← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 17

Sashe 13

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Seda ta ajiye jakar ta da files ɗin hannun ta ta gyara wanda zata kai masa Sannan ta ƙwanƙwasa ƙofar, amsa mata da akayi tareda bata izinin shiga ya sa ta buɗe ƙofar ta shiga ta ƙara sa gaban table ɗin sa ta ajiye masa files ɗin duk da bata gan shi a kan kujerar sa ba, juya tayi da zummar fita amma ya dakatar da ita daga cikin inner office ɗin sa kan ta zauna ta jira shi, zama tayi ta shiga bin office ɗin da kallo a hankali cikin admiration, office ɗin ya daɗe yana birge ta ba tun ba yau ba yadda ba'a cika masa shirgi da hauragiya ba amma komai a tsare fes wajen da ya kamata.

Cikin haka ta sauke duban ta kan ƙofar inner office ɗin dake buɗe ko kafin ta kai ga ɗauke idon ta tuni ya bayyana cikin shadda riga da wando ɗinkin tazarce sedai maɓallayen wuyan a buɗe suke yana gyara su, haɗa idon da suka yi yasa ta maza ta sauke nata gaban ta na faɗuwa, iya zaman ta a Companyn zata iya rantsewa yau ne ƙwayar idon su ta shiga cikin na juna dan indai tana gaban sa kanta ya kan kasance a ƙasa ne har se sanda ta bar wajen sa shiyasa ba zata iya cewa ga cikakkiyar ainahin kamannin sa ba dan kwarjinin sa kaɗai kan hana mutum iya kallon sa fuska da fuska.

Idon sa a kanta ya shiga takawa har ya ƙarasa ya ja kujerar opposite ɗin ta ya zauna tare da ɗaukar wayar sa ya shiga kiran Haisam

"Kasan tafiyar da zamu yi da tsawo amma kabar mutane na jira?".

Yana gama saurarar abinda yace ta can ɓangaren ya kashe wayar tare da ajiyewa ya shiga gyara agogon hannun sa, files ɗin ta jawo ta shiga yi masa bayani cikin mamakin yau kam be da niyyar zama kan kujerar sa sedai tuni ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu se kuwa taja bakin ta ta tsuke.

Ƙwanƙwasa ƙofa masinjan sa yayi ya bashi izinin shigowa, leda ya ajiye masa cike da girmamawa sannan ya juya ya fita, ledar ya jawo ya buɗe tare da kallon kayan ciki sannan ya tura mata gaban ta

"Ki shiga ciki ki canja wannan uniform É—in dan ba zan iya tafiya dake dasu a jikin ki ba".

Binsa tayi da kallo har ya fice kafin ta sauke ajiyar zuciya, ta canja kaya to akan me, ina ruwan sa da kayan jikin ta ko basu ne suka bata a matsayin kayan aikin ta ba da yau ze kawo mata wani sabon sanaben ta canja.

Haka dole ba dan taso ba ta É—au ledar tare da shiga toilet É—in sa ta cire kayan jikin ta ta maida wannan, doguwar riga ce ta mata se mayafin ta, kayan coffee and milk se suka yi mata kyau sosai dan tana da hasken ta daidai gwargwado.

Cikin ledar ta fito tana ninke uniform É—in ta zuba su ta sake neman kujerar da ta tashi ta zauna

"Mrs Gamji bismilla ko".

Haisam ya faɗa daga ƙofa bayan ya buɗe, da rashin fahimta take kallon sa jin sunan da ya kiraye ta dashi yau

"Muje salma, inda zamu ba nan kusa bane".

Jiki ba laka ta miƙe ta bi bayan shi dan har ya fita, Allah ya sani bata san zuwa ko ina da su tunda ba muharraman ta bane haka ba wani cikakken sani tayi musu ba banda na wajen aiki yanzu kuwa mutum abin tsoro ne bare ma ita da bata da galihu ba wanda ze tdaya mata in wani abu ya same ta.

Gaban mota Haisam ya buɗe mata, cikin ɗarɗar ta shiga tana me karanto addu'a a bakin ta, wani irin sanyi ne ya ratsa fatar jikin ta na Ac dake tashi yayinda hancin ta ya shaƙo mata daddaɗan ƙamshin turaren motar da na jikin sa da suka gaurayu suka bada wani launi na ƙamshi daban.

Rufe murfin Haisam yayi ya koma ya buÉ—e bayan motar ya shiga, tada motar Abu Aulad yayi suka fita daga Companyn yayinda ma'aikata ke aikin kallon su sedai shi kam ko mutum É—aya be nuna yasan da zaman shi ba balle ya kalle shi.

"Garin ku fa zamu je Madam".

Da sauri ta shiga ta kalli Haisam da yayi maganar kafin ta juyo ta kalli Abu Aulad da idanun sa ke bisa titi, bakin ta na É—an rawa ta furta

"Taraba, suna school, ba wanda ze je É—aukan su".

"Ba ze yiwu muje mu dawo kafin su tashi ba?".

Da sauri ta girgiza kanta,

" ƙarfe huɗu suke tashi".

"Ze yiwu muje har mu dawo". Da sauri ta shiga girgiza kanta

"A'a nidai mu tsaya a É—auke su, ba zan iya tafiya in bar su ba, pleaaseeee".

