Sashe 17
Aisha Siddiqa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bisa dalilai guda biyu; na farko son da yake mata, na biyu tsoron shi na kada ta kwadaici wani, idan shi din yaki biye mata. Da wannan Hasinah ta dulmiyar dashi a baya cikin rayuwar soyayyar shan minti, kazamar rayuwar da ’yammata irinta ke yi a turai, rayuwa ta rashin tarbiyya da baya ko son tunawa yayi da Hasinah yanzu. Duk da haka a kullum yana godewa Allah da bai taba sanin Haseenah diya mace ba (as in having sex) bai taba ba. Sai abinda ba’a rasa ba bisa jagorancinta. Amma duk da soyayyar shan mintin da ya biye mata suka soma ba don yana jin dadin afkuwar hakan ba, saboda a irin son da yake ma Hasinah yafi so ko meye zai shiga tsakanin su sai ya mallaketa ta hanyar aure, amma ta nuna ita bazata iya jira har zuwa wannan lokacin da Nenne zata amince da maganarta ba, dole ya biye mata suke kananan abubuwan da har ransa baya so. Don kuwa mace duk inda take komai kankantarta shaidaniya ce, balle shaidancin Hasinah mai license ne tunda ‘yar kwararo ce, amma duk da hakan biyemata din domin ya katangeta bai sa ya iya ya rike sha’awarta da hangenta da kwadayinta na abinda shi har lokacin ya kasa yi mata ba, saboda addu’ar Uwa ta dare da rana dake tasiri a kansa, ya kasa rike sha’awar Hasinah daga sauran mazan da basu kaishi komai ba. Amma a bukatun rayuwarta kam na yau da gobe baya jin ya gaza, sai dai don ta kasance mai son bushasha da sha’awar rayuwar kere sa’a. By Allah! Yayi duk wata bajinta da namiji kamarsa mai gata da asali da nasaba tsarkakakkiya ta sarauta da ilmi mai zurfi da malanta bazai yi akan matar da ya tsinto a kwararon gidan marayu ba! Bayan duk wannan wane irin sakamako ya samu a mahaukacin son nan kuma gurbatacce da yayiwa Hasinah??? Prince ya runtse ido da karfi, yana tuna Hasinah a ranar, da kazantaccen yanayin da yazo ya samesu ba zato, mantuwa yayi ya dawo, abin mamaki tareda kaninsa Adetokumbo Abdulfatahi Akanni, the worst part dinma kuma a dakinsa sannan a kan gadonsa. Saboda kawai Abdulfatahi ya fishi kudi, ya fishi iya shege ya fishi rashin tsoron Allah, uwa uba yanada ra’ayin yin bushashar arzikinsa ga matan banzan duk da zasu bashi jikinsu, don a lokacin shi Abdulfatahi wani babban Automobile Business Mogul ne, kasancewar a tsakanin Japan da Spain yake harkar shigo da motocinsa, to duk sanda ya shigo Tokyo a wajen dan uwansa Prince Abdulrasheed yake sauka, baya sauka a hotel, kuma ta haka ne ya san Hasinah a matsayin fiancée din dan uwansa, har suka saba shi da ita suna tsokanar juna irin dai wasan nan na kanin miji da wadda Yayansa zai aura. Yaya akayi-yaya akayi suka sarke a bayan idonsa kuma bai taba gane komai a tsakaninsu ba banda sani da yayi tun fila azal Hasinah mai dogon buri ce, mai kwadayi ce, mai son kyale-kyalen mata na fita tsara ce wato (Hasinah is a designer baby) sannan yana ankare da cewa tana son wannan harkar, a hakan kuma yana iya bakin kokarinsa akanta, don ganin bata rasa komai take bukata ba, kusan duk abinda iyayensa ke aiko masa a matsayinsa na dalibi a lokacin akan bukatun Hasinah masu dan Karen tsada yake karar dasu da kwalliyarta na sittiru tsadaddu, da kayan kawa da khyale-khyale