← Book details A Dalilin Da Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 20

Sashe 6

A Dalilin Da Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kadan kadan idanuna suka lumshewa suna budewa nan da nan na fara ganin komai hurhudu, Don haka na gyara kwanciya a kan gadon na juya wa kwalaben da na gama amfani da su baya.
“Inna lillahi wa inna ilaihirraji’un!” abinda farima ta furta kenan hankalinta a tashe, tana kallon na yi daidai ina barci a kan gadon. Sadaf-sadaf ta tashi daga inda take zaune har zuwa gurin kwalaben.
Benelyn, Totalyn, sunayen da aka rubuta a jikin kwalaben kenan. A hankali ta janyo akwation ta bude, Abubuwan da suke ciki suka yi matuqar tayar mata da hankali. Kayan maye ne wadanda ba ta san iyakarsu ba a ciki, Qwayar da ta ga na tauna ba tare da ruwa ba, qwayar roci ne. jikinta a sanyaye ta rufe akwatin ta mayar inda ta dauko.

Kallo na take tsawon daqiqun da ba ta san iyakarsu ba, Fatima ta raya a ranta, kyakkyawa ce ni ta gaban kwatance, ta lura ba na jerin baqaqen mata, amma kuma ni ba fara ba ce. Kuma na fi kalar chakulet haske. Wani irin haske fatata take dauke da shi mai matuqar daukar hankali.
Ba ni a cikin jerin mata masu qiba, amma ni ba siririya ba ce, dukiyar fulanin da suke tsaye kyam kuma cikakku a qirjina shi ne abinda yake kara fisgar hankalin maza da mata a fuk lokacin da na fita sanye da qanana kaya (English wears). Cikina a dame yake tamkar ba na cin abinci.
Ina da yalwataccen qugu mai firgita hankalin duk wani lafiyayyen namiji. Gaba daya a jikina babu wani abu na kushe, sai dai ga hasidin iza hasadin. Dara-daran idanuna wadanda har ‘yan uwana mata daukar hankalinsu suke, ga wani irin lumshewa da suke a duk bayan second hudu, wanda wasu suke tsammanin gayu ne irin nawa, amma haka Allah ya halicce ni.
A fuskata za ka gane ni din qaramar yarinya ce, a tunanin Fatima idan na yi wuta in kai shekaru sha bakwai. Ba ta tunanin zan dara haka ko kadan. A dan fahimtar da ta yi mana duk sauran ‘yan matan gidan sun girme ni.
"Idan akwai kuskure a hasashena ai zan tabbatar tunda ina gidan.”
Ta fadi hakan a zuciyarta. A dan fahimtar da a yi min daga daren jiya zuwa safiyar yau ni yarinya ce mai tsananin ibada, don ta lura tun daren jiya ban bar kan darduma ba saida na je jikin gadon na tashe ta ta yi sallar asubahi. Ina tashin ta kan dardumar na koma. Sannan na dauki tsawon awa daya da rabi ina karatun Alqur’ani mai girma bayan na idar da sallar asubahi.

Abinda ya daure mata kai a game da ni shi ne abinda ya faru tsakanina da ita a daren jiya, da kuma rayuwar shan kayan mayen da na daukar wa kaina ina ‘yar qaramar yarinya. Babbar matsalar shi ne, na yi mata kashedi a kan duk abinda za ta gani a tare da ni.
“Amma… a juri zuwa rafi…”

