Sashe 12
Aisha Siddiqa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
samar masa abinda zaya ci mai zafi da nauyi wato Amalar bawon doya miyar Ewedu data ji naman turkey da smoked fish zuku-zuku. Saida ta tabbatar ta masa favourite food dinsa ya ci sosai ya sha tea na nescafe mai zafi, sannan ya kishingida akan sofa da Kiki a gabansa yana wasa da ita. Ko a kwayar idonsa ta lura yunwa tayi masa lahani a kwana biyar ba kadan ba, kasancewarsa mutum mai yawan cin abinci, kullum Nenne na cewa “his best friend is food”. Idan akwai abinda yafi karyawa namiji zuciya toh Hasinah ta karya maza, ta karya zuciyarsa raga-raga. A daren shi da Taiwo sun zauna sun kara tattaunawa kan al’amarin da ya faru dashi da Hasinah, kuma Taiwo bata barshi da mummunan tunanin da ya riga ya tsirga ya samu muhalli a zuciyarsa ba na cewa duk mata haka suke, tayi ta bashi baki da kwantar masa da hankali da bashi kyawawan misalai iri daban – daban na halin lalacewar da al’umma ke ciki a wannan zamanin, tace don haka wannan bazai zamo wani abin mamaki daga halayyar dan adam ba. Taiwo ta kara da cewa “ka yarda ba kuma duka mata muka taru muka zama daya ba a halayya da dabi’a, ta kara da nuna masa cewa Hasinah ba itace karshen rayuwarsa ba, sannan ba itace autar mata ba, wasu matan ma nagari ko haihuwarsu ba’a yi ba, tace kada hakan yasa ya fidda kyakkyawan fata akan mata tagari. A cewar Taiwo, “mata nigari yanzu aka fara haifarsu”. Shirmen Kiki ma ya taimaka kwarai wajen cheering dinsa up. Ya fara murmushi, murmushinnan nasa mai matukar kyau da aji, da Kiki ta hau jan kasumbar daya bari a fuska wadda bata saba gani a tareda shi ba, ya dan fara sakin ransa da mantawa da damuwar Hasinah Ambursa don ita tafi bashi mamaki fiye da Adetokumbo wanda dama su maza ai kunyarsu ragagga ce akan macen da zuciyarsu ta kwadaita musu. Shikuwa Tokumbo Akanni a ranar bai kara kwana a Tokyo/Japan ba, yana jin karshen shigarsa kasar Japan din kenan gabadaya, har dai in Abdulrasheed yana cikinta, duk da a can ne harkokin kasuwancinsa suka fi yawa. Taiwo da Kiki, basu baro Tokyo ba saida suka kwashe sati tare da Prince Abdulrasheed (Kehinde), har sai da ta tabbatar Prince din ya manta da damuwar da Hasinah ta haddasa masa, ya koma harkokinsa da rubutun project dinsa amma ko sunanta yace kada ta kara ambata masa. A zahiri Prince Abdulrasheed ya saki ransa sosai yadda Taiwo keso, har ya koma harkokinsa na baya ya soma duba schedules na tournaments, yayi kokarin da ya kammala project dinsa kaf tun kafin barin su Taiwo gidansa. Musamman da komai Taiwo ke masa cikin gidan na kula da abincinsa da tsaftar gidansa da lallashinsa shi kawai aiki yake wuni yi akan kwamfuta. Amma abinda Taiwo bata sani ba shine mummunar illar da incidence din yayi a zuciya da tunaninsa, ya riga ya gurbata psyche na tunanin sa akan mata da soyayyar dukkan diya mace in general. Ranar da suka kwana bakwai tare dashi Taiwo da ‘yarta suka juyo gida Lagos cike da kewarsa. Da alkawarin sai sun zo bikin kammala karatunsa nan da ‘yan watanni masu zuwa. ***** ***** **** WACECE NENNE SAPPA? N enne (na nufin ‘Uwa’ kenan), da harshen fulatancin Arewacin Najeriya na sassan Gombe, Adamawa da Taraba, wanda Hajiya Sappa ta fito daga cikinsu, kuma da shi yaranta ke kiranta, Nenne Sappa, irin iyayen mun nan