Sashe 23
Aisha Siddiqa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kawai in karaso asibitin in sameku can, ai bani ita zakiyi in tafi da ita Lagos kawai ko na sati biyu ne taga likitan Firdausi, tunda an yi hutun makaranta, Dr. Femi ya kware sosai akan treating asthma”. Umman Siddiqah ta kwatanta mata inda zata same su a female ward. Tana fadi aranta “ba inda zata iya bari Petel taje inba cikin dakinta ba, in ka san soyayya ta rabin rai ta Aisha-Siddiqah da Ummanta ne”. Mintuna ashirin ta kawo su har kofar dakin da Aisha Siddiqah take kwance, sai Nenne ta kira Haj. Zainab ta sanar da ita suna bakin kofa. Hajiya Zainab ta fito ta yiwa Nenne jagora zuwa cikin dakin har gaban gadon Aisha-Siddiqah. Wanda daki ne na mutum daya (sideroom) a sashen kwanciya na bangaren mata. Nenne ta sa kai a dakin bakita dauke da sallama. Kallo daya Nenne Sappah ta yiwa “AISHA-SIDDIQAH YUNUS” dake kishingide a gadon marassa lafiya da karin ruwa a hannun ta taji wani bakon yanayi a tare da ita. Idanun Nenne basu sauka a ko’ina ba sai akan warawaran zinaren dake hannun ta wadanda suka kawata halittar fatar hannunta fara sol. Ga yarinyar ‘yar karama da ita (mai karamin ruwa) wato irin amsu karamin jikin nan ce siririya sosai kamar in ta sunkuya karyewa zata yi. Idanunta kamar na kwan zabo, masu haske da kyau. Nenne tayi birki a gaban gadon Siddiqah ta kama hannunta mara allurar a jiki tana kallonta da murmushi, Siddiqah wadda ke kishingide akan filo, rike da dan littafin addu’o’I na hisnul muslim a hannunta ta daga fararen idanunta a hankali tana kallon Nenne Sappa. Umma bata lura da yanayin kallon kaunar uwa da Haj. Sappa ta fada akan Siddiqah ba, tana ta faman lale-maraba da Hajiyar Lagos, (jabbama-jabbama), ta bata farar kujerar roba ta ‘yan dubiya don ta zauna amma ina! Hankalin Nenne Sappa ya tafi ga wani tunani daban. Ya bar jikin ta gabadaya. Domin dai yau ji take a jikin ta ga uwar jikokin ta, wato ga matar Prince Abdulrasheed Kehinde Idris Akanni, yau Allah ya nuna mata da sauran numfashinta, wadda ta dade tana ganin surarta a cikin mafarki duk ranar data yi istikhara akan sha’anin auren Prince Kehinde. Ta dade, ta jima tana ganin wannan kyakkyawar fuskar a cikin barcin ta, bata taba sanin alaqar yarinyar da mafarkan istikhararta ba. Taji a ranta bata iya barin Gombe ba tareda Aisha-Siddiqah ba. Lokacin da Aisha-Siddiqah ta bude baki tana gaida Nenne da sassanyar muryarta ta mai jinya Nenne kasa amasawa tayi, domin Aisha da komai nata ya shiga ran Nenne farat daya (daga gani na farko). Ji tayi kamar ta sace ta kawai ta gudu da ita Ikko, in yaso ta aurawa Prince Abdulrasheed Kehinde. Ta san dai ko zaiki kowacce mace banda wannan kyakkyawar halittar dake gabanta. Da kyar ta iya amsa gaisuwar Siddiqah da wani kyakkyawan (maternal feeling) akan fuskarta. Kafin su zauna su bude babin hirar Saudiyyah tsakanin Hajiyar Lagos da kawarta Hajiya Zainab irinta wadanda suka aminta da juna, tabbas kawancensu hadin Allah ne kawai, domin ajin rayuwarsu ko kusa ba daya bane. Allah shi yake hada mutum da mutum su kaunaci juna saboda Allah. Nenne tace da Haj. Zainab