Sashe 15
A Dalilin Da Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alh. Buba qwararre kuma shahararre wajen safarar duk wani nama da ya shafi sassan jikin Bil’adama. Babu wanda ya san asalin garin Alh. Buba. shahararren mai arziki ne na qarshe, ya tara dukiyar da shi kanshi baisan iyakarta ba.
Yayi aure-aure kala-kala, duk manyan jihohin arewacin Najeria babu jihar da bai auri mace ba, duk matar da ya aura kwanaki talatin take yi a gidanshi sai ta rasu.
Wannan yasa mutane suka kafa mishi kahon zuka, karshe da ya ga asirinsa yana neman tonuwa sai ya haqura da aure gaba daya.
Duk matar da ya aura idan ta mutu baya tava kawo gawar ga iyaye da danginta, Sai dai ya je ya sanar musu Allah ya yiwa xiyarsu rasuwa. Idan ya auri mata a Kaduna sai ya kaita gidansa na Abuja bayan kuma yana da gida a Kadunan. Ko kuma idan ya auro daga Kano ya kaita gidansa na Katsina, babu matar da ta tava haihuwa dashi a duk cikin matan da ya ta6a aura har su ashirin da daya.
Yana da mutane da yawa wadanda suke aiki a qarqashinshi, akwai shi da hannun kyauta, ya gina gida daban – daban wadanda shi kanshi bai san iyakarsu ba. Matuqar kana aiki a qarqashinshi zaka huta Amma da dukiyar haram, haka kawai Allah ya saka mishi qaunar mahaifina da yake cikin ma’aikatanshi, qaunar da yake mishi ita ta sa ya kasa sanar mishi da sana’ar ainihin sana’arshi. Mafi yawancin tafiye tafiyenshi da mahaifina yakeyi yanada manyan masu arziqi da yake harkar har amtaccen kasuwanci tun daga qasarmu Nijeria har zuwa qasashen qetare, duk abinda kake nema na sassan jikin bil’adama zaka samu a gurinshi, idan ma babu alokacin zai baka lokacin da zaka dawo ka samu.
Yana da kebantattun gidaje a garuruwa daban – daban inda ake gudanar da yanka mutane tamkar kaji. Yanada ke6antaccen gida da yake sato mahaukata mata don biyan buqatar wasu masu neman duniya. Ko ciki yaga anyiwa mahaukaciya yakansa a saceta yaci gaba da ciyar da ita har sai ta haife abinda yake cikinta, babban burinshi ya samu jaririn ko jaririyar da take dauke dashi don sai da shi ga wasu masu neman duniya.
Yana tura mutanenshi asibitoci don su sato mishi jarirai, a gefe guda kuma Alh. Buba shahararren matsafi ne, duk wanda ya nemi kawo mishi tangarda ko kuma tona mishi asiri sai dai a wayi gari an kashe shi, duk wanda yake shirya mishi mugun abu yana sani.
Al’umma da yawa sun zuba ido don ganin qarshen Alh. Buba, amma a kullum tamkar ana qara mishi lafiya da qarfi akan harkokinshi.
Wani babban Costomern shi ne ya bugo mishi waya akan yana son ko wani sassa daga jikin budurwa ‘yar shekara goma sha biyar, a lokacin sai Ubangiji ya gwada mishi ikonshi duk yarinyar da aka sato daga wacce bata kai shabiyar ba sai wacce ta haura shabiyar, hankalin Alh. Buba ya yi matuqar tashi, domin anyi mishi alqawarin miliyoyin kudi akan wannan harka, tsafinshi ne ya gwada mishi bazai ta6a samun wannan yarinya ba sai ta hanyar Sa’ad (mahaifina) da yake ya dade da sanin masifaffen san kudi na mahaifina, baishi wata wahala wajen shawo kan mahafina ya sai da mishi da ni a kan Naira miliyan dari ba.
Sannan bai 6oye mishi komai ba kan cewa tsafi zai yi da ni, sa’annan ya qara da nunawa mahaifina Alh. Musa wanda ya sai da mahaifiyarshi, don ya samu abin duniya.
*****
Wannan daki da na bude idanu na ganni a ciki daya ne daga cikin dakunan tsafin Alh. Buba.
Ina zaune a cikin matsanancin duhun da ko tafin hannuna bana iya gani, naji an bude qofa an shigo cikin dakin, koda aka bude qofar ban gane mai shigowa ba don idona ya fara sabo da duhun dakin kuma kafin idanuna su washe aka maida qofar dakin aka kulle.
Tsayin mintina biyar naji wata qatuwar murya ta cika dakin tana wasu irin surutai wanda sam bana fahimtar abinda ake cewa, tsayin minti talatin naji muryar ta fara rawa tamkar yana shirin fashewa da kuka, second goma tsakani muryar ta fara kusanto inda nake zaune a qasa don haka na cigaba da takure jikina guri guda ina karanto duk addu’ar da tazo bakina a zuciyata, kamar walqiya naga wani haske ya zagaye ni, a hankali tsoro ke ficewa daga zuciyata don haka na sami damar daga ido don ganin mai wannan qatuwar muryar.
Yana tsaye a dan nesa dani tsakanina dashi bai wuce taku biyar zuwa bakwai ba, gajere ne na qarshe kuma baqinqirin, hannunshi riqe da qwarangwal din kan mutum, Tsirara haihuwar uwarshi yake tsaye don haka na sadda kaina qasa inajin qyamar ganinshi, minti biyu tsakani yana tsaye inda yake tamkar an dasa shi amma ya yi shiru sa6anin dazu da yake sambatu, da baya ya ringa tafiya har ya fice daga dakin, yana fita hasken daya zagayeni ya 6ace bat na ci gaba da zama a cikin duhu.
