Sashe 17
A Dalilin Da Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abinda yake kara daure min kai da sanya ni tunani shi ne, rashin ganin bil’adama ko guda ya ratso ta inda nake a wannan daji. Idan na yi kamar zan tambayi su Aunty sai kuma wani abu ya dauke min hankali na bar tambayar a cikin zuuciyata.
A ranar da na cika shekara goma sha shidda a duniya suka shaida min zan bar wannan daji izuwa wannan gida da muke rayuwa a yanzu. Duk kayan da na yi amfani da su a cikin wannan daji sun umarci in bar su a can za su sa a kwashe, a yi sadaka da su. Sanin za su sai min wasu kayan masu kyau da tsada ya sa ko musu ban yi musu ba.
Tafiya mai tsananin nisa muka yi muka iso gurin mota Sienna irin kirarta daya da wacce mahaifina ya dauke ni ranar da zai saida ni ga Ubangidanshi matsafi Alhaji Buba.
Wani kyakkyawan saurayi mai kama da Larabawa shi ne a mazaunin direba, har qasa ya durqusa ya gaishe mu, sannan yayi key din motar bayan dukkanin mun shiga bayan motar.
Tafiyar minti talatin ta kawo mu wannan gida, duk wadannan motocin da kuka ga muna amfani da su da duk kayan cikin gidan nan a nan na tarar da su, tambayoyi fal a raina amma na kasa furta su.
Bayan su Aunty Hassana sun gama zagayawa da ni lungu-lungu da saqo na cikin wannan gida, Aunty Hassana ce ta gyara zamanta a kan kushin ta fara da cewa;
"Bayan samun nasarar tserewarki daga gidan tsafin Alhaji Buba, hankalinshi ya yi mummunan tashi. Bayan asarar miliyan dari biyar din da ya yi, wanda aka yi alqawarin za a ba shi matuqar ya kai sassan jikin yarinya budurwa ‘yar shekara goma sha biyar, wanda a cikin kudinshi ne ya saye ki Naira miliyan dari cif a hannun mahaifinki kuma ya yi mishi transfer na kudin a take zuwa cikin account dinshi domin yana tunanin zai samu ninkinsu matuqar business din ya kammala, kafin ki samu nasarar gudu sai da kika karya lagon duk wani tsafi da yake taqama da shi a dalilin taka wadancan k'ok'on kawuna da yake taqama da su.
Bai ta6a tunanin za ki samu nasarar gudu ba, duk da ya san akwai wani 6oyayyen al’amari mai girma a tare da ke dalilin wannan haske da yake hana shi isa gare ki. Tsafinshi ya raunana matuqa, qaunar da yake yi wa mahaifinki ya sa bai hallaka shi don huce haushin abinda kika yi ba, amma kwana biyu kawai ya ba mahaifinki sai da ya sato mishi yarinya mai shakaru irin naki don dama gunkin tsafinshi ya tabbatar sai ta hanyar mahaifinki zai samu wannan yarinya.
Matsalar da ya kara samu shi ne, shi kuma wancan kwastoman nashi lokacin da aka ba shi ya kai sassan jikinki ya riga da ya qure, don haka wannan miliyan dari biyar ba su samu gare shi ba da lallami da ban baki da qaunar da yake yi wa mahaifinki ya sa ya yafe mishi.
Wannan gida da kike ciki Alhaji Buba ne ya dau tsawon shekara guda yana ginawa da niyyar dawo da duk harkokin tsafinsa wannan gida. A ranar da ya gayyaci manyan abokan harkarshi wannan gida don su sanya mishi albarka wani bala’i ya auku gare su. Su goma sha biyu ne cikinsu har da mahaifinki. Idan kika duba ga wadancan motoci za ki ga guda goma sha biyu ne. Wadannan mashina kuma na gardawa majiya qarfi ne da suke gadin Alhaji Buba.
Suna zaune a kan wanan dining din Allah ya dauki rayuwarsu dalilin guda da direban da suka aika ya amso musu abinci ya zuba a ciki, kuma suka ci ba tare da sanin ajali ke kiran su ba.
Alhaji Buba na mutuwa lagon tsafinshi ya qarasa karyewa gaba daya. Duk gidajen da yake aikata mugun abu Allah ya toni asirinshi. Yau kwana goma kenan da faruwar wannan abu. Direban da ya zuba musu guba shi ya kwashe gawarwakinsu gaba daya ya kai su daji ya cinna musu wuta.
Duk motar da kika gani akwai mukullinta. Akwai kud'ad'e masu matuqar yawa wanda har ‘ya’ya da jikokinki ba za ku yi talauci ba, ki ringa yawan aikata alkhairi, ki ringa ba da sadaka, don yi wa mahaifiyarki da mahaifiyarmu addu’a. Zunubi yana kan wadanda suka aikata su Alhaji Buba ke dai kawai duk abinda kika gani ki tafiyar da shi ta hanya mai kyau. Daga yau ba za ki qara ganinmu ba sai dai musayar saqonni a tsakaninmu. Duk abinda kike buqata ki shiga cikin gari ki nema. Ki yawaita kai ziyara gidajen marayu da asibitoci, duk wacce take neman taimako ki taimaka mata, za ki had'u da mutane mata da maza masu yawa amma kar ki ta6a sakankancewa da Da NAMIJI.
Duk abinda ba ki gane ba za mu turo miki da amsa ta wayar hannu da za ki ringa amfani da su, kar ki matsa ma kanki da yawan tunani Ubangiji yana tare da ke, ba zai ta6a ba wani ko wata ikon cutar da ke ba. Duk wacce take buqatar taimako ki taimaka mata, duk wacce aka zalinta idan kina da iko ki taimaka mata. Duk inda kika shiga za mu kasance ma su yi miki addu’a.”