Ta faÉ—a wannan karon directing to Abu Aulad

"Ya sunan Makarantar?".

"Star light Academy".
Be Kuma cewa komai ba ya saki hanyar da yake kai ya É—auki wadda zata kai shi makarantar da ta faÉ—a.

Har ciki ya shigar da motar sannan ta fita zuwa wajen principal, uzuri ta bayar kan dalilin da yasa za'a ɗauki yaran, be Musa ba ya yarje mata dan yaran ta are one of their daily and punctual students da basa fashi sake da ƙwaƙƙwaran dalili.

Rungume su tayi a tare lokacin da suka fito daga aji kafin ta ja hannun su zuwa wajen motar suna ta yi mata surutu.

Tun da suka tunkaro su ya kafe yaran da ido cike da sha'awa da muradi, sha'awar dama nasa ne, muradun samun kamar su ya cike ransa.

BuÉ—e musu bayan motar tayi suka shiga a hankali sannan ta sa musu lunch box É—in su, gaishe da Haisam suka yi inda suka kira shi da uncle batare da sun lura da Abu Aulad ba se da ta nuna musu shi

"Babies, baku gaisar da other uncle ba".

"Yes, baku gaishe da daddy ba". Haisam ya gyara mata da sauri

"Mamman wai daddy ne da gaske?".

GyaÉ—a musu Kai tayi a sanyaye dan bata so yace daddy ba, in suka girma suka san ba daddyn su ne ba fa.

Da sauri Ifty da tafi ƙiriniya dan itace Ussaina ta tsallake ta shiga gaba tare da faɗawa kan shi tana tsallen kiran Daddy

"Daddy dama mamma tace Mana kayi tafiya ne, daddy yanzu ka dawo kenan?".

Da murmushi a fuskar sa ya gyaɗa mata kai tare da shafa fuskar ta cike da shauƙi, juyawa yayi ga ibtisam da tayi tsaye ya ruƙo ta itama ya zaunar kan sa, wasa wasa seda suka ɓata kusan 30 minutes sannan suka tafi bayan yaran sun koma baya kusa da Haisam ita kuma ta koma mazaunin ta.....................✍🏻.

©️ Ouummey 📚✍🏻.

☑️Ote, Comment and share fisabilillah.

Ouummey 09 [ 12/1/2022 1:04 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★

_*PAID BOOK*_

Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.

From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.

                     FREE PAGE 009

₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.

_________________________📖 tafiya ce sosai daga Gamji kafin a kai ƙauyen Ba muni dan har se dasu Ibty suka gaji da kwaramniya suka yi bacci a jikin Haisam dake baya a tare dasu.

Ita kam salma wani irin nervousness da faɗuwar gaba ne ya sarƙe ta, after good five years da barin ta gida yau gashi zata koma kan mau'idin da bata san wanne bane, abu ɗaya ta sani shine akan maganar auren ta ne aka tashi tafiyar.

Motar shiru baka jin tashin komai se numfashin su a hankali a hankali da kuma gudun Ac dake tashi, Haisam kam wayar sa yake pressing hankalin sa kwance yana chat abinsa da budurwar sa yayinda a ta gaban motar kuwa tamkar wasu kurame ko saƙaguna haka suke zaune.

Shi tuƙin sa kawai yake ita kuwa ba abinda take se bin hanya da kallo kamar me irga bishiyun da suke wucewa, tunanin yadda zata riski garin bayan shekara biyar da tayi bata cikin sa take, maganar tarba kuwa tasan ba wata tarba da zata samu a wajen ƴan uwan mahaifin nata.

Abu ne ba ɓoyayye ba cewa murna da jin daɗi suka yi lokacin da ta zaɓi barin su saboda ƴaƴan ta, irin wulaƙancin da suka yi mata na ƙin barin ta ta ɗau ko tsinke a gidan be bar kanta ba kuma bata jin ze barin har nan da gaban abada.

Wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ta saki lokacin da suka shiga garin tana me lumshe ido cikin kiran sunan Allah a ranta, a kaikaice ya kalle ta dan sosai ajiyar numfashin nata ya fito fili.

Gidan maigari ya nufa kamar jiya, seda duk suka fita daga motar suka barta dan ji tayi gaba É—aya kamar bata da wani sauran laka a jikin ta, jikin yayi mata nauyi kamar baya tare da ita, Haisam da ya lura bata biyo su bane ya juya ya tabbatar sannan ya maida kallon sa kan Abu Aulad

"Madam fa bata fito ba, ina ganin kaje kaji ko da damuwa ne ni Bari in ƙarasa ciki". Ya faɗa yana yin gaba da sauri dan yasan kaɗan daga aikin bawan Allah yace shi yaje ya duba.

Ganin yadda ya tafi yabar shi a wajen yasa cikin takaicin abinda tayi kamar wata ƙaramar yarinya ya koma wajen motar, murfin ɓangaren da take zaune ya kama ya buɗe da ɗan ƙarfi dan ransa ya ɓaci da abinda tayi, ya zata wani nemi waje ta zauna a mota bayan tasan suna da abubuwan yi da yawa a gaban su.
Chapter 13 · 0% Book details