ne na zamanin da, masu halin zuhudu (gudun duniya), taqawa, da tsananin yawan ibadah wadanda duk halaye ne na NANI OUMMANA. Mahaifiyar ta Nani Ummana ta kasance mace mai yawan kaskantar da kai, da gudun rudin duniya, wadannan sai suka zamo halaye ne wadanda dasu ta raini Sappa, duk wani halin tawali’u wato humbleness (a down to earth personality) Nenne Sappa ta hada shi cikin kyawawan halayenta. Nenne Sappa ta kasance kyakkyawar dattijiya, fara ce kal, jazur da ita mai yalwar sumar kai, gira data idanu, mahaifiyarta Nani bafullatanar garin Gombe ce don haka kusan zamu ce kamanninta Sappa ta debo, wadda yawan shekaru baisa kyawunta ya gushe ba sabida hutun da take ciki kuma jikinta mai boye shekaru ne, yanayin jikinta ya nuna cewa an zuba kyau da farin jinin manyan sarakuna a zamanin kuruciya. Kai kace Sappa ita ta zabarwa kanta duk wata kankanuwar halittar dake jikinta don kyawun fasali, har zuwa yanzu data baiwa sittin da biyar baya, Nenne Sappa, na nan da extra added beauty dinta (zallar kyawunta). Kenan a takaice sai mu ce Nenne, (Hajiya Sappa) ta samo personality dinta na (Down to Earthiness) ne daga mahaifiyarta Nani Oummana, wadda ta kasance uwargida a cikin duka matan Maimartaba Uban Kasar Gombe, Sarkin Gombe na goma, wanda duk da kasancewarsa basarake to gawurtaccen Shaihun malami ne shima. Nenne itace ‘ya ta biyu cikin ‘ya’yan da ya haifa masu tarin yawa da matansa na aure hudu. Cikinsu duka yafison Oummana da suke kira Nani wadda ta kasance mahaifiya ga Haj. Sappa. Bayan rasuwar Sarkin Gombe wato mahaifinsu Nenne a dakinsu ne aka gaji sarautar. A halin yanzu Yayanta da suka fito ciki daya ne akan karagar mulkin Gombe wato Maimartaba Sarki AbdulYassar Jalloh Umar (CFR). Tsohuwa Oummana ta cigaba da zama ne a dakinta bayan rasuwar sarkin Gombe Ahmadu Jalloh Umar, yayinda sauran matan da yake da sauran kuruciyarsu duk suka fita suka sake aurarraki. Don haka ta zama uwa ga ‘ya’yan sarkin Gombe bakidaya wadanda ta haifa da wadanda bata haifa ba wato diyan kishiyoyinta duk ta hada ta rike ta mayar nata don yanzu babu iyayensu mata a gidan. Sarki AbdulYassar babban dan Nani Oummana shi Hajiya Sappa ke bi haihuwa, sai autan Nani Abdulmajid wanda ke kasar Morocco da iyalinsa, sukenan ‘ya’yan da Nani ta haifawa uban kasa, sauran ‘ya’yansa maza da mata guda goma sha biyu duk na kishiyoyinta ne amma bazaka taba iya banbance wadanne ne wanda Nani Oummana ta haifa da wadanda take rikewa marigayin mijinta ba, saboda adalci da halin dattaku irin na mutanen da. Da irin wadannan kyawawan halaye Nani Oummana ta raini diyarta Sappa mace daya (Nenne Sappa) cikin maza har itama ta girma suka aurar da ta ga zuri’ar Akanni’s tun mahaifinta yana raye, har itama a yanzu gashi ta tara nata bataliyar iyalin. A yadda Hajiya Nenne take gudanar da rayuwarta wajen kula da tarbiyyar ‘ya’yanta hudu dake gabanta, sak halin mahaifiyarta Nani Oummana, ba bazaka taba cewa ita din ‘yar Sarki kuma jikar Sarki, sannan matar babban dan Sarki, uwa ga jikan Sarki na farko bace. Sabida yadda take nuna musu gudun duniya da mantawa da madaukakiyar nasabarsu, ita dai burinta shine su bi Allah, su kasance masu tausayawa mara karfi, su kiyaye sallah akan lokaci, su nisanci zinah kowacce iri kowanne nau’I ce, wannan itace tarbiyyar Nenne kullum ga yaranta