← Book details Bana Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 25

Sashe 19

Bana Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace"Kai maman yan biyu kiji tsoron Allah yanzu sharri Zaki min?yaushe rashin mutunci ya taba shiga tsakanina dake?"Yana magana ne Yana tafiya har ya bar gidan yana fita kofar gida ya ruga da gudu Dan bazai manta kashedi da Aayan yayi me ba akan umma bayan ya bashi filin da yame alkawarin ya gargade shi akan ya fita harkan umma ya daina takura mata

Aayan ya sunguna har kasa yace"umma ku fara shiri gobe zansa a zo a d'auke ku a maidaku kano

Umma tace"Nan ma yayi,mun gode"

Abdul yace"umma ki dubi Girman Allah ki bari akwai gida a can kano din"

Zatayi magana Aayan ya katseta yana rokonta da k'yar suka shawo kanta ta amince inda Suka ce muhimman kayanta zata kwashi akwai komai a can

Godiya ta musu tare da fatan samun nasara a tafiyar su

Sun ji dadin addu'a ta daga gidan sukayi gidan su yusura Suka Fadi laufinsu

Sosai Abba ya ji ba dadi Amma yasawa zuciyar shi hakuri domin aikin gama ya riga ya gama addu'a yayi musu na samun nasara a tafiyar su

Bayan sun bar gidan makaranta su Hamza sukayi bayan sun cika me booth da kayan provision

Bayani sukayi me domin be san su ba Sosai ya ji dadi

Aayan yace"yaushe zaku gama waec?"

Yace"jibi zamu gama"

Yace"ok jibin in kun Gama sai ku tafi kano in result dinka ya fito ka kaiwa jibrin zan me bayani

Cikin sanyi jiki yace"toh Kai Ina zaka?"

Yace"tafiya zanyi zanje peace keeping "

Yace"toh Allah ya Kare"

Shafa kanshi Aayan yayi yace"take good care of your sister"

Yace"I promise"

Daga makaranta suka d'au hanyar kano

Sai da misalin karfe hud'u Suka Isa garin kano

Yusura najin muryar Abdul yana magana da maigadi dariya ya sub'uce Mata

Rahma ko bugun zuciyarta karuwa yayi

Da sallama suka Shiga falon inda ummi ta kallesu tace"Ina fatan dai kun gyra kuskuren ku?"

Aayan yace"

Maman Nur
Share
[2/20, 8:35 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄👄
*BANA SONSHI*
💋💋💋💋💋💋
_By maman noorul_
_Hudah__

*👄💡NUR WRITERS ASSOCIATION💡💋*

*💡N W A💡*

*Lightning and bringing smile to your world is our perority*

*NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~

🅿8⃣7⃣-8⃣8⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Aayan yace"eh ummi sai ka ce ba ya'yan ki ba kinsa Mana zafi"

Murmushi tayi tace"ai gaskiya ne"

Tashi tayi domin Basu wuri tunda tasan da safe zasu wuce kowa ya gana da matarsa

Abdul na ganin ta shige ya tashi ya koma inda yusura ke zaune ya koma kujeran da yusura ke zauna

Yace"babu sannu da zuwa balle a bani ruwa?"

Murmushi tayi tace"toh bari in d'auko"

Tashi yayi yace"muje d'akina kawai akwai sa'idawa a nan wurin

Murmushi tayi ta mike ta bi bayan shi

Aayan ko satar kallon Rahma yayi sai ya gan ta basar Kuma in ba ya fara Mata magana ba bazata yi me ba

Mikewa yayi yaje inda take yace"hi"

Tace"hello"

Yace"babu gaisuwa?"

