← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 17

Sashe 10

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da suka je school É—in bata bar su ba seda ta raka su class É—in su primary one Sannan ta tafi bayan ta sake jaddada musu zama good girls.

Cikin rashin jin daɗi ta tare wani napep ɗin ta shiga zuwa wajen aikin ta, sam bata so ba yau tayi latti, tun da ta fara aiki dasu zata iya cewa yau ne kawai ta makara amma se ta ke jin kamar ta aikata wani crime babba duba da yadda aka dinga maimaita mata rashin son makara a gare ta kasancewar tana riƙe da post ɗin secretary ɗin C.E.O na wajen baki ɗaya.

Bakin makeken building É—in ta tsayar da me napep ta biya shi kuÉ—in sa ta nufi gare É—in.

Ƙarin building me da yaji glass ta kusan ko ina haka kana kallon shi zaka bashi hawa kusan biyar ko bakwai a ƙiyasce, daga can saman building ɗin aka rubuta da manyan harufan, A.A GAMJI Company.

Kamar ko da yaushe yau ma se da aka caje ta duk kuwa da kasancewar ta ma'aikaciya a wajen wanda wannan doka ce hatta shi kan sa C.E.O É—in in ze shiga ko so nawa ne se an caje motar sa da shi kan sa, wannan yasa kamfanin ke daga cikin manyan kamfanonin da ke da cikakken tsaro da doka.

Tun a bakin gate ta zare baƙar after dress ɗin da ta ɗora kan white hijab ɗin ta iya kafaɗa da rigar jikin itama fara iya gwiwa se dogon dark blue ɗin wando daga ƙasa, ƙafar ta kuma sanye da blue ɗin socks da takalmin ta wedge baƙi.

Da sauri da sauri ta dinga takawa batare da ta kula gaisuwar da ma'aikata ke mata ba ta wuce lifter tayi pressing kan fifth floor inda nan ne office É—in C.E.O É—in yake, seda tayi wani gasping air ganin yau ya rigata zuwa dan ga nan office É—in a buÉ—e alamun yana ciki.

Kan table ɗin ta ta ajiye jakar ta da komai ta ƙara sa cikin office ɗin sosai da sallama, kanta a ƙasa amma yaji sautin amsawar sa can ƙasa.

Ta jima a tsaye shiru tana jiran yace wani abu da zata sami damar bashi haƙuri kan lateness ɗin da tayi sedai shiru bece komai ba kamar ba kowa a ciki se sautin Ac dake aiki a hankali.

"Ehm..am..amm..sorry sir..for the...lateness...it wasn't intentional, am sorry please".

Ta faÉ—a a rarrabe baki na É—an rawa jin shiru be da niyyar cewa komai.

"Any schedule for today?".

Da sauri ta ɗago tana gyaɗa kai uwa ƙadangaruwa

"Yes...sure sir".

Ta fice da sauri zuwa table ɗin ta tare da fara ƙoƙarin ciro iPad ɗin ta, inda Allah ya taimake ta duk sanda ta zama less busy ba wai ɓata lokacin take a banza ba, a'a tana rage wasu ayyukan ne kamar wannan schedule ɗin tun jiya ta haɗa shi gashi kuwa se mata amfani.

Komawa tayi office É—in.ta matsa gaban table ta ajiye masa iPad É—in ta shiga yi masa bayanin schedule É—in É—aya bayan É—aya, seda ta gama gaba É—aya sannan yasa hannun sa dake cike da gargasa ya É—au ipad É—in yana bi, sanar mata da wanda zeyi attending yayi yayinda yace ayi postponing ragowar.

With due respect ta karɓa ta juya ta fita first office inda nan take, gyara kayan ta tayi kana ta zauna ta shiga aikin ta cike da ƙwarewa da sanin makamar aiki.

Tana nan zaune ya taho shiga office ɗin, kamar kullum cikin mutunta juna suka gaisa dashi, tana matuƙar girmama shi domin yasan mutuncin ma'aikata haka kuma ya riƙe nashi mutuncin, manager kenan HAISAM ƘADEER, babban makusanci ga CEO ɗin su da alama dan shi kaɗai ne bashi da wani shamaki na shiga office ɗin sa a duk wadda yaso.

Alarm ɗin da ya shaida mata lokacin meeting ɗin da zasu yi yayi yasa ta miƙe ta tafi duba tsaruwar wajen, komai yayi yadda ya kamata se gabatar wa kawai, komawa tayi ta sake daidaita nutsuwar ta sannan tayi knocking a ƙofar, sakanni kaɗan aka bata umarnin shiga, kanta a ƙasa ta shiga

"Its time for the meeting with Al-azhar group of companies sir".

Takardun kan tables ɗin sa ya tura mata ta ƙarasa ta shiga tattara su har ta gama shirya su tas sannan ta riƙe a hannun ta ta fice dasu.

Duban sa ya maida kan Haisam dake zaune ba shida ko alamun tashi

"Haven't you heard what she said or you're deaf?".

"Won't mind repeating sir".

Dukan table ɗin yayi da hannun sa cikin nuna ɓacin ran sa da ba wanda ke katarin yawan gani se Haisam ɗin

"For God sake ba wasa nake ba Haisam ka kuma san ba lokacin wasan bane, when it comes to business kafi kowa sanin wane ni dan akan haka zamu samu matsala, babbar matsala wallahi cos I won't mind suspending you".

