← Book details Aisha Siddiqa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 25

Sashe 3

Aisha Siddiqa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta, musamman mata. Hassana (Taiwo da harshen Yoruba) wadda ainahin sunan ta na yanka (Murjanatu) da Hussaininta Prince Abdulrasheed (Kehinde da harshen Yoruba) tagwaye ne masu abin mamaki. Su din ‘yan biyu ne da aka haifa tare amma ta girmeshi da awanni biyu, suka kuma taso tare bisa doron tarbiyyar islama cikin shakuwa da kaunar juna mara misaltuwa, duk da kasancewarsu mace da namiji, sai suka maida kansu sune aminan junansu daga kuruciyarsu har girma basu da abokan shawarar da suka fi junansu. Taiwo (Morjanatou), da dan uwanta Abdulrasheed (Prince) wasu irin twins ne kebabbu a cikin kafatanin zuri’arsu saboda sune manyan jikoki kowa na girmamasu, amma a halayya da dabi’a basu da alaqa da juna don Taiwo mai wasu baudaddun halaye ce, wanda iyayenta ne kadai da shi dan uwanta kadai suke iya gane inda ta dosa, sune kuma kadai suke iya tafiyar da ita da baudadden halinta, amma ko Toufeeq wani lokacin haurawa suke su fado kasa saboda bashi da hakurin jurewa halin Mourja. Hadin kansu itada Prince shine kan gaba wajen nuna cewa su ‘yan biyu ne masu fahimtar juna, da tolerating each others’ attitude. Prince ne kadai in Taiwo tayi ba daidai ba zai zare ido ya gaya mata tayi ba daidai ba ba tare da yayi la’akari da girman awannin data bashi ba da cika idon ta ga al’umma, nan kusa babu irinsu a family dinsu ta fuskar closeness da sincerity ga juna. Su haka su rufe su binne sirrin juna ba wanda ya ji ba wanda ya gani, don haka wajen hadin kai da kaunar junansu basu da na biyu. Zumuncinsu ga juna mai burgewa ne, ban sha’awa da ban kaye, in kai mai nazarin ilmin mu’amala da zamantakewa ne har kaso yin rubutu a kansu, domin kuwa zumuncin su ya zarta normal irin wanda ke tsakanin ‘yan biyu na ciki daya, wadanda akasari kusan koyaushe zaka samu suna against junansu, ko yiwa juna cin diddige wato suke yin rivalry da junansu. Su kam nasu zumuncin na musamman ne, a kullum AbdulRasheed da Murja cigaban juna da farin cikin juna suke hangowa junansu. Abin hannunsa nata ne da ‘ya’yanta. A wasu lokutan har feelings na zukatan junansu suna iya ji a jikinsu, na farin ciki ko akasinsa, idan ya samu dayansu. A takaice tagwaitakarsu extraordinary tagwaitaka ce ta bada labari da bugawa a jarida. A wancan lokacin da na waiwaya na hasko muku su (flashback), Hassana Murjanatou da Hussaininta Prince, sun mallaki shekarun matasa ne talatin da haihuwa tana housemanship dinta a Lagos State Teaching Hospital. Ta iso gida kenan tana kokarin sanya motarta a ma’adanarta, wayar ta dake aje gefe ta hau ruri kiran Hasinahn Prince ya shigo mata. Da far’a sosai Aunty Murjanatu ta daga kiran Hasinah, duk kuwa da gajiyar dake tare da ita, ta kwana biyu bata ji ta ba dama, don kusan kullum sai sunyi waya tun barinta gidanta da fara karatun Digirinta a kusa dashi a birnin Tokyo. Taiwo ta daga wayar Hasinah (fiancée din Prince) tana tsokanarta da waka cikin yarbanci yadda ta saba koyaushe sukayi waya. “Hasinah ta Prince, Hasinah kanwar Taiwo, Hasinan Taiwo & Kehinde, ta Abdulrasheed PRINCE bada kanki a sare kije gida kawai kice ya fadi!”