Sashe 2
Aisha Siddiqa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
SHIMFIDAR LABARIN WAIWAYE ADON TAFIYA (1) D r. Murjanatu, wadda kowa a gidansu da danginsu bakidaya da “Taiwo” yafi kiranta, kannenta kuma suce mata “Aunty Taiwo”, abokan karatu su ce Murjanatu Akanni. Murjanatu baka ce ba sidik ba, bakin da akewa lakabi da (chocolate beauty) sabida sanyin kyawunsa da haskensa, doguwar mace mai ‘yar kyakkyawar kiba ta jikin hutu, irin kibar da batayi munin da za’a ce mata lukuta ba. Saboda duk da kasancewar ingarman jiki keda Dr. Murjanatu to suffar jikinta mai tsari ce duk da kibarta, gata da doguwar fuska irinta fulani da dara-daran idanun yarbawa masu haske, Taiwo-Murjanatu, nada dogon hanci sambal irin na Kakarta ta wajen Uwa wadda ta kasance bafullatanar jihar Gombe da suke kira “NANI OUMMANA”. Sannan tsayin ta masha Allah shima bai wuce misali ba. Komai na Dr. Taiwo kamar ita ta aunawa kanta ta kuma zaba. Domin dai a fasalce baza’a kira Aunty Taiwo doguwa irin sambal ba, saidai ace kamar kwalbar nan ta coca-cola ga kauri ga tsayi da dirin jiki mai zati, tana a ma’aunin daidai na tsayin da akeso a tareda mace. Shekarun Murjanatu na haihuwa a wancan lokacin da muka waiwaya talatin cif. Murjanatu-Taiwo Akanni ga tsayi ga zati irin na mace mai aji da kasaitar nasaba, girman jikinta mai ban sha’awa ne don bai sa mata muni ba. A takaice komai na jikin Taiwo irin na matasan matan kabilar Yoruba ne, wato daga kabilar Yarbawa ta fito. Tafiyar Taiwo mai daukar hankalin mai kallonta ce, domin tana tafiya ne cas-cas akan tsinin dugaduganta, cikin rangaji na jan aji da kasaita sanna ga iya ado mara misaltuwa, kullum haka take cikin tsantsar gayu da yawan ado, duk yadda ta motsa ko tayi magana ko murmushi sai kaga wannan ajin na musamman irin na jinin sarautar gidansu ya nuna kansa a tareda ita. Kallo daya zaka yiwa Taiwo da dabi’unta da iya kasaitarta kasan ta hada jini da sarautar Yarbawa mai tushe, ko daga yanayin takun tafiyarta dinnan mai kayatar da idon mai kallonta kamar Dawisun da ya baza adon jikinsa yake tafiya. Tafiyar Murjanatu cikin kasaita da iya sarrafa jikinta da yake mul-mul irin na kosassun ‘ya’yan kabilar Yoruba da suka ci suka tada kai. A daidai wannan lokacin da Murjanatu ta shigo gidanta, yamma ce lis, hadari ya gangamo, sararin samaniya yayi duhu, sai cida da iska ke kadawa, gab ake da kecewa da ruwan sama mai karfi. Wannan na faruwa ne a cikin daya daga manyan biranen Najeriya mafi yawan al’umma da kabilu daban-daban, wato birnin Legas ko Ikko da aka fi sani da jihar Lagos. Gidan nata matsakaicin gidane kyakkyawan (Duplex Mansion) wanda anan Dr. Taiwo da iyalinta ke zaune tun dawowarsu Jihar Lagos da zama daga Ilorin, gidan yana nan a shiyyar babbar unguwa mai tsari ta masu hannu da shuni ‘Eko Atlantic’, gidan Murjanatu nada farin fenti mai dan duhu da ratsin ruwan madara-madara (off-white/milk), kuma gida ne da in ka gani ko daga nesa kasan masu shi sun jima da kama kasa. Zamu iya kimanta lokacin da misalin karfe shidda na yamma, daidai lokacin da Taiwo-Murjanatu, ta shigo da kan motarta kirar ‘Hyundai Creta’ harabar gidannata, bayan tasowarta daga asibitin da take (housemanship) acan, wato asibitin koyarwa na jihar Lagos. (Murjanatu-Taiwo Akanni, dalibar