"Ai fa an taɓo rayuwar ka dole bakin ka ya buɗe, dan rashin mutunci tun ɗazu nake maka magana kamin banza amma yanzu ka cika min kunne da ihu, an ƙi aje meeting ɗin in ka tashi ba suspending ba kayi firing ɗina oga sir, aikin banza kawai".

Haisam ya faɗa yana ficewa daga office ɗin bayan ya doka ƙofar da ƙarfin da har yasa salma ɗan firgita.

Fashionable wrist watch É—in ta ta duba taga its five minutes past exactly lokacin meeting É—in, me yake damun boss yau, shine abinda take tunani, he's always a man of his word and time, Yana mutunta lokaci ta yarda ba'a jiran sa sedai ya jira, wannan principle É—in sa ne.

Buɗewar ƙofar yasa ta gyara tsayuwa ta yi ƙasa da kai, seda ya wuce gaba sannan ta bi bayan sa har zuwa scheduled hall ɗin, kamar yadda tayi zato kuwa kowa ya hallara hatta da manager kuwa se ita dashi ne kawai.

Wajen zaman su suka ƙarasa ya zauna ita kuma ta ajiye kayan hannun ta ta gaida mutanen wajen ta shiga gabatar da bayanan da ya kamata ta wajen ta har ta gama tsaf kafin ta zauna ana tafa mata manager ya miƙe yayi nashi ƙarin bayanin da su kaɗai suka gamsar da mutanen siyan share a Company ɗin so shi bece komai ba se negotiation kaeai da aka yi dashi.

Ya daɗe yana respecting yarinyar dan ta san ta kan aikin ta uwa uba tana da kaifin tuanni ga basira ga kuma kamewa ba kamar sauran mata da ya dinga ɗauka kan post ɗin ta ba da ko daɗe wa ba sayi yake sallamar su saboda halayyar akuyancin da suke yi......................✍🏻.

©️ Ouummey 📚✍🏻.

☑️Ote, Comment and share fisabilillah.

Ouummey 07 [ 11/30/2022 3:18 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★

_*PAID BOOK*_

Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.

From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.

FREE PAGE 007

________________________📖 Seda ta tabbatar an gyara an kuma rufe hall ɗin sannan ta koma bakin aikin ta.

Haka ta wuni aiki kamar yadda ta saba se in ta samu ɗan lokaci ta huta se kuma ta ɗora, ƙarfe biyu lokacin sallah yayi dan haka ta ajiye ta wuce cike da tunanin dawowa ta gyara wajen da tayi mistake.

Ana idar da sallah cikin babban masallacin Company ɗin da suke sallah ta miƙe bayan ta idar da azkhar ɗin ta ta nufi komawa ta steps Wanda haka kawai taji tana son bi ta nan dan ta motsa jiki.

A step na kusan Ashirin da something suka yi bumping into each other batare da sun lura ba, baya tayi zata gangara ya yi maza yasa hannu ya tallafe ƙugun ta yayinda itama cikin firgicin tasa hannun ta ɗaya ta riƙe rigar sa ta wajen ƙirji ɗayan kuma ta zagaye wuyan sa dashi.

Se da tayi regaining balance ya sake ta sannan ta lura da abinda tayi, da sauri ta zare hannun jikin ta na ɗaukar rawa, raɓawa yayi ta gefen ta ya wuce yana adjusting rigar sa da ta cukurkuɗa masa.

Ranar har suka tashi aiki by 4 kamar yadda suka saba she wasn't herself tana dai daurewa ne kawai.

Seda ta biya ta makarantar su Ibty ta É—ebe su dan four thirty ake tashin su kasancewar boko haÉ—e da Islamic school sannan suka wuce gida.

Ta daɗe kwance kan katifar su kafin tayi ƙarfin halin miƙewa ta dafa musu ruwan wanka ta musu itama tayi sannan ta dafa musu spaghetti Dan tana da soyayyar miya.

Ranar kasa gane kanta tayi dan gaba ɗaya jikin ta ya rikice kasancewar wannan karo na farko da ta taɓa samun close intimation da namiji babba kamar haka, a duk rayuwar ta tsakanin ta da maza baya baya ne ma'ana daga nesa nesa se gashi yau itace ɗare ɗare kan ƙirjin wani baligi hannun sa a cikin jikin ta.

Duk da it was an accident amma se take jin ta wani guilty, kamar wata me laifi ko wadda ta aikata wani gagarumin laifi.

Da ƙyar ta yaƙi tunanin ta shiga rayuwar ta kamar ko yaushe, ka shegari bata bari sun makara ba da wuri ta miƙa su school ita kuma ta wuce.

Tun daga bakin gate ta lura da wani irin kallo da security ɗin ke bin ta dashi kamar wata mai laifi ko kuwa irin kallon kin shiga ukun nan, sosai ƙirjin ta ke bugu ta dai daure ta shiga ƙara sawa kaina building, ko a nan ɗin ma bata canja zabi ba haka mazan wajen ke mata kallon kamar munafuka ko me fuska biyu matan kuma na mata kallon an ji kunya.

Jiki a sanyaye ta ƙarasa office ɗin sa ta gyara abinda ya kamata itace zata gyara ta gama ta koma nata, a irin kallon da mutanen Company ɗin ke mata yau se taji sam ba zata ko iya sarrafa jikin ta wajen yin wani aiki ba har se taji ba'a sin kallon hakan ya sa ta zauna jiran CEO ko manager taji gagarumin laifin da ta aikata.
Chapter 10 · 0% Book details