← Book details Aisha Siddiqa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 25

Sashe 8

Aisha Siddiqa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

**** **** ****

ASALINSU
(ILORIN EMIRATE)
B
ari mu dauko tarihin tun daga tushe, wato asalin kafuwar masarautar Ilorin. Kamar yadda kowa ya riga ya sani Masarautar Ilorin da aka fi sani da ‘Ilorin Emirate’ tana nan a jihar Kwara a yammacin Najeriya, tana daya daga cikin manyan masarautun Najeriya masu dimbin arziki, Ilorin Emirate, wata babbar attajirar masarautar Musulman Yarbawa ce a kasarmu mai dimbin albarka, wadda kafuwar tarihinta ya faro ne daga rayuwar Shaihu Salih Janta, da aka fi sani da (Shehu Alimi).
Kenan su din duk da kasancewarsu Sarakai, kuma manyan sarakunan kabilar Yoruba, to manyan Malamai ne, ma’abota sani na na addinin Musulunci da kyakkyawan riko dashi. Su din, har ila yau, sun kasance Shehunnan Yarbawa ne masu dauke da sani na Alqur’ani da Hadisi, wadanda sukayi gadon sahihiyar sarauta ta malunta da arziki mai dimbin yawa daga Kakan-Kakan su Shehu Alimi, sarautarsu sarauta ce mai asali da da kyakkyawar nasaba tun kafuwar kasar Ilorin.
Ilorin Emirate, ta kasance (multiethnic Muslim Kingdom) wato cakude take da kabilu da yarurruka daban – daban na kasar Najeriya guda hudu, wadanda suka hadu suka samar da Ilorin Emirate din, sun hada da; Balogun Gambari (Hausa), Balogun Ajikobi (Yoruba), Balogun Fulani (Fulani), Balogun Alanamu (Yoruba).
Kowanne bangare wato kowanne Balogun, nada (district head) wato sarkin dake wakiltar wannan bangaren/yankin, karkashin babban Sarki Emir of Ilorin, dattijo mai ran karfe Sarkin wannan zamanin da muke ciki a lokacin yanzu, wato Emir AbdulRasheed Dan Abdullateef Akanni.
Engnr. Edrees Abdulrasheed Akanni, ya kasance Da na farko ga Sarkin Ilorin; Maimartaba Sarki AbdulRasheedu Akanni, (the 11th Yoruba-Speaking Fulani Emir) wato Sarkin Ilori na goma sha daya.
Engnr. Idris shikadai ne Da a wurin mahaifiyarsa marigayiya Olori Murjanatu (Olori na nufin Queen bisa ga al’adar masarautar), tun Edrees yana yaro ta rasu sanadin cutar sankarar mahaifa.
Sai bayan rasuwarta ne aka bawa Emir Abdulrasheed Sarautar mahaifinsa, aka kuma kawo masa mata har hudu daga garuruwan yammacin Najeriya daban-daban ya sake aure, sune suka haifa masa sauran ‘ya’yan sa maza guda tara, har Edrees da matarsa ta farko Morjanatu ta haifa in an hada su goma kenan gabadaya maza ‘ya’yan Sarkin na Ilorin.
Emir Abdulrasheed da ya tashi yiwa dansa na fari aure wato Edrees Akanni, sai ya tsallaka ya auro masa Gimbiyar Gombe mai suna (Sappa) diyar abokinsa maimartaba Sarkin Gombe, Ahmadu Umar Jalloh (CFR) daga can cikin yankin jihar Gombe dake arewacin Najeriya.
Engr. Idris Akanni tun lokacin da mahaifinsa ya aura masa Sappa Allah ya zuba masa matsananciyar soyayyarta, aure ne na gata irin na ‘ya’yan sarakuna don bai wuce shekaru 27 ba lokacin da aka aura masa Sappa, ita kuma bata fice 17 ba, tun daga lokacin yake kula da ita, don yana matukar son ta kamar ya hadiyeta.
Sappa a hannun mijinta Engnr. Idris ta karasa girma ta kuma san rayuwa, ya shiga da ita duniya ta budi ido, wata irin soyayya Idris Akanni yake mata irin dai soyayyar Yarbawa ga kyawawan matan Fulani, (mazan Yarbawan Ilorin na matukar son matan Fulani) har dai in aka yi katari kyawawa ne masu farar fata da gashi yalalaa kamar dai ita Nenne Sappa din.
Auren nan nasu ya kafa tarihi a cikin duka zuri’arsu daga bangarensa da nata, domin aure ne irin wanda ba'a taba yi a masarautar Ilorin da masarautar Gombe ba, wato aure tsakanin masarautar Ilorin data Fulanin Gombe, albarkacin amincin dake tsakanin Babansa Emir da mahaifinta Sarki Ahmadu Umar Jalloh (Uban Kasar Gombe).