Tace"welcome"

Yace"follow me"

Da dai kamar bazata bishi ba sai Kuma ta mike ta bi bayan shi

Tana kaiwa d'aki tace"uhrmmm gani"

Murmushi yayi ya karasa inda take yana kallonta yace"sunana ba urhmm ba yau dai sai kin Kira sunana"

Tace"aini ban sani ba"

Yace"karya kikeyi"

Rufe fuska Rahma tayi tace"kunya nikeji"

Rungumeta yayi ta baya yana shinshina kamshin wuyanta yace"Rahma ki ce kina Sona ko zan samu kwanciya hankali please"

Shiru tayi,yace"please I want to know my stand in your life"

Hawaye ne ya shiga gangaro Mata

Yace"subhannallah kiyi hakuri tunda baki so"yana gama magana ya koma gado ya kwanta

Tsayawa tayi tana kukan da babu dalili shiko kwanciyar shi yayi domin ta fara b'ata me rai

Kasa wucewa tayi sai ma Zama da tayi a kasar tiles ta jigina da bango

Duk wani abinda takeyi yana kallonta amma sai yayi Kamar me bacci har baccin gaske ya d'auke shi

Bayan awa biyu ya farka a zaune ya ganta ko motsawa batayi ba sai ma bacci da takeyi karasawa yayi ya gyra matasuman kanta da ya barbaze a fuskarta sanan ya shiga bayi domin d'auro alwala

Cikin dare ko babu inda beyi ba dan ta furta me kalman so amma taki harya gaji ya kyaleta

Washe gari

Da asuba sun gama shiri yusura sai kuka take

Rahma dai ji tayi bata da lafiya rokosu sukayi zuwa d'akin ummi tayi musu addu'a tare da musu nasiha sanan tace"matarsu su rakasu

Abdul ya makakle yusura sai shagwab'a takeyi shiko Aayan fushi yake da Rahma dan haka be jirata ba ya shige mota ya zauna

Kawai sai ta fashe da kuka ganin ya kulle motar jiran Abdul kawai yake su wuce

Kukanta ne yasa shi bude motar a fusace yace"toh miye in kika yi hakuri yanzu zan bar Miki garin tunda kin tsane ni karki damu zan bar Miki gidan yanzu"

Karfin kukanta ne ya Karo ranshi na Kuna yace"please ki koma ciki Kar ummi ta fito ta d'au wani abu nayi Miki "

Kafin tayi magana Abdul ya karaso da yusura bayan ya gama lallashinta Shiga motar yayi driver ya jasu

Abdul na d'agawa yusura hanun suna barin gidan Rahma ta zube a kasa da guiwowinta ta saki kuka .

Yusura tace hakuri zakiyi haka aikin nasu yake"

Amina ce ta fito ta jasu zuwa ciki kowa yayi d'akin mijin shi ya kwanta rai babu dadi"

Rahma da ta dunkule rike da rigar Aayan tana shishinawa tana kuka

Cikin takaici tace"

Maman Nur

Share
[2/20, 8:35 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄👄
*BANA SONSHI*
💋💋💋💋💋💋
_By maman noorul_
_Hudah__

*👄💡NUR WRITERS ASSOCIATION💡💋*

*💡N W A💡*

*Lightning and bringing smile to your world is our perority*

*NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~

🅿8⃣9⃣-9⃣0⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Meyasa bazaka kalli kwayar idona ba ka gane Ina sonka shin SOJA kasan inda Nike jin ka kuwa a raina?meyasa bazaka gane ba karka tafi ka barni kasan halin da zan shiga kuwa?
Haba SOJA a da ban tab'a tunanin zan so wani Kamar amir ba Amma bansan meyasa ba ko tunanin shi banayi why?meyasa baka bari munyi sallama ba?"

Amina ne ta shigo tace"da kin San kina sonshi kika bari ya tafi da b'acin rai?Rahma ko wani soja in zaiyi tafiya Yana son ya tafi hankali kwance da tunanin matar shi na gida tana me addu'a shin kin San irin abubuwa da sukeyi dan su Kare mutane?meyasa kika me haka wallahi Yaya bai tab'a soyayya ba da a ce ya tab'ayi nasan da zai gan tsansan soyyayar shi a kwayar idonki,keda ya kamata ki koya me soyyaya inda zaije fa ko ya kashe ne ko a kashe shi kika San ko bazai dawo ba?meyasa kikayi wasa da damarki?"

Kukan Rahma ne ya karu,Sosai take kuka tana yiwa mijinta addu'a sai cewa"take Allah ya tsare ya Kare min Kai mijina na tuba"

Amina tace"Bari in Kira Miki shi nasan basuyi nisa ba in basu fita garin kano ba ya fadamin inda suke in kaiki"

Cikin kuka Rahma tace"yauwa Kira shi"

Dialling numbershi akayi bugu uku ya d'auka

Rahma tace"sojana ina kuke?"