. A baya a duk lokacin da take mata irin wannan wakar mai kama da kirari kan Hasinah kumbura yake yi tayi ta blushing ita kadai kamar Aunty Taiwo na kallon ta, domin hakika tana jin dadin wakar gtana alfahari kwarai da son da Aunty Murja ke mata, amma a yau sabanin kullum sai tayi shiru tana kakarin magana amma maganar taki fita daga makogaronta tiryan-tiryan. Murjanatu ta fakamota ta kashe sai ta zauna a ciki ba tareda ta fito ba, ta ce. “Yaya akayi ne kanwata nake jin muryar ki a shaqe kamar mai fama da mura? Kin fadar min da gaba. Kwana biyunnan ban jiki ba dama, Dear Haseenah in ce ko lafiya?” Shiru Hasinah tayi bata ce komai ba ta daina kakarin maganar ma sai ciza lebe. Aunty Taiwo ta sake cewa “In ji dai lafiya kuke keda shi? I mean Prince din? Kuma yaya kuke coping da wheather din sanyinnan na winter da karatun naku ke da shi?” Amma ga mamakinta sai taji kamar Hasinah sheshshekar kuka take yi. Kukan ma irin na fitar rai da ta kasa dannewa, irin mai cin zuciyar mai yinsa, da dugunzuma zuciyar wanda ake yimawa. Murjanatu was shocked! Stunned daga zaunen da take a cikin mota, duk da ta kashe motar a ma’adaninta kukan Haseenah yasa ta kasa fitowa kuma. Da kyar taji muryar Haseenah na fita zuwa cikin kunnenta, cikin sauti mai nuna matsananciyar nadama. “Ki taimakeni ki bashi hakuri Aunty Taiwo, kaddara ce!!!” Murjanatu ta zaro ido, kafin tace komai Haseenah ta sake cewa “kema kin san ba halina bane, kullum kina gargadina akan hakan, kuma na dade ina kiyayewa, kun sani lafiya kuka dauko ni a ‘virgin’ daga Ambursa, wallahi kafin na zo school ban taba yi ba, sau daya ne, sai wannan na biyu, shima kuma wallahi da kudi Tokumbo yake jan ra’ayi na, na dade ina kaucewa fitinarsa, wannnan din ma akasi aka samu, tsautsayi ne. Nayi masa babban laifi Aunty Taiwo, kaddara ce ta fada mini. Zina ba hali bace afkawar kaddara ce da karfin sha’awar da ya gagari dan adam. Prince ya daina daga wayata yau kwana biyu kenan…. ya min iyaka da zuwa gidansa…. Ya ce kada in kara nuna masa mummunar fuskata ko a lahira! Laifina bai kai haka ba. I didn’t deserve such a severe punishment, zan jure kowanne hukunci banda na rabuwa da Prince. Na shiga uku Aunty Taiwo, yau kwana biyu ban saka Prince a idanuna ba… I am dying without him! Truly I am dying! Aunty Taiwo ki taimakeni! Ki cece ni ki ceci marainiya, ke kadai nake da yanzu, a duniya banda kamar ki, ki ceci soyayyar gaskiya da Prince yake yi mun, nasan Tokumbo ba aurena zai yi ba ya cuce ni ne kawai!”. (She screamed!!!). Irin ihunnan na girgiza zuciyar uwardaki. Har cikin kwakwalwar Murjanatu ihun nata ya ratsa ya kusa kurumta kunnuwan Murjanatu. Ta shiga afi da hurwa, tana tumami a kasa cikin hawaye da majina, kamar Murjanatu na kallonta, kalamai take na tuba da nuna nadama, amsar kaicon kai, da kuma daukar alkawarin bazata sake ba. Begging for “one more last chance”. Amma taki fadin hakikanin laifin nata, cikin matsanancin kuka na tashin hankali kawai take rokon Taiwo kamar itace Prince AbdulRasheed din da kansa. Ta kwana da sanin idan Aunty Murjanatu ta yafe mata, tamkar Abdulrasheed da kansa ya yafe mata ne. Kasancewar kowa dake tare dasu ya san Prince (AbdulRasheed) bai iya tsallake rarrashin Taiwo dinsa. Kamar yadda bai iya tsallake abinda ta umarceshi inta bullo masa da lallashi da banbaki ta bayan