ba tareda Nenne ta sani ba. Ko dama ita Nenne from day one, Hasinan bata kwanta mata ba tunda aka ce a gidan marayu aka daukota, tun a lokacin Nenne tace “NASABA” wato tsatso, wani abu ce mai girma da muhimmanci a neman aure to amma Hasinah fa? Suwa zata bugi kirji ta kira Kakannin jikokinta na wajen uwa na jikin Abdulrasheed Kehinde? Shikuma har a lokacin lallaba Nenne yake yi akan ta yarda ta karbi Hasinah a matsayin surukarta, ita kadai zuciyarsa keso, ita yake yiwa kauna ta saboda Allah ba zai iya auren kowacce mace in ba itaba. Shi ya bata surname da Bello Ambursa lokacin da zai shigar da ita makaranta, sunan abokinsa Bello da ya rasu. Sakamakon da ya samu a duk wannan sadaukarwar da yayiwa Hasinah shine Hasinah ta bige da cin amanarsa, itada dan uwansa mafi kusanci dashi, mafi kazantar cin amana har a gadon barcinsa kuma a gidansa. A cire maganar girman zina wadda lahani ce mai girma ga martabar diya mace. Abin ya kara dawo masa sabo. Kamar yanzu-yanzu ya faru. Shekaru goma sha hudu kenan da faruwar al’amarin a can baya, amma kullum sabo scene din yake koma masa a idanu da zuciyarsa, in ya tuna ko aka yi masa fadan yin aure ko ya kamata ya zabi matar aure a family dinshi. Nan da nan jikin sa ya hau tsuma, zazzabi mai zafi ya rufe shi, makwallatonsa na kaiwa da komowa, zuciyarsa kamar ta hudo kirjinsa ta fito sabida yadda take hawa da sauka don bacin rai….. Ya dade bai shiga bacin rai irin na yau ba sakamakon wannan dogon tunanin da yayi. Ita da kanta Nenne ta lura da halin canjin mood da kalamanta suka jefa dan ta Prince AbdulRasheed, sai taji wani irin babu dadi a zuciyarta da kasan ranta. Ita ta san Abdulrashid dinta is always bold and smart fiyeda Taiwo, kasancewarta mace tanada saurin nuna rauni (sai karambani da rawar kai da shiga sharo ba shanu), but today he looks pale har fiyeda Taiwo uwar kankanba idan ta raunana. A ganinsa tunda har uwar data haifeshi ma ta fara yarda da zargin da duniya ke masa na cewa wai (he is gay), don kawai yana rayuwa a cikin turawan yamma, kuma yana practicing wasansu na tseren Doki a matsayin sha’awar ransa kuma sana’a mai girma, hujjar kowa ta makala masa wannan zargin shine kawai don ya ki yarda yayi aure ko kawo mace gidansa da sunan matarsa? Zargi wani abu ne mai girma da muni a musulunci balle zargi irin wanda duniya ke masa. Auren ai Sunnah ne ba farillah ba tunda Alhamdulillah yana iya rike kansa ta hanyoyin da addini ya koyar. Kusan kullum baka Abdulrasheed da azumin litinin da alhamis a bakinsa, baya kallon haramun, balle kai kansa inda ake aikatata, he is always busy planning and scheduling his Polo time-tables across the globe da tsara ayyukansa na Consultation a matatar man fetur a (Qatar refinery). Zina ai sai mutum ya bata kafa take shigowa rayuwarsa. Ga kuma addu’ar tsayayyyar Uwa irin Nenne Sappa a kansa kullum wadda zamu iya cewa itace babban makamin dake katange Abdulrasheed ga ayyukan sabo in akayi la’akari da yanayin rayuwar ‘yan Polo. Duk da cewa Nenne ta yi dana sanin furta masa damuwarta, amma kuma hakan ya taimakawa zuciyarta, yanayin da ya shiga kadai yasa ta rage tasirin zargin na mutane daga ranta akan dan nata, ko daga irin halin rudu