← Book details A Dalilin Da Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 20

Sashe 13

A Dalilin Da Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da nayi kuka ya isheni wanda ya daukeni tsawon awa uku, amma duk cikin wadanda nake kiran ba wacce ta amsani.
Shiru na yi ina ajiyar zuciya, idanuna sai zafi suke min saboda kukan dana dauki tsawon lokaci ina yi, rintse idanu na yi ina jiran barci ya daukeni ko zan sami sauqin baqin cikin da yake cunkushe a zuciyata.

Tsawon lokaci ba barci ba alamarsa daga qarshe dana gaji da juye-juye sai na tashi na zauna na sanya kaina a tsakanin cinyoyina na fada duniyar tunani mai zurfi.

Abu fa kamar wasa karamar magana na neman zama babba, kwana biyu ana wasan buya tsakanina da Abbana, kuma a wadannan kwana biyun ko barcin minti biyar ban samu ya daukeni ba.
Idanuna duk sun tashi saboda barci ba a cin bashinsa, duk iya tsawon awoyin da zan dauka a kwance ina jiran barci ya dauke ni sai dai in gaji in tashi zaune amma barcin ba zai zo ba.

Ina matuqar son in yi barci don har layi na ke yi idan ina tafiya a tsakar gida, kuma a wannan ranar tun daga sallar asubahi da mahaifina ya fita gida bai dawo ba, hankalina a tashe yake matuqa, na yi kuka harna gaji ba wani sassaucin dana samu.

Misalin qarfe biyu na ranar dana cika kwana uku a wannan hali na yanke wa kaina shawarar fita qofar gida ko zan sami mai taimakamin.
Sanye da riga t- shirt da wandon jeans wanda ya fito da dukkan suroin jikina, rigar ta kamani sosai, 'yan kananun kirgan dangin dana fara suna tsaye cas cas a qirjina.
Hula ne sanye a kaina amma duk da haka sai da ya tona asirin dogon gashin da nake dashi.

Qafata sanye da silifas din wanka na tura qofar get din gidanmu na leqa kaina waje a hankali, da yake layi ne na masu hannu da shuni, kuma ranar litinin ce ranar aiki unguwar tsit babu alamar mutane, ko na masu gadin gidaje.

Ina tsaye a qofar gidanmu ina hawaye na rasa ina zan dosa? kamar daga sama naga qofar get din gidan da yake kallon namu ya bude, wani kyakkyawan saurayi matashi ya fito sanye da kayan motsa jiki.
Kallon kallo ya gudana a tsakaninmu idona share-share da hawaye.
“Qanwata lafiya?”
Ya tambaye ni da kulawa a muryarsa.

Shiru na yi ban amsa masa ba, kuma ban daina kukan ba.
“Ko kina kukan tafiya da abbanki yayi ne?”
A bakin sa na ji wai mahaifina ya yi tafiya don haka na yi qarfin halin girgiza masa kai alamar a’a.
“To mene ne? Kina jin yunwa ne?” kai na sake daga masa alamar a’a.
Bai gaji ya sake tambayata
“Ko baki da lafiya ne?”

Da hanzari na daga masa kai alamar, “Eh.” Na qara da fadin “Don Allah ka taimaka min da maganin da zan samu in yi barci, yau kwana ina ta so inyi barci amma ko gyangyadi bana iya yi.” Ina gama fadin haka na rushe da kuka mai tsananin qarfi na tsuguna a qasa, hannu biyu na dora akai ina shassheqar kuka.
“Oh, sorry qanwata mai kyau, ba dai barci kike son ki yiba?”

“Eh.” Na fada bakina har rawa yake yi gurin fadin haka.

“Jirani a nan ina zuwa.”
Cikin gidan da ya fito ya koma ya tattaro min kwalaban magungunan tari da qwayoyi masu gusar da hankalin mutum leda guda ya kawo min.
“Ki yi ta sha har sai kin ji barci mai nauyi yana fizgarki sannan za ki daina sha.”

Abin da yace min kenan ya fara tafiya gudu-gudu zuwa inda ya nufa.

"Wannan rana ita ce ranar farko ta fara shaye-shaye na"

Ina fadin haka na fashe da kuka su Fatima suna tayani, sai da muka yi ya ishe mu, sannan na ci gaba da basu tarihin rayuwata.

"Tun daga wannan ranar matsalar rashin barci ya kau daga gareni, sabo mai qarfi ya shiga tsakanina da Mahfuz (kamar yanda ya bayyana min sunansa) ina kiranshi da “Yayana” shi kuma yana kirana da “Qanwarshi mai kyau”

Tun daga lokacin ya zama idan zan yi barci sai na sha wadannan kayan mayen nake yin barci, idan sun kusa qarewa zan sanar da shi, shi kuma bai tava gajiyawa gurin kawomin wadansu ba.

Idan mahaifina baya nan har gidanmu yake shigowa, kai har cikin dakina, amma ni ban taba kwatanta shiga gidansu ba.

Mu’amala tsakanina da Abbana kuwa ba yabo ba fallasa, daga gaisawa babu abin da yake hadani dashi, babu ruwanshi da ni, naci abinci ko banci abinci ba duk bai damu ba.
kuma baya kwana biyu a gida, kullum cikin tafiye-tafiye yake, yayin da ni kuma kullum qara shaquwa muke da Mahfuz.

