← Book details Bana Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 25

Sashe 20

Bana Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Barin d'akin ummi tayi ta leka d'akin Abdul hango yusura tayi tana bacci

Hamdala tayi a ranta sai dai fa bacci yusura ya fara bata tsoro

Abu dai Kamar Wasa yau kwanan su goma Sha uku Amma ko waya babu Kuma ankira be shiga domin daji suke

Rahma ne zaune dasu Amina sai murmushi takeyi tace"Amina kin iya kitso?"

Amina tace"ah'ah "

Tace"lalli fa?"

Amina tace"ban iya ba toh Mai zai hana muje saloon "

Rahma tace"babu inda zani in Kigan na fita gidan nan toh soja ya dawo na nimi izinin shi yace min bayason yawo Kuma ni bana son in b'ata me rai

Yusura ta mike taje zubar da miyau a waje ta dawo ta zauna

Amina tace"wai lafiyar ki kuwa tashin ki fa yafi goma"

Rahma ta kalleta sai Amina tace"yusura kamar fa cikine dake"

Zaro ido tayi sai Kuma murmushi ya sub'uce Mata tace"da gaske?"

Amina tace"it obvious"

Rahma ta fashe da kuka Mai cin rai

Amina tace"lafiya?"

Rahma tace"na aikata babban kuskure a rayuwa yau gashi yusura nada ciki ko ba komai ta wani fanni Abdul na tare da ita nifa?

Yusura tace"Rahma wai wani laifi kikayi ne domin kukan tayi yawa"

Cikin kuka Rahma ta Bata labarin komai ta Kare da cewa a daren da zai tafi babu irin rokona da beyi ba akan in bashi hakkinshi har kuka ya min yanzu yusura in wani abu ya faru ya zanyi wallahi bazan iya rayuwa babu shi ba"

Yusura tace"inshaallah gobene zasu dawo"

Rahma tace"eh shiyasa nike son in gyra kaina wallahi in na tuna abinda ya Shiga tsakanin mu kafi n ya tafi sai inji zuciyata na zafi "

Ummi dake labe tana jinsu ta koma ciki tana dana sainin fad'awa Rahma zai dawo gobe"

Amina tace"please ku tashi muje gidan umma zaku ji dadi"

Yusura tace"wata umm?"

Amina tace"umma Rahma sun dawo kano da Zama Yaya ya basu gida"

Rahma tace yaushe?"

Amin tace"yau kwanan su goma Sha biyu da dawowa ban dai fada muku bane tunda na gan kowa na cikin damuwa"

Rahma tace"ni bazani ba sai ya dawo muje tare yace Kar inje yawo"

Washe gari tunda Rahma ta tashi sallah asuba bata koma bacci ba kicin taje ta had'a girki ta gyra part dinshi sai kamshi yakeyi cikin kayan lafen da aka kawo musu kwana biyar da suka wuce ta bude akwatin ta ciro wani dinkeken material tasa

Yusura ce ta leko d'akin tace"wow mashaallah kinyi kyau"

Tace"hmm ai da nayi kitso da lallai dana fi yin kyau"

Yusura tace"gaskiya ne ai ke kika ki zuwa ni ba gashi naje nayi ba yau nasan Abdul bazai bari in huta ba domin yasan dinkina ya warke wallahi Rahma abinfa da zafi"

Rahma dake gyra d'aurin d'an kwalinta tace"niko yau ko mutuwa zanyi sai na mallakawa mijina kaina yayi inda yaso "

Yusura tace"kayan lafe mu sunyi kyau Kuma komai iri d'aya"

Rahma tace"ai addu'a kawai zamuyi musu domin sunyi kokari"

Sauka sukayi Rahma ta zauna ummi sai kallonsu takeyi tana rasa daga inda zata fara domin Rahma sai kallon agogo take jefi-jefi tana saki sai tace" ummi har yanzu shiru"

Ai ranan anyi drama domin wuni Rahma tayi tana jiran Aayan amma shiru tana ganin magrib nayi ta fashe da kuka da tun tafiyar Aayan batayi irinshi ba