likitanci ce a Lagos State Teaching Hospital). A wannan lokacin duk tunaninta da hankalinta na kan karamar diyarta (Kiki) wadda ta baro a gida hannun sabuwar mai rainonta Bunmi, tun bayan data fara housemanship ta samo Bunmi ‘yar kabilar Ibira suke zaune tare. Kiki ‘yar kimanin shekaru uku wadda saboda son da dan uwanta yake mata, yasa a yawancin lokuta bata dauka cewa ita ta haifeta, tafi dangantata da ‘yarsa shi kadai, ko cewa zata yi Kiki sai ta hada da inkiyarshi, tace “Kikinshi” ko “Kikinsa”. A lokuta da yawa idan ana hirarsa, kasancewarsa ‘Polo Celebrity’ ne, ‘yar uwarsa Murjanatu data fi kowa kusanci dashi ta kan gayawa kawayenta daliban LUTH, musamman wadanda ke bibiyar kallon wasan shi a kafar talbijin ta “Global POLO TV, suke kuma mayatar son jin wani abu da ya shafeshi personally, Taiwo kan basu labarin irin son yaransa ne, ta kan ce da dai ace maza na haihuwa da kansu, ba mata ke haifa musu ba, da tasan shi zai yi nakudar Kiki ya haifeta, wato da bazai bar mata ta haifota ba, saidai shi da kansa, saboda sonda yake mata a matsayin karamar diyar ‘yar uwarsa, wadda duk duniya bashi da makusanci, amini, amar ita ‘yar uwarsa Taiwo. Ya sha gaya mata cewa ya raina adadin kulawar da take baiwa Kiki, tunda har ta zabi karatun likitanci akan zaman gida ta kula da kyautar ‘ya’ya biyun da Allah ya bata. Tana basu labarin irin yadda yake bata lokacinsa in yana gaban Kiki, don mayar da shekarunsa yake daidai da nata, su taru suyi ta zuba shirme na (Daddy and Daughters’ love). Wani lokacin Taiwo har addu’a take yi tace Allah ya bashi nashi ‘ya’yan shima. Saboda son yaran shi har yaso yayi yawa. Tana matukar marmarin ganin yaranshi, ko ba don komai ba don ta taya shi son su, irin dai yadda yake tayata son Kikin data haifa. Murjanatu kullum addu’arta kada Allah ya baiwa dan uwanta matar da zata raba soyayyar shinnan da ‘yarsa Kiki. Don ko ubanta Toafeeq albarka. “Kiki rigimammiya amanar Uncle dinta “Prince!”. Wakar da Aunty Taiwo ke yawan yi mata kenan, wadda ainahin sunan Kikin na yanka (Ruqayyat). To amma tana ji tana gani ala dole Prince ya mayar mata da sunan diya “Kiki”, wai a cewarsa saboda kibar ta, da kazarniyarta, da rikicinta irin dai na yara lukutaye ‘yan shekaru uku, yace Kiki ne ya dace da ita ba sunan Nanin Gombe ba. don kam ita Kakarsu Nani Oummana bata da rikici kona tsufa, balle irin na Kiki. Murjanatu na tafe ne tana tuki take wannan tunanin na dan uwan haihuwar nata, mafi soyuwa a ranta a duk cikin ‘yan uwanta da suke iyaye guda, kuma namiji daya tal a cikinsu. Gabadaya gidansu tafi shiri dashi watau shi Hussaininta, wanda suka zo duniya a tare, ta tuna ya hanata barin Kiki a gun masu raino, ba sau daya ba ba sau biyu ba, to amma yaya zata yi tunda ta saka ma ranta son zama likitar mata kota halin kaka? Shi, a matsayinsa na (lifetime) dan “Polo” ba zai taba gane hidimar aikin asibiti bata haduwa data kananan yara ba, dole sai da taimakon mai raino da raba hankali gida biyu, da kuma taimakon makarantar nursery ne kadai kowannensu zai samu isashshen lokacinta. Kuma dai tayi sa’ar samun Bunmi wato mai rainon Kiki yarinyar kirki ce, bata da matsalar komai sannan gata musulma don kuwa daga Ilorin ta taho da ita, tana kula mata da Kiki sosai. A yadda Prince yake son niece din