gida wanda ita kadai ta san lagonsa. Amma itama Hasinah duk da wannan tabbacin data ke dashi, ita da kanta wannan karon tana shakka. Ta yaya take da tabbacin laifin nata mai yafuwa ne ga Taiwo dinma? Since they sometimes share the same feelings itada kaninta Prince? Akan-karan kanta ta san laifinta ba mai yafuwa bane saboda girmansa. Musamman ga babban mutum, mai kishin kansa, dan babban gida da yasan ciwon kansa kamar PRINCE ABDULRASHEED. Wannan shine babban tashin hankalin Hasinah Bello, idan ta tuna lokaci yazo da Prince da zai barta (lokacin rabuwa da gatanta Prince Abdulrasheed yazo) ko taki ko ta so, duka wannan ihu ne take yi bayan hari Abdulrasheed bazai taba mantawa ba balle ya yafe mata, wanda shine komai nata kuma masoyin da suka kulla alkawurran soyayyar da bazasu lissafu ba, soyayya mai tsabta wadda ikon Allah ce kadai ta wanzar da ita don ta san bata kai nan ba, bata is aba, bata kai matsayin ba. Haba! Wannan tunanin yasa sai ihunta ya ninka na baya. Ta kuma kasa ambaton sunan Allah don tasan shima Ubangiji bata da uzuri a wurinsa don bata yi godiya da ni’imar da yayi mata ba ta bata sahihiyar soyayyar Abdulrasheed ba don isarta ba. Bata taba tunanin akwai abinda zai iya yin sanadin da Prince zai ce mata “You! The bastard WHORE! Don’t dare show me your ugly face again!!!”. Wadannan sune kalaman Prince na karshe a gareta, mafiya daga hankalinta, domin a sanda ya fadesu ta tabbata ya fadesu ne baka da zuci babu wata rana da zaiyi nadamar furtasu. Tunda abinda yayi Kehinde shi yayi Taiwo. And they often share the same feelings, kowa nasu ya san hakan. To idan har Aunty Taiwo ta ji laifinnata ma, anya zata kara kallonta da idanun rahma? Ko dubanta da aminci da kaunar da take mata wanda duk sanadin Prince dinne??? Kowa bai ishi Murjanatu kallo ba, in dai baida sarauta, mulki ko dukiya, itama din albarkacin Prince ta ci hawa-hawa a wurinta tunda har ta riketa na shekaru a hannunta, sai kuma jininsu yazo ya hadu daga bisani saboda dukkansu halayensu yazo daya masu son rayuwa ne sosai. Wannan tunani ya kara dugunzuma zuciyar Hasinah, ta kara kururuta kukan da take yima Dr. Taiwo a waya kamar zata fasa dodon kunnenta, fatan ta dai Murjanatu taji tausayinta. Ta kuma tuna ita marainiya ce, da bata da kowa sai su. Murja ta kasa gane komai akan kukan Hasinah da maganganunta, wadanda bata san ina suka dosa ba, ta bata su ne a lullube, a kudundune, amma hakika ta daga mata hankali fiyeda yadda Hasinan tayi zato, kasancewar Taiwo a very cool and reserved person, wadda ko kusa bata son iface-iface da hayaniya yasa ta sa hannu ta toshe kan wayar da hannunta, ita dai ta san daga ita Hasinah har ubandakinta AbdulRasheed son juna suke kamar su hadiye juna don soyayyah, AbdulRasheed na takun-saka da mahaifiyarsu Nenne akan taki yarda ya auri zabinsa Haseenah, wani cikinsu bai taba kawo karar dan uwansa gareta ba sai yau da Haseenah ta kawo karar Prince, don haka Taiwo ta kasance a uku, ta rasa bayan wa zata bi a cikinsu. Da kyar ta nisa tace da Hasinah cikin lallashi, da gajiyawa da jin kukan da ihun nata na marassa tawakkali, cikin nuna matukar concern ga damuwarta tace. “Hold on Hasinah, kina ji na ko? Ki bar kukannan haka take it easy Hasinahty, ki tsaya har in yi
Chapter 3 · 0% Book details