← Book details Auran Jareemee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 21

Sashe 11

Auran Jareemee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

..........................📖"Rashin hankalin zakumun anan, to baku isaba ubanku zanci gaba dayanku" Nuratu ce tana huci tace "kana ganin daga zuwana wan-nan 'karamar 'yar barikin take zagina hada kokari dukana ita 'yar uban wacece ko ance mata ni sa'ar uwartace" kafin yayi magana Saudat tace "sannu babbar 'yar bariki ai nayarda tunda ke kike kawo kanki da kanki gidan miji kuma ubana yafi 'karfinki 'yar ma tsiyata me....!" tsawar da ya 'kara daka musuce tasa Saudat kama bakinta cikin fushi yace "nasan dukanku kunsan halina ko to duk wadda na 'kara jin bakinta anan ranta zaiyi mummunan 'baci dan walahi ayau saita koma gidan ubanta da fashashshan jiki mtss banzai kawai plz ina shiga ciki inji muryar wata daga cikinku" yana gama fadin haka ya huce ya barsu a gurin

hararar Saudat Nuratu tayi ta dau pilet 'din tabar gurin kwafa Saudat tayi ta koma ta zauna tanajin ciwon marin da Nuratu tayi mata bata rama ba amma taci alwashin ko ba yauba saita rama marinta walahi

YJ yana shiga 'dakinsa ya zube akan bed zuciyarsa na masa zafi duk duniyar sai yaji ta isheshi jiyake kamar duk yasake su ma ya huta amma ba hali yanzu yana sakin ko 'dayace sunansa zai 'baci a gari amma lokaci yake jira yayi yasan matakin da zai dauka

mikewa yayi yashiga toilet ya watsa ruwa ya dawo ya kwanta yana tunane tunane kwatsam Yuseera ta fado mishi a rai tan bayar da yayi wa kansa itace me mami take nufi da ta riketa a gurinta duk da hakan datayi ya rage mishi wani hawan jinin dan yasan inda tana nan masifar da zasuyi ba tawasa bace dan yaga yarinyar batada kunya tunda har shi take harara bare matansa wani 'bangare na zuciyarsa yace mezai hana ka budewa mami huta tabaka matarka ka jarba ka gani ko akanta zaka dace kasamu cikar burinka kai ya girgixa a fili yace "a'a ba lalai itama nasameta a buduwa tunda nayi 2 banji dadiba kawai hakura zanyi dan banida sa'a bansai meyasa Allah be cika mun burinda nake dashi sama da 20years ba wata kila sai a aljana in ana bude mace a leda na budeta amma a duniya na hakura"
[8/23, 14:14] Anty Baby: 📘🖊️

🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*AURAN* *JAREEMEE*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸

storry and writting
by
*FATEEMAH* *S* *OMAR*

*PAGE* 25-26

.....................📖Huci ya fara yana magana da 'karfi "ki bude ko far nan ko idan na bude jikin ki zai fa'da miki walahi" dariya tayi tace "hmm ni mahau kaciyace da zan bu'de ka jibgeni to walahi baka isaba" kwafa yayi yace "ki kuka da kanki" tsaki taja ta fara wake-wakenta ta rabu dashi kai ya girgiza ya bar gurin zuciyarsa na suya

ita kuwa Nuratu tana shiga 'dakinta ta kulo tana maida nunfashi ta zauna kan bed sai lokacin kuka ya kwace mata tana jerowa YJ Allah ya isa bata ta'ba kawo Yuseef zai daketa tana kwana biyu da zuwa gidansa duk yadda yake dauki da zumudin kawota gidansa amma a kwana 2 yayi mata irin wannan dukan amma zata 'dau mataki dan be daki banza ba mikewa tayi tashiga bethroom ta ha'da ruwa me zafi tayi wanka ta fito ta sauya kaya ta kwanta amma saita kasa bacci tunda ta 'dan 'dani zumar YJ jiya taji nan duniya ba namijin da ya kaisa da'di ga tana mugun bukatarsa amma ya hanata ra 'barsa amma ita tasan matakin da zata 'dauka da 'kafarsa zai kawo kansa