Da haka muka yi sallama da su Aunty Hassana suka fice ba tare da sun dauki ko tsinke a cikin gidan ba. Sai da na yi kwana uku, sannan na gama fahimtar komai na ciki da wajen gidan nan. Da taimakon wannan direba, da rashin tsoro da qarfin zuciya na iya tuqa kowace mota a cikin gidan nan. Mashin bai zame min wahala ba. Ranar da na fara fita zuwa cikin gari na hadu da Baba Jummala, wacce ita ta qara wayar min da kai a kan komai har Allah ya sa muka hadu da kowacce daga cikinku.”
Aisha ta qarasa fadin haka tana kallon fuskokinsu daya bayan daya.
“Hmmn! Ta6dijan! Gaskiya rayuwarki na cike da abubuwan ban mamaki da al’ajabi.” Fatima ta fadi haka tare da sauke tagumin da ta yi da hannu bibbiyu.
Nan take kowacce ta fara fadin albarkacin bakinta. Duk dai a kan abubuwan mamakin da suke tattare da tarihin Aysha. Ita kam ba ta cewa komai sai murmushi da take bin kowaccensu da shi.
Kiran sallar asubahin da wayarta ta rangada shi ya katse duk wani maganganu da suke yi. Ko waccen su daki ta nufa don sauke faralin sallar asubahi.
***
Dariyar da ta dinga qyalqyalawa ba qaqqautawa bayan ta gama ba ta labarin silar karayar hannun na ta shi ne abinda ya fi qona ma ta zuciya, tun ta na cijewa har ta 6ige da daka mata tsawa tana fadin
“Hidaya wannan wane irin wulaqanci ne? a zatona tausaya min ya kamata ki yi a matsayinki na aminiyata amma sai kiyi ta tuntsira min dariya saboda mugunta?”
Dif ta dauke dariyar, sannan ta sanya babban dan yatsanta tana dauke hawayen da ya taru a idanunta saboda dariya sannan ta ce,
“Yi haquri qawata, Allah ya huci zuciyarki, wallahi na tausaya miki sosai ma kuwa, kawai dai jin da na yi kin ce daga riqe miki hannu kika sami karaya, kuma wai mace ce silar karayar taki shine abinda ya bani dariya, amma kiyi haquri…”
Duk da haka ba ta saki fuskarta ba don ranta ya baci sosai, sai da Hidaya ta sake fadin
"Yanzu wane mataki shi angon naki ya yi alqawarin zai dauka akan yarinyar? Don sanin irin matsanancin son da yake miki kuma Inspector ne na yan sanda nasan ba zai bar wannan zaluncin ya tafi a banza ba.”
Saida tayi murmushi jin an ambaci angonta Abdul, kuma an fadi irin son da yake mata, duk da a fili kowa ya san ita ke son shi ba shi yake tsananin son ta ba.
"Eh to… a yanzu dai kam bai ce dani ga irin matakin da zai dauka ba, amma kamar yanda kika fada, hankalinshi yayi mummunan tashi, nasan tabbas bazai qyale wannan 'yar iskar yarinyar ta ci bulus ba”
“Amma hannun naki da sauqi sosai ko?.”
“Eh ba kamar shekaranjiya ba qila nan da 2 weeks in fara fita.”
“Allah ya qara sauqi….”
Sallamar Abdul-Ahad da kutso kanshi cikin falon shi ya hana Yasmin amsa addu’ar da qawarta Hidaya ta yi mata. Gaba dayansu suka bishi da wani mayen kallo kamar zasu cinye shi danye.
“Ba kwa amsa sallama ne?”
Ya fadi hakan yana qoqarin daidai ta zaman shi a kan kujera.
“Yi haquri ba mu ji ba ne Yaya Abdul. Barka da shigowa.”
Yasmin ce ta amsa tana jifanshi da tattausan kallo irin na masoya.
“Yau wa, ya jikin na ki?”
Ya amsa ba tare da ya sake kallon inda take ba.
“Sai a hankali Yaya Abdul, wallahi ina matuqar shan wahala…” Ta fadi haka murya a marairace, don a tunaninta zai nuna mata kulawa irin wadda ya sa ba a gaban mahaifanta, amma ga mamakin da ya shayar da ita shine ko kallonta bai sake yi ba, balle tayi tunanin samun amsa ko kuma kulawa daga gareshi, saima maida hankali da yayi wurin canza tashar talabijin daga wanda suke kallo zuwa wadda yake so.
A dan kunyace ta kalli Hidaya tana zungurin ta da hannun ta mai lafiya, tayi mata gyaran murya a hankali tana fadin “Yaya Abdul"
Ta gane manufar ta don haka ta yi gyaran murya tana fadin
“Yaya Abdul barka da yamma.”
Sai a wannan lokacin ya kalle su tare da amsa gaisuwar ta fuskarsa ba yabo ba fallasa.
Cike da yanga da kwarkwasa a muryarta ganin ta samu shiga harya kalleta ta ce,
“Ashe kuma abinda ya faru kenan?”
“Eh”
Ganin ba shi da niyyar qara wata maganar daga haka, ya tabbatar mata bata samu kar6uwa ba, itama bata ja da nisa ba ta ce,
“Allah ya kyauta gaba.”
A lokacin yana gab da ficewa daga cikin falon, bai amsa ba, kuma tana da tabbacin ya ji abinda ta fada. Bayanshi suka sake bi da kallo tamkar zasu janyo shi ita da Yasmin din.