Sashe 5
Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Muryar Salame da fiye da rabin ƙauyen zasu ce basu taɓa ji ba se gata ana jiyo ta tun daga farkon hayin maigari saboda yadda take ihun da iya ƙarfin Muryar da Allah ya bata, duk irin tsawa da zagin da babannin ta ke mata bata ma san suna yi ba balle ta saurare su ta daina ihun har se da maigari yasa fadawan su janye daga kusa da ita kafin tayi shiru ta sake matse ƴaƴan tana sauke numfashi sedai sam hankalin ta be kwanta ba dan tasan ba wai an ƙyale ta bane.
Seda megari ya gama ƙare wa jama'ar wajen kallo kafin ya muskuta yana zarar ido
"Tun da har wannan yarinya taƙi yadda da hukuncin mu to mun bata zaɓi biyu kuma a yanzu a nan gurin zata bayyana mana wanne ta ɗauka, na ɗaya ko dai ta bada yaran nan ayi kamar yadda aka saba dasu ko kuwa na biyu ta tattara ta bar mana garin ma'ana mun kore ta daga ita har ƴaƴan haka kuma duk sanda muka sami labarin shigowar ta to tabbas hukunci mai tsananin tsauri ya hau kanta, wannan sune zaɓin".
Shiru kowa yayi kallo ya koma kan Salame da take jin komai da aka faɗa haka kuma ba tare da second thought na halin da ita ko yaran zasu shiga ba sanadin zaɓin ta ta buɗe baki ta zaɓi abinda take ganin ya fiye mata
"Ba gari ba ko ƙasa ce zan iya haƙura in bar ta akan ƴaƴana dan haka na zaɓe su akan komai da nake dashi ciki kuwa har da asalina".
Kusan a tare duk su baba Habibu, baba Adamu da baba iro suka miƙe jin abinda ta faɗa, wato ta zaɓi ta bar garin saboda ƴaƴan ta haka ta zaɓe su akan Asalin ta wato su dangin ta kenan.
Shi kan sa maigari ba haka yaso ba dan a tunanin sa zata zaɓi bayar da yaran ne tun da in ta bar nan wa ta kama?, Bata da kowa banda dangin baban ta, mahaifiyar ta kuwa bama ƴar nahiyar bace, a yawon tuƙin babban mota baban ta ya auro ta dan haka ba wanda yasan komai a kanta kamar yadda basu faɗa wa kowa komai game da ita ba har kuwa ranar da ta bar duniya sanadin hauka da aka sa mata da ya kai sedai a ɗaure ta a ɗaki.
Umarni me gari ya bayar kan dogarawa su bita gida ta É—ebi abinda zata É—auka a rakata bakin gari ta tafi sedai fir baba iro yace ba abinda ta aje a sassan sa bare ta koma É—auka dan haka su rakata bakin garin kawai, bata Musa ba ta shiga gaba dogaran na binta a baya dan tun da ta shafa taji jakar makarantar ta na jikin ta hankalin ta ya kwanta.
Seda suka tabbatar tayi nisa da gari kafin suka juya zuwa gidan maigari suka sanar dashi an cika umarnin sa inda ya amsa da cuskunenniyar fuska dan ba haka yaso ba.
Abinda mutanen garin basu sani ba shine maigari siyar da jarirai yake wa ƴan birni da suka rasa haihuwa da kuma masu aikin asiri though be san me suke dasu ba, shidai kawai a bashi kuɗi shikenan, da an samu yarinyar da tayi ciki se ya hana a zubar yace ta haife shi kuma ya sami ƙarin jari.
Lokutan da kuma ba'a samun na banza hatta na sunna kaiwa yake dan akwai ungozomar da suka haɗa kai in ba na shege se a kai na sunna, yadda suke yi kuwa se an gama haihuwa lafiya lafiya se ta shafawa yaron wani magani da ta samo a wata asibiti dan ta taɓa zaman birni shikenan yaro se ya birkice da koke koke, ƙin kama nono da sauran su daga nan se a nufi wajen babban me maganin da suka yadda dashi da dukkan imanin su, dake shima nasu ne se yace ai ɗa ko ƴa na aljanu ne sun ɗauke naki sun musanya miki dan haka maza maza akai daji kaza daidai wuri kaza a ajiye musu kayan su, se an kai an ajiye ita kuma tabi dare ta ɗauka ta kaiwa maigari cikin gidan sa na sirri dake can bayan gari gefen dajika inda yake harƙallar sa.
Guri ta samu ta zauna tana haɗiyar busasshen yawu dan gaba ɗaya bakin ta ya bushe da ƙishirwa, tafiyar ƙafa sabon tace dan haka ba zata ce ta gaji ba sedai rashin ruwan ke neman kassara ta ga kuma ƴaƴa har biyu gaba da baya ga jaka me nayi se abin yayi mata yawa.
Mutsu mutsun Ussaina da taji yasa ta san ta farka dan haka ta sauke ta dan ta É—an huta da goyon sedai ita ba hutun take nema ba abinci take nema da bata samu ba kuwa ta buÉ—e baki ta shiga canyara kuka da Æ´ar Muryar ta na jarirai, kukan Salame ta shiga yi itama dan abin ya haÉ—e mata goma da ashirin.
