komai ai kaima Yar ka ce"

A nan take akayi abinda ya kamata ayi kafin aure har sadaki sun biya maganar lafe Kuma general yace"ayi musu afuwan sai bayan auren a kano zasu zauna"

Abba yace"ba komai ai dama lafe maganar matane "

General yace"matar shi tayi ordering"

A haka suka sallami juna Abdul Yana so yace"a Kira me yusura amma Yana jin kunya ashe Abba ya lura akwai magana a bakin shi sai yace"Bari in turota ta gaida ku"

General yace"toh"

Yana shiga gida b'angaren Mami ya ganta zaune tana kallo"

Zama yayi yace"hajara akwai magana"

Tattara hankalinta tayi tace"Ina ji baban Walid"

Yace"hajara aure fa ya tabbata domin gobe za a d'aura auren yusura "

Tace"dama da gaske kakeyi jiya na d'au andai fad'a ne Dan a bata tsoro ta natsu"

Yace"toh yanzu maganar da Nike Miki suna falona kudin nan ma sadakinta ne sun taho da Wanda nikeji kunyar shi babu inda zanyi kwata-kwata yaron nan be bani breathing space ba daga magana jiya ashe ya d'au da gaske nike nifa harga Allah jiya na dai fad'a ne sai gashi ya d'aureni yanzu maganar da nike Miki general sojoji na falona ga malam haruna da alhaji mansur wai duk waliyar shi ne,dama ai kowa yasan malam haruna da general aminan juna ne"

Mami ta zaro ido tace"Amma dai ba mal haruna Mai wa'azi a tv ba"

Abba yace"shifa"

Mami tace"toh gaskiya an d'aure mu ko Allah ma yasa ba a amshi ko sisin Umar ba Amma me zai hana mu roki alfarma su bamu lokaci?muma mu shirya"

Abba yace"hmmn hajara kenan ai duk nayi iya kokarina amma Suka ce Kar in damu basa bukatar ko sinke Kuma yaron zai tafi peace keeping ne a wata kasar ba a asa ran zai dawo da wuri kin San sojane"

Mami tace"toh Allah ya Sanya alkhari amma naso a bamu lokaci"

Yace"yanzu ba wanan ba kirata taje ta gaishesu"

Tashi mami tayi taje d'akin yusura ta ganta kwance ido a kumbure

Tace"ki saka hijabi kije ki gaida iyayen mijin da Zaki aura minti uku na baki"tana gama magana ta bar d'akin

Tashi yusura tayi jiki ba kwari ta d'auki hijabi babba tasa sai kuka takeyi
Chapter 7 · 0% Book details