← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 17

Sashe 4

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiye ta tayi inda yarinyar ta shiga cilla ƙafafu tana wasa da hannayen ta, ƴar uwar ta ta ɗauka itama ta tashe ta tare da bata kunun, itama ta sha da ɗan yawa duk da be kai yawan na ɗayar ba, ajiye ta ta ƙara ɗaya na biyar ɗin kan wanda suka rage ta ƙara sugar ta shiga sha itama dan ta san yau kam ko itace tafi kowa maita ba zata samu abinci ba a gidan nan, da ɗan dama ta rage saboda kar yaran su ji yunwa su nema kuma babu, jakar ta ta ɗora ta rufe cup ɗin dashi sannan ta juya ga yaran ta ƙure su da kallo.

Kyawawan yara ne Masha Allah kamar ƴaƴan turawa, ba ramammu bane dan da ƙibar su daidai sanye da kayan masu kyau suma kansu an kakkama da soso da ya daɗa ƙara musu kyau, addu'a ta shiga yi musu tana tofa masu na Mayu da baki dan akwai Mayu sosai a ƙauyen.

Seda ta gama yi musu addu'a sannan tayi wa kanta ta nemi waje kan buhun ta ta kwanta dan zannuwan ta biyu ta haÉ—a ta shimfiÉ—a wa yaran da har yau bata san sunan su ba dan maman su bata faÉ—a mata ba ita kuma bata san da sunan da zata kira su ba.

Washegari kuwa tun kiran sallar biyu da ta tashi bata koma ba, tana idar da sallah ta fita tsakar gidan su ta hau aikace aikace kamar yadda ya zame mata wajibi muddin tana garin, tana gama wa ta ɗau bokitan su ta fita rijiya ta shiga jido ruwa, se da ta cika ko ina kafin ta hau kunna ruwan komo, tana juye kokon ta kai duban ta kan ƙofar su Inna mariya dake kulle har lokacin, da sauri da sauri ta dafa ruwan zafi ta kai ɗakin ta ta ɓoye cikin wata madaidaiciyar roba sannan ta dawo wajen ta kashe wutar.

ÆŠakin ta ta koma ta surka ruwan a bokitin ta ta shiga yiwa yaran wanka, wankan jariri ba sabon abu bane dan tun tana shekara bakwai aka fara bata rainon yara haka kuma tana shekara sha biyu suka fara sa ta wankan jariran su, tana gamawa Hassana kamar yadda ta raÉ—a wa wadda taga tafi girma a idon ta ta É—au Ussaina ta mata ita ma sannan ta É—au ruwan nasu ta shiga banÉ—akin su ta kwarawa jikin ta ta maza ta fita tare da maida bokitin ta bayan É—aki.

Ko da ta koma tuni yaran sun koma bacci da alama sun ji daɗin wankan, murmushi tayi tana jan kumatun Ussaina daidai lokacin da taji Muryar kawu habibu cikin ihun kiran sunan ta.......................✍🏻.

©️ Ouummey 📚✍🏻.

☑️Ote, Comment, share and patronize fisabilillah.

Ouummey 03 [ 10/12/2022 12:08 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★

_*PAID BOOK*_

Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.

From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.

                      FREE PAGE 003

_________________________📖 A gigice ta Fito daga ɗakin har tana yin karo da durƙusasshen bangon ɗakin wanda banda tsari da kariyar Ubangiji wata iska me ƙarfi nan in aka yi ze zube ne.

A firgice ta ja baya tare da maƙewa jikin garun ganin dukkan su mazan gidan ne a wajen wanda tasan ba dan kowa suka haɗun ba se dan ita.

Wani irin rawa jikin ta ya ɗauka haka ma zuciyar ta ta shiga addu'ar Allah ya taimake ta kar su ƙara mata wani ciwo da nauyin jikin da sabon dukan da ta san in ba Allahn ne ya tare ba se ta sha shi.

"Shegiya munafuka me suffar muminai, tana sussunkwi da kai tana baɗala a haka kuma take cutar wasu suke mata kallon saliha ta gari se gashi ƴaƴan namu dai da ake zagin sune nagarin, kin matso kusa ko se na harbo ki da ƙafa ta, tambaɗaɗɗiya kawai".

Da sauri ta matsa dan ta san kaɗan kenan daga aikin baba iro ya harba tan kamar yadda yace, ƙasa ta sa gwiwoyin ta tare da kai kanta ƙasa abinda su kuma suka fi tsana kenan dan sunce hakan wani salo ne na munafurci.

"Me zata zauna tayi mana a nan iro, kawai taje ta kwaso ƴaƴan shegun nata mu wuce wajen megari dan wallahi ji nake kamar in watsa a turmi in dake shegu ita kuma uwar in shaƙe ta har se ta mutu".

Baba habibu ya faɗa da iya gaskiyar sa yana demonstrating da hannayen sa, ita dai tana duƙe har lokacin dan ba'a ce ta tafin ba shawara ce suke yi a tsakanin su.

Uban dundu Inna mariya ta É—uma mata ta kuma bita da zagi

"Ka ga min fitsararriyar da ba zata rama ragon sunan ta ba, wato ga sa'annin matacciyar uwar ki na magana shiyasa kika zauna kina kallon mu, to bari in kwaso shegun yaran in watsa a masai muga ta tsiya".

