← Book details Bana Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 25

Sashe 4

Bana Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace"Allah sarki baby"kallon jibrin yayi yace"babu shakka Rahma ne kwance da wani Amma ni ko karuwa ce Rahma ni Ina sonta a haka domin bazan iya rabuwa da ita ba kuma ni babu abinda za a nuna min da zai sa in rabu da farin cikina so ka fita ka bani wuri "

Cikin sanyi jiki jibrin ya bar office din shiko Amir ya jawo waya ya Kira Rahmat Suka Sha hiransu Kamar kullum ko kad'an be nuna mata komai ba"

Jibrin ko mota ya shiga yana tunani me zaiyi sai wayar shi tayi Kara Aayan ne

Tsaki yayi yace"duk shi ya sani a wanan matsala"

Yana d'agawa Aayan yace"ina Minna ka sameni a guest house Dina zuwa yamma"

Jibrin yace"ok"

Yana yankewa yace"in Kai baka yarda ba iyayen ka nasan in sun gan videon nan baza su yarda ka aureta ba'

Sai karfe shida ya tafi ganin Aayan zaune yayi zamar takama

Jibrin na tsaye kallonshi yayi yace"akwai progress?"

Jibrin yace"an dai kusa oga"

Aayan yace"ok"waya ya jawo ya Kira Wanda yasa ayi me bincike cikin minti talatin ya iso"

Abdul ya kalli farouq yace"Ina ji"

Zama farouq yayi ya bude tab dinshi yace"thou ban samu wani interesting abu akanta ba amma Bari in baku kad'an daga cikin tarihin ta"

Wacece *_Rahmat_*

Rahmat Kabir shine cikkeken sunanta ya'ce ga marigayi malam kabir Wanda ya kasance classroom teacher ne da mahaifiyarta Aisha ba wasu masu hali bane sai dai kuma suna da wadatar zuci abin wani baya tsole musu ido

A Niger aka haifesu nan tayi firamari da secondary dinta a garin Minna sai dai fa su yan gari kuta ne kasancewarta gbagyi gaba da baya

Su hud'u iyayenta suka Haifa ita ce babba sai kanneta uku duk maza Wanda yanzu me bi Mata yana federal technical college Minna but boading sunanshi hamza sai kuma kanana Yan biyu ne Hassan da husaini yanzu duk suna jss 3

A lokacin da Rahmat ta gama secondary school ne Allah yayiwa mahaifinta rasuwa a lokacin sun Shiga wani hali sosai domin Basu da wani mai maitaimako domin kwata-kwata kanin mahaifin nasu baya taimakonsu
Malam Musa shine kanin mahaifinsu uwa d'aya uba d'aya sai dai halayen su ya bambanta domin shi Allah yayi shi da mugun son abin duniya domin in ya gan kudi jikin shi har rawa yakeyi zai iya yin komai saboda kudi bashi da taimako balle ya taimakawa ya'yan marigayi d'an uwanshi

Hakan yasa mahaifiyarsu sayar da fili da suke dashi domin taimakawa ya'yan ta

Ana cikin hakane Allah ya hada Rahma da wani lecturer Mai suna Aamir a bikin wata secondary school class mate dinta Nan fa suka kulla soyyaya me karfi domin kowa gida da makaranta ansa soyayya Aamir da Rahma domin a kowani lokaci suna jone tun a lokacin ya nuna yana son ya aureta amma sai mahaifiyarta ta nuna sai tayi karatu domin ko bayan ranta ta rike Yan uwanta be Musa ba shi da kanshi ya Nima Mata admission a c o e inda yake lecturing ya so d'aukan nauyin karatun amma umma ta hanashi a cewarta Kar yayi mata gori Nan gaba inshaallah da buga-buga zata biya Mata kudin makaranta domin ko wani sana'a ta kama umma Yi takeyi Kama daga kayan Miya zuwa kayan sanyi da dai sauransu