ta nema mata iznin Baban Aisha tana so ta tafi da ita Lagos taga likitansu Firdausi, kwararre ne sosai akan lalurar huhu da numfashi, wanda shi yake duba Princess Firdausi (itama asthmatic ce), daga nan tana so Aisha ta karasa hutun wannan zangon a hannun ta. Hajiya Zainab tayi dan jimmm! Kafin tace “Babanta yana wajen aikinsa amma na san ba zai ki baki Petel ba, don ba tun yau yake da labarinki ba, zan masa bayani idan ya dawo kafin ki gama abinda ya kawo ki Gombe, kwarai nice dai zanyi kewarta, don bama raba gari tun haihuwarta sai da ta fara makaranta a Billiri. Akwai yaron da ke rikon neman aurenta Ishaqa dan makwabtanmu, yana jami’a a Ibadan, yanada da hakki shima a sanar dashi kafin ku tafi din”. Nenne tace cikin jin faduwar gaban ta sameta a take “an yi musu baiko ne?” Kafin Haj. Zainab ta bata amsa Nenne ta kira sunan Allah sau ba adadi tana neman daukinsa akan Allah yasa Aisha rabon su ce. Wani ikon Allah sai Haj. Zaina tace “A’ah tukunna, Ishaqa dalibi ne a jami’a, mahaifinsa yace sai ya kammala ya fara aiki koda zai masa aure, suna dai matukar kaunar juna shi da Petel kowa ya sani, sabida shi Aisha bata sauraron kowa. Gida biyu ne a tsakanin mu dasu, tare suka taso tun suna kanana soyayyar ba ta yau bace, kuma dai Ishaq yana da hankali da nasaba mai kyau, ya dade yana hidima da ita don haka dukkanmu mun yi na’am da shi tuntuni sai fatan Allah ya nuna mana lokacin”. Aisha na jin su, kunya kamar tayi yaya! Sai ‘yan mutsu-mutsu take kamar tace kasar ta tsage ta shige. A karshe Haj. Zainab da Haj. Sappa sunyi sallama kan sai jibi zata zo ta gana da Baban Aisha, in ya amince ta wuce da ita Lagos ganin kwararren likitan numfashi da huhu. Da Nenne zata tafi ne ta matsa gaban gadon Siddiqah. Tana murmushi tasa hannu ta shafa gashin kanta cike da damuwar ganin yadda take ta kokawa da inhaler ita kadai, tace “get well soon my dear, Allah ya baki lafiya kinji ko Siddiqah? Sai na dawo”. Har bakin mota Haj. Zainab ta raka Nenne. Suka sake kafa sabuwar hira kafin suyi sallama da kyar. Nenne Sappa ta samu dan uwanta Uban kasar Gombe da iyalinsa lafiya, suka sha hirar zumunci irin wadda suka dade basu sha ba. Kafin ya gaya mata maqasudin abinda yasa shi kiran da yayi mata, wanda dama ta tsammace shi tun ma kafin ta ji shi. Maganar dai guda day ace. Gabadaya danginta da iyayenta da dangin mahaifinsa da nasa mahaifin basu da damuwa yanzu sai ta auren Prince. “Ki turo AbdulRasheed ya zo ya ga ‘yar uwarsa Naziha, malaman fada sun gayamin idan har ba auren muka yi masa da kanmu ba, a haka zai kare rayuwarsa bazai taba kawo mace yace yana so ba don sunce aljana ta aure shi. Sannan ance dani akwai aguminsu na maketan Yarbawa makiya Kakansa, akwai kuma sihiri irinna magauta gidansu duk a jikin sa, bazai taba ganin mace yace yana so ya aura ba”. Nenne tayi ajiyar zuciya cikin damuwa, bata son irin wannan false beliefs din ita sam, gasgata malaman tsubbu da Yayanta Uban kasa ke yi a rayuwarsa yana damunta, ita tafi yarda da cewa auren Abdulrasheed LOKACI ne bai yi ba, kuma koda yayi din, duk da za’a kira shi ‘LATE MARRIAGE’ tofa ba zai wanke masa