Sashe 16
Aisha Siddiqa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da tunasar dashi soyayyar Manzonsa, saidai in basu kadaice a dakin jinyar ba. Har ila yau Nenne bata gushe ba da nasiha sannan bata fasa ba. A kullum bata gajiya wajen nuna masa muhimmancin aure da ajiye iyali ga faein ciki da cigaban rayuwarshi, cikin nasiha da lumana, ta kan ce masa ‘ya’ya sune gatan bawa duk arzikinsa, tunda su zasu dinga yi masa addu’a a bayan ransa. Kuma su tsaya masa a sanda yake bukatar su. Auren kuma da yakewa kallo na daban Nenne tana kokari wajen nuna masa cewa ibadah ne ba son rai bane. Koma meye dalilinsa na gudun yinsa bai isa dalili a wurin Ubangiji ba, tunda dai ya bashi lafiya da abinda lafiya zata amfana. Tace ana yinsa ko ba’a so domin katange kai daga sabon Allah da tsarkake kai daga daudar zinah da katange zuciya daga sha’awar aikata sabo kowanne iri ne. Wadannan sune ire-iren kalaman Nenne Sappa ga danta Prince Abdulrasheed lokacin jinyarshi. Princess Fatima kuma ita ke bashi abinci a baki da cokali. Yau daya gama cin abincin rana, Princess Fatima tana gyara masa filon da zai kishingida ta bayansa, a cikin tarin sumar kansa sai ta hango tsillin ‘furfura’ a cikin gashin kansa. Ta kai waje guda 20 a cikin lallausar sumar kansa, ta kuwa ce me zata yi ba sakin shakiyyar dariya ba. Princess Fatima tasa hannu ta tsigo furfura guda daya daga saman kansa, tana dariya tana kanne ido ta nunawa Nenne, tana fadi cikin yanayi na (banter) harda neman sikewa don dariya, “someone has finished, ooh my Dear! Getting white hair before even getting a first wife… Nenne furfura ce fal! A kan Hamma!”. (Ta kara gishiri). To ma yanzu sabida Allah Nenne, wacece zata yarda ta auri mutum over 40 kansa duk yaci furfura? Ai saidai kwantan ‘yammata kamarsa dan (mid forties), irin bazawara mai ‘ya’ya biyu haka, ko widow (wadda miji ya mutu ya barta) haka dai, amma ba dai (sweet 16) ba!”. Nenne an sosa mata inda yake mata kaikai, sai ta gyada kai tace “in ya samu sweet 16 din sai ki hana ruwa gudu! Furfura baiwa ce ‘yar nan, ba itace tsufan namiji ba, wani ma sai ya fara ta yake fara jin mazantaka da karfin samartaka, rashin aure haka kawai babu dalili shine mishkilarsa, domin tamkar izgili ne ga rahamomin da Ubangiji yayi maka Abdulrasheed. Saidai kuma bansani ba ko abinda mutane suke fadi marar dadi a kanka din, ko gaskiyane Abdulrasheed?” Yanayin fitar sautin muryar Nenne, a halin yanzu ya nuna helplessness din da take ciki akan situation din, wanda hakan yayi matukar karya zuciyarsa, jikinsa yayi sanyi matuka, amma dai bai yi magana ba. Princess Fatima, ganin yanayin da suka shiga na damuwa su duka, sai ta dauki ipad dinta ta bar musu dakin, ta koma can reception na asibitin ta samu kujera ta zauna tayi tagumi itama, don taga zancen na Uwa da Danta ne, kuma yau raunin Nenne da bakin cikin ta na shekara da shekaru akan rashin aurensa yafi na kowacce rana bayyana a tare da ita da nauyin shekarunta da suka bayyana kan kyakkyawar fuskarta yau saboda damuwa. Wai AbdulRasheed ya fara furfura ba aure!!! Wannan al’amari ya tsorata Hajiya Sappa matukar tsoratawa. Fitar Princess Fatima keda wuya, sai ga hawaye mai kauri ya tsinke a fuskar Nenne Sappa. Kamar