Sarki Ahmadu Jalloh Umar wato (Uban Kasar Gombe) da Sarki AbdulRasheed Abdullateef Akanni (Emir of Ilorin) sun hadu ne tun kafin su zama sarakuna magadan iyayensu, wato tun suna samari ‘yan bana bakwai a jami’a, sun hadu ne a yayin karatun digiri na farko da sukayi tare a can kasar Venezuela (South America) da iyayensu suka turasu inda dukkanninsu suka karanta siyasar duniya (International Politics).
Kenan mahaifinsu Idris Akanni wato Emir of Ilorin (AbdulRasheed Abdullateef Akanni aboki ne na jiki tun na kuruciya ga Baban Nenne Sappa, sarkin Gombe Ahmadu Umar Jalloh.
Kowa da ya sansu ya shaida Idrisu Akanni na ma Sappa wani irin mashahurin so, kamar babu wata mace a fadin duniya bayan ita. Banbancin harshe da yare bai zamo musu barrier ga soyayya ba.
Da fari Nenne ta samu kanta cikin bakunta, kasancewar ta shigo cikin wata kabila da ba tata ba, al’adu da dabi’u sun banbanta, amma gradually tayi hobbasa ta koyi yarensa duk da wahalarsa cikin dan lokaci, shima kuma dama ya iya fulatanci, wannan ne ya taimaka mata sosai wajen zama a cikinsu.
Sai ya zamanto Idris tun daga kanta bai kara marmarin auren kowacce mace ba har zuwa inda yau ke motsi da suka cimma shekarun girma shi da Nenne Sappa, da zaratan tagwayen ‘ya’yansu saiti biyu.
Bayan aurenshi da Sappa da kadan ya samu aiki da wata masana’antar safarar jiragen ruwa a kasar Japan (Japanese shipping authority), sai ya dauketa da karamin ciki ya tafi da ita Japan, ya saka ta a makaranta tayi ilmin zamani mai zurfi a fannin aikin jinya (Nursing) ba don tayi aiki ba sai don ta samu ilmin kula masa da lafiyar yaransu a gida.
Sappa ta fara da haihuwar ‘yan biyu mace da namiji a haihuwarta ta fari. Yaran da al’adar Yoruba ta riga ta basu suna “Taiwo” da “Kehinde” watau Hassana da Hussaini. Taiwo sunan Kakarsu ta wajen uba mai rasuwa taci wato “Olori Murjanatu”, Kehinde kuma kai tsaye ya samu sunan Kakansa Emir (Abdulrasheed) ake kiransa “Prince”, kenan Sarki aka yiwa takwara.
Taiwo da Kehinde sun taso cikin koshin lafiya da samun kulawar iyaye wanda ya haifar musu da saurin girma, saidai kowannensu da irin halinsa da irin dabi’unsa.
Kowa ya shaida Taiwo nada fitina, korafi, da mita tun tana karama, duk wani hali na matan yarbawa Taiwo nada shi musamma daukan tsegumi daga kannenta. Nenne Sappa bata shiri da Taiwo saboda kiriniyarta da wadannan halayen nata, gata da tsokanar yara ‘yan uwanta, Abdulrasheed kuwa gashi dai bas hi da aboki na jiki kamar Taiwo to kwatakwata halinsu ba daya bane, mahaifinsa na kiransa “Prince” Emir kuma yace masa “Kehinde”, a zahiri shi irin yaran nan ne kamammu, salihai, introvert, wadanda magana ma wuya take musu a zahiri saidai suyi action a gani, wato Abdulrasheed lumbu-lumbu ne da ake cema wutar kaikayi saidai yanada temper, babu mai sanin abinda ke zuciyarsa don fuskarsa bata bada expression na abinda yake ransa, wato kwarai ya iya waskewa da shanye expression, Nenne Sappa kadai ke iya karantarsa tana ganewa in abu yayi masa a fuskarsa ko bai masa ba. Babansu da suke kira “DADE” sanda suka fara budar baki shi da Taiwo, yaga yadda Prince yake saka Taiwo kuka ta ruwan sanyi, ba tareda iyayensu sun san me yayi mata ba, ya kance “Prince GREEN SNAKE ne”.
Sun rayu tsayin shekaru kusan goma sha biyar shi da Sappa da ‘ya’yansu na fari a kasar Japan, domin saukar su a Japan da watanni kadan suka haifi ‘Prince Kehinde’ da ‘Princess Taiwo’.
Chapter 8 · 0% Book details