Sashe 18
A Dalilin Da Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abdul-Ahad Muhammad hadad'd'en saurayi kuma dan qwalisa, wanda duk wata mace da za ta yi arba dashi sai tayi sha’awar ina ma ace ya zamo mallakinta. Kallo daya za ka yi mishi ka gane dan fulani ne asali. Duk girman zuriyarsu shi ne ya biyo kakansu Ardo Amadu tamkar kwabo da kwabo, kuma shi ne babba a cikin jikokin Ardon shi yasa tako wane vangare ake matuqar ji da shi.
Familyn Ardo Amadu a garin Adamawa ba boyayyu ba ne , domin sun shahara akan abubuwa da dama musamman ilimin boko, dana addini da dukiya, da tsantsar kyau da kuma kyan dirin jiki.
Wata dabi'a da suka shahara a kanta shine sam basa auren kad'o sai jininsu na fulani. Duk yawan Family dinsu suna zaune ne a Adamawa, illah daidai ku da suka bar jihar Adamawa zuwa wasu jihohin. kamar mahaifinsu Yasmin da ya dawo garin Kaduna da zama.
Shi kuma mahaifin Abdul-Ahad yana can Yola ya na gudanar da kasuwancin shi.
Matan aure har guda uku Ardo Amadu ya mallaka wadanda suka haifa mishi ‘Ya’ya goma sha hudu, maza takwas mata shida, mahaifin Abdul Alhaji Muhammad shi ne babba aduk cikin ‘Ya’yan Arxo Amadu, kuma shi yaron matar Ardo Amadu ta biyu ce mai suna Ladi. gidan suna da matuqar hadin kai, bazaka taba iya banbance dan wannan dakin da dan wancan dakin ba.
A bayan Abdul Ahad akwai jikoki da dama a zuriyar Ardo Amadu.
Ardo ya haura shekara saba'in da biyar a duniya, amma idan ka gan shi za ka yi tsammanin bai wuce shekara hamsin da biyar ba, domin ya yi tsufa ne na ilimin addini, duk wanda ya yi tsufan ilimin addini kuwa ba ya kwarkwancewa.
Abdul -Ahad tun yana dan qaraminshi yaro ne mai matuqar sha’awar aikin dan sanda, idan yana zaune da kakanshi ba shi da wata magana sai ta idan ya girma Police zai zama
"Ashe za ka zama abokin kowa kenan.”
Amsar da Ardo yake ba shi kenan tare da alqawarin matuqar yana raye sai ya cika mishi burinshi. duk Familynsu ba su san wannan aikin na dan sanda da yake buri , amma da yake gaba da gabanta tunda ya samu goyon baya daga Ardo dole kowa ya tsuke bakinshi tareda yi mishi fatan alkhairi.
Kwanci tashi ba wuya a wurin Ubangiji ga shi yau har Abdul ya zama Inspector a gurin aikinshi na 'yan sanda. yana samun qarin girma akai akai saboda jajircewa da qwarewa akan aikin shi, dan sanda ne mai matuqar gaskiya wanda bayajin kunyar gurfanar da duk wani wanda ya yi laifi agaban hukuma, koda kuwa jininshi ne.
Addu’ar kakanshi yana bibiyar shi aduk inda ya shiga, yasha fadawa hadari da dama amma cikin hukuncin Ubangiji yakan tsallake.
Irin su Abdul su ake buqata a hukumar ‘Yan sanda saboda aduk inda ya tsinci kansa yakan tuna da rantsuwar da ya yi akan zai aikata gaskiya ko mahaifansa ne.
Ardo kullum yana qara ba shi qwarin gwiwar tsayawa akan gaskiya.