Tana fadin haka ta janyo bargo ta lulluba min, cikin tausayi da qauna ta da take ji a zuciyarta. Karatun Alqur’ani ta jiyo yana tashi cikin tattausan sautin muryar “Ahmad Sulaiman” a falo, don haka ta nufi can.
Duk su shidan da bata san sunayensu ba in banda “Rahma” da taji na kira sunanta jiya, sai kuma “Baba” da na ba ta umarnin ta shirya mata abinci a jiya, suna zazzaune a kan kujeru daban-daban.
Har qasa ta tsuguna ta gaida Baba, ta amsa mata da fara’a har tana tsokanar ta; “Ya kuwanan baqunta?”
Murmushi kawai ta yi sannan ta yi jam’in gaida su gaba daya.
“Akwai abinda kike buqata ne?” Safiyya ta tambaye ta tana kallon ta cikin kulawa.
“Alhamdulillahi, ba na buqatar komai, na gode.” Ta mai da mata da amsar hakan bayan ta fadada fuskarta da murmushi.
Qarfe ara da rabi Baba ta gama hada kayan karin kumallo a kan dinning table, suna zazzaune akan qananan kujeru zagaye da babban teburin da aka shirya kayan abinci. Kowa a cikinsu qoqarin hada kumallonshi yake yi, sabanin ita da ta zabga tagumi hannu bibbiyu.
Abinda ya kara bata mamaki har ya sanya ta tagumi shi ne ganin dukkaninsu babu wanda ya damu ya duba yadda na tashi. Kuma ko ita da muka kwana muka tashi daki daya ba su tambaye ta ya nake ba, qoqarin cika cikinsu kawai suke yi bayan kuma a yadda ta lura nice shigaba a cikinsu.
“Ya dai Fatima? Ko kina buqata wani abin karyawar ne daban?” Baba ce ta yi mata wanan tamvayar da damuwa a fuskarta, ganin kowa yana cin abinci amma ban da ita.
“A’a, ..yanzu zan hada nawa” Ta amsa tana qoqarin bude gwangwanin madara da cokalin hannunta.
***
Sanye nake da singlieti fara wacce ta yi matuqar dacewa da fatar jikina, wando na sanya three-quarter amma yana da fadi bai kama min jiki ba, duk wani lungu da saqo na jikina fidda kalar qamshi daban yake yi don haka zai yi wuya mutum ya iya tantance wane irin turare na fesa.
Qarfe sha daya da minti arba’in da biyar agogon falon ya nuna min. tsawon awa hudu ina barci, Minti arba’in da biyar kuma na dauka gurin wanka da shiryawa, Ganin fitowata falon ya sa dukkansu gyara zama suna min barka da fitowa.
Gaban Baba na wuce na tsuguna har kasa na gaisheta sannan na nemi gurin zama.
Hada baki suka yi gurin gaishe ni, na amsa da murmushin da bai cika yankewa a fuskata ba. “Ya dai Fatima? Ina fatan baki takura ba?” na tambayeta bayan na lura da kallon da take ta bina dashi tun bayan fitowa ta.
“Kin tashi lafiya?” abin da ta tambayeni kenan, ta share waccen tambayar da na yi mata.

“Alhamdulillah.” Na amsa mata ina dan dariya don in kara kwantar da hankalinta.

“Sadiya taimaka ki hada min ruwan lipton. Rahama bani remot din T.V pls.”
Da sauri suka miqe don cika umarnin da na basu duk da na yi umarnin ne cikin salon roqo.
“Zamu fita yammacin yau don samawa Fatima duk abinda zata buqata, so kowa ya kasance cikin shiri zuwa qarfe biyar na yamma. Fatima ki yi lis din duk abinda kike buqata.”

“Toh! Na gode, qwarai.” Ta amsa min.

"GA CIKAKKUN LABARAN DUNIYA..
A jiya da daddare ne wasu ‘yan bindiga mata da ba a san ko su waye ba suka kai hari wa gidan yarin da yake hanyar Kaduna zuwa Abuja, Sun yi amfani da bindiga gurin harbin qafafun mutum shida daga cikin jami’an tsaron da suke gidan, sannan suka zarge qafafun mutum tara daga cikin jami’an tsaron, mutum biyu kuma a can bayan gidan aka gansu kwance suna sharar barci sakamakon hoda mai sanya nannauyar barci da ‘yan matan sukayi amfani dashi.
Sunbi jami'an tsaron gaba daya sun shaka musu hodar, hakan yasa har yanzu da suke kwance a kan gadon asibiti na SALAMAT ba su san inda kansu yake ba.

