← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 17

Sashe 16

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ta koma part ɗin nasu tana cizon yatsa, taso taji me waccan karuwar ke faɗa masa wanda har ya tsaya saurara haka sedai kash bata samu ji ba, ya zama dole ta tunzura Hajiya Babba ayi ayi ai bikin su ko hankalin ta ya kwanta, daga lokacin da ta sami wannan damar a lokacin ita kanta Hajiya babbar zata raina kanta dan kallon ta kawai take itama da tata tsarin da buƙatar akan Abdallah ɗin.

A hankali yake rage kayan jikin sa cike da gajiya, wanka yake buƙata yake kusan sanyi dan yadda yake jin jikin sa na ƙaiƙayi shine kawai abinda se yi yaji sauƙi.

Singlet ɗin jikin sa yake ƙoƙarin cirewa se kuma ya fasa sanadin hango inuwa da yayi jikin labulen sa alamun akwai wani laɓe a ta wajen.

Cikin nutsuwa ya shiga takawa har ya kai wajen yasa hannu ya yaye curtains É—in da suka rufe tagar, tsaye take cikin shaiÉ—anun kayan da dasu da babu a jikin ta basu da wani banbanci, suna haÉ—a ido ta sake masa wani arnen murmushi cike da barikanci kafin cikin kwarkwasa ta shiga lauya jikin ta tana magana da wata seducive voice

"Sannu da zuwa Abu Aulad, ga dukkan alamu ka gaji, don't mind I can takeaway all your stresses, yanzu dai muje kayi wanka ko super man?".

Kamarw anda garwashin wuta ya taɓa haka yayi watsi da hannun da takai jikin sa, ya rabbal alameen be san ya zai yi da rayuwar sa a cikin wannan gidan da a wajen sa gara kabari dashi ba.

Wani irin birkitaccen mafi ya watsa mata da yasa ta yin katantanwa ta faɗi can gefe kanta ya bugu da jikin Centre table ɗin dake falon, cikin wata irin zuciya da ta ciwo shi ya bita yasa ƙafa ta taka sangalalin hannun ta har se da yayi ƙarar dake shaida alamar in har bata sami fracture ba to tabbas ƙashin nan ya fita daga bigiren sa.

Wani wahalallen ihu ta saki da be wani fita da karfi ba saboda tsabar wahala yasa a take Muryar ta ya shaƙe, cikin wani dakusasshen Muryar da ɓacin rai ya haifar masa ya shiga yi mata concrete warning

"This is the first and last time da zan kuma ganin ki a part ɗina, na rantse da Ubangijin da ya busa min rai da second time na kuma ganin ki zan iya ɗaukar ranki dan ko banza an rage mugun iri, annoba kuma jinin shaiɗan, before the count of three ki fice min ɗaga ɗaki in ba haka ba wallahi rataye kibzan yi jikin fanka, fitsararriyar fasiƙa kawai mara kunya da tsoron Allah".

Ai ko kafin ya gama bayanin sa tuni ta tarkata hannun ta tayi waje da mugun sauri dan a yadda ta gan shi da kuma rashin imanin da ya gwada mata ta tabbatar ze iya rataye tan kamar yadda ya faÉ—a.

Da numfarfashi da komai takai kanta part ɗin ta zube kan kujera tana maida numfashi, wani irin zufa ne ke keto mata na wahala da azabar da take sha a jikin ta, bata taɓa sanin haka zafin karaya yake ba se yau.

Ƙwalla take zubar wa tana bin hannun da kallo yayinda cikin ranta take shan mugayen alwashi kala kala a kan shi, tun da ta riga ta ɗora ido a kan shi takuma kwaɗaitu da shi ta rantse ita kuma se ta same shi, in kuwa ba haka ba to tabbas sedai ayi biyu babu uku ba ko ɗaya ma'ana indai ba zata same shi b ato sedai kowace mace ta rasa.

Da sauri ta runtse idon ta lokacin da ta auno shi a idanun ta tare da wata mace, inaaa, ba'a haifi macen da zata amfane shi ba, ada dai tayi wannan imanin amma a yanzu zata iya yin komai in tace komai tana nufin komai wajen ganin ta saka kyakkyawar barrier tsakanin sa da duk wata Æ´a mace kowace ita kuwa.

Ranar haka ta kwanan cikin azaba da raÉ—aÉ—in zuci da na jiki, ga dai jinya ya kwantar da ita kuma wai batare da ya bari ta amfanu da komai daga gare shi ba, ita da ta samu abinda taje nema to da sauki ba karya ta ba ko kashe ta yayi ba zata damu ba tunda ta cika burin ta.

A ɓangaren Abu Aulad ma haka ya kwana a zaune cikin wani irin yanayin da baze fassaru ba, be san da wane suna ze Kira gidan da yake ciki ba haka be san da wane suna ze kirayi mutanen cikin sa ba, be taɓa sanin bawa kan zaɓi mutuwa kan rayuwar sa ba se a kan shi, da ace kisan kai ba haram bane a musulunci da tuni ya daɗe da sheƙe kan sa ya huta.

Tun tasowar sa be san wani abu wai shi farin ciki ba, kullum cikin baƙin ciki da damuwa yake tun fara wayo sa har kawo yanzu da yake shekarun sa na cikakken namiji mai ji da sabon jini da ƙuruciya.