Amma Kash matsala network ya hana Aayan ya ji magana sai hello yake cewa karshe ma wayarshi ya d'auke service baki d'aya

Kallon Abdul yayi yace"babu network ga Amina na kirana"

Abdul yace"ga nawa wayar ka kira"

Tsaki yayi bayan ya amshi wayar yace"ga wayar ka Mara amfani tunda Kai cajin waya wahala take baka"

Abdul yace"mantawa Nike in saka Kuma jiya yusura kwana tayi tana kallo dashi"

Cikin ikon Allah Suka Isa Lagos lafiya direct office sukaje

Suka fara shirya tsarin tafiyarsu Sai kusan cikin dare Suka koma gida inda washe gari da asuba suka Kama hanyar cerelion

Kwata-kwata basu samu sunyi waya da gida ba duk inda suka so Yin haka abin ya fassakara domin suna kaiwa aka turasu inda zasu Kai agaji domin Yan ta'ada sun hana mutane sakat sai dai fa wani ikon Allah rabasu akayi biyu Abdul na jagoran wasu team Aayan ma da nashi team din Wanda duk aikin Yan kungiyar Al'qibila ne dan akai Aayan wuri me had'arin gaske shiko zuciya d'aya ya tafi inda shi Wanda aka bawa kwangila kashe shi a daji ya gama shirya komai domin a ganin uche Aayan shike hanashi cigaba

Babu b'ata lokaci kowa ya jagoranci team dinshi

Rahma ko kwana tayi tana kuka ko abinci taki ci ummi tayi lallashi ta gaji sai bata baki takeyi ganin irin kukan da Rahma takeyi domin zuciyarta nauyi take yasa yusura fashewa da kuka a ganin yusura mutuwa zasuyi shiyasa Rahma ke kuka

Ummi dake rike da waya a hanun tana trying layin su amma baya shiga

Zama tayi tace".....

Yana da kyau kayi Abu a lokacin shi domin ba kowa yake samun dama na biyu a rayuwa ba Rahma kinyi kuskure gaskiya

Maman Nur
Share
[2/20, 8:36 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄👄
*BANA SONSHI*
💋💋💋💋💋💋
_By maman noorul_
_Hudah__

*👄💡NUR WRITERS ASSOCIATION💡💋*

*💡N W A💡*

*Lightning and bringing smile to your world is our perority*

*NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~

🅿9⃣1⃣-9⃣2⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Ummi tace"toh ni ya kuke so in Yi ne kunsa ni a gaba Kuna min kuka wanan wani irin bala'i ne ku tuna fa d'ana ne Nima ji nike Kamar in Yi kuka,shifa auren soja yana bukatar mutum ya Zama jaruma nima haka na kasance har Allah yayiwa abban ku rasuwa"

Yusura tayi shiru zuwa yanzu Rahma ta daina kuka zuciyarta zafi yake Mata"

Ummi tace"Rahma zo ki kwanta kina bukatar bacci"

Babu musu ta kwanta a gado ummi na shafa kanta,lumshe ido tayi

Bayan minti ashirin ummi ta tashi zata bar d'akin Rahma ta rike Mata hanun

Ummi ta juya ta kalleta

Ba tare da ta bude ido ba tace"ummi kwana nawa zasuyi a can?"

Ummi tace"sati biyu"

Ai tashi tayi tace"sati biyu? gaskiya tayi yawa "

Ummi a ranta tace"toh in tasan Basu da ranan dawowa fa?"

Rahma tace"yau sun kwana d'aya kenan ko?saura kwana goma Sha uku"har lissafi take da yatsun ta"

Ummi jikin ta yayi mugun sanyi cikin sanyi jiki tace"kwanta kiyi bacci"

Tace"umma bazan Yi bacci ba addu'a zanyi me kema ummi je kiyime kinsan ke mahaifiyarshi ne karki damu dani ummi banSan meyasa nike jin ba dadi ba gabana fadiwa yakeyi,ummi bana son komai ya samu soja"

Ummi tace"karki damu babu abinda zai sameshi inshaallah"
Chapter 19 · 0% Book details