hudu, duk wani burinta a yanzu shine ya zamo cewa halinta suke kwaikwayo, halin kankan da kai da tawali’u, shi takeso Taiwo da Kehinde da kannensu twins mata guda biyu wato Firdausi da Fatima su siffantu dashi. Amma me? Cikin ‘ya’yan nan nata guda hudu kowa halinsa daban da nata, babu mai irin halinta na kaskantar da kai. Suna gudanar da rayuwarsu ne bisa tsari na ‘ya’yan manyan sarakuna da irin tarbiyyar gidansu na Akanni’s wato yadda suka taso suka tarar a masarautarsu ta Ilorin. Kakansu Sarki Abdulrasheed da kansa ya taba cewa Nenne ta haifo masa jikoki masu halaye daban-daban da yake tinkaho da dabi’unsu na sarauta. Abdulrasheed baya rayuwa irin wadda take so, baya zama a kasarshi, rayuwa ce yake yi daidai data ‘ya’yan gata kamarsa, domin Kakansa ya tsaya masa. Taiwo kuma miji ya tsaya mata don ba karamin dukiya Toufeeq ya mallaka a turai ba. Sannan Fatima da Firdausi Yayansu Abdulrasheed da suke kira Hamma wato (Prince) ya dade da tsayawa rayuwarsu matuka, tun shigarsu jami’a yake dawainiya dasu, bai yarda Dade (mahaifinsu) ya kashe komai akan karatunsu da bukatunsu ko dawainiyarsu tayau da kullum ba, shine komai nasu, baya so su kannen sa su nemi wani abu komai tsadarshi su rasa tunda shi ba iyali ya ajiye ba, so kusan zamu iya cewa komai na Prince na ‘yan uwansa ne baida wani buri bayan walwalarsu da wadatuwarsu. Princess Fatima da Princess Firdausi nada albashi mai tsoka duk wata kai tsaye daga account dinsa zuwa nasu. Haka Kiki da Hakeem ‘ya’yan Taiwo. Hajiya Sappa kullum tsaye take a kansu da addu’a, shine kadai saukinta. Musamman shi da yayi nisa da ita, kullum ko a waya bata fasa tunasar da shi bin Allah, kaunar musulunci da kiyaye sallah, ko yana dauka ko baya dauka ita dai Nenne bata fasawa kuma bata fasa yi masa addu’a ta musaman a duk inda yake cikin duniya Allah ya kare mata shi daga rudin zamani dana kuruciya, kasancewarsa namiji daya tal a cikin mata uku da Allah ya bata. A yadda Hajiya Sappa take rayuwa cikin yawan ibadah kullum, da kula da bautar aure da mijinta uban ‘ya’yanta, kai sai kayi tsammanin ita din wata waliyya ce. Shigarta kullum cikin hijabai (jilbabs) kala-kala kamar bata da alaqa da kowacce sarauta. Duk shekara Hajj da umarah basa wuce Nenne Sappah, bata azumin Ramadhan a gidanta dake Lagos sai a birnin Makkah da Madinah duk shekara, wani abun burgewa da Nenne in zata je Hajji bata bin International saidai Pilgrims duk cikin halinta na (down to earthiness) da kaskantar da kai, wanda take bi duk shekara daga hukumar alhazai ta jihar Lagos zuwa Saudiyyah. Shekarun Nenne Sappa a halin yanzu sun kai kusan sittin da biyar a duniya. Yayin da mahaifiyarta Nani tayi tsufa mai inganci saboda ibadah, har yanzu cikin koshin lafiya Nani Oummana take rayuwa a Gombe da jinta da kuma ganinta garau. Tun Nene Sappa nada shekaru akalla sha biyar take gidan aure, kamar yadda na fada a baya mahaifinta Uban Kasar Gombe Ahmadu Umar Jallo, ya bada aurenta da hannunsa ga dan abokinsa kuma babban amininsa wanda ya kasance Bayeraben Ilorin (dan kabilar Yoruba). Saida Prince AbdulRashid ya cika shekaru ashirin a duniya, bayan Nenne Sappa da Waziri Idrisu sun fidda rai da sake haihuwa, sannan kuma yaki kara auren kowa saboda son da yake ma Nennen Prince Hajiya Sappa, AbdulRasheed shi ya saka mata suna