A lokacin da Rahma take 100level ne ta had'u da wani soja a supermarket ya bigeta by mistake Nan fa ta zazzage me rashin mutunci kasancewarta tana da baki sai dai akwai tsoro as in bata d'aukan raini shi Kuma sai ta birgeshi domin tunda yake babu macen da ta tab'a kallon kwayar idonshi tayi me abinda Rahma tayi me

Ga mamaki Rahma tana matsifa ya natsu Yana kallonta sai murmushi yakeyi a haka yusura ta zo ta janyen ta Suka tafi

Wanan sojan ba kowa bane illah Aayan a lokacin madadin ya nuna Mata yana sonta beyi hakan ba sai kawai yasa wani jibrin yayi ta binta ko ina Wanda tun bata zargin jibrin har ta zo ta fara gane ana binta tayiwa jibrin tas akan ya daina binta shima a lokacin jibrin ya gaji kawai sai ya koma gida yayi ta hutun shi har akasa bikin Rahma be sani ba domin shekara yayi baya Niger itama zainab da yake biya ta daina zuwa department dinsu domin dama department dinsu ba d'aya ba biyanta yayi a dole ta cusa kanta dan tayi ta samo labarinsu

Farouq ya kalli Aayan yace"sir wanan shine hoton mahaifiyarta ga kaninta Hamza ga twins wanan shine kawunta da maganar auren ke hanunshi "duk a laptop yake nuna musu hotuna

Abdul yace"Kai me kake ganin za a yi a fasa auren ka bamu shawara"

Mikewa Aayan yayi yace"kafin nan jibrin Ina son jin dalilin da yasa na saka ka aiki kayi tafiyar ka ka barshi"

Jibrin dake rawar jiki yace"oga dan girman Allah ka bani dama ta biyu zan gyra kuskurena"

Aayan yace"ai dole ne ma kayi duk inda zakayi sai na aureta zan hukunta ka"

Farouq yace"hanya d'aya ne za a iya bi dan b'ata auren nan "

Abdul yace"which is?"

Farouq yace"a bi ta hanyar mahaifiyar Aamir domin kwata-kwata ta tsane Rahmat domin so take ya auri yar kanwarta Aneesa a cewarta Rahma talakawa ne
Sai Kuma hanyar kawo Ina ganin in kuka cika me al'jihu zai san abinyi"

Abdul ya kalli Aayan yace"

Maman nur
[2/20, 8:23 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄👄
*BANA SONSHI*
💋💋💋💋💋💋
_By maman noorul_
_Hudah__

Dedicated to NIDA mijina fans group

🅿1⃣7⃣&1⃣8⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Yace"yanzu miye abin Yi?"

Aayan yace"wallahi sai na aureta da karfin tsiya dan bazan bari ya aureta ba"

Abdul yace"ka barsu please wallahi friend zakayi hurting dinta badly you will break her heart in ka nace ka bari ta auri Wanda take so Kar ciwon zuciya ya kasheta"

Kallon Abdul yayi da jajjayen idonshi yace"eh na gommace ta mutu in San bata raye da in bari ta auri wani"

Jibrin yace"oga karka damu ni zanyi handleling iyayen Aamir ku sai ku kula da kawon nata"

Aayan yace"wallahi in ka min shirme sai na halbe ka"

Yace"this time around Ina da perfect plan"

Abdul yace"wallahi ko bayan auren ku da ita ta gane Kai ka rabasu da Wanda take so zaku kwashe yan kallo"

Aayan yace"in na Bata fuska kenan Kai dai in zaka taimaka min ka taimake in kuma bazaka taimakeni ba ka fad'a min"

Abdul ya kalli farouq yace"akwai Karin bayani ne?'