Ai kafin inna ta gama rufe bakin ta tuni ta ɗiba tayi ɗakin a guje jin za'a watsa mata su a masai, Hassana ta riƙe a hannu yayinda ta goya Ussaina dan ta fahimci Hassanar tafi haƙuri dan bata fiya kuka ba se in Ussaina nayi ta kama.

A saɗaɗe ta fito dasu wannan karon kanta a daidai tana bin su da kallo har ta kai gaban su ta sake tsugunnnawa, a yanzu kam Inna A'i da kallon da take bin su dashi ya ɓata wa rai itace ta kai mata duka a fuska, ba wai mari ba dan ba kuncin ta ta nufa ba kuma ta na sane ta kuma same ta a idon ta na dama, duk yadda idon ya ɗau raɗaɗi bata ko motsa hannun ta da niyyar taɓa wa ba.

Ta daɗe da sanin idanun ta na ɗaya daga cikin abubuwan dake jawo mata tsana, kyara da tsangwama a cikin gidan, wato wani irin ido Allah ya halitta mata me kamar na maciji ko mage za'a ce, dan ƙwayar idon ta ba baƙa bace haka ma ba brown ba, wata color so similar to golden, sedai golden ɗin irin me ɗan duhu kaɗan.

So da yawa su kawu, matan su ko Æ´aÆ´an su sun sha goranta mata yanayin idanun nata duk tayi laifi, kai koma bata yi ba indai zasu haÉ—a ido se sun tanka mata, shiyasa tun lokacin da malamin Islamic studies É—in su yayi musu addu'o'i ciki har da na baki shikenan ta ke yi, la haula kuwa kowane dare se tayi adadin da bata sani ba dan ba carbi ne da ita ba ta shafa a fuskar ta kafin ta kwanta haka kuma da asuba in ta tashi.

Bata san a wajen wa ta gado irin wannan idon ba cikin iyayen ta dan bata yi wayo da ko ɗaya ba sedai da alama ba wajen babanta da yake ƙanin baba Habibu da baba Adamu wa ga baba iro ba ne, tafi kyautata zaton wajen mahaifiyar ta ta gado ko kuwa dai Allah ne yayi mata nata halittan daban, ko a makaranta seda hakan yaso ya zame mata barazana dan har se da shugaban makarantar ta tsawatar tukunna shiyasa har tayi ta gama bata da wasu cikakkun ƙawaye sedai na gaisuwar mutunci, kowa gudu da tsoran ta yake saboda kalar idon ta da ba'a saba gani ba cikin jama'a, tun bata saba da hakan ba har ya zo ya zame mata jiki ba ta ma damuwa.

Zama suka yiyyi kan tabarmin da ke shimfiɗe a fadar me gari kafin suka shiga kai gaisuwa shikuma dattijon dake amsa sunan maigari na zaune kan kujerar ƙarfe kan sa ɗaure da rawani yana amsa musu.

Kafin kace me jama'a sun fara ciki dan haka ake wa duk Æ´aÆ´an da suka yi ciki a garin amma fa marasa galihu dan da Allah yasa Æ´ar maigarin tayi shiru kake ji wai maye yaci shirwa, karuÉ—uf Æ´ar magulmaciya tayi ciki, ba wanda yasan da zancen seda faÉ—an kishiyoyi ya haÉ—a shima kuma har rana wata yau ba'a yi irin wannan zaman a kanta ba gashi har ta haife tuni.

Seda fadar ta gama cika sannan maigari ya fara sanar da abinda ya tara su wato dai batun cikin da Salame tayi ta haife batare da sanin su ba har gashi ƴaƴa sun kusa rufa watanni uku, hayaniya ce ta shiga tashi inda mutane da yawa ke Allah wadai da ita yayinda ƙalilan da abun ya faru kan ƴaƴan su suma suka shiga yi mata fatan Allah ya shirya a ganin su ai hakan ƙaddara ce (saboda ya faru ga nasu).

Se da gurin ya lafa kafin maigari ya shiga jawabin sa kamar yadda ya saba

"Bisa ga tsari na wannan gari bamu yadda da abun kunya ba ko yaya yake kuwa dan haka zamu aiwatar da abinda muka saba yi duk sanda aka samu irin wannan san zuciyar, a yanzu haka zamu karɓi ƴaƴan a kai su can nesa inda ba wanda ze san nata ne balle ayi mana gori kamar yadda muka saba tun da wannan shine karon ta na farko, da na biyu ne kuwa ko sama da haka to fa kun san hukuncin kora ne a kanta".

Yana gama faɗar haka wasu fadawan sa suka nufo ta da zummar amsar yaran inda ita kuma cikin matsanancin firgici da tashin hankalin jin abinda ake kiran ze faru ta sake ƙanƙame ƴaƴan ta ta shiga kurma ihun ba ta yadda ba ba zata bayar dasu ba, kowa a gurin ya shiga mamakin abinda tayi, a ganin su ƴaƴan shegen take ihu dan za'a raba ta dasu, to meye abin so cikin ɗan shege?!.
Chapter 4 · 0% Book details