Wata rana da daddare misalin qarfe tara da rabi na dare, a wannan lokacin na shekara har da wata biyu a gidan mahaifina, kuma har a wannan lokacin sai na sha kayan maye nake iya barci.
Mahaifina baya nan, don haka tun qarfe takwas na dare na rufe gida da qofofin dakunan mu, Kamar a mafarki nake jiyo qwanqwasa get din gidan mu a hankali, lokacin na yi mankas da kayan maye barci kawai nake shirin yi, jin bugun qofar ya qi qarewa yasa na miqe ina tangadi na fita zuwa gurin get din.
“Wa...ne...ne..?” Na tambaya da muryar maye.

“Qanwata mai kyau ni ne.” Ya amsa muryarshi qasa-qasa.
Bude masa qofar nayi ya shigo, ni kuma na lallava na koma ciki don ji nayi ina shirin faduwa qasa warwas, shi ya mai da qofar ya rufe ya biyo bayana zuwa cikin falo.
Bani a falon don haka ya bini zuwa cikin dakina.

Ina kwance nayi daidai a kan gado ina sharar barci, sanye nake da kayan barci masu matuqar ban sha’awa da nuna surar jiki.

A wannan dare Mahfuz ya yi niyyar keta min haddi kota wane hali. Amma ina Allah bai bashi sa’a ba, daga inda yake tsaye a tsakar dakin yana kallon surar jikina sanye da dan pant fari da farar best wacce ta kamani tsantsan. A saman best da pant din ne na dora rigar barci mai nuna tsiraici.

Yana tsaye yana kallonta cike da sha'awa, idan ya yunqura da nufin fadawa gadon kusa dani sai wani farin haske ya dakatar dashi. Wannan shi ake kira ga “Qoshi ga kwanan yunwa” ya fadi hakan a zuciyarsa,
“Ina... wallahi ba za ta savu ba, tsawon shekara daya da wata biyu ina wahala da yarinya amma lokacin fanshewa kuma ya gagara? Wannan sam ba zai yiwu ba.” Ya fadi hakan a fili yana maganan yana tube kayan jikinsa.

Yana tsaye haihuwar uwarsa a tsakar dakin, yana safa da marwa da tunanin ta inda ya dace ya afkamin don samun nasarar aiwatar mummunan manufarsa a kaina.

Rintse ido yayi ya yi miqa sannan ya daka tsalle da niyyar fadawa kaina, wanna karon ba haske bane ya tare shi, shoking ne da wani tiriri mai matuqar zafi daga jikina suka watsar dashi a jikin bangon dakin.
Take ya zube qasa a sume kansa ya bugu da jikin bango, iska mai matuqar qarfi ya ci gaba da hurgi dashi a jikin bango daga wannan kusurwa zuwa waccan kusurwa.

Duk wanna abin da yake faruwa bani da masaniya ina kwance ina sharar barci hankalina kwance da taimakon kayan maye, ban farka ba sai da gari ya waye tangararan, duk jikina ba qarfi tamkar wacce aka yiwa dukan tsiya, da qyar na lallaba na dauro alwala na gabatar da sallar asubahi ina ta “Istigifari” a zuciyata.

Motsin da nake jiyowa a falo yasa na fara tunanin ko Abbana ya dawo ne? Ina shirin miqewa don zuwa gaidashi naga an turo qofar dakin an shigo da sallama.
Fuskar wacce na gani yasa na miqe da sauri ina nunata da dan yatsa manuniya sannan na ce, “Anty Hassana...” da gudu na rungumeta ina ihun murna daga bisani kuma na fashe da kuka, ita ma kukan take tana shafa kaina alamun rarrashi, sai da na yi mai isata sannan na dago da fuskata ina kallonta na ce,
"Ina Anty Hussaina?”
Da hannu ta yi min nuni zuwa qofar dakin, tana tsaye ta nade hannuwanta a qirji tana share hawaye da dan qyallen da yake hannunta.
Da gudu na qarasa gareta na rungumeta ina hawaye.

Saida muka nutsa muna zaune a tsakar dakin, in kwanta a jikin waccen, in koma jikin waccan zuciyata cike da farin ciki.
“Kun manta dani tunda Ammi ta rasu baku qara waiwayata ba sai yau.”
Na fadi hakan kaina yana cinyan Anty Hassana, qafata kuma yana jikin Anty Hussaina tana jamin ‘yan yatsun qafar a hankali.
“Shit...! kar ki sake fadin haka, bamu manta dake ba, wasu al’amura ne suka sha kanmu, amma a kullum kina zuciyarmu, kuma daga yau ba zamu sake nesa dake ba, a kullum zamu kasance tare idan mahaifinki baya nan.”

“Wanene Mahfuz?” Anty Hussaina ta jefo min tambayar ido cikin ido take kallona.
“Maqwacin mu ne, a kullum shi yake debe min kewarku da ta Ammi, amma baya zuwa sai idan Abba baya nan.”

“Kin manta da nasihar da Ammi ta yi miki ko? Kin manta kullum saita fada miki kiyi hankali da maza saboda yawancinsu mugaye ne ko? Ko kin manta tarihin zaluncin mahaifinki ga mahaifiyarki? Kin san babban illar da Mahfuz din nan yaso ya yi miki kuwa?”
Nan ta bani labarin duk abinda ya faru a daren jiya da ya shigo.

Tuni idona ya fara tsiyayar hawaye, a zuciyata ina tuna