← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 17

Sashe 6

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗan jim tayi gaban ta na faɗuwa na sabon batun da ya Kunno Kai, ita kanta ta san a kwana da wuni da suka yi a hannun ta sun rame saboda yunwa sedai bata san yadda zata yi musu ba haka kuma wannan na cikin tunanukan da ke kai kawo a kanta dan su ɗin ƴan ƙauye ne so sun san muhimmancin nonon uwa ga jariri

"Dama...dama haka kawai ya É—auke shine ban san yadda zan yi ba".

"Ikon Allah, abinda mamaki amma mafita ba zata gagara ba sedai kafin nan ina son sanin wacece ke da abinda ya rabo ki da garin ku dan mu samu kwanciyar hankali da yardar zuciya akanki cewar ba me cutar wa bace, haka kuma kiji tsoron Allah ki faÉ—a mana iya gaskiyar ki".

"Isyaku Maƙeri Dattijo ne da yayi suna a garin BA MUNI ba dan komai ba se dan sana'ar sa ta ƙira da Allah ya sanya masa nasibi akai dan yana iya ƙera duk kalar abinda ake so kama daga kan makami har zuwa kayan amfanin yau da gobe na gida da na waj   en sana'a.

Matar sa ɗaya har yayi rayuwar sa ya koma ga Allah wadda ƴaƴan ta ke kira Kulu d an Asalin sunan ta Hauwa'u ne, ƴaƴan su biyar rayayyu dan tayi ta haifa suna mutuwa se biyar ɗin ne suka tsaya suma ba a jejjere ba, Baba Habibu shine babba se baba Adamu duk da akwai ratsin matattu biyu tsakanin su se kuma babana wato kamisu shi kuma matacce ɗaya ke tsakanin sa da wan nasa, daga shi se gwaggo Larai se kuma auta baba iro.

Dukkan su suna zaune a madaidaicin gidan gadon da mahaifin su ya mutu ya bar musu ne sedai kowa da sashen sa inda ya killace suke rayuwa da matar sa da ƴaƴan sa, sedai banda gwaggo Larai dake aure a can wani ƙauye me nisa da namu shiyasa ma se ta shafe watanni bata zo gida ba.

Babana direban babbar mota ne inda Allah ya taimake shi ya shiga makarantar yaƙi da jahilci har ya samu abinda ba'a rasa ba na ilimin zamani dan yaga komai seda ilimin ko yaya ne hatta ko da tuƙin.

A can wajen sana'ar sa ta zuwa gari gari ya taho da mahaifiya ta daga garin da bamu san ina bane bayan ya aure ta sedai kawai ganin sa da mace Æ´an uwan sa suka yi yace matar sa ce.

An sha rikici da shi kafin ƴan uwan su haƙura su bar shi da ita dan se da uwar su ta nemi yi musu baki akan maganar dan ba ƙaramin so take yi wa babana ba kasancewar sa mutum me kyauta da tausayin iyaye hakan yasa duk ciki ya fi kyautata mata.

Cikin wannan hali rayuwa ta cigaba da gudu har iyayena suka shafe shekaru tare amma haihuwa shiru, tun abin baya damun Inna ta har ta fara yiwa babana kuka sedai ya bata haƙuri duk da shima yana damuwa dan habaici da baƙar magana duk yana kwasa wajen ƴan uwan sa da matan su sedai bata kulawa dan shi ba me san rigima bane.

Ba'a daɗe ba Baba iro da yayi aure bayan su ya haihu shima wannan ya ƙara wa iyayena damuwa, a taƙaice dai seda suka shekara biyar sannan Allah ya basu cikina, murna kuwa a wajen su ba yasu a lokacin su da kakata bayan su kuwa ba wanda yake farin ciki dan ba wanda yake so a haɗa musu zuri'a da Inna ta a cewar ƴan uwan sa tunda basu san asalin ta ba.

Cikin ikon Allah Allah ya sauki inna ta lafiya ta haife ni, ƙauna da soyayya na same ta ɗaga kowane ɓangare na iyayena da kuma kakata har na kai shekara ɗaya da rabi kafin mahaifina ya rasu sanadin haɗarin motar da ƴan fashi masu tare hanya suka jawo.

Itama inna ta ban ciki shekaru biyu cikakku ba ta haukace Æ´an uwan mahaifina suka dinga faÉ—in rashin tawakkali ke gare ta, wai ta kasa dangana da rashin babana ne.

Wasa wasa abu ya zama sedai a rufe ta a ɗaki ga ba me kula da ita se tsohuwar kakata da nake kira biba dan lokacin ban iya baba sosai ba haka kuma kula dani se abin ya taru yayi mata yawa to abu ga jikin girma, wannan yasa yunwa, ƙishirwa da rashin lafiya yaci ƙarfin Inna ta se wayar gari aka yi aka tsince ta amace.

Ba wanda ya damu da mutuwar se kaka ta dan da ƙyar dangin babana suka sallaci gawar bayan kaka tayi iƙirarin tsine musu a cewar su wai haram ne sallatar gawar da ba'a san asalin ta ba.

Tun daga lokacin na zama marainiyar ƙarfi da yaji amma biba bata gaza akai na ba, kullum idanun ta na kai na tunanin ta nice da rayuwata har aka wayi gari ta makance dan dama tana fama da ido ga kuma shekaru dan a ƙalla a lokacin tayi saba'in da hawa dan se da ta shekara sha ɗaya da aure kafin baba Habibu yazo duniya.

