← Book details A Dalilin Da Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 20

Sashe 3

A Dalilin Da Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Zan turo Nasir ya kaiki asibiti” ya faxi hakan yana ficewa da sassarfa don karya makara zuwa Office.
Ganin zaman bazayyi mata ba yasa ta miqe ta nufi banxaki da niyyar watsa ruwa ko zata ji qarfin jikinta. Heater bayinta ya lalace kuma ta manta ba sanar da Alhaji ba don haka ta ciko bokiti da ruwa ta jona a jikin soket abayan kujera a falon, tana zama Nasir ya shigo ba tare da sallama ba, kallonshi tayi sama da qasa yana sanye da qananan kaya jeans da T.shet.

“Oh My God! Babyna wai baki da lafiya inji Daddy?” ya faxi hakan yana kusantar ta nufinshi don jin yanayin jikinta.

“Dakata Nasir, karka kuskura ka matso kusa dani.” Ta yi mishi gargaxin hakan muryarta tangaran babu alamar rashin lafiya a tare da ita cak ya tsaya tamkar an riqe shi, shi bai qarasa kusa da ita ba kuma bai koma baya ba.
“Kina tunanin akwai abinda zai hanani biyan buqata ta dake a yanzu?”

“Qwarai kuwa” ta faxa muryarta babu alamun tsoro ko kaxan.

“Meye shi?” ya tambaya da tsananin mamaki a fuskarshi.

“Allah bazai baka nasara a kaina ba.”

Dariya ya qyalqyale da shi tamkar sabon hauka sannan ya qara kusantar ta da niyyar haxa jikinta da nashi ko ta halin qaqa.

“Dakata” ta sake bashi umarnin haka a karo na biyu lokacin baifi saura taku biyu ya isa gareta ba, bayyi niyyar tsayawa ba amma ga mamakinshi sai ya tsaya.

“Bani minti biyar inyi wanka…” ta faxa sannan ta rava ta gefenshi ta wuce zuwa bayan kujera inda ta jona heater.

“Fatima shure shure ba ya hana mutuwa duk abinda zakiyi yau sai na biya buqata ta a kanki, don haka jeki dawo ina jiranki” yana gama faxin haka ya zauna akan kujerar da ta tashi yana qyalqyala dariya.

Idanun shi kaxai ta kalla ya tabbatar mata da cewa tabbas yau da gaske yake don haka gara ta nemi mafitar qarshe tun kafin wankin hula ya kaita dare, ruwan yana tafarfasa don ya haura minti talatin da jonawa, tana xaukar ruwan a bayan kujerar da yake zaune ta xaga bokotin ta sheqa mishi tun daga tsakiyar kanshi ba tare da ya ankara ba.
Raxaxin da ya ji tun da ga tsakiya kanshi zuwa sassan jikinsa yasa ya qwallah gifitaccen qara saboda azaba, second goma tsakani ya sume akan kujerar sai a lokacin ta ji dana sani mai tsanani ya mamaye zuciyarta jikinta ba inda ba ya rawa saboda tsabar tsoro.

Tsawon minti biyar ta rasa waqar farawa sai kuka take tana safa da marwa a tsakiyar falon, daga qarshe ta yanke shawarar kiran number wayar Alhajin, kuka kawai take a wayar tana faxin Alhaji Nasir ne…..”

“Me ya faru da Nasir din…..?” Ya tambaye ta hankalinshi a tashe.
Ta kasa furta komai bayan sai kuka daga bisani ta jefar da wayar ta ruga cikin xaki ta kulle kanta.

Duk inda aka tava a jikinshi savewa yake yi, gaba xaya likitocin sun taru akanshi don qoqarin ceto rayuwarshi.
Alhaji Muhammad yana jikin qofar hankalinshi a matuqar tashe, Nasir kawai ya samu a sume akan kushin duk jikinshi a jiqe da ruwa ba Fatima a gidan ba alamar ta, sai da ya kama hannun Nasir yaga ya saluve fatarshi sannan hankalishi ya qara mummunan tashi da taimakon Allah dana Drivern da ya kawo shi daga Office suka kama Nasir duk jikinshi a qone zuwa asibiti tswon minti talatin kenan likitoci suna cikin xakin da aka kaishi amma har yanzu ba wanda ya fito.

