← Book details Auran Jareemee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 21

Sashe 4

Auran Jareemee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da dare Yuseef yazo gaida mami bayan sun gaisa tace "dazu kawunka yazo kuma na amunce zaka auri Nuratu amma ba yanzuba sai ka fara auren Yuseera dalibata" cike da mamaki ya kaleta yace "Yuseera kuma mami wace ita" fuska ta daure tace "dalibatace kuma yazama dule ita zaka fara aura inkuma baka amunce ba saidai a fasa duka" cikin tashin hankali yace "Allah yasa hakan shi yafi alkairi" da haka ya mike ya fice ko salama bai mataba baki ta ta 'be ta mike ta kuma bedroom 'dinta

yana koma wa gida ya zube a parlour ya rufe ido kamar me bacci yana huci Saudat ce tafito daga 'daki ta kaleshi tace "hmmm ahaka zaka kare baka da aiki sai bin mata da yauma ka koma ka 'kara kwana a gurin karuwar taka" bu 'de ido yayi yace "so kike jikinki ya gaya miki ko" baki ta murguda tace "hmmm me hali baya fasa halinshi aikinka kenan daga dukan mata sai lalibarsu" mikewa yayi cikin fushi yayu kanta sauri shigewa kitchin tayi tasa key

kai ya girgiza yace zaki shigo hannu yarinya bedroom 'dinshi ya shige ya zube a kasan carpet yana zancen zuci yaro dashi ina zai iya rike mata 3 guda 1yama ta addabeshi bare 3 ga Nuratu da kishi shi yanzuma ta yadda zai mata bayani yakeji gashi beson irin yarinyar da za'a aura mishi amma yana da tabbacin saita gudu da 'kafarta dan azabtar da ita zaiyi har saita gaji ta gudu da 'ka farta
haka ya kwana tunani har gari ya yawaye duk da yau monday amma bayajin zai iya zuwa office

da yake monday ce da huri Yuseera ta tashi ta shirya tsaf tayiwa mama salama ta tafi school
bayan tajene ta zauna a class akashigo akace "Yuseera Sa'ad tazo inji Principal" gabantane ya fa 'di "to" kawai tace tana mikewa aranta tana cewa metayi

shiga office 'din tayi da salama bakiwa a office 'din sai Principal ta amsa mata cikin fara'a gaida ita tayi kanta a 'kasa tace "gani" murmushi hajiya tayi tace "tan bayarki zanyi dama" kanta akasa tace "inaji" "yauwa so nake kibani number babanku" cikin tashin hankali Yuseera tace "plz hajiya inwani laifin nayi kiyi hakuri karki fadawa baba walahi hanani cigaba da zuwa makaranta zanyi" dariya tayi tace "kwantar da hankalinki Yuseera ba abunda kikayi ki bani number shi magana zamuyi dashi kuma ki kwatanta min gidanku" kwanta mata tayi ta bata number baba dan ta haddace ta a kanta har zata tafi hajiya tace "Yuseera naji kince baba zai hanaki zuwa makaranta ko ankusa bikinkine" kanta a kasa tace "a'a amma yace inayin candy in fito da miji" "masha Allah kina da wanda kike so kenan" cikin kosawa da tanbayar kwakwkwafi da Principal take mata tace "a'a" "okey Allah ya kawo na gari" "ameen" ta furta a hankali ta mike ta fice hajiya ta bita da kalon sha'awa tana me kwadaitawa Yuseef auran yarinyar

Yuseef na kwance yaji wayarsa na ruri mika hannu yayi ya dauka yaga Nuratu ce ta kara a kune ajiyar zuciya Nuratu ta sauke tace "haba dear tun dazo nazo office 'dinka baka zo ba" "sorry baby banaji dadi kizo gidana muyi magana" "okey ganinan" ta katse wayar ya ajiye ya maida kai ya kwanta

