Sashe 14
Aisha Siddiqa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
soyayya da gatan da Saheeb ke samu. A ka’ida duk bayan shekaru biyu sai ya sake lafiyayyen Doki, amma shi wannan da ya kira “Saheeb” abokinsa ne da bai taba sake shi ba, kula yake da shi kamar dan cikinsa, kasacewar ya fito daga hannun daraja, wato hannun Kakansa da yake matukar so (dattijo mai ran karfe), tun lokacin da Kakan nasa yayi masa kyautar sa har kawo yau yake son Dokin sosai. Kakansa ya saya masa Dokin ne a wani zuwa da yayi musamman har kasar Argentina da kansa, don ganewa idonsa yadda babban jikan nasa yake gudanar da wasan nasa na Polo, a lokacin gasar ‘World Polo Championship’, wanda shima an gudanar dashi ne anan kasar Argentina. Haka yake bata lokacinsa da aljihunsa wajen kula dashi da lafiyarsa, kamar yadda yake kula da tasa lafiyar. Abincin da ake masa cusa dashi daban dana sauran Dawakai ‘yan uwansa, haka yanada kwararren Vetrenary Doctor dinsa (likitan dabbobi), wurin kwanan Saheeb na musamman ne cikin duka Dawakansa. Saheeb yana kwana ne a cikin korran ciyayi masu taushi (pitch grass) dake cikin (stable) dinsa. Mai kula da taje gashinsa da rage shi da gyara shi da yankan kumbarsa zaman Dokin yake a gidansa dindindin, ma’aikaci ne specialist akan raino da kula da Dawakai yake zaman albashi domin kula da Doki “SAHEEB” a (ranch house) din mamallakinsa shine Pareto. Albashi na musamman Pareto yake lamushewa daga aljihun maigidansa don kula da hamshakin Dokin nan nasa (Saheeb). Shi wannan saurayin Ba’ajantine (Pareto) wani kwararren ‘Horse Breeder’ ne, wanda yayi karatunsa da kwarewa musamman akan kiwon Dawakai da kula dasu. **** **** **** Umarni na biyu wanda ya fito cikin matukar fusata daga Ubangidansa, da dukan da yayi masa da sandar Polon dake hannunsa (polo mallet), shi ya sanya Doki SAHEEB yin fitar kibiya don bin umarnin ubangidansa, ya daddage ya taka a guje, yabi bayan sauran Dawakan har nan da nan kamar kiftawar ido ya cimmasu. Daganan mahayan suka saki ragamar Dawakan a guje, da wani irin gudu mai gigitarwa. ‘Helmet’ din dake kan kowannensu, wadda ta rufe rabin fuskokinsu ta bar rabi a waje, shi zai sa ka gane cewa Abdulrasheed (Kehinde) shikadai ne bakar fata dan Africa a cikin su, kuma dan kasarmu ta “Najeriya” mai wakiltar hadakar kasashen Africa ta yamma a ‘tournament’ din. Baka jin komai na tashi daga bangaren ‘yan kallo (sashen ‘yan Africa) sai ‘applause’ na kiran sunansa da fito da usur, cikin ambaton “…. PRINCE!!! PRINCE! PRINCE!” Suna masu daga masa hannu cikin tarin kauna da bada karfin guiwa…. As he started to lead the match now…. wato ya zamo shine akan gaba, dokinsa ya yiwa sauran fintinkau, duk da kasancewar dokinsa yayi jinkiri da farko, amma daga bisani dokin gudu yake baya ko sassautawa kamar ma ya fita a hayyacinsa sabida sabo da yayi jinkiri, gudu kawai SAHEEB yake zubawa kamar zai tashi sama dashi, har shi da kansa ya sha jinin jikinsa cewa gudun da Saheeb yake yi yau ya zarta kima. Gab da zasu isa ‘goal’ ne mummunan tsautsayin mara dadin ji da gani mai muni sosai ya afku. Taki kadan kafin isar su ga ‘goal’, PRINCE ya fado kasa daga dokinsa ji kake timmm! Sakamakon faduwar bazata da dokin nasa Saheeb yayi, alhalin yana gab da isa ‘goal’. Nan da nan hankula suka tashi, ‘yan kallo suka mike tsaye cikin alhini, Alkalan gasa ma haka suka dakata, aka kawo gado nan da nan aka dauke shi daga wajen zuwa asibiti, bayan an fara bashi duk wani taimakon gaggawa tun a hanya kafin a isa asibitin dashi. Karo na sau ba adadi da faduwarsa a Doki, a duka tarihin hawa dokinsa tun na kuruciya, bai taba faduwa yaji rauni irin na wannan karon ba, Saheeb ya raunata shi sosai, bayan kwashe kusan shekaru masa dan dama yana wasan Polo dashi a wurare daban daban cikin kasar Argentina. Duk da bashi kadai yake hawa ba, wato wani zubin yana hawa wasu Dawakan bayan Saheeb kuma lafiyayyu kamarsa, amma ya camfa cewa yafi jin kaimi da sakewa da nishadi idan ya hau shi don yin wasan Polo, kuma yafi samu nasara idan Saheeb ya hau. Ko babu komai ya fito ne daga hannu mai albarka, hannun Kakansa Sarki AbdulRasheed Akanni. Playing Polo has been the hobby of his life. Ya sha cin kofin zinare a wasan ‘polo’ a ciki da waje, a garuruwa daban-daban na kasashen duniya. Don haka wannan faduwar bazata da ta faru yau da Prince, ba ‘yan Africa kadai masoya Prince ta dagawa hankali ba, har dasu Turawan na Ajantina, wato (host country) na wasan da ake gudanarwa, da mahukunta gasar na kasar ta Argentina. Wani hamshakin asibiti mai zaman kansa aka kai Prince AbdulRasheed yake zaman jinya a can ba nisa da gidansa. Zaka yi mamaki in kaji cewa, duka raununnukan nan da yaji a jikin sa, har da karaya a kafa da hannu, sabida ba karamin faduwa yayi ba, domin Dokinnan sai da ya wulwula shi a sama sannan ya tika shi da kasa, amma raunukan nan basu dame shi ba, haka zugin ciwon su bai dami Prince Abdulrasheed ba, kamar subucewar kofin gasar nan, na ‘champion’ din duniya a POLO daga hannunsa.…. Wanda da wannan tsautsayin bai faru ba, ya saka ran zai kai shi ga attaining 10+ goal polo handicap (highest rank of the world’s polo player). **** **** **** BANANA ISLAND, LAGOS P rincess Fatima, ta shigo da dan saurinta tana cewa da mahaifiyarsu Hajiya Sappa. “Ni me ya faru da kunnen Nenne na ne? Anata kiran ki a waya tun dazu kina kallonta ido hudu amma dagawa ta gagara, halan baki ji kiraye-kirayen bama Nenne? Tun daga falo nake jiyo ringing din wayarki ba kakkautawa. Nenne meke damunki haka yau? Tun safe nake ganinki haka sukuku (moody) cikin tagumi da damuwarnan, duk kin birkice”. Princess Fatima, ta karasa shigowa dakin na mahaifiyar su cikin shiga ta alfarma ta ‘ya’yan manyan sarakuna, ta fadawa mahaifiyarta Nenne Sappa kalaman cikin taushin murya, Nenne dake gyangyadi akan dardumar data yi sallahr walha ta dago tana duban Fatima fuskarta fal damuwa. A hankali ta bude ido sosai daga lumshewar data yi musu ta dubi doguwar diyarta Gimbiya Fatima, kyakkyawa ta karshe, wadda ke tsaye a kanta da wayar Nenne din a hannunta data sunkuya ta dauka a gabanta, har zuwa lokacin anata kira ba'a daina ba. Da sauri Nenne tace “Miko min wayar, Allah yasa shine, bana cikin nutsuwa Fatima, saboda yau kwana biyu bai kira ni ba, gyangyadinnan da kika ga nake yi mafarkinsa nakeyi a cikinsa, wai bashi da lafiya, dadin dadawa tun shekaranjiya rabon da ya kira ni, abinda bai taba yi ba, jinkirta kira na a duk yanayin da yake ciki (koda kuwa ace yana kan Doki ne)”. Fatima