nashi Kiki, wadda ainahi soyayyarsa da yarinyar ta samo asali ne daga sunan Kakarsu da taci wato Nanin Gombe Hajiya Ruqayya da suke kira (Nani Ummana), Taiwo ta tabbata da ace zata bashi ita ya rike a inda yake zaune, ta san tsaf zai karba babu musu, zai iya aje hidimomin Polo dinsa na wasu lokutan, ya zauna ya kula da Kiki da kansa sabanin ita, tunda gidansa babu mace har yau har gobe, amma kuma hakan bai hana shi kwadayin ta bashi rikon Ruqayyatu-Kiki ba. Fatanta dai yanzu shine Allah ya taimakesu iyayensu wato “Nenne” da “Dade” su amince da maganar marainiya Haseenah, dan uwanta ya samu abokiyar rayuwa, yayi settling rayuwar iyali hakanan (at the age of 30) kamar kowanne lafiyayyen matashi. Ita tasan ba wani uzuri da zata baima dan uwanta ya karba akan cewa kulawar da take yima Kiki tayi kadan, a wurinsa Kiki tafi karatun nata muhimmanci dari bisa dari don shi bai ga dalilin da Murjanatu zata ce sai tayi aikin likita ba. Watakila ko don yana ‘life-time’ dan Polo ne yasa yake ganin kowanne Profession na duniya wahala ne, sannan takurawa kai ne, kuma babu riba a cikinsa banda Polo Sport, don ko tabbataccen aikinsa na man fetur an shaida, baya baiwa muhimmancin da ya baima wasan Polo dinsa. A cewar Murjanatu ita kuma, karatun data zaba take yi na kishin kasa ne, bashi da alaqa da matsayin gidansu, reputation na gidansu ko na mijinta Toufeeq Adebayo. Sarauta bazata hanata yunkurin kokarin amfanar da al’umma ba ko neman abinci ta hanyar ilminta, don kuwa sun kere ma hakan. Taimakon kasarta takeso ta yi da nata dan effort din (with full patriotism) sabida karancin likitoci mata da ake dasu a kasarta, tunda kuwa gwamnati take da burin yiwa aiki da mata ‘yan uwanta ba private ba a ganinta aikinta mai hujja ne babba ba karama ba ko a cikin addini. Har ila yau, bazai hanata hidimar iyali ba. Bayan kasancewarsu ‘ya’yan sarauta mai suna sarauta data amsa sunanta, sarauta irin ta gado bata taka-haye ba, kuma jikokin manyan sarakuna gaba da baya, maigidanta Toufeeq Adebayo, har ila yau, ma’aikacin majalisar hadin kan turai ne (European Union) kuma yanada matsayi mai girma a cikinta. Don haka Toufeeq ba mazaunin gida Nigeria bane sosai. Karin dalilin da yasa Taiwo tayi amfani da damar wajen yin karatunta cikin nutsuwa a Ilorin, wanda ta tabbatar zai amfanar da al’ummar kasarta musamman mata ‘yan uwanta (Obstetrics & Gynaecology). Babban burinta mata su amfana daga ilmin likitancin data wahala tayi, a Public University ta Ilorin. Ta fara karatun ne da farko saboda rashin Taofeeq a kusa, madadin tayi ta zaman gida miji baya kusa, don a kalla Toufeeq sai yayi watanni uku ba tare da ya leko su ba ko meyasa? Nenne kance ita bazata iya zaman da Murjanatu ke yi ba na bin miji agindi-agindi akai-akai. Don itace tafi zuwa masa da yaran lokaci-lokaci inda yake, in ta samu hutu, wanda shi bai cika son haka ba. Toufeeq yafi son su zauna a gida inyaso duk sanda ya samu sarari shi ya zo, amma Aunty Murja bata yarda sai taje. Kenan zamu iya cewa Dr. Murjanatu da aka fi sani da (Taiwo), tana karatun aikin likita ne ba don albashin da zata samu ba, sai don dalilai guda biyu; debe kewar mijinta tun na auren saurayi da budurwa hutsun bature Dr. Toufeeq Adam Adebayo, da kuma burinta na amfanar da al’ummar kasar