Sai da wannan gajeren mutumin ya jera tsawon yini uku yana shigowa yana irin wannan sambatu, idan ya fara kusanto ni sai wannan hasken ya lulluve ni, a karo na uku ne daya nemi qarasowa gareni ta qarfi wannan hasken ya yi jifa dashi can jikin bango. Da alamun yaji jiki matuqa domin ya fi minti talatin bai tashi daga inda aka watsar dashi ba, ya tashi kuma da dingishi ya fice, kuma anan ya bar wannan kan qwarangwal din da yake shigowa dashi.
Bayan fitarshi wannan hasken daya zagaye ni bai bace ba, kamar a kunnena naji wata murya tana umarta ta da in isa gurin wannan kai in take shi da qafata na dama.
Ban jira komai ba na aikata hakan, ina takewa kan ya dagargaje, take naji dakin da nake ciki ya dauki wani qara mara dadin sauraro, qasar gurin ta fara girgiza tamkar dakin zai rushe in rufta ciki, minti daya tsakani hasken ya bace sai komai na dakin ya koma tamkar yanda yake ada, wannan ihun ma ya tsaya cak tamkar anyi ruwa an dauke.
Duk iya wadannan lokacin ban san ko kwanaki nawa na yi a wannan dakin ba, ko kiran Sallah ba na ji, Ina cikin matsanancin duhu, don haka na zubawa sarautar Allah ido ina Istigfari a zuciyata ta.
Lokaci mai tsawo naji an budo qofar dakin a karo na hudu, wannan karon wani abu aka feso min irin wanda mahaifina ya fesa min, sai gani a wani daki na daban, sabanin wanda nake ciki a da.
Shima wannan dakin mai duhu ne amma ba kamar wancan ba, akwai dan wadatar haske kadan, sabanin wancan da ko tafin hannuna ba na gani.
Yini uku aka sake dauka wannan mutumin yana shigowa don aikata tsafi irin na wancan dakin, amma tarihi ke maimaita kansa.
Sai da aka canja min dakuna har guda bakwai abinda ya faru a dakin farko shi yake faruwa a kowane daki, Kuma duk dakin da aka canja min sai na taka qwarangwa din kan mutum da qafata ta dama, bayan ihu da girgiza ya cika dakin komai zai koma daidai, sannan wannan haske yake bacewa.
Tun da na take wannan kai na bakwai na tsinci kaina a wani irin yanayi tamkar ba ni ba, ina gurin amma kamar ba ni a gurin, umarni kawai ake ba ni daga zuciyata ni kuma ina aikatawa ba tare da ko zurfafa tunani ba.
Ina zaune guri daya zuciyata ta yi min umarnin in tashi in nufi yamma na dakin, cikin duhun nasa kai a inda zuciyata ta tabbatar min nan ne yamma. Bangon da ya tare ni ya tabbatar min na isa jikin bango. Zuciyata ta ba ni umarnin in yi bismillah sau uku, in shafi bangon dakin, Ina aikata hakan qofa ta bude, a wani babban falon mai wadataccen haske na tsinci kaina, Falon ya hadu iya haduwa. Domin kuwa an zuba komai na jin dadin rayuwar duniya. Tun daga kan kujera da labulaye da kafet (capet) din komai koraye ne, amma suna da haske. Tsawon minti biyar ina kalle-kalle amma ban ta6a komai na cikin falon ba ina tsaye a inda nake.
Yamma na sake nufa kamar yadda zuciyata ta umarce ni, ina isa na yaye labulen da ya tare jikin bango, kofa ce mai tsananin kyau da daukar ido ta bayyana a gurin, hannun dama na sanya na bude qofar tare da fadin
“Bismillahir rahmanir rahim.”
A wani daki na bayyana mai cike da abubuwan ban tsoro da firgitarwa, wasu manyan qorai ne guda biyar, girke a jikin bangon kowane kusurwa na dakin, cikin manyan qoren cike suke da wani irin ruwa jajir mai hade da baki-baki (jini)abinda aka fada min kenan da na yi tunanin ruwa ne a cikin qoran.
Qwan lantarki qwaya daya ne tal a tsakiyar wannan dakin, kuma haske mai kama da jini yake bayarwa.
Motsi da wani irin gurnani daya ringa fita daga tsakiyar dakin shi ne abinda zai fi tsorata duk wanda yake cikin dakin, wani abun mamaki shine zuciyata a tsaye take, babu tsoro ko kadan a cikinta.
Yamma na dakin na sake nufa, kamar yadda zuciyata ta umarce ni. Ina isa jikin wannan qore masu dauke da jini na ja na tsaya.
“Rufe idanunki.”
Aka fadamin haka a kunne na.
Ban 6ata lokaci ba na aikata abinda aka umarce ni. Minti uku tsakani aka umarce ni da in bude. Ina budewa na tsinci kaina a wani daki na daban mai dauke da wata qatuwar tukunya a tsakiyar dakin.
Babu abinda ke fita a kowace kusurwa na dakin sai turiri mai matuqar zafi. Sakwan goma na hada zufa na yi sharkaf amma duk da haka ban fasa tafiya zuwa yamma na dakin ba.
Abin mamaki shine ina tafiya amma tamkar ba na yi, domin ga bangon yamma na dakin ina gani a can nesa da ni amma na kasa isa gare shi. Hakan ya fahimtar da ni a guri daya nake bayan kuma tafiya nake yi.
Wata mahaukaciya dariya da ta cika dakin ita tasa na ja na tsaya cak, ba tare da na shiryawa hakan ba. Tukunyar na zurawa ido don kuwa ta cikinta dariyar ke fitowa.... tsawon minti biyar ana 6a66aka dariyar sannan muryar ta dauke tamkar daukewar ruwan dama.