da damuwar da ya shiga akan maganar kadai ta gane ba haka bane, zargi ne mai muni ake masa da shaci-fadin mutane da basu da gadon ka sai gadon magana akan ka. Ita kawai tayi la’akari ne da fadar nan ta hausawa dake cewa “ka haifi Da, amma baka haifi halinshi ba” kuma akace wai “ba’a shaidar ‘ya’yan yau”, da kuma yadda kana tufka a matsayinka na uwa; modern society da influence na ilmin zamani na warware maka tufkar ta baya, musamman shi AbdulRasheed da in akayi la’akari da irin ‘life-style’ dinsa, wato yanayin rayuwarsa da yadda yake gudanar da ita gabadaya kome aka ce akansa al’umma bazata musa ba. “To me ya hanaka aure har yau Kehinde? Na roke ka da girman Allah yau ka gayamin. Ni mahaifiyarka ce da baka da wanda ya fini ba kuma wadda zata rufa asirinka a duniya irina. Shin idan baka sanar dani hakikanin matsalarka ba, wa zaka sanarwa a duniyarnan?” Zuwa lokacin ya soma dawowa cikin hayyacinsa, amma maimakon ya baiwa Nenne amsar data dace da tambayar data yi masa, wato menene hakikanin abinda yasa ko zancen aure baya kaunar a yi masa? Sai ya bige da maida zancen wani kala daban, don Nenne ta bar zancen, don har gobe babu wanda ya san abinda Adetokumbo yayi masa kaf cikin zuri’ar su, daga shi sai shi Tokumbon, sai kuma Taiwo, sai ita shaidaniyar HASINAH! Da bai san a wace duniyar take yanzu ba. Sai kuma Allah da ya haliccesu. Zai kuma cigaba da barin wannan zancen a ransa yana haunting dinsa shikadai ba tareda ya gayawa wani a danginsu ko iyayensu ba bayan Taiwo, albarkacin zumuncin Akanni’s da hadin kan gidansu. Yau ace wani cikin zuri’ar Emir Abdulrasheed Akanni yana zina da macen da ba tasa bama abu ne da zai taba mutuncin su bakidaya, abun kunya ne ba karami ba, ga zuri’ar sarki Abdulrasheed Abdullateef Akanni a idon talakawansu dake ganin martabarsu da girman nasabarsu, wanda zai iya lalata hadin kan gidansu gabadaya wanda gida ne ko kuwa zuri’a ce data zamo abun buga misali a ciki da wajen jihar Ilorin. Sai ya maida abun zolaya ga Nenne, bayan ya maida murmushi mai sanyi akan fuskarsa, Prince ya soma magana cikin lallashin mahaifiyarsa. “To yanzu Nenne, ki gayamin saboda Allah, duk fadin Najeriya wacece kike ganin zata aureni da tsillin furfura kamar yadda Fatima tace, umh? Ta kuma kaunace ni da furfurar nikadai ba tare data hada soyayyata data wani na ba? Ba kuma don abin duniya da reputation dina (shaharata) a kan wasan Polo ba, soyayya pure nake nufi tsarkakakkiya ta saboda Allah! A dai yawan shekaru irin nawa, wadanda babu sauran kuruciya a cikinsu yanzu? Believe me Nenne, duk matan zamanin nan, ina fade ina karawa kullum (are nothing but gold-diggers) sannan karnukane babu daraja a tare dasu. Daga kan HASINAH AMBURSA… na gama rufe babin mata Nenne, (they just want money over pure LOVE), don haka basa gabana gabadayansu Nenne, har abada babu ni babu ‘ya’ya mata”. Nenne sai ta bishi da ido zuruuu! Ta kasa gane inda zantukansa suka dosa. Me Hasinan da ta san yanaso kamar ya cire ransa ya bata tayi masa da ya karya zuciyarsa haka? Ashe a kanta ne yake gudun mata tun zamanin samartakarsa? Ta dade bata kara jin komai game da Hasinah din ba. Ko daga bakin aminiyarta uwar dakinta (Taiwo) bata kara jin