← Book details Aisha Siddiqa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 25

Sashe 21

Aisha Siddiqa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sanye da fararen kaya da bakake kusan bakidayansu, kalar kayan jikin maza fari, na mata baki ne tako kasa gane ko mai kama da ita. Haka ta daure jakar nan a cikin jikinta taje ta karasa jifanta ta dawo Hemarsu, tana ta addu’ar Allah Ubangiji ya hada fuskarta da Hajiyar Lagos kafin su gama zaman Minna su koma Makkah. Dadin abun ma ba’a sayen abinci a Minna, da bata san yaya Hajiyar zatayi ‘coping’ a wannan lokacin ba. Duk inda ta ga ‘yar Najeriya sai tayi kokarin ganin fuskarta, ko Allah yasa ta dace da ganin wannan kyakkyawar bafullatanar baiwar Allah, wadda haka kawai ta shiga ranta domin ta ga tsantsar mutunci da kamala a tareda ita. Washegari Haj. Zainab din tayi wani tunani, me zai hana taje Hemar alhazan Lagos ta duba ta a can? Sai ta kira maigidanta wanda tare sukazo kasancewarsa ma’aikacin hukumar alhazan jihar Gombe, sun samu kujerar Hajji ne ma sanadin aikin nasa ba karfine dasu cancan ba. Maigidan nata Malam Yunus, tsohon malamin (federal government) ne da ya jima yana koyarwa a makarantar sakandiren ‘yammata ta Bajoga, shekaru biyu baya Allah ya tarfawa garinsa nono aka dauke shi aiki a Gombe State Pilgrims Board (ma’aikatar alhazai ta jihar Gombe). Tun daga lokacin ne kuma suka samu damar da duk shekara yake samun kujerar hajji biyu, karkashin hukumar alhazai don su zo su kula da mahajjatan Gombe a Saudi. Shine yake baiwa maidakinnasa. Da kyar ta samo Hemar ‘yan Lagos, bayan ta ci tafiya da zagaye a cikin Minna har ta gode Allah. Haka Haj. Zainab tayi ta bin fuskokin mata Yarabawa daya bayan daya tana dubawa amma ko mai kama da wannan kyakkyawar dattijiyar bafullatanar bata gani ba, ita gashi ko sunanta bata sani ba balle ta tambaya, amma tabbas ta rike kamannin fuskarta da kyau. Ita gani take ma fuskar na mata yanayi da wata popular fuska data sani ko a hoto ne ko a zahiri, amma ta kasa gane inda ta san fuskar Hajiyar Lagos. (A rashin saninta, fuskar Haj. Sappa na mata yanayin kama ne data Sarkinsu na Gombe, wato Uban Kasar Gombe na wannan lokacin, wanda suke kamar an tsaga kara da Nenne Sappa, don shi ya sha nono ya saki ta kama. Allah bai tashi hada su ba sai ranar hawan Arfah a kan dutsen ARFAH. Bayan Haj. Zainab ta fidda ran ganin Nenne Sappa don damka mata dukiyarta. Har ta fara tunanin kaiwa hukumar kasar Najeriya ta Saudiyyah kudin tayi musu bayani. Haduwar tasu a filin Arfah ya zo ne indirectly ba tareda zaton kowaccensu ba. Addu’ar data ji matar bayanta ta daga hannu sama tana yi a fili ne ya ja hankalinta gareta. Hannayenta biyu matar ta daga cikin kaskantar da kai ga Ubangiji da tsananin ikhlasi da tawali’u cikin addu’arta, sannan cikin zubar da hawaye mai yawa a kan dutse mai alfarma na Arfah, ranar da Ubangiji yayi alkawarin baya juyar da addu’ar bayinsa akan wannan tsarkakakken dutse, taji matar tana yin addu’a ga haularta (abinda ta haifa) a fili cikin harshen fulatancin Gombe ziryan. “Ya Ubangiji ga Dana ABDURRASHEED dan IDRIS ABDURRASHEED (Kehinde), managarcin bawanka mai kyautatawa iyaye da kula dasu, mai tsantseni wajen ibadarka da kulawa ga ‘yan uwasa mata, mai yawan