Lallashi Amina keyi ummi ko ta wuce ciki domin ta gaji

Yusura ko ta koma cikin d'aki ta bude shafin bacci

Amina ne ta taimakawa Rahma ta kaita part din Aayan domin jiri take ji

Da k'yar tayi sallah tana idarwa ta koma ta kwanta rungume da hoton Aayan

Kiran umma tayi Suka gaisa umma tace"Rahma ki godewa Allah da ya baki Miji irin Abubakar kin gan irin gidan da muke kuwa? duk harda hamza mun dawo"

Rahma ta fashe da kuka tace" ya tafi ummi be dawo ba wallahi ya tafi umma zan mutu ki Kira ki bashi hakuri"

Umma tace"Yi hakuri zai dawo kin ji?"

Katse wayar tayi domin bata jin zata iya dogon magana
________________
Abu dai kamar Wasa yau
watan su hud'u ba labari duk Wanda ya gan Rahma sai ya tausaya Mata Bata cin abinci kiriki domin kullum da azumi take tashi in kuma lokacin bude baki yayi be wuci ta Sha tea ba

Ummi ne zaune a falo tasa su gaba sai sun cinye abincin plate dinsu sai fada takeyi

Tace"ke yusura ko baki ci Dan kanki ba ai Zaki ci Dan abinda ke cikin ki haba kasheni zakuyi toh wallahi bazan iya ba yau zaku tafi gidan umman ku

Rahma dake kuka sosai tace"ummi wallahi azumi nikeyi"

Ummi tace"yau sai kin karyashi ai bana Wasa dake"

Rahma ta b'are baki tana kuka tace"wallahi baki Sona ummi in soja ya dawo sai na fad'a me ya tafi dani"

Dariyar dole ne ya sub'ucewa ummi sai Kuma ta hade rai

Yusura ta kwabe fuska tace"ni na koshi"

Ummi tace'ina ruwana karki ci Mana in baki ci ba in cikin ya zube kin huta"ai fara ci tayi tace"ummi ina ci cikin bazai zube bako?"

Kallon Rahma tayi domin harga Allah ta tausayawa Rahma tace"ke Kuma in baki ci ba in ya dawo zansa ya maidaki gida in aura me wata ai kinsan Yana jin maganata "

Rahma ta fara dire dire tana bata hakuri duk inda ummi taso taci abinci dayawa kadan taci tana Gamawa ta koma dogon kujera ta kwanta

Yusura ta mike da d'an cikinta da ya fara fitowa ta koma d'aki

Bacci Rahma beyi minti goma ba sai ta fara mafalki

Mikewa tayi a razane da kalmar inalillahir wa Ina ilahihi raji'un, addu'oi takeyi sosai

Ummi tace"lafiya?"

Mikewa tayi ta ruga a guje ta shige d'aki ta rufe toilet taje ta d'auro alwala ta dawo ta shimfid'e sallaya ta tada sallah nafila

Ummi yau da fadiwar gaba ta tashi

B'angaren su Aayan ko

Maman nur
[2/20, 8:36 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄👄
*BANA SONSHI*
💋💋💋💋💋💋
_By maman noorul_
_Hudah__

*👄💡NUR WRITERS ASSOCIATION💡💋*

*💡N W A💡*

*Lightning and bringing smile to your world is our perority*

*NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~

🅿9⃣3⃣-9⃣4⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

B'angaren su Aayan ko a hankali yake zubewa kasa bayan uche ya halbe shi a wuri biyu kirji da gefen cikinshi Wanda sanda ya bari sun gama da Yan ta'ada ya cika burin shi

Kara me yayi a kirji,sanan ya bar wurin zuwa mota domin d'auko bomb dan ma Kar a gane kashe shi akayi baya Mason ayi bincike balle a gane kashe shi akayi

Koda ya dawo be Lura da ko gawan na wurin ko bayanan ba daga nisa ya wurga bumb din wurin ya tashi boom sanan ya bar wurin

Abdul ko sati d'aya kenan da Suka gama jiran Aayan yakeyi

Komawa su uche sukayi sai dai babu Aayan

Abdul da jikinshi rawa yakeyi ya tambaya Amma sai uche ya fashe da kuka yace"those terrorist don kill oga Aayan"

Cikin tashin hankali Abdul yace"how?"