Rayuwar sa a hagunce ta faro kuma har kawo yanzu a haka take, be san se yaushe ne ze samu daidaito na rai, ruhi da rayuwa ba balle har ya samu salama, a duk sanda yaga mutane na rayuwa suna dariya da nishaɗi ya kan tsinci kansa da ayyana dama shine, so da yawa yasha kusan yin saɓo in ya zauna tunani dan ya kan dinga aiyana me yayi wa Allah da yasa ƙaddarar jarabawar tazo a haka, me yasa ba wata daban ba.

Kiran sallar asuba da ake yi ne yasa shi miƙewa yana dafe kan sa dake sara masa ya shiga toilet, daga tsayen da yake ya sakarwa kansa ruwa masu sanyi sanye da wandon shaddar da singlet ɗin batare da ya cire ba, tsayin lokaci Sannan ya gabatar da wanka ya ɗaura alwala ya fito.

Jallabiya ya zura a jikin sa tare da É—aukar tasbah É—in sa ya wuce masallaci, seda aka idar da sallah har gari yayi haske kafin ya taho gida.

Jiri yake gani dan rabon shi da abinci tun na safen jiya kafin su tafi ƙauye ga kuma rashin bacci sedai kasancewar tsayayyen namiji ba wanda ze fahimci hakan se wanda yayi masa sani na sosai.

Wata jallabiyar ya canja kawai ya É—au key É—in motar sa zuwa gidan su, É—auko ta ze yi dan se yayi hakan hankalin sa ne kwnata, mutanen gidan su are so cunning, gwara tun kafin su farga yayi outsmarting É—in su ya shayar dasu mamaki ya kuma basu tsoro ba kuma ta kowace hanya ba se ta kawo macen da ya nema wa kan sa auren ta cikin gidan.

Ya sani in da mace a tare dashi abubuwa da yawa zasu masa sauƙi sedai matsalar shine shin itama irin su ce, wane assurance yake dashi na ba zata zama kamar su ba, shin in aka mata tayi da zunzurutun kudi ko matsayi zata karɓa ko kuwa?!.

Wannan sune tarin abubuwan da tuntuni suke hana shi aure sedai a yanzu da yayi ba wai ze saki jiki da ita bane, hasalima auren su na da wa'adin da ya É—ibar masa wanda yana cika ze sauta, zaman sa shi kaÉ—ai ya fiye masa dan be yarda da kowa ba baya kuma jin ze yarda É—in.

Yaro ya samu ya aika gidan, tana cikin sawa Ifty rigar school ta jiyo Muryar yaron na faÉ—in aiken da aka turo shi

"Wai salma ta fito inji Abdallah".

Sedai rigar ta kubce ta faɗi daga hannun ta saboda yadda zuciyar ta ta doka da jin sunan sa, hannun ta na rawa ta sake ɗaukar rigar ta shiga kici kicin sa mata sedai ta kasa saboda ruɗewar da tayi, Hajiya ce ta amsawa yaron da gata nan fitowa saboda jiya ta zauna tayi mata bayanin komai dan kamar mahaifiyar haka ta ɗauki Hajiya saboda ba ƙaramin taimako tayi mata ba a rayuwar ta.

Ɗakin Hajiya ta shigo ta karɓi shirya Ifty dan tuni ta gana da Ibty

"Je ki bashi uzuri daga nan ki nemo yara su fara fitar miki da jakunkunan, in an kwana biyu insha Allah zan zo in ga mazaunin ki, tashi kije".

Jiki ba laka ta fita, zaune cikin motar ta same shi ƙafar sa duka biyu a waje ya lumshe idanun sa tare da jingina kan sa da makarin kujerar, seda ta tattaro duk dauriyar dake gare ta kafin ta iya gaida shi

"Barkada safiya".

Saukar Muryar ta yasa ya buɗe idon sa, kallo ɗaya yayi mata ya kau da kai tare da maida ƙafafun sa cikin motar ya fara ƙoƙarin kunna ta

"Kayi haƙuri Ban ƙara sa shirya Ifty ba amma yanzun nan zamu ƙarasa, Bari in Sami yaro ya fitar min da jakunkunan".

Fasa kunna motar yayi ya koma ya kwanta kamar ɗazu ita kuma ta matsa ta sami wani almajiri suka koma ciki tare, ko da ta shiga tuni Hajiya ta gama shirya Ifty tare da haɗa musu launch box ɗin su, manyan jakunkunan kayan su dake shaƙe ta fara jawowa tana fitarwa tsakar gida almajirin na fita dasu har suka gama, kallon ɗakin take cike da matsanancin kewar sa da zata yi kafin kuma ta maida kallon ta kan Hajiya, matar da tayi mata halaccin da har abada ba zata manta ba, a rayuwa da ita da bana Husaila sun mata abinda in har ta manta to ita ɗin butulu ce cikakiya.

Nasiha sosai Hajiya ta yi mata da har tasa ta kuka ba dan komai ba se dan kewar mahaifiyar ta da kakarta da ta taso mata, ta sani da suna nan su zasu yi mata wannan nasihar.

Haka Hajiya ta rakata har mota, ko da suka je tuni ya zuba jakunkunan a booth É—in motar sa ita kawai yake jira.

Duk yadda yake moody be san lokacin da ya saki fuska ba da Ifty ta ƙarasa tana ɗane shi Ibty kuma na gaida shi, haka ya ɗauke su duk biyu ya riƙe yana kallon su cike da shauƙi yana sauraren shirmensu har Hajiya ta gama mata nasihar da zata yi suka idasa bakin motar, har ƙasa ya tsugunna ya gaida Hajiya abinda yayi salma matuƙar daɗi a rai.
Chapter 16 · 0% Book details