tarihin cewa ya jima bai yi aure ba, don haka ba kowacce mace zata yarda ya aura ba musamman cikin ‘ya’yan ‘yan uwa don kada abata zumunci in ya jingine musu ‘ya’ya saboda Polo. Ta rasa abinda zata ce da Uban kasa, a karshe ta samu bakinta yana bashi hakuri, tana fadin ta yi wa AbdulRasheed mata, kuma anan Gombe, sannan cikakkar bafullatana diyar dattijai. In sha Allahu data koma Lagos zata gabatar da maganar ga mahaifinsa. Uban kasa bai ce a’a ba, duk da yafi matukar son Abdulrasheed yayi aure a cikin gidansa, saidai ya nemi jin su waye iyayen yarinyar data ke ikirarin ta samar masa ta kuma fada masa, yace zai yi bincike akan Malam Yunus din da sana’arsa da gaggawa. Ba’a kwana ba, ba’a yini ba saida komai na Malam Yunus ma’aikacin hukumar Alhazai tsohon malamin federal government na jihar Gombe ya zo kunnen Uban kasa har asalinsa, duk wata shaidar arziki da kyakkyawar nasaba malam Yunus Hamza da maidakinsa Haj. Zainab Hamza sun gama samun ta a unguwarsu Jeka da fari. Sunyi waya da Haj. Zainab a ranar da zata wuce Lagos bayan an sallamesu daga FMC cewa tana tafe a hanya zuwa gidan Malam Yunus. Yau ko fita Abba bai yi ba, yana jiran zuwan Haj. Zainab. Bakuwar da matarsa take ambata da alkhairi kamar tafi kowa kirki da darajta dan adam a duniya. Nenne ta iso wajejen karfe goma na safe don taredasu ma ta karya kumallo da kunun gyada da kosai mai zafi a falon Haj. Zainab. Aisha na daki tana ta kumburi, Ummah tace wai zata bi kawarta Lagos tayi hutu kuma taga likita. Tunda Aisha take a duniya bata taba barin garin Gombe ba, kai ko Azare bata taba shiga ba banda Billiri makaranta, balle akai ga kwana da wani wuri da ba makaranta ko dakin ta ko na Ummanta ba. Aisha akwai makon UWA, irin yaran nan ne da gasu dai sun girma, amma kamar yaran goye suke agaban iyayensu mata, ko kusa bata son gusawa daga jikin Ummanta. Amma yanzu maganar zata je tayi sati biyu a Lagos ake yi. Tun jiya da taki hada kayanta Umma da kanta ta hada mata. Tana ta lallashin ta da cewa Haj. Zainab bazata roki alfarma ta kasa yi mata ba. Kuma dai lafiyarta ake son ingantawa. Budar bakin Aisha sai cewa tayi (cikin alamu na karyewar zuciya da damuwar cewa yau Umma tace zata tafi wani gari ta kwana ba tare da ita ba). “Amma dai Umma kinsan ba yau na fara ciwona ba ko, wane irin likita ne ban gani ba? Kuma Umma kin dai san Asthma bata da wani magani bayan inhaler ta da wadanda nake sha yanzu ko?” Umma ta girgiza kai itama ranta a dame da damuwar Aisha tace “babu ciwon da bashi da magani sai tsufa sai mutuwa kinji ko Petel, shi magani dace ne, shin Siddiqah in baki koyi shiga mutane yanzu ba sai yaushe ne? Ko wajen yan uwana ko na Abban ki ba kya yarda ki je ki kwana, kada ki manta watarana aure ne zai raba mu gabadaya”. Ai kuwa Aisha ta balle da kuka tana fadin “Umma in kika sake cewa zamu rabu in nayi aure to bazan yi auren ba har abada”. Umma na dariya tace “to ai Ishaq din bazai yarda ya daukemu mu biyu ba, mun yi yawa a gidan Ishaqa”. Aisha ta hau rantsuwa, kan cewa sun dade suna kulla alkawari itada Ishaq cewa in yayi kudi ya tashi ginin gida zai ginawa Umma daki a gidan sa,