ta mika mata wayar, sannan ta zauna a gefe tana bata labarai. “Nenne jiya ne ‘Championship Tournament’ din su Hammah fa, a can Argentina, bashi da lokacin kansa kin sani. Na so inje kallo physically Dade (Baba) ya hanani, tun dazu kuma na kunna ‘PoloLine.TV’ ba’a nuno gasar ba. “I am worried too”. Ta karasa fada da harshen yarbanci. Wato itama cikin damuwar take kwatankwacin ta mahaifiyarsu. Ba tareda ta amsawa Fatima maganarta ba Nenne ta amsa wayar da ake tayi mata ba kakkautawa da sallama cikakkiya irin tata ta nutsuwa, ta hanyar nemawa wanda ya kirata amincin Ubangiji ba tare da ta san cewa katon Bayahude bane ke kiranta ba musulmi bane ba kuma Dan nata ba, duk kuwa da cewa da lambarsa aka kira ta. A wayar aka shiga yiwa Nenne bayani da harshen da ba ganewa take yi ba, wato yaren “Araucano” na Argentina. “Sunana Pareto Danny, ina magana daga wayar ubangidana, ya samu tsautsayi ne… muna asibiti, inason magana da Mother dinsa…”. Don haka sai kawai ta mikawa Princess Fatima wayar cikin yamutsa fuska tace “ungo nan Fatima, kiji me wannan yake fadi haka?”. Ba don ma taga lambar ta Ajantina bace da bazata amsa kiran ba, a ka’idarta Nenne Sappa bata amsa bakuwar lamba, amma kasancewar ta san cewa AbdulRasheed yana can, kuma yau kwanaki biyu kenan tana alhinin rashin kiran wayarsa da bata samu ba kamar kullum, domin duk halin da yake ciki baya kasa kiranta kona minti uku ne, shine yasa ta amsa wannan kiran da gaggawa don jikinta ya bata ya shafe shi. Maganar mintuna kusan uku Princess Fatima tayi da Pareto a wayar, ta fahimci me yake kokarin sanar dasu, wato Prince ya fado daga Doki, ya jikkata fiyeda koyaushe, yana asibiti a kwance da karaya a hannunsa, don haka Fatima sarkin raki sai kawai ta saki wayar a kasa ta dora hannuwa aka ta sakawa Nenne kuka. Kasancewar Fatima mai tsananin so ga Yayan nata kuma mai saurin kuka. Suna son junansu suna kula da juna shigowar bare cikinsu ne dai karbarsa sai a hankali. Nenne nata tambayarta ta gaya mata me aka ce mata? Da kyar, kafin Fatima tace cikin hawaye “Nenne Hammanmu wai, ya fado daga Doki yaji raunuka a jikinsa, yana asibiti can a kwance, an kira Dade a gaya masa ba’a sameshi ba shine aka kira ki”. “Subhanallah!” Inji Nenne, cikin kidimewa da mikewa tsaye, tana cewa “wannan DOKI!” Nan dai ta nemi fulatancin da take gwadawa akan AbdulRasheed sau tari yau ta rasa, Nenne bata jure rashin lafiyarsa ko kadan, duk da yana jimawa bai fadi a doki ba amma ko ya fadi baya jin wani ciwo na azo a gani, yaushe rabon ace yana kwance a asibiti ma ta manta koda ya fado daga Doki bai taba kwanciya asibiti ba sai dai ya sha maganin ciwon jiki yakwanat zuwa wayewar gari ya shiga harkokinsa, bait aba samun mummunan wani rauni ba. Cikin damuwa ta ce da Fatima tayi mata ‘booking flight’ mafi kusa, tace da kanta zata tafi har can ta yi jinyarsa, tunda dama duk suna da Visa na shiga Argentina sun saba zuwar masa koyaushe suke so. Kasancewar a kasar Argentina Prince AlbdulRasheed ya mallaki gidan kansa (Ranch House) mai ‘field’ na ‘Polo’ a cikinsa. Iyayensa, Taiwo da danta na fari Hakeem (kafin a haifi Kiki) da kannensa mata ‘yan biyu Firdausi da Fatima, na yawan kai masa ziyara gidan, kafin ya samu aiki a Qatar refinery y araba rayuwarsa