Haka Ussaina tayi kukan ta har ta gaji baccin yunwa ya ɗauke ta kafin itama ta haƙura ta goge fuskar ta ta maida ta baya dan ba zata iya riƙon hannu ba ta cigaba da tafiya.
Se da rana ta faɗi gaba ɗaya kafin ta shiga wani ƙaramin ƙauye dan gaba ɗaya gidajen dake ciki basu fi a ƙirga ba haka kuma daga ganin gidajen su kasan har yau su kam suna cikin duhun rayuwa wato ba wayewa ko ta misƙala zarratin dan duk bukkoki ne ba gidan ko ƴar jar ƙasa ɗaya.
Kan wani kututturen dabino ta kai zaune tana ajiyar zuciya tare da numfashin ta dake fita ɗaiɗai saboda wahala da jigatuwa, nan take zaune har se da wani tsoho ya zo wucewa ya ankara da ita kafin ya ɗan matsa nesa da ita ya shiga ƙare mata kallo Sannan ya gyaɗa kai ya wuce.
Be daÉ—e ba ya dawo dashi da wasu dattijan da kuma matasa suka dinga magana da Yaren su da bata san wanne bane kafin É—aya daga cikin matasan ya nufi ta.
Tambaye ce daga ina take, me ta shigo nema a shiyyar su, me take buƙata haka dai, amsa ta bashi da sunan garin su wato BA MUNI wanda sunan ya samo asali ne daga yadda duk wani ɗan garin yake kyakkyawa sedai wani yafi wani amma mummuna kam babu sedai ko baƙo shiyasa suke saurin gane baƙo a cikin su.
Iyayen sa ya koma ya sanar da amsar da ta bashi, sunan garin su da kuma taimakon da tace ta zo nema, seda suka kuma sake zantawa cikin dai Yaren nasu kafin wani saurayi ya tafi be daɗe ba ya dawo da wata tsohuwa sedai ba tukuf ba, nuna mata ita suka yi inda ita kuma ta ƙarasa ta kamata ta miƙe kuma cikin fara'a tace mata
"Kunto min jikokin nawa mana, da alamu sun daÉ—e a goye".
Bata ƙi ba ta kunto Hassana ta bata ta bar Ussaina
"Ita ma sauko ta ta huta hakana".
"Tana da kuka ne Inna".
Murmushi innar tayi alamun ta gane kafin suka shiga tafiya hannun ta dafe da zanin ta dan cikin sa ta ɓoye jakar ta da zasu je wajen Maigari ashe Allah ne yayi suna da rabo da yadda kawu iro yace ba zata koma masa gida ba shikenan sun salwanta.
Bukka ce me ɗan girma suka shiga sedai abin mamaki har dasu gadon ƙarfe a cikin ta, fita Inna kamar yadda ta kira tsohuwar tayi bayan ta kwantar da Hussaina tsawon lokaci tukunna ta dawo da bahon katako a hannu, ruwa ne masu zafi a cikin sa haka kuma ba fari bane da alamun an zuba wasu abubuwan banda kuma ganyayyaki dake ciki, tuɓe Hassana tayi ta mata wanka da yasa yarinyar ta ringa sauke ajiyar zuciya a jejjere, Ussaina kam ta sha ihu da ana yi mata dan alamu sun nuna ba su taɓa shiga ruwa masu zafi haka ba.
Se da ta tabbatar sun gasu kafin ta É—au abin ta fice inda Salame ta yi saurin isa ta É—au yarinyar ta shiga jijjiga da lallashi har tayi shiru,
"Ga can ruwa ki je kiyi wanka kema ko kya watsar da gajiya".
"Toh Inna".
Tace tana kwantar da Ussainar a hankali gudun kada ta tashi daga É—an baccin da ya fara sanÉ—ar ta............................âœðŸ».
Â©ï¸ Ouummey 📚âœðŸ».
☑ï¸Ote, Comment, share and patronize fisabilillah.
Ouummey 04 [ 11/26/2022 9:17 PM ]
★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★
_*PAID BOOK*_
Story/written by Ouummey.
Wattpad @ouummey.
From The author of:
*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*
₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.
           FREE PAGE 004
________________________📖 Ba ƙaramin daɗi taji ba da tayi wankan, wani irin mulmulallen sabulu ne da bata san wane iri bane Innar ta ɓata tayi wankan dashi ga kuma ruwan zafi da har yake tashin tururi.
Gaba É—aya se take jin kamar an kwashe rabin ta an yar haka kuma wata daddaÉ—ar iska ke ratsa fatar jikin ta tana shiga har cikin ruhin ta.
Bata san ina ta samo kaya ba se gani tayi ta kawo mata har kala biyu, duk da tsofaffi ne sedai ai basu kai nata mutuwa ba dan haka ta shiga godiya kamar zata ari baki.
Hankalin ta ta maida kaf wajen Inna da tace zasu yi magana
"Ƴar nan nace yaran nan zasu yi wata nawa ne yanzu?".
"Watannin su biyu da rabi".
Ta faÉ—awa Inna tana tabbatar wa kanta ba zasu fi hakan ba ko zuwa uku.
"Amma na lura ba kya son shayar dasu tunda seda nayi Æ´an dabarun mu na tsoffi na samu abin baiwa Ussaina tukunna itama Hassanar ta samu".