← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 17

Sashe 14

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ɗan firgice ta buɗe idon ta da ke lumshe hakan yasa suka yi wani walai kafin suka shige cikin nasa da ya tsare ta dasu, da sauri ya kau da kan sa dan jin wani dam da gaban sa yayi ganin ƙwayar idon ta, be taɓa sanin haka ƙwayar idon ta take ba se yau,

"Kina jira a É—auke ki ne kafin ki fito?".

Tsam tayi jin abinda ya faÉ—a dan bata gane me yake nufi ba

"Malama ki fito mu yi abinda ya kawo mu dan ba kwana zamu yi ba kin sani ko?".

Ƙafarta dake ajiye gaban motar ta ɗaga a hankali ta fitar waje kafin ta fara ƙoƙarin fitar da gangar jikin ta hakan yasa aya matsa daga tsayuwar da yayi jikin motar, seda ta gyara mayafin kanta sannan ta yi gaba shi kuma ya kulle motar da mukulli bayan ya buɗe glass ɗin baya kaɗan saboda su Ibty dake kwance suna bacci.

Gaba ɗaya ido mutanen wajen suka zuba mata suna kallo yayinda ƙananan maganganu ke tashi dan jiya da yawa da suka san abinda ya faru da ita da suka ji batun ɗaurin auren ta ba ƙaramin tu'ajjabi suka yi ba barin ma da suka ga zuƙeƙen mijin da Allah ya bata.

Yanzu kuwa ba wai sun gane ta bane maganganun kan irin kyan ta da kuma na kayan jikin ta ne, Æ´an gayu irin ta dasu Haisam ba kasafai suke shigowa garin ba shiyasa duk sanda suka shigo suke zama abin kallo da sha'awa ga jama'ar garin.

A hankali ta saluɓe brown heel shoe ɗin dake ƙafarta ta kai zaune kan shimfiɗar fadar maigari kafin cikin sanyayyar Muryar ta ta shiga gaida shi kamar yadda suke yi a al'adance.

Cikin rawar jiki maigari ya amsa duk da bai shaida cewa Salame bace, a tunanin sa wata ce daga dangin su É—an birni suka zo da ita tare maybe dan taga mahaifar matar da ya aura ko wani abu.

"Ala gafarta malam, ga Salman nan gaban ka mun zo da ita dan kayi mata bayanin yadda auren ya ƙullu jiya a kuma bata sadakin ta dan ta shaida".

"Ikon Allah, yaro kana nufin nan Salame ce a gabana, lallai Allah mai iko, sannu Salame, sannu kinji".

Maigari ya faɗa cikin ruɗewar jin wai wannan tsaleliyar budurwar ce Salame da suka kora da goyon ƴaƴa biyu shekara biyar da suka gabata, yarinyar da ko da ta bar garin ba komai gare ta se tarin tsumma dan hatta takalmi babu a ƙafarta ranar.

"Nice baba maigari, fatan mun same ku lafiya".

"Lafiya lau salamatu, ya yaran naki? Ko kin bar su a gida ne?".

"A'a baba suna mota bacci suka yi shiyasa ba'a É—auko su ba".

"Allah Sarkin hikima, yanzu sun girma abin su ko, hekara biyar ai ba nan bace dole yanzu sun girma".

"Aikuwa dai". Ta faɗa tare da jan bakin ta ta tsuke ganin surutun na maigari bame ƙare wa bane ita kuma ta zaƙu taji bayanin da aka ce yayi mata da in ba kunnuwan ta ne basu jiyo daidai ba kamar taji ana batun an ɗaura mata aure ne tun jiya

"Wato salamatu jiya yaran nan suka zo nan suka same Ni da batun neman auren ki, duk da ko a Shari'a ni me bayar da auren ki ne amma se na bawa iyayen ki haƙƙin su ta hanyar sawa a ka kira su na shaida musu abinda ke shirin aukuwa sedai dake Habibu ba ɗan bana da arziƙi bane se yace shi sam babu shi a lamarin ki haka ma iro, se Adamu ne shi dake wani sa'in yana da tunani ya saurari yaran nan amma yace sedai in a ɗaura auren a jiyan dan baze juri a Kuma tado shi daga wajen sana'ar sa domin ki ba wannan yasa dole aka ɗaura auren bisa sadakin da shi mijin ki ya biya wato dubu hamsin gashi nan a zaune, yanzu bari in tashi in ɗauko su gare ki, kin ji yadda batun ya kasance".

Wani irin suya zuciyar ta ta shiga yi cikin ƙirjin ta jin irin cin kashin da ƴan uwan mahaifin ta suka aikata yayin neman auren ta, shin me ta kashewa mutanen nan ne da suke neman se sun wulaƙanta ta ido rufe?, Shin akwai ɓoyayyen dabi ne tsakanin mahaifin ta dasu ko kuwa, su dai ba ƴan uba ba balle tace ƴan ubanci suke gwada mata, ko kuwa duk ƙiyayyar mahaifiyar ta ce ta shafe ta har haka.

Hannu tasa ta goge hawayen da suka gangaro kan kuncin ta daidai lokacin da maigari ya miƙawa Abu Aulad sadakin ta shikuma ya ajiye mata kan cinyar ta, murya na rawa ta shiga magana

"Nagode sosai baba, Allah ya saka da alkhairi ya ƙara girma sedai Ina son ganin su baba habibun game da gado na dake wajen su".

"Babu komai salamatu, ke ɗin ai ɗiya ce gare ni, abinda ya faru a baya ma saɓanin fahimta da kuma zugar iyayen ki ne, yanzu bari in aika su zo se ayi batun gadon naki".