10m ta 'karaso gidan tana zuwa da yake getman 'din yasanta ya barta tashiga gidan ko salama babu ta shiga gidan a parlour ta tadda Saudat tana kalo a tv ko kalonta batayiba ta huce bedroom 'din Yuseef saurin mikewa Saudat tayi ta shiga kitchen ta dauko huka tafi bayanta shiga dakim tayi da gudu tayi kan Nuratu da take zaune a gefan bed tanayiwa Yuseef sannu saurin mikewa Yuseef yayi ya riketa amma ina saida ta samu............!

by
*XAHRA*
[8/23, 14:14] Anty Baby: *FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )

*( F.W.A)🖌*

https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/

🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*AURAN* *JAREEMEE*
🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀

wannan novel 'din naku'deene na maidashi naku'di sabuda wasu dalilai game bukata xai iya samunsa a #100 kacal duk meso zai iya tuntu'bata ta whatsapp number 08035407419 nagode

pree page

*PAGE* 9-10

..................📖Yuseef Jibirin(YJ) shine asalin sunansa ma haifinsa haifafen garin Kano ne su 2 ne shida kaninsa malam mudee(kawo) sunada yan uba amma suna kebbi su 3
sun taso komai tare sukeyi har aurema rana 'daya sukayishi amma bayan 3years matar Alhaji Jibirin ta haihu tasumu Yuseef da yake su 'yan bokone sai suka dakatar da haihu wa har saita sukayi 18years san-nan suka haifi Muwadat batafi 5years ba Allah yayiwa Alhaji Jibirin rasuwa mutuwar ta bigi kowa musam man kawo da shi ka 'dai gareshi gashi ko haihuwar Allah be bashiba

tunda Alhaji jibirin ya rasu kawo ya maida hankali akan tarbiyar yaran 'kaninshi amma me duk yadda suka tsaya kan Yuseef shida Hajiya tarbiyarsa so tayi ta gagara sabuda abukan banza tayake mu amala dasu dayaga ananeman salamashi yasa ya daina komai a gaban su ya koma mutumin kirki a gaban iyayensa amma a bayan ido saidai addu'a

yana gama maka ranta wani abokinsa yajashi sukeyin DJ tare tunsuna DJ har aka fara daukasu rawa daga haka suka fara yin tasu da kansu har a film suka fara fitowa

lokacinda mami taji labari har kwanciya tayi a husbitel saida ta kwana 3 aka salamuta da tadawo ta samu Yuseef tamai fata fata tace indai ya 'kara film karya dawo mata gida
shikuma yaje yasamu kawo da maganar kawo nason farin cikin yaran 'dan uwansa tunda shi be haifaba gara ya bauta wa na 'dan uwansa

yaje ya samu mami da maganar itakuma sabuda kara bata iya yimishi musu dan karyaji ba dadi yace dan behaifabane yasa takemishi iko da yaran 'kaninshi wan-nan tunanin ne yasa idan yaimagana akansu batayi mishi musu hakance ta faro yana yi mata maganar ta amunce

haka YJ ya cigaba da harkar film 'dinshi har ya sha hara ba irin 'yammatan da basa kawo kansu gurinsa wasu ya kulasu wasu ya watsar ana haka ya hadu da Saudat yaji yana kaunarta sosai besha wahala gurin taba amma iyayenta sunso tuburewa dagabaya suka amunce akan kome yabiyo baya ba ruwansu
ba a 'dau time ba akai aurensu ranar farko tunda Yuseef ya kusanci Saudat ya tadda ta ba budurwa ba ya tsaneta dan yana da mugun kishi duk dashi dan barikine amma ko saudaya yanaso yasamu ya bare mace a leda yaji abunda akeji yasa rai akan Saudat amma hakanshi be cumma ruwa ba haka suke zaune ai fada ai dadi har ta shekara 5 ko batan wata bataiba ita kuma Mami tunda batada yara da yawa ta keso taga jikokinta a duniya ganin saudat ta 'ki haihuwa tace Yuseef ya 'kara aure ko Allah zaisa a dace da dafari ya 'ki tunu muradinsa na san bere mace a leda yasa ya baza ido dan samu mace tagari ba ida tunaninsa ya zame sai akan Nuratu
'yar film ce tare sukeyin aiki inta kama ya kula yariyar akwai kamun kai gashi in zasuyi sati 3 suna aiki tare bata kula kuwa cikin jarimai maza kame kanta takeyi bakamar sauranba ga alkinta jikinta badai ka ganta ba mayafi ko hijab ba la akari da halin kirki irin nata yasa ya zabeta amatsayin wace zata zamu matarshi ta biyu