jira take Fatima ta gusa. Hankalin AbdulRasheed yayi tashin da bai taba yi ba yau, ba yau Nenne ta soma korafi da kuka akan rashin aurensa ba, amma na yau yafi na kullum daga hankalinsa ko mai yasa? Don ya ga bakin cikinta muraran a idanunta. Abdulrasheed ya shiga rokon Nenne cikin kaskantar da kai, akan ta gaya masa menene exactly damuwarta har haka akan rashin aurensa, take irin wannan zafafan hawayen dalilinsa, masu barazanar tarwatsa rayuwarsa? “Zubar hawayenki a kaina Nenne masifa ne a gareni kin sani”. Nenne Sappa saida ta yi sharbe son ranta, tana gogewa da habar hijab dinta. Kafin ta soma Magana cikin rauni da karaya. “Na soma zama cikin zargi mai girma a kanka nima! Na soma yarda da zargin da duniya ke maka, na cewa neman maza ‘yan uwanka kake yi (you are gay) shine abinda yasa ka juyawa auren Sunnahr Ma’aiki SAW baya. Haka ne ko ba haka bane Kehinde?” Nenne ta tsatstsareshi da jikakkun manyan idannunta da suka rine kamar garwashi suke jike shatab da hawaye mai yawa. Ko kadan babu firgita kan kalamanta a tare da shi, ko don ba yau ya fara jin ana zarginsa da hakan ba? Jin maganar yau daga bakin mahaifiyarsa shine babban abinda yafi tada hankalinsa. Amma ko kadan babu tashin hankalin maganar akan fuskarsa sai tsantsar damuwa da yanayin da mahaifiyarsa ke ciki. Abdulrasheed yace (cikin despair). “Nenne in kowa zai min wannan mummunan zargin ke UWATA (mahaifiya) ya kamata ki kyautata min zato. Ban taba zaton Nenne ranki zai yi bacin da zakiyi duba da wannan banzan zargin na mutane marar tushe da hujja ba, tunda kin san irin tarbiyyar da kika yi mun da hannunki, ba wani ya tarbiyyantar miki ni ba, kuma kinada tabbaci a kan ingancinta, na cewa ko bayan ranki bazan zubar da ita ba, balle da ranki da lafiyarki in yi wannan mummunan aiki. Anyway, bazan musa ko daya ba, cikin abubuwan da ake zargina dasu din. Allah ne kadai ya san zahiri da badinin zuciyar bayinSa, da abinda suke aikatawa na fili dana boye, kuma shaidarsa nake nema bata mutane ba Nenne, tunda ke kanki da kika haifeni kin kasa shaidata….…”. Yayi shiru, ya koma ya kwanta yana maida numfarfashi da sauri da sauri kamar mai ciwon asthma. A hankali AbdulRasheed ya rufe idanunsa…. Mummunan ‘scene’ din na Hasinah da dan uwansa kuma wanda ya rika a matsayin “amini” duk cikin family dinsu Adetokumbo akan gadonsa na gilma masa. Abinda ya faru kusan shekaru goma sha hudu a baya, amma har yau yake ‘haunting’ dinsa… ‘trauma’ din abun ya kasa barin ransa ya huta, zuciyarsa ta sake da mata. Cousin dinsa Adetokumbo Abdulfatahi Akanni da fiancée dinsa Hasinah Ambursa turmi da tabarya, kuma a kan gadonsa sannan a dakinsa mallakinsa a gidansa dake kasar Japan. Wani ‘incidence’ ne da kullum yake komawa ‘GREEN’ a idanunsa… ya kasa barin duhun idanunsa su huta ko hasken wata mace ya ratsa ta cikinsu. Shikuwa me zaiyi da mata yanzu? Ai ya dade da rufe babinsu daga kan Hasinah Bello Ambursa. A cewarsa dukkansu are nothing but ‘Gold-Diggers’, wadanda in dai namiji zai basu kudi to ya gama samun mutuncinsu, kowanne kare da kowanne doki ma yazo ya fanshi mutuncinsu da diyaucinsu in dai yana da kudi. A tasa mummunar fahimtar da ya dade da yiwa mata daga kan Hasinah, wadda ta dade da yin babakere