Ɗaya daga cikin dogaran sa ya aika azo dasu baba Habibu dukan su, ba'a jima ba dogarin ya dawo tare dasu suna bin shi abaya se ƙunƙuni suke na yadda ake shiga rayuwar su kan wata banza can Salame da suka daɗe da tsamewa matsayin jinin su.

Gaban maigari suka zube suka yi gaisuwa, salma ya nuna musu bayan ya amsa ya shiga kora musu bayani

"Ga Salame nan mijin ta ya kawo ta na mata bayanin auren su da aka É—aura jiya se kuma gashi tazo da batun gadon ta dake hannun ku tana neman a bata kason ta".

Maigari ya ƙarashe yana gyara saɓa hannun babbar rigar jikin sa tare da furzar da tiƙar goran dake bakin sa, ido waje baba Habibu da ƴan uwan sa ke kallon tsaleliyar budurwar da aka nuna musu wai Salame, cikin rashin yarda baba Habibu ya furta sunan ta

"Salame".

"Na'am baba barka da rana".

Ta faɗa tana buɗe idanun ta sosai a kan su dan su san fa yanzu ba da bane da take shakka da tsoran su, cikin sanyin jiki baba iro yai gyara zama dan ƙwayar idon ta kawai ya kalla ya shaida ita ce.

"Dama nace gadon baba na dake hannun ku nake buƙata baba dan Ina son yin amfani dashi".

"Eh to, gado ko, tabbas kam kamisu ya bar gado sedai yana wajen Adamu ai bani ba".

Da sauri baba Adamu da yaji baba Habibu na neman zame wa ya bar shi a ciki ya buÉ—e baki

"Ina ce gona ce kawai a wajena Habibu?".

"Ai dama ita nake nufi, am ke Salame sedai fa kiyi haƙuri dan kiwon da ya bari tuni babu su, da su ne mukai ta amfani wajen ciyar dake har zuwa lokacin da kika bar wajen mu dan haka gona dai tana nan ban da ita kuma babu komai". Ya faɗa yana kai da kai gefe cikin rashin gaskiya.

Girgiza kai akwai tayi dan tasan ba wani an ciyar da ita an cinye ne kawai babu su yanzu, gonar ma tasan ban da albarkacin yanayin da ya ganta na wadata da kuma waÉ—anda ke tare da ita da baze bayar ba itama cewa ze yi an siyar an kula da ita.

"Allah ya amfana gonar, sedai ina da buƙatar ta ujila zan yi amfani da ita".

"Amma ina ce kinji ance tana hannun Adamu, shima amfani yake da ita dan haka sedai kiyi haƙuri, gona na mazaunin taki amma ya riga yayi shuka dan haka se yayi girbi se ki karɓa".

Cikin rashin tsoro ko shakka ta dubi baba Habibu dake maganar cikin hatsari da gadara

"Zan bar tane sabida a hannun baba Adamu take banda haka bana jin da wani ne ba shuka ba kome yayi se dai ya kwashe ya kai inda yake dashi tun da dai gona mallaki nace".

Daga baba Habibu har baba iro tsumu suka yi cikin kunya dan sun san da su take, wato da ba Adamu bane dole a bata a bar ta, lallai yarinyar nan ta goge.

Abu Aulad da yaji an kawo matsaya ya miƙe dan tuni yake kallon agogon hannun sa, baya san suyi dare kamar jiya dan a tsarin sa a yau yake son ta tare a gidan su dan ya nuna wa duk wani dake tunanin ce iya juya shi ko iko dashi ƙarya yake, be isa ba kuma be kai ba, anyi a da amma banda yanzu!.

"Mungode sosai, ga wannan a siya horo, Allah ya ƙara girma, ku tashi ku tafi ko?".

Ya faɗa yana ajiye wa maigari bundle ɗin ɗari bibbiyu, miƙewa tayi tana adjusting pin ɗin mayafin ta da taji ya ɗan matse ta, har bakin mota maigari ya raka su inda su baba Habibu suka zama ƴan kallo, Haisam ne ma yayi tunanin basu ƴan canjika dan shi uban gayya ko kallo biyu basu samu daga gare shi ba.

Tun jiya mutuncin su ya zube tsaf a idanun sa saboda abinda suka yi, me É—an daman cikin su ne baba Adamu dan shine kawai ya samu gaisuwa daga gare shi.

Haisam na buɗe bayan motar Ibty ta fito tana mutsittsika ido tare da tura baki gaba cikin son fashewa da kukan rashin ganin Mamman ta, da sauri Salma ta riƙo hannun ta tare da jawo ta gaban ta.

Duƙawa tayi zuwa tsayin yarinyar ta cire mata hannun ta dake kan fuskar ta, ɗaga mata gira tayi tare da jan kumatunta tana sakin mata murmushi itama yarinyar ta maida mata sannan ta shige jikin ta tana sakin ajiyar zuciya, seda ta tabbatar ta dawo daidai sannan ta kama hannun ta ta buɗe gaban motar zata shiga baba maigari dake kallon su ya magantu

"Masha Allah, tubarkallah, hala wannan É—aya daga cikin yaran ne salamatu?".

"Eh baba, Hassana ce Ussaina na bacci bata tashi ba".

"Allah Sarkin hikima da buwaya, tubarkallah yarinya kyakkyawa kamar Æ´ar turawa, Allah ya raya yayi musu Albarka, Allahu Akbar da girma yake".

Da Ameen ta amsa masa tare da shigewa motar dan shima tasan borin kunya ne ya ke yi na abinda yayi mata lokacin da tafi buƙatar taimakon su shiyasa duk wani rawar ƙafar sa be ɗaɗata da ƙasa ba.
Chapter 14 · 0% Book details