Ya shake wuyar uche yace"tell me how?"

Uche ya fara kuka yace"na only 3of us come back some are in the hospital some don die"

Abdul ya saki kuka kamar yaro

Da k'yar ya bari washe gari aka koma dajin anyi niman duniya babu Aayan in takaice muku sati biyu akayi ba a ganshi ba sai dai Abdul ya gan agogon hanun shi ya d'auka ya rungume Yana kuka kamar yaro mamaki yakeyi ya akayi hakan ta faru shidai yasan suna sa bullet proof to kodai bomb ne ya tashi dashi?

Shima hanunshi katon bandage ne domin shima an halbeshi fuskar Nan duk ciwo

_____________

Tundaga wanan ranan da Rahma tayi mafalki ta fara rashin lafiya sosai ga rashin cin abinci kullum kuka ummi dai damuwa ce sosai a ranta yusura ta tausaya mata Kuma taki zuwa wajen umma ko asibiti kin zuwa tayi sai dai a Kira Dr ya zo gidan

Yau ummi ta Kira umma tace"ta zo gidan ta duba Rahma"dama ummi na son ganinta kunya ne kawai da kawaici

Tace"inshaallah gobe zan zo"

Washe gari ko ta zo da safe,Nan fa suke ta bawa Rahma baki Amma kukan Rahma karuwa yake inta tuna mafalkin da tayi

Ummi tace"ikon Allah Rahma dama haka kike da kafiya wanan wani irin zuciya ce ni da nike mahaifiyar shi na danne zuciyata "

Amina ta rungume Rahma tace"karki damu Yaya zai dawo"

Cikin kuka da maganarta da bai fita tace"ai dama nasan zai dawo mafalki ba gaskiya bane,bama zai tafi ya barni ban fad'a me Ina sonshi ba,umma be tab'a cin girkina ba,ummi sati d'aya fa mukayi dashi hiran kirki be tab'a Shiga tsakanin mu ba,ummmi ni"ta nuna kanta babu abind....."kuka ne sosai ya ci karfinta da k'yar numfashinta ke fita

A lokaci d'aya yusura da Amina harda umma suka fashe da kuka domin babu Wanda zai gan Rahma beyi Mata kuka ba shekaran jiya sanda Amina ta taimaka Mata tayi wanka tun ranan Kuma batayi ba

Ummi tace"ikon Allah kema umma yara kuka zakiyi dana sani da ban kira ki ba"

Umma ta fita ta Kira Wanda ta Saba kira a Lagos abokin aikinsu ta tambayeshi ko akwai labari

Nan fa yace Mata sun dawo Amma ya b'oye Mata Aayan ya mutu

Cikin jin dadi ta koma tace"Rahma an ce sun dawo gobe zasu zo kano "

Rahma ta mike ta shige toilet tana cewa"umma dan Allah ki Kira me kitso da lalli a min"

Umma tace"alhmdullilah "

Yusura ta fara Jan cikinta tace"Nima zanyi lallin "

Amina ta harareta tace"ke baki tausayin kanki?"

Tace"eh din Ina ruwanki"

Umma tace"ni zan tafi gida"

Umma tace"habadai ai Nan Zaki kwana mu fara Shirin tarban shi ki Kira gida kawai

Rahma ta fito jallabiya kawai tasa tace"umma ni nayi kicin zan had'a abubuwa

Da k'yar ma take tafiya domin bata jin dadin jikinta

Aiko gidan busy yayi sosai kowa da abinda yakeyi

Rahma ko tana trying number Aayan Amma be shiga

Murmushi tayi tace"nasan surprised kake son yimin sallamar me lalli da kitso ne yasa ta mikewa taje ta bude lalli Mai kyau akayi musu da kitso

Washe gari tun asuba ta farka tayi girki tayi wanka ta saka d'ikin Riga da skirt

Umma sai fad'a takeyi Mata wai ta daina zumud'i ko kunyar ummi bata ji?"

Rahma tace"ummi uwace a gareni ba suruka ba"
Chapter 20 · 0% Book details