Transfer ya samu daga Abuja zuwa Kaduna, hutun kwana bakwai aka ba shi don ya gama kimtsawa zuwa Kaduna da wannan damar ya yi amfani ya je Yola ya kwana uku. Ardo ya bashi addu’o’i na musamman wadanda zai gudanar ranar da ya fara shiga ofis dinshi na Kaduna. Sannan ya sake mishi tuni akan lokacin aurenshi da ‘yar uwarshi Yasmin da a kullum yake qara kusantowa. (shekarun Abdul-Ahad talatin da biyar a duniya amma sam ba shi da niyyar yin aure, haduwar Familyn Ardo maza da mata gaba daya da babbar sallah yasa aka yanke shawarar hada aure tsakanin Abdul da Yasmin, mahaifan gaba daya sunyi farin ciki, ya yinda sauran ‘yan matan Familyn baqin ciki ya cika zuciyarsu kowacce taso zabin na Ardo ya fada kanta, amma sai ya fada kan Yasmin da take kallon kowa a dage, bayan sunfi ta kyau da komai da komai.
Dole suka hadiye baqin cikinsu gurin yi mata fatan alkhairi, a fili Yasmin take nuna tsananin so da kishin Abdul-Ahad.
A gurin Abdul kuwa ba yabo ba fallasa, dole yaso duk abinda Ardo ya za6a masa don haka ya fara qoqarin cusa sonta a zuciyarshi.
Rashin tarbiyya da rashin sanin ya kamata shine babban abinda yake hada shi da ita. Bayan taron ne Ardo ya kebe da Abdul yayi mishi bayanin dalilin da yasa ya za6a mishi Yasmin a matsayin matar aure.
"Baffanku na Kaduna masifar son ‘Ya’yanshi biyu tak da ya mallaka a duniya Ahmad, (Abba kenan mai sunan Ardon) da Yasmin ya rufe mishi ido, shiyasa ya kasa basu kyakykyawar tarbiyya, duk wanda aka hada Yasmin aure da shi ba za suyi zaman dad'i ba, kai ne kawai kake da qwanjin da za ka iya tanqwarata tabi umarninka, bayan haka kuma na fahimci tana son ka”
Da wannan qarin bayanin da Ardo yayi mishi yasa ya daina damuwa da duk wani al’amarinta)
Abba Yayan Yasmin babu abinda ya tasa a gaba sai shaye shaye da neman mata, qungiya suke da ita mai suna Big Boys a cikin garin Kaduna, hatta irin askin da suke yi a kansu ya fita daban, da an gansu ake ganesu, duk yarinyar da suka dora idanunsu akanta ta shiga uku, ko ta wane hali sai sun biya buqatar su a kanta.
Wani abin takaici shine duk iyanyansu manyan masu kudi ne, da an kamasu basa yini a kulle ake sakinsu, duk wani iskanci sunayinshi ne da daurin gindin mahaifansu.
Tunda Abba ya gama Secondary School a daddafe ya watsar da karatun, su kuma iya yanshi suka zura masa ido domin suna matuqar son shi, tun yana dan qarami suka 6ata shi, don haka har ya girma ba kwa6a ba hantara, idan ya tasasu agaba da masifa sai kayi tsammanin shine uban su kuma ‘ya’yan. Amma hakan bai hana idan ya fita ya dawo iyayan su fara rarrashinshi.
Yasmin tana masifar tsoronshi, don sam baya mata da wasa, idan ya fara dukanta tamkar Allah ne ya aikoshi.
Da magiya da ban haquri iyayan suke qwatar ta a hannunshi, shi yasa indai tasan yana gida bata ta6a yin abinda za ta kuskure a gareshi.
A duniya idan akwai wanda Abba yake masifar jin tsoro to Abdul ne, shi ya sa iyayanshi da Yasmin suke matuqar qaunar zuwan Abdul gidan domin hatta tsawon daren da yake dauka bai dawo gida ba matuqar yasan Abdaul yana gari to yana ragewa, hatta abokan shaidancin shi yana jan baya dasu kuma yana gargadin su ja baya da ziyartar shi har sai Abdul ya bar garin Kaduna, shi yasa a ranar da Abdul ya tabbatar mishi ya dawo garin Kaduna da aiki kusan kwana biyu yayi bai yi barci ba, hankalinshi ya yi matuqar tashi, domin ya san duk inda yasa qafa Abdul yana bin diddiginshi a fili da 6oye, amma daya samu tabbacin ba gidansu Abdul din zai zauna ba sai hankalinshi ya dan kwanta, don yana tunanin komai zai zamo mishi da sauqi tunda ba makwancinsu daya ba.
