Sashe 6
Aisha Siddiqa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a lokuta na bacin rai irin wadannan. ***** **** **** WAIWAYE ADON TAFIYA (2) (AMBURSA ORPHANAGE) A mbursa karamin gari ne a jihar Birnin Kebbi. Prince ya saba da irin wadannan tafiye-tafiyen cikin garuruwa da kauyukan Arewa a duk lokacin da yazo kasarshi ta haihuwa, kasancewar rayuwarshi tafi yawa a yankin Tokyo ta (Japan). Dabi’arsa ce kaunar marayu, don haka duk inda ya samu labarin akwai gidan marayu ya kan ziyarta, komai nisan garin daga inda yake, baya kasa a gwiwa zai je don kai tallafi. Idan yaje din kuma sai ya zaga ciki ya gansu, ya gaisa dasu, ya shafa kawunnansu, yana mai godewa Allah cikin zuciyarsa dashi yayi masa ni’imar iyaye, masu kykkyawan asali daga tsatso mai albarka, iyayen ma jajirtattu irin ‘Nenne’ da ‘Dade’ da ba duk duniya ake da irin su ba. Shi ba attajiri bane a lokacin dalibi ne, amma yanada attajirar zuciya, ‘philanthrophy’ musamman ga marayu a cikin jininsu ne na iyaye da kakanni. Kusan zamu iya cewa ya gaji wannan (positive attitude) din na son marayu da son inganta rayuwarsu ne daga Kakansa. Sarki Akanni mai ran karfe. A zuciyarsa yana tausayin maraya a duk inda ya ganshi, yana kuma jin maraicin da suke ji a ransa, ba don shi din maraya bane. Yana yawan kwatantawa a ransa inda ace shine su, yake rayuwar da suke yi a kange, babu Nenne da Dade a gefensa, a samansa da kasansa, ko yaya rayuwa zata kasance masa? Yana kan hanyarsa ta isa gidan marayun Ambursa ne daga Birni Kebbi, inda yaje halartar daurin auren abokin karatunsa Bello Dasuki. Bello D. abokinsa ne tuntuni da sukayi karatun sakandire tare a Japan a lokacin Baban Bello Jakada ne acan, dan asalin Birnin Kebbi. Don haka ne bai ji kiwar yin tattaki tun daga Lagos ya halarci daurin aurensa ba. Hira ce tayi hira tsakanin shi da Bello Dasuki bayan kammala reception na daurin aure, Dasukin na tsokanarsa da UBAN MARAYU! Inda sabo ya saba da wannan sunan daga bakin Dasukin, tun daga lokacin da ya nemi rakiyarsa zuwa wani gidan marayu a Bauchi. Dasuki yace dashi cikin hira ai kwanannan suma an bude musu sabon gidan marayu a garin iyayensa wato Ambursa. Zancen ya wuce, kamar bai ji ba ma, suka shiga wata hirar ta abubuwan da suka shafesu na POLO. Har sukayi sallama da Bello Dasuki zai wuce Airport, inda daga nan zai tashi zuwa gida Lagos, bai gaya masa zai ziyarci gidan marayun nan da ya bashi labari ba. Kawai tunaninsa na alkhairi ya gaya masa akwai bukatar yaje sabon gidan marayunnan ya gani, domin akwai wasu kudade tare dashi masu dan dama da yayi niyyar kaiwa gidan marayu na jihar Gombe, kuma ya tuna bazai samu zuwa Gombe ganin Kakarsa Oummana kafin ya wuce Japan ba lokaci zaya kure masa, tunda kuma daga Birnin Kebbin zuwa Ambursa babu nisa bari kawai ya karasa can, ya basu tallafin sannan su wuce Airport din Sokoto. Umarni yayiwa direban Bello Dasuki wanda ya dauko shi a motar Dasukin, da ya karkata kan motar ya juya dashi zuwa Ambursa. Ya ce dashi ko basu san wajen ba suyi ta tambaya. Don haka suka tasarma kauyen Ambursa, kuma koda suka shiga garin basu sha wahalar tambaya ba kasancewarsa kwararren direba kuma dan gari, suka samu sabon gidan marayun, wanda ba’a dade da kafashi