“Kaine mahaifinshi ko?” wani siririn likita daya fito daga xakin ya katsewa Alhaji Muhammad tunanin da yake yi. “Qwarai kuwa" ya amsa yana gyaxa kai don qara tabbatar da abinda ya faxa.

“Biyoni ciki don tunda ya farfaxo yake roqon a kira mishi Daddy”

Duniya ba komai ba ce, duk wanda bai ji tsoron Allah ba ya shiga uku cikin lokacin da bai wuce awa xaya ba Ubangiji ya canzawa Nasir halittan jikinshi yana kwance tamkar gawa. Daqyar ya yi qarfin halin faxawa mahaifinshi cewa:-
"Fatima … Fati ce … tamin haka!!! Saboda… saboda …” Allah bai bashi ikon qara faxin koda kalma guda ba bayan haka Mala’ikan zare rai ya zare mishi ranshi.
Cikin kuka Daddy ya ke xaukarwa kanshi alqawarin ko zai yi yawo tsirara sayya xaukar mishi fansa, bai iya haqurin ankai Nasir ma kwancinsa na gaskiya ba sai da ya danqa Fatima a hannun ‘yan sanda. Bayan angama addu’ar bakwai aka turasu kotu, Alhaji Musa qanin mahaifinta ya bita har gidan Prison ya yi mata “Allah ya isa rainon da ya yi mata ya qi bata dama kokaxan tayi mishi bayanin yanda abin ya faru, kuma ya qara tabbatar mata da cewa bashi ba ita har abada.
A wannan ranar ne Fatima ta yanke qauna da rayuwar duniya, shi ya sa ko da aka shiga kotu bayan amsa laifinta babu wani qarin bayanin da ta yi har zuwa yau da aka yanke mata hukunci.

***

Na xago idanuna daga kan wayar ina kallon fuskokin ‘yan matan da dukkansu hawaye suke saboda tsananin tausayawa Fatima, Idanuna abushe suke qamas, babu ko alamar hawaye amma zuciyata suya kawai ta ke saboda tsananin takaicin halin maza da mugunta irin tasu.
“Wannan labarin ka xan kenan daga cikin rashin adalci irinna maza, kunga dai A DALILIN XA NAMIJI ta shiga cikin uqubar daya janyo za ta qare rayuwarta a gidan yari, shi yasa a kullum nake qara fada muku maza azzalumai ne! Tsakanin mu da maza ba sani ba sabo, duk wacce takeso rayuwarta yazo qarshe ta qulla dangantaka da Xa namiji, zamu gudanar da kyakykyawar rayuwa ba tare da Namiji ba, kuma ko a gurin Allah ba laifi bane.”

“Qwarai kuwa ‘yar uwa Aysha”
Dukkan su suka haxa baki gurin faxin haka cikin nuna gamsuwa da maganganu na.

Dayar wayar tawa na janyo na buxe saqon da aka turo min daga 7777.

“ZAKU KAI HARI GA GIDAN YARIN DA AKA AJIYE FATIMA”