Farouq yace"kawayenta uku ne amma yusura ta daban ce domin tare suka taso sai sadiya a c o e Suka had'u har shakuwa ta Shiga tsakanin su sai zainab sai dai zainab aiki takewa jibrin,ga hoton sadiyar"nuna me hoton sadiya yayi yace"itace sadiya tana da saurayi Ibrahim sai dai ba a sa bikinta ba sai ta gama makaranta Wanda yanzu semester d'aya ya rage masu,wanan kuma ita ce yusura"ai Abdul na ganin yusura ya dinga kallon hoton farouq yace"ita Kuma bikin ta da saurayinta umar Nan ne da wata biyu"ai besan lokacin da yace"what ba"

Duk Suka kalleshi yace"waye shi ina ne gidansu ?shima Kar a bari ya aureta please zuciyata zata buga

Kallon Kai mahaukacine Aayan kema

Abdul yace"dan Allah bani address dinta zani yanzu in fad'a Mata sirrin zuciyata turomin hoton na bude xender"

Aayan yace"kana da lafiya kuwa"

Abdul yace"na ma fika hauka Kuma na ratse ranan juma'a za d'aura mana aure ni ba Wawa bane kamar kai"

Kallon farouq yayi yace"ka min bincike akanta zuwa gobe"

Farouq yace"toh"

Aayan yace"wai ni ka roko ko ka zo yin naka aikin"

Abdul yace"both"

Bayan kwana uku biki ya rage sauran kwana biyu ana jibi kenan

Jibrin ne zaune a falon mummy Yana jira ta sauko

Ko minti goma beyi ba sai gata ta sauko cikin katon hijab har kasa

Kallonshi tayi tace"Amma ban waye ka ba"

Jibrin yace"eh hajiya wani abu na zo fad'a Miki akan matar da d'an ki zai aura domin bazan Yi shiru in cuce d'an uwana musulmi ba domin nasan kowa ce uwa zata so d'an ta ya samu zuri'a na gari"

Zama mummy tayi tace"Ina jin ka"

Yace"kwana uku Ina zuwa ba a Bari in shiga yanzu ma sanda na nuna musu I'd dina"

Tace"ka fad'a min ina ji"

Gyra Zama yayi bayan ya ciro tab dinshi ya Shiga video yace"hajiya yariyar nan ba Yar mutunci bane tana fita yawon dare ga biye-biye har office naje Dan in sanar da Amir amma ya koreni a cewar shi ko karuwa ce zai aureta Kuma har video na nuna me dan yasan ba karya nikeyi ba"

Amsa tab din tayi tace"muga"hanunta har rawa yake

Mika Mata yayi yana murmushi samun nasara domin ya gan nasara shi a kwayar idonshi

Ai tana gani tace"na rantse da rabbi ba a isa ba bazai aure Yar iska ba,d'an nan turo min videon yanzu ba sai anjima ba zani gidan su in sanar dasu maganar biki babu shi a dawo Mana da kayar mu in kuma baza su bayar ba mu bar musu ni zasu ciya mutunci wallahi ko mutuwa Aamir zaiyi sai dai ya mutu"

Tura Mata yayi ta bar gidan

Hayaniyar mummy ne yasa jama'a da Suka zo biki taruwar a falo

Anty hafsat tace"

Please kuyi hakuri yau aiki ya min yawa ne

Maman Nur

Share
[2/20, 8:23 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄👄
*BANA SONSHI*
💋💋💋💋💋💋
_By maman noorul_
_Hudah__

Dedicated to Mai Mata biyu paid group

🅿1⃣9⃣-2⃣0⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Anty hafsat tace" Yaya meke faruwa ne?"

Zayyana musu komai tayi harda nuna musu video

Anty hafsat tace"shikenan ki ce karuwa ce a ce kamar Aamir ya auri karuwa ai wallahi Yaya karki yarda Ashe saboda Yar iska ya guji ya'ta aneesa Yar mutunci Yar uwarsa toh a gaskiya Yaya ba haka kawai ta kyaleshi ba nasan da ita da uwarta sun dafa shi a tunkunya sai inda Suka Yi dashi kin San abin ka da tarbiyar mace Kuma kin San fa tunda mahaifinsu ya rasu batayi aure ba kwanaki har ji nayi an ce tana kawo maza"sai ingizata take

Mummy tace"toh miye abinyi?"

Anty hafsat tace"shine kawai ki je ki Mata tas da ita da uwarta sanan kawai ranan juma'a a d'aura da Aneesa ai Yar uwarshi ne zata rufa me asiri tunda mun tara jama'a"
Chapter 4 · 0% Book details