koda yasamu mami da maganar kin amuncewa tayi ya samu Nuratu da maganar ya hakura aikuwa hankalinta ya tashi tashiga ta fita aikowa Yuseef ya zauce akanta dan ji yake duk duniya bazai iya rayuwa in ba Nuratu ba dan haka ya kula damarar samunta ko ta halin 'ka 'ka

*cigaban* *labari*

bayan kwana 2 baba ya kara kawo a waya ya sanar da shi ya amunce
kawo yaji dadi sosai yacewa baba jibi suna tafe da kudin aure insha Allah

haka kuwa akayi kwana biyu a tsakani su kawo suka je suka kai kudin aure suka ce suna so a tsada biki 2mouth dariya baba yayi yace "duk da bikin dan talaka a kano shekara gudane wasu wata 10 amma ni inada wadatar zuci nasan Allah bazai ta barda muba dan haka na amunce Allah ya nuna mana lokaci" su kawo suji dadi sosai sukayiwa baba da 'kaninsa salama suka tafi cikin farin ciki miko masa kudin Sageeru yayi amma yaki amsa yace ai yarkace Sagiru dan haka baxan amsahi wan-nan kudin ba
ba musu kawo Sageeru ya mada kudin aljihunsa yaiwa baba salama ya huce gida

baba na shiga gida ya tadda su duk suna hira ana dariya
xama hayayi ya kali mama yace saiku fara shiri ansa bikin autarki wata 2 tea 'din da yazid ya kurbane ya furxo dashi waje yana neman kwarewa yace "baba wace autar kake nufi" dariya baba yayi yace "akwai wata auta a gidan nan bayan Yuseera"
xaro ido Yaxid yayi yace "yan zu baba karasa wa zaka aurar sai autar mama bata isa aureba tunda tayi 18years ba" daure fuska baba yayi yace "Yuseera 'yatace ni nakeda iko da ita kuma ni nakeda ra ayin aurar da ita a lokacin da naso kuma ga wadda naso dan haka banason kowa yakara samun baki acikin maganar nar inda nasan xakuyi gardama da bazan bari muta nannan sutafiba sai an daura auran nan yamxuma saina kirasu bawani abun bane" saurin kalonsa mama tayi cikin rawar murya tace "a'a kayi hakuri abari sa nan da wata 2 ba wadda zai 'kara magana insha Allah" san-nan ta kali Yazid ya yacika yai fam tace "mara kunya tashi kabawa mutane guri" mikewa yayi ya fice daga gidan yana kunkuni

kalon Yuseera baba yayi da tazama kamar gunki a gurin batako mutsi yace "Allah yayi miki albarka auta ke naso bazakiyimun musuba" sai yanzu taji kuka yazo mata cikin kukan tace "ameen baba nagode" da haka ta mike tabar gurin tana cigaba da kukanta meban tausayi
da kalon tausayi mama ta bita dan batasa sanda kwala ta tahu mataba tai saurin gogewa kar baba ya gani
haka ta jure suka cigaba da hirarsu da baba

Yuseera shiga daka tayi taita kuka me tsuma zuciya tanayi tana magan ganu barkatai takamo can ta kamo can har ta gaji tayi shiru dan bane rarrashinta itaba me yaya mace ba da saitaje gidanta kota kwantar mata da hankali ya Kabeeru ne kuma be zo ba
Chapter 4 · 0% Book details