washe gari bayan su mami sun gama brekfast mami ta kali Yuseera tace "kifara shirinki insha Allah jibi zaki koma 'dakinki yayanku yada bu'katar me kula dashi" kan Yuseera a 'kasa tace "to mami" murmushi mami tayi tace "Allah yayi miki albarka 'diyata" "ameen" tace tare da mikewa ta bar gurin

bedroom ta shiga ta zauna ta saki kuka me cin rai a fili tace "ya Allah kai ka hukun tamin auren ya Yuseef kuma kai kasan yadda zakayi dani a gidan sa ina rukunka da ka zama gatana ka kareni daga sharin me shari ka kareni daga aita abunda ba daidaiba ya Allah" sakuka yaci 'karfinta tana jin dadin zama da mami amma ya zatayi dule tayi hakuri ta barginda tunda bazata iyayiwa mami musuba

Muwadat ce ta shigo ta tadda ita tana kuka ta 'karaso da saurinta tace "haba aunty meye abun kuka kuma" kawar da kai tayi ta cigaba da kukanta itama Muwadat 'din saitasa kuka kalonta Yuseera tayi a razane tace "me yasameki kike kuka" "haba aunty dule nai kuka dame zaji da zafin rabuwa dake ko da kukan da kikeyi" share hawayenta tayi tana 'ka'kalo murmushi tace "indai kukane na daina kema ki daina dan Allah" share hawaye ita Muwadat 'din tayi tace "nima na bari aunty" dariya sukayi san-nan suka cigaba da hirar duniya

ater 2 days

yau ta kama Yuseera xata koma gidan YJ tun safe mami taketa shiri takasa zaune takasa tsaye kayan ma hanata ha 'dawa tayi tace ta bari zata ha'da mata

shi kuwa YJ yau tunda ya tashi ya shirya zai tafi office ya fito parlour Nuratu ta mike tana kalonsa sama da 'kasa tace "hmm gaskiyane 'dan 'da'di office to baka salameni ba zaka fita" harararta yayi yace "amma kedai bakida hankali ko" dariya tayi tace "hmm kasan mesa har yanxu Allah bai cika maka burinka ba sabuda ya dubi zuciyarka dama muma ba samu kakeba kuruciyar mu kake so kuma baka samuba ko da kasamuma daga baya hula kantamu zakayi shi yasa Allah be bakaba" duk da jikin YJ yayi sanyi kuma yasan Nuratu gaskiya ta fa'da masa amma bai nunafa saima cewa yayi "ai banga abunda zanso a jikin kuba shiyasa ban aureku dan so ba kuma abunda naso 'dinma ban samuba kuma duk lokacin dana gaji daku sakinku zanyi na auri wasu" "to saime dan mun rabu da 'kaddararren miji irinka" Saudat ta fa'da tana rike kugu murmushi yayi ya juya yabar musu gurin sunata masifa shi zuwa yanxu ma dariya suke bashi wai dashi zasuyi fito na fito

me makon ya huce office sai ya tafi gidan mami
yana zuwa yaga mami tanata soye soye da dafe dafe duk kanshi ya cika mishi hanci murmushi yayi bayan ya gaida ita yace "mami me akeyi mana ne haka" baki ta ta'be tace "girki nakeyiwa 'diyata" cikin rashin fahimta yace "wace 'yar taki kuma" harararsa tayi tace "wa nake da ita da ta huce Yuseera" fuska ya ha'de yace "me zatayi da wannan tulin kayan" mikewa mami tayi tace "kaga bani da lokacinka yanxu akwai abunda nake Allah ya tsare naga office zaka" fuska a ha'de yace "ameen" ya mike ya fice ransa ba 'dadi

sai 5 mami ta gama shiya komai tasa Yuseera tayi wanka ta tsantsara kwaliya ta dauko mata kaya masu kyau ta bata tasa driver ya kaita gidan YJ