a jihar Kebbi ba, sakamakon yawaitar tsintar ‘ya’ya da walagigin marayu a jihar. A saman gidan manyan rubutu ne da shudiyar kala an rubuta AMBURSA ORPHANAGE. Shugabar gidan marayun Mrs. Taibat ta karbeshi sosai, domin da gani babu tambaya; irin bakin da suke maraba-lale dasu ne, wato ‘ya’yan manyan kasa masu zuciyar taimako. Wato masu kawo tallafin kudi, ko na karatu ko na suttura ko abinci ga yaran, duk da bata san waye shi ba, amma ko daga yanayin tafiyarsa da kasaitarsa da maganarsa tasan dan manya ne, mai alaqa da sarauta. Don haka ita da kanta tayi masa jagora har wajen jarirai da ake kulawa dasu da madara, daga nan suka isa gun toddlers, ya gansu, ya shafa kansu harda yi musu wasa sosai kasancewarsa mai son yara. Sannan ta kaishi bangaren yara mata masu tashen balaga (teens) ‘yan makaranta. Anan idanunsa ya kyallo masa ita, bahaushiya ce, babu ko tantama mai kyau ce sosai, daga duba na farko zaka ga kyawun nata a zahiri, duk ‘yammatan sun lura da shigowar Madam tareda bakon, amma ita yarinyar bata lura ba, suka soma gaishe su duk hankalinta bai kai kansu ba, sai da Madam Taibat tace “Haseenah baki ga baki bane?” Da sauri yarinyar ta dago jin an ambaci sunanta, yayi mata murmushi ya karaso har gabanta yace “sannu da karatu Haseenah!” ta amsa, ta kuma gaishe shi sai ya karbi littafin hannunta yana dubawa. “Basic Science and Technology” ya ga an rubuta a jiki. (For junior secondary schools). Yarinyar zatayi sa’ar Hakeem dan abokiyar tagwaitakarsa Murjanatu. Don haka kawai babu shawara da Nenne yace bari ya dauketa daga nan ya kaiwa Murja in yaso ta hadata da Hakeem su cigaba da makaranta. Kyawunta ya fisgeshi sosai a matsayinsa na namiji, sannan jan ajinta. Dama ance irin wadannan ‘ya’yan kyau ne dasu. “Ajinki nawa Haseenah?” “Bana na gama JSS” (tana magana kai a sama, cikin ko’in kula) da gani ba wadatar tarbiyyah. “Kinada burin cigaba?” “Sosai ma kuwa, Enginiya nake so na zama”. Sosai yaji yarinyar ta bashi tausayi ko don yadda take magana kanta tsaye da boldness kamar ba marainiya a gidan marayu ba, don mostly yaran zaka same su basu da karsashi, basu da ko guts na karfin gwiwar kallon mutane ma cikin ido, sabida (inferiority complex) dake dabaibaye dasu, amma ita kar take kallonsa cikin ido, idanunta a tsaitsaye, ko kuma don kasancewar fanninsa kenan wanda ta zaba din a matsayin burinta yasa yaji ta burge shi? Don haka koda suka koma ofis shida Mrs Taibat yayi abinda bai taba yi ba tunda yake zuwa gidan marayu daban daban, watau yabi duk process din da ake bi na daukar yaro a gidan, na daga cike-ciken takardu ha a karshe yayi (adopting) dinta. Amma a ransa ya san ba dai ya kaiwa Nenne ba, yayi abunsa kai tsaye without a second thought, saidai ya kaiwa Murjanatu, it ace mai biyewa komai yake so mai kyau ko mara kyau, in yaso ya dinga daukar nauyin karatunta a makarantar kwana, shi dai yaji ransa na son kyakkyawar yarinyar, in yaso in akayi hutu ta zauna gidan Murjanatu har ta isa shiga jami’a ya nema mata admission a fannin Engineering din duk da take so. Ko iya haka aka tsaya ya gina rayuwarta, tunda in ta gama zata iya samun aikin da zai isheta kula da kanta har watarana ta tallafi gidan marayunsu da marayu ‘yan