alheri ga danginsa da kyakkyawar zuciya ga kowa, mai tarin halayen kwarai na kyautata zumunci. Na roke Ka, Ka dubi halin da Kehinde yake ciki na rashin aure. Ya Ubangiji ka yanke masa, kasa yana da rabon yin aure a rayuwarsa, ka kare min shi daga duk wani nau’I na aikin sabon ka a dalilin rashin aure, Ya Allah”. Ta shafa addu’arta a daidai lokacin da take ji a zuciyarta Allah ya amsa mata, Mala’iku sun ce Ameen Abdurrasheed zai yi aure, kamar yadda Hajiya Zainab dake bayanta ma tace “Ameen” a fili, ta kuma tayata da shafa addu’ar itama zuwa tata fuskar cikin tausayawa, ganin yadda Nenne ke kuka tana addu’ar. Sai Nenne taji an dafa kafadarta a hankali ta baya, anyi mata sallama cikin nema mata amincin Ubangiji. Da far’a ta juya ta amsa tana share ido, kuma nan da nan suka gane juna. Suka rungume juna suka sauko daga kan dutsen Arfah tare rike da hannun juna. Hajiya Zainab ta kwanto lalitarta daga cikin jikinta, ta damkawa Nenne Jakarta hannu da hannu. “ga nan kudinki ne masu yawa da kika manta nake ta nemanki in baki. A bandakin da muka shiga a Munna kika mantasu, na nemeki kamar ba gobe, har Hemar ku ta ‘yan Lagos naje nemanki Allah baiyi haduwarmu ba, inata addu’a dai da rokon Allah ya hada mu cikin sauki in baki, don in aka shiga Makkah bansan halin da zaki fada wajen sayen abinci ba idan babu guzuri a tare dake, don kamar dukkan guzurinki yana cikin jakar nan.” Baki Nenne ta saki tana mamaki. Ta tuna zunzurutun dalolin dake cikin jakar. Sai ta kara rike hannun Haj. Zainab gam. Tare suka zauna akan kananun katifunnan na filin Arfah Haj. Sappa ta rasa da bakin da zata godewa wannan baiwar Allah. Abinda ya bata mamaki shine na farko da ganin matar ba wata wadata ce irin tasu a tareda ita ba, amma ta iya wannan halin na mutanen kwarai, mai wuyar samu a wannan zamanin. Dala na gugar dala da har dala dubu biyar ne a cikin battar, data kirga suna nan cif yadda ta lankwasasu ta ajiye a cikin zip ko guda daya bata yi ciwon kai ba. Ashe dama har yanzu akwai mutane masu wadatar zuci da gudun abun duniya irin haka? Nenne Sappa, ta tambayi kanta domin kwarai Haj. Zainab ta burgeta. Kudine da Abdulrasheed Kehinde ya bata domin tayi guzurin aikin Hajjinta dasu kamar yadda ya saba bata duk shekara. Da ta tabbatar ta yar da su taji babu dadi amma bata yi mamaki ba sabida irin gajiyar datayi da tafiya a lokacin a Munna, ji take kamar ta yanke kafafunta bakidaya ta yar, don suma sun mata nauyi da kyar take iya cirasu, balle jakar guzuri. Nenne da Hajiya Zainab basu rabu ba daga filin arfah ba sai da suka karbi adireshin junansu na hotel din da kowacce take zaune a cikin Makkah. Bayan sun koma Makkah Nenne ta soma tunanin me zata baiwa wannan matar a matsayin kyauta ta jinjinawa, sabida taji dadin wannan halin kwarai data gwada mata har fiye da kudin data maido mata. Nenne Sappa na matukar son mutum mai tsoron gamuwa da Allah, mai gudun duniya mai cin halal. Don haka da taje sayawa Princess Fatima warawaran zinaren data bata sautu a kasuwar Jiddah, sai ta sayi wasu warawaran (bracelet) again, sak irin na ‘yan biyunta Firdausi da Fatima wadanda kudinsu mai kima ne da daraja sosai. Data dawo daga Jiddah shagon zinaren kai tsaye ta wuce gidan ‘yan Gombe wato masaukin ‘yan