Abinda aka rubuta kenan da manyan baqi a saman saqon, da qarfi na karanta don sauran ‘yan matan suji abinda ya qunsa.
"Gidan yari ne da ake ajiye mata a hanyar da mutane da suke bi idan zasu je Abuja daga Kaduna, akwai masu gadi da makami a hannunsu su biyu daga qofar get xin gidan yarin, katangar gidan yana da matuqar tsawo ya wuce ace za’a haura ko kuma a dira, koda da tsani ne za’a xauki tsawon lokaci don haka ta get xin zaku shiga bayan kun janye hankalin masu gadin ko da ta hanyar sumar dasu ne. Xakuna ne a jere sama da guda xari cikin gidan, ako wani xaki ana zuba mata su goma sha biyar duk da qanqantar xakin, akwai jami’an tsaro guda goma sha biyar daga gaban xakunan, duk wani shige da fice na masu laifin akan idonsu suke yi, babu wata hanya da zaku iya fitar da Fatima face sai kun fafata da jami’an tsaron, idan kukai amfani da hikima zaku ya xauke hankalinsu har ku cimma burinku. Xaki mai lamba 87 anan aka ajiye Fatima abayan rigar ta an rubuta lamba 268, da farko zata yi muku gardama kan cewa ba zata biyoku ba tunda ba ta san ku ba.
To dukkanku ku juya mata bayan rigar ku taga tambarinku, ku da ita daga yau ta zama ‘yar uwarku, duk matsalarku iri xaya ne A DALILIN XA NAMIJI kuka tsinci kanku a halin da kuke ciki.
zaku fita da misalin qarfe goma sha biyu da rabi na dare, ku lazimci karanta “HAZBUNALLAHU WA NI’AIMAL WAKEEL” don samun nasara kamar yanda ku ka saba."

Iyakar abinda na saqon ya qunsa kenan don haka ban tsaya vata lokaci ba na janyo dayar wayar na buxe saqon da aka turomin a cikinta daga Number 7777.

“GAREKI AYSHA AZZAHRA’U”
Ganin hakan da aka rubuta ya tabbatar min da saqon zuwa gareni ne kaxai banda ‘yan matan, don haka na fara karantawa a zuciyata, “Ki tashi da misalin qarfe sha biyu da kwata lokacin da ya rage minti goma sha biyar ku fita, ki xauro alwalarki sannan ki tada sallar nafila raka’a biyu ki karanta fatiha da ko wacce irin sura bayan kinyi sallama ki xaga hannun ki izuwa sama ki yi wannan addu’ar “Allahumma inni as’aluka bi anna lakal hamdu la’ilaha illa antal Hannanul Mannanul badi’us samawati wal aradi zuljalalu wal ikhram.” Sannan ki roqi Allah nasara a kan fitar da zakuyi sai ku kama hanya. Muna bayanku ni da ‘yar uwata, kuma mu na muku fatan NASARA"
qarshen saqon kenan don haka na ajiye wayar ina kallon sauran ‘yan uwana. “Da fatan dukkanku kun fahimci yanda fitar tamu zata kasance?”
“Qwarai kuwa" suka amsa gaba xaya.

“Ubangiji ya bamu sa’a.”

“Amin summa Amin" suka amsa gaba xaya cikin samun qwarin gwiwa.

“Barkan ku da yammaci… Jummala mai dafa mana abinci dattijuwa ‘yar shekara talatin da takwas ta faxi hakan bayan tayi sallama an amsa mata ta shigo cikin falon.
“Barkanmu dai Baba sannu da qoqari” muka amsa a tare fuskata xauke da murmushi, da sauri na qarasa gareta na xan durqusa na karbi kular hannunta na xora a kan Dining table.
“Sannu Aysha Allah ya miki albarka.”

“Amin summa Amin Baba” na amsa cikin jin daxi don ganinta nake tamkar mahaifiyata, kusa da ita na koma na tsugunna kusa da qafa funta murya a sanyaye nace,
"Baba yau muna da fita da daddare muna da buqatar addu’ar ki.”

“Allah ya baku sa’a Allah ya kareku daga dukkanin abun qi, mutum da aljan.”

“Amin summa Amin”
wannan karon dukkanmu muka amsa.”
Idona ne ya faxa akan agogo qarfe bakwai da kwata na dare, “Subahannalahi” na furta don ganin har lokacin sallar Magariba ya wuce bamu gabatar ba ga Isha’i ta kusanto,
"ya kamata mu gaggauta mu gabatar da sallah kafin mu faxa fushin Allah.”

“Baba barin shiga ciki inyi sallah”
na faxi hakan ina kallonta ba tare da na saurari amsarta ba na wuce da sassarfa zuwa cikin xakina.

“A fito lafiya Aysha.”
Na jiyo muryarta ta na faxin haka.
Chapter 3 · 0% Book details