uwanta. ***** ***** **** Ya damka amanar yarinyar a hannun wato Aunty Murjanatu, ya kuma fara biyan komai na karatunta tareda Hakeem yaron Murja. Lokacin ba’a haifi Kiki ba. Murja ta kaisu makarantar kwana ta British int’l school a garin Lagos. Kasancewar duk abinda dan uwanta ke so bata opposing tana taya shi ne su cimma abinnan. Ta dade da sanin philanthrophic heart dinshi, na cikin dabi’un shi masu kyau, da suka banbanta shi da sauran matasan zuri’arsu kaf! Ta yarda ta amince babu mutum mai zuciyar halin girma da daukar girma tun bai girma ba cikin jikokin gidansu kamar Prince, duk wani hali irin na Kakansu Emir Abdulrasheed ya kwashe shi ya bar kowa da sudin kwano. A kafatanin zurri’ar gidansu ba mai kyakkyawar zuciya ta taimakon mara galihu irin ta dan uwanta Prince. Tun daga kan kannen mahaifin su, har zuwa tulin ‘ya’yan da suka haifa, ba wanda baya shan rabar taimakonsa (in one way or the other). Shi Da daya ne tamkar da goma ga iyayensu. Gidansu ba’a tara ‘ya’ya maza ba, shikadai ne namiji a cikinmata amma ya tarewa iyayensu gurbin misalin yara maza goma! **** **** **** Shekaru uku suka zo suka wuce da tarin cigaba ga yarinya Haseenah, bai yi kasa a guiwa ba yana biyan kudin karatunta tare dana Hakeem duk shekara, wadda da aka tashi bata permanent name a makaranta sai ya bata surname da sunan marigayin abokinsa Bello Ambursa, wanda ya rasu gaba kadan da daurin aurensa. Hakika Prince ya ji mutuwar Bello ba dan kadan ba, kullum ya ga Hasinah sai ya tuno shi har kaunarshi da Bello Ambursa ta shafi Haseenah Ambursa, ko bakomai sanadinsa yaje har inda take ya daukota. Daga kan Bello bai kara yin aboki ba sai Tokumbo wanda dama Cousin dinsa ne da suka taso tare. Duk sanda ya zo kasar Najeriya zai je wajenta a makaranta suyi ta tadi, in kuma suna hutu ne tana gidan Murjanatu acan yake ganinta har sabo mai tsanani ya gitta a tsakaninsu. A haka har Haseenah ta gama sakandire, a shekarar data kammala ya samar mata gurbi ya kuma yi sponsoring karatunta a wata jami’a a kasar da yake nasa karatun a lokacin, wato Tokyo. Wannan ne ya kawo kusanci na kamshin soyayya tsakanin sa da marainiyar da yake riko Haseenah, wanda (in no time) ya rikide musu zuwa soyayya. Har shi da Murjanatu suka yanke shawarar ya aureta kawai, don a zamanta a Japan duk da a hostel take rayuwa, tofa kullum tana like dashi a gidansa fiyeda sanda take hannun Murjanatu da gaisuwa da hirar makaranta kadai ke shiga tsakaninsu, acan kuwa bata san kowa ba sai shi, shiyasa koyaushe take like dashi a gidansa a lokutan da bata da karatu, musamman da idanunta suka fara budewa da maza ta san menene soyayya. Sun yanke shawarar shawo kan Nenne don ta yarda ya auri Haseenah shida Murjanatu gudun sharrin shaidan ya gifta tsakaninsu, to kullum suna tare a inda ba idon kowa nasu a kansu, yace da Murjanatu yana tsoron watarana ayi abinda ba shikenan ba duk da yana fin karfin zuciyarsa, amma Nenne ta kafe ta ki. Soyayyarsu shi da Hasinah tayi tsananin karfi a lokacin har suka soma sakin layi. Sun buga sun buga da Nenne ta bari ayi auren har lokacin ta ki, don zaman da take yi dasu ma Nenne bata so, tafi so kowanne irin taimako zata yi maka tayi maka shi daga nesa, ba tareda ta dauko ka ta saka cikin