A ranar da Abdul’Ahad ya cika kwana hudu da zuwa garin Kaduna a ranar ya fara shiga sabon Ofishinshi, ya yi addu’o’I da dama akan Allah ya bashi ikon tsayuwa akan gaskiya komai dacinta, kuma yayi addu’ar Allah ya bashi ikon gyara hukumar su ta ‘Yan sanda don ya fahimci akwai gyare gyare masu dama a hukumar ta su, cin haci da rashawa ya zama tamkar ruwan sha da abincin mafi yawa daga cikinsu
“Matuqar ka ce ba zaka karbi cin hanci ba to kana tare da fuskantar qalubale mai matuqar girma daga gurin gur6atattun manya na sama damu.” Wannan bayani ne da wani dan sanda da yake qarqashinshi ya yi mishi lokacin da suke tsaye suna duba duk motar da za ta shige layin gidan Gwamna, wani Alhaji ne ya damqo ‘yan dubu dubu har guda biyar ya miqa mishi lokacin da ya umarci motar tasu ta sauka can gefen titi don yayi binciken qwaqwaf a kanta.
“Ba ko wane dan sanda zaka gani akan titi ka miqa mishi cin hanci ya kar6a ba…” Ya fadawa Alhajin haka fuskarshi a daure tamau, zuciyarshi a mugun 6ace.
“Inspector ba cin hanci na ba ka ba, ganinka nake tamkar dan cikina, don haka na baka wannan ne kasha ruwa.”
Alhajin yayi saurin juyar da maganar don ganin tayin nashi bai samu shiga ba.
“Ok to na gode, ka bar kudinka, ina buqatar ganin takardun motar ka.”
Sai da Alhajin ya bata sama da minti ashirin a gurin, domin duk wani lungu da saqon motar sai da Abdul ya duba sannan ya bashi umarnin wucewa, haka kawai jikinshi ya bashi Alhajin ba shi da gaskiya amma duk iya binciken shi bai gano komai ba. Bayan motar ya bi da kallo a zuciyar shi yayi qwafa tare da fadin “Lokaci na gaba….”
Shi ma Alhajin ta jikin madubi yake kallon Abdul yana jinjina qarfin hali irin na yaron, wannan shine karo na farko a tarihin rayuwar shi da wani dan sanda yayi mishi bincike a motar shi, duk Check point din da zai wuce sai dai ‘Yan sanda suyi mishi kirari ya basu na kashewa, don haka hoton fuskar matashin dan sandan ya zauna daram a zuciyar shi.
****
Muna zaune a falo muna hira cikin farin ciki da annashuwa, Baba Jummala ce take mana tatsuniyar Yar mowa da ‘Yar bora, hatta Fatima da take baquwa ta saki jikinta dau ta zamo ‘yar gida, yau kwananta takwas kenan amma idan ka ganta sai ai tsammanin ta shekara damu.
“Ai Allah ba azzalumin bawa ba ne, kunga da yake ‘Yar mowa sunyi nufin cutarwa ne ga ‘Yar bora sai gashi zuwa nemo ruwan bagaja ya zame mata silar arziqinta.”
Baba ce ta yi wannan qarin bayanin bayan mun fahimci ta kammala tatsuniyar.
"Qwarai kuwa.” muka amsa gaba daya.
“Amma ‘Yar bora tasha wahala, ta bala’in bani tausayi duk da dai tatsuniya ce.”
Nice na fadi haka ina dan lumshe idanu.
“Wallahi nima na tausaya mata, har qwalla na kusa yi lokacin da akace dole sai ta nemo rafin ruwan bagaja sannan zata wanke kayan fitsarin ‘Yar mowa.”
Fatima ce ta fadi haka cikin jimami.