Nuratu YJ na fita ta kali Saudat duk da tunda tazo ba suyi maganar arxukiba tace "nikuwa 'yar uwa ina matar gidan nan da aka aurawa Yuseef?" baki Saudat ta ta'be tace "uwarsa ce ta zo ta dauketa" kai Nuratu ta girgiza tace "walahi in ta dawo a kan shegiya zan huce duk abunda YJ yakemun" "hmm nima ai kai na fasa mata tazo ta dauketa" "kinmun daidai walahi" san-nan cikin nutsuwa tace "wai sister ko ada haka kike fama da YJ" "hmm abunda yafi hakama yana mun musaman gurin sex dan yaga banida juriya sai yaita zalintata" 'buye dariyarta Nuratu tayi a ranta tana cewa lalai kin raku mata duniya in ba hakaba miji kamar YJ meye abun gudu a gurinsa saima so nima da ya 'kin zanyi maganinsa kwaya zan zuba masa yasha dule ya neme ni a fili kuma cewa tayi "hmm gaskiya Yuseef mugune anya baya shaye shaye" "no gaskiya bayayi da yanayi da ko bamu sani dukan muba cikinmu 'daya zai sani tuna tare kuke aiki dashi kinga da yana sha da acan zaisha ko gida kuma nima ban ta'ba ganinsa ya shaba" "hmm hakane kuma" daga haka ta mike tabar parlour

tunda suka 'karaso gidan gaban Yuseera ke fa'duwa badan komai ba saidan tsoron ha 'duwarta da Nuratu da salama suka shiga ba kowa a parlour suka huce 'dakin Yuseera saida suka gyara komai san-nan mami ta kira Yuseef tace yazo tana nemansa a gidan sa

ba a 'dau time ba ya 'karaso gidan
yana zuwa ya tadda su a parlour kafe Yuseera yayi wadda kanta ke 'kasa da ido dauke kansa yayi suka 'kara gaisawa da mami yace "ai da kin kirani a zo na 'daukota ba saikin wa halar da kankiba" "eh ai nasan da kai na za'bi inkawota da kaina" kai ya sun kuyar yana satar kalon Yuseera wace hakannan yaji bayaso dauke ido daka kanta

nasiha mami ta fara yimasa harda Yuseerama Nuratu dake 'daki ta jiyo kuskus a parlour ta dauka 'yan uwan Saudat ne dan haka ta mike harda gyara riga a fito da 'kirji ta fito parlour da Saudat ta ci karo zata kitchen tace "sister ashe baki mukayi?" "au suwaye suka xo?" "dama ba bakinki bane" "eh zo muje muga suwaye"

tare suka 'karasa mami na ganinsu tace ku 'karaso dama ina nemanku zama sukayi suka gaida ita ta amsa tana cewa "ga 'kanwarku na dawo muku da ita ku rike ta amanece a gurinku" har saurin kai idonsu suke kan Yuseera mikewa Nuratu tayi da sauri tana nunata tace "dama kece matar YJ?" kan Yuseera na 'kasa 'kirjinta na lugude batace komaiba sai mami ce tace "eh itace kin santane" kai ta gyada tace "eh nasanta.............!"

by
*XAHRA*
[8/23, 14:14] Anty Baby: 📘🖊️

🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*AURAN* *JAREEMEE*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸

storry and writting
by
*FATEEMAH* *S* *OMAR*

*PAGE* 27-28

........................📖..."Ko ba itace ka kusa kadaiwa a mutaba kanaki da kayan makaranta?" tayi tabbayar tana kalon YJ shima Yuseera ya kala sai yanxu ya tunu inda yasanta ya gyadawa Nuratu kai yace "amma meye na raxana haka" baki ta bude zatayi magana sai kuma ta fasa gudun kar a gano munifarta akan Yuseera tsaki Yuseef yaja yace "malama samu guri ki zauna ana magana" zama tayi mami ta tabe baki ganin shirme da shashanci irin na Nuratu
Chapter 11 · 0% Book details