jihar Gombe a Makkah. Da yake ta rike lambar dakin da haj. Zainab ta gaya mata, sai ta hau lifta (elevator) ta isa har kofar dakin, ta danna ‘door-bell’ daga ciki akayi mata iznin shiga sannan tasa kai ta shiga dakin da sallama abakinta. Nan ta tadda Haj. Zainab ita kadai a dakin dawowarta kenan daga Dawafi. Haj. Zainab tana ganinta nan da nan ta shaidata, ta kuwa shiga lale marhabin da hidima da ita da duk abinda take dashi a dakin na sakawa a baka, itace kawo Laban(Al-mara’i) itace kawo ‘Aseer’ wato jus mai sanyi. Kai har Gahwah data koyi sha a kasar ta hada mata wadda ake kira (Gahwah Al-Arabiyyah) ta zuba musu a kananan kofunan karau suka zauna a gefen gadon Haj. Zainab suna sha sai suka balle da hira. Ko daga yadda Nenne Sappa take magana kadai cikin yanayi na kasaita Haj. Zainab ta alakantata da Sarauta mai girma cikin zuciyarta, in kuma ba sarauta ba to da arzikin da ya zauna a muhallinsa, komai na jikinta kadai dake walwali cikin zobban zinare ya fallasa hakan. Sun dade suna hira kafin Nenne ta ce zata koma hotel dinta, don ta baro autarta Firdausi a daki kwance bata jin dadi tun dawowarsu Arfah a nasu Fundaq (hotel) din. Ta ciro warwaron data zo dasu a cikin battarsu ta damkawa Haj. Zainab a cikin hannunta. Ta ce kyauta ce tayi mata don su rinka tuna juna in su koma garuruwansu mabanbanta. Tana son mutane masu irin halinta na gaskiya da rikon amana. Sama da komai tsoron abin duniya. Haj Zainab ta ce “ba’a maida hannun kyauta baya, don hakata gode”. Kuma duk da bata san darajar wadannan warawaran ba, amma ko ba komai aka ce ido ba mudu ba ya san kima. Tayi godiya mai yawa sosai ga Nenne, tanakokarin gwada warawaran, cikin ‘yar dariyar jin dadin alkhairin da aka yi mata Haj. Zainab tace da Nenne. “Yo ni wannan ai bazasu shiga hannu na ba, sun min kankanta na yara ne, sai dai in kaiwa PETEL (AISHAH-SIDDIQAH), yafi kama da na ‘yan mata”. Nenne ta ce “har nawa kike da bazakiyi kwalliya da awarwaro ba?” Nan ta daga nata hannun tana nuna mata nata warwaron guda shidda tace “bana rabo dasu a hannayena don su din adon diya mace ne. suna karawa kwalliyar mace kima su da zobuna, wacece Petel-Aisha-Siddiqah kuma? Halan kinada ‘ya budurwa ne kema kamar su Fatima? ‘Yan biyuna (Firdausi da Fatima) na sayawa, shine kema nayi miki sha’awarsu”. Cike da far’a Haj. Zainab tace “eh, inada Petel-Siddiqah a gida, itama ‘yan biyu ce, su biyu aka haifa tun lokacin Hassanar ta rasu a wurin haihuwa, ita kadai ta saura mana. Allah ya dora min iftila’in WABI, domin kuwa haihuwata goma amma AISHA-SIDDIQAH ce kadai Allah ya bar mana a raye”. “Allahu akbar!” Inji Nenne, “lallai dole ki so AISHAH-SIDDIQAH. Har nima yanzu zan tayaki son nata, naji a raina ina son SIDDIQAH. Ajinta nawa yanzun?” Murmushi sosai Haj. Zainab tayi tace “Petel na ajinta na biyar a makarantar gwamnatin tarayya ta Billiri Gombe”. Sun dade a bakin kofar suna hirar Aishah, kafin Nenne ta karbi lambar wayar Haj. Zainab ta gida Najeriya, da alkawarin duk ranar da Allah yayi mata shigowa Gombe (kasancewar tana yin shekaru kusan biyu bata zo ganin gida ba), zata nemi Haj. Zainab har unguwarsu su gaisa. Kafin dan lokaci kakkarfan kawance ya kullu tsakanin matan biyu a aikin Hajjin bana.
Chapter 21 · 0% Book details