‘Yan bindigan dai ko da suka sami nasarar shiga gidan basu dauki kowa ba sai wannan mai laifin Fatima Ibrahim wacce aka kaita gidan a yammacin jiya, sun yi amfani da dan mabudi mai lalata ko wani irin kwado ne gurin bude qofar dakin da fursunan take, kuma sunyi umarni ga duk matan dakin su kama gabansu idan suna buqata.
Wata mata mai suna Hajara Musa daga cikin fursunonin da suka fice daga dakin amma ba ta yi nisa ba ta suma a hanya ita ce ta bayyana hakan bayan farfadwarta, ga yanda ta bayyanawa wakilanmu faruwar al’amarin.
(Take aka dallaro hoton fursunan a fuskar talabijin)

Dan jaridan ne ya fara tambayarta da cewa,
“Ya sunan malamar?”
“Hajara Musa.” Da alamun galabaita a muryarta, fuskarta da jikinta ma sun nuna gajiyawa.
“Ya aka yi wannan al’amarin ya faru tunda kina cikin fursunonin da komai ya faru a gabansu?”
“Muna cikin barci muka fara jiyo harbin bindiga daga can bayan gida, daga bisani kuma muka ji shiru, minti goma tsakani muka ci gaba da jin harbe-harben ba qaqqautawa, sai kuma can muka ji ana bude kwadon qofar dakin mu, tsananin tsaro yasa duk muka miqe tsaye, fursunar da aka kawo ta jiya ne kawai ba ta miqe ba, tana zaune tana kuka, wasu ‘yan mata muka gani sanye da riga da wando, sun rufe fuskarsu da manyan tabarau, kai tsaye gurin wacce take kukan suka nufa, sun dan yi maganganu a tsakaninsu daga bisani suka kama hannun junansu suka fice da ita.”
“Kun ji maganganun da suka yi da ita?”

“A’a, qasa-qasa suke magana.”
“Yanzu idan kika ga ‘yan bindigan za ki shaidasu?”
“A’a, lokacin a rude muke, ba zan iya gane fuskar ko daya daga cikinsu ba.”

“Su nawa ne ‘yan matan?”
“Ban yi tunanin qirga yawansu ba, amma a hasashe na za su kai su goma.”

“Me yasa duk sauran ‘yan dakinku suka gudu, kema kin yi niyyar guduwa Allah ne bai baki sa’a ba.”

Duqar da kanta ta yi na wasu ‘yan sakanni sannan ta dago hawaye na bin fuskarta ta ce, “Su suka ce duk mai buqatar gudu qofa a bude take.”
“Kin san hukuncin wanda ya yi yunqurin gudu daga gidan yari kuwa?”
Shiru ta yi ba ta amsa ba, bai gaji ba ya qara tambayarta da cewa “Tun tsawon wani lokaci kike zaune a gidan nan?”

“Watanni uku da suka wuce…”

“Me kika yi har aka yanke miki hukuncin zama a gidan yari?”
Shiru ba ta amsa ba (sai kuma suka dauke hoton hirar)
Wakilin namu ya sake zantawa da I.G na ‘yan sandan jihar Kaduna, in da ya tabbatarwa da wakilin namu cewa (nan take suka hasko hoton inspector general din tare da 'yan jaridu a cikin gidan yarin.

“Ranka ya dad'e me zaka iya cewa akan wannan abin da ya faru?”

“Wannan shi ne karo na farko da hakan ya tava faruwa da wannan gidan yarin, kuma abin mamaki ne qwarai da muka ji cewar mata ne ‘yan bingidan ba maza ba.”

“Ko akwai wani mataki da zaku dauka akan hakan?”

“Qwarai kuwa, akwai matakan da zamu dauka sosai kuwa.”
Chapter 6 · 0% Book details