Haka tana ji tana gani ba yadda zata iya ta baiwa baba Habibu ni bayan ta jaddada masa amana ce ta basa kuma Allah ya kallon sa, da farko zaman kamar abin arziƙi kafin daga baya komai ya kwaɓe, a ƙananun shekaru na na huɗu a lokacin haka ake sani wanke wanke, shara, ɗebo ruwa kai har ma da wanki wani sa'ilin bayan ƴaƴan sa har da me aure ciki banda ragowar matasa da ƴan matan da ke cike.

Duka kuwa kamar baiwa sedai in ban kuskure umarnin su ba daga Æ´aÆ´an har iyayen, wani sa'in biba ta jiyo Ni wani sa'in Bama ta sani nima kuma bana faÉ—a saboda irin tsoratar dani da Inna uwale dashi baba Habibun suka yi.

Haka nayi ta shan wannan baƙar azabar har na kai shekara bakwai wanda ina shekara biyar Allah ya ɗau ran kakata biba, ba ciwo ba komai ajali ya sauka se fatan dacewa kawai, a lokacin duk da banda shekaru amma ina da wayo da kaifin basirar da maraici ya koya min dan haka nasha kuka sanin ragowar gatana babu dan duk wannan labarin na same shi ne wajen ta gaf da zata rasu, in na gama aiki na se in gudu can muyi ta hirar mu shine fa na taɓa tambayar ta ni ina babana da Inna ta shine ta sanar dani.

A shekaruna na bakwai na iya raino fiye da zato dan hatta da wankan jarirai yi nake, kai a aikin gida ko kula da É—a ba abinda ban iya ba lokacin haka kuma azaba ba wadda ta ragu wajen uwale matar baba Habibu.

Se da na kai sha biyu sannan suka maida ni wajen kawu iro kan cewar suma su amfana dan lokacin ita uwale bata da ƙananan ƴaƴa, shi kam kawu Adamu ko da aka yi masa tayi cewa yayi a'a dan shima ba shida ƙanana se matasa, haka na koma hannun kawu iro na cigaba da wahaluwa wajen Inna mariya.

Ban san wadda tafi wata rashin imani ba cikin matan biyu wato uwale da mariya dan ita uwale da wuta take min azaba ita da mijin ta ita kuwa Inna mariya cewa tayi kowane sassa na zan dinga musu ayyuka.

Sauƙin abin ɗaya da mai gari yasa dole aka bar ni nake makarantar boko ganin yadda nake sha'awar na ƴaƴan shi dan haka tun ina shekara tara na fara haka kuma karatun makarantar gwamnati ba wani nursery daga primary ne kawai.

Ko da na gama ban yi sanya ba na garzaya na faɗa masa buƙata ta na ɗorawa ta kuwa same su da maganar kuma dole suka yadda, farin cikin da nayi lokacin da na sami makarantar kwana ba zai bayyanu ba dan ina ɗaukar makarantar da wajen da zan fake in ji sanyi a raina.

Duk irin wahalar da ake faɗa na makarantar kwana ban damu ba dan a wajena bata kai ko rabin ta gidan mu ba, haka kuma in naga ƴaƴan masu dashi ko rufin asiri na ciye ciye bana ɗorawa kaina sanin ni ko shege ƙanzo ba a haɗa ni dashi ba hasalima Ni na kai kaina makarantar a ranar farko da kowane iyaye ke kai ƴaƴan su.

Tun a lokacin principal ɗin ta kafe ni da kallo alamun tana nazari ne a kaina kafin kuma ta bani komai na buƙata tace naje aji bayan ta haɗa ni da wata ɗaliba.

Washegari se gashi ta aiko an kaini har gidan ta dake quarters É—in Malamai ta tambaye ni tarihina bayan ta bani abinci naci ganin alamun yunwa a tattare dani.

Kamar yadda nake faɗa miki haka na sanar da ita inda se da ta koka min, haƙuri ta shiga bani kamar ita ce mai laifi kuma tun daga lokacin ita ke kula da komai na na karatu har mamaki nake yadda bata ƙyashin kashe kuɗin ta a kaina, hatta tsangwar da ɗalibai suka so ɗora min ita tayi tsaye taga ta hana duk dan naji daɗin Makarantar.

Ina aji na biyar muka yi aure da wani malamin mu da yazo bautar ƙasa batare da sanin dangi na ba dan nasan ba zasu yadda ba ni kuwa ba zan iya haƙura ba dan gani nake auren ne kawai ze sama min sauƙi na dindindin, wata biyar da auren na samu juna biyu.

Mama Hadiza wato principal ke kula dani dan ta shaida aurenmu.

maigadin mu na aika da izinin Mama yaje ya sanar musu ba zan dawo hutun zango na biyu ba zamu shiga lesson na jarrabawar ƙarshe dan haka zan zauna a makaranta, ba wanda ya ko kula zance na dan tuni suke min kallon wata mara amfani kuma ba tsatson su ba.

Wata daya kafin fara jarabawar mu na haife su, muna gama jarabawar da ta É—auke mu wata É—aya da rabi ne muka koma gida shine suka shegan ta min Æ´aÆ´an suka koro mu saboda bamu je da baban su ba an masa canjin waje aiki ya bar mu akan zeje ya dubo inda aka tura shi muka yi dashi wata biyu ze dawo yanzu kuwa kwana huÉ—u kenan a cikin satin farko".
Chapter 6 · 0% Book details