a zuciyarsa ya gama yardarwa kansa duk matan yanzu irin Hasinah ne, masu son holewa ta jiki data aljihu, ya yarda mafi akasarinsu namiji daya ba zai taba isarsu ba, batare da sun zagaya sun ci amanarsa ba ko me zai musu na halacci kuwa, ko me zai basu iya karfinsa don kula da lalurorinsu, kuma koda zai yagi naman jikinsa ya basu bazai hana su hango wanda ya fishi samu ba, they are totally greedy, rashin wadatar zuci ya yiwa zakatan ‘yammatan yanzu katutu, babu soyayya ta saboda Allah a zuciyarsu yanzu. Shiyasa yake ganin bashida mata a duniya, ba’a haifi macen da zai kara gangancin so ba, bazai kara yarda da mace a duniya da sunan soyayya ba in ka cire soyayyar da yake yiwa Nennensa da ‘yan uwansa mata. Bai ki ba dai a gidan aljannah in yana da rabo. Me yasa mostly kyawawan mata kamar Hasinah ne kullum suke yin dage, domin hango wani wanda bai kama kafar mijin da Allah ya basu a komai ba? Marasa shararren kyau zaka samu basu cika dage ba. Me ya rasa da Da namiji ya rasa daya cancanci abinda Hasinah tayi masa? Me Tokumbo zai nuna masa banda cikar aljihu a lokacin? Idan har aljihun wani namiji dan uwansa ne zai sa Hasinah yi masa haka, to kuwa duk matan duniya ya dade da yi musu jimilla da ‘gold-diggers’, kwadayayyu, hadamammu, ma’abota manta halaccin mai halacci, wadanda burinsu kawai namijin da zai basu kudi suyi bushasha, ba wanda zai so su saboda Allah ba, kuma wanda zai kwatanta irin soyayyar da suke so ta banza da da sunan itace soyayyar da zata bulle dasu, koda kuwa ace babu abinda Allah ya rage ka dashi a rayuwa. Ya rasa wane irin jin dadi mata ke nema a wurin namiji fiyeda daya. Shi kuma Allah da ya halicceshi yayi shi mai matukar kishin kansa da kishin macen da yake so, watakila shine dalilin da yasa daga kan Hasinah ya daina sha’awar kowacce mace sai Polo dinsa, yanada kishin kansa fiyeda yadda harshe zai iya bayyanawa! Nenne ta rainesu akan turbar tsoron Ubangiji, tana tare dasu ko bata tare dasu suna tuna Allah, ta rigada ta dorasu akan turbar gujema ketare iyakokinSa. In aka duba kuma, a rayuwa ba abinda bai yiwa Hasinah ba, a matsayinta na wadda yaso aure da dukkan zuciyarsa ba tareda tunanin banbancin nasabarsa da tata ba, kuma marainiyar da ya fiddo daga gidan marayu, ya maidata daliba mai ‘yancin higher education, ta hanyar sponsoring karatunta daga gidan marayu zuwa Lagos eventually zuwa kasar Japan ba tareda sanin kowa nasa ba bayan Taiwo. Bayana fara karatunta na jami’a ya zama shine uwarta shine ubanta a Tokyo, shine cinta shine shanta, shine sutturarta da duk wani shopping dinta duk don ya katangeta daga neman wani abu ta rasa a rayuwarta duk da shima a lokacin ya dogara ne da abinda Kakanshi ke turo masa duk wata, da na mahaifinsa, a matsayinsa na dalibin postgraduate, soyayya ta gaskiya ba irin wadda bai yi mata ba, har da ta kauce hanya, domin ta saka shi ya danyi deviating daga tarbiyyar da Nennensa ta bashi, duk don ya faranta ma fiancée dinsa Hasinah ya kuma katangeta daga sha’war wasu mazan ba don yana so ba. A dalilin ganewa da yayi cewa ta soma wayewa da irin wannan rayuwar da tazo ta tarar ‘yammata da samari kamarta nayi a jami’a, lokacin da ya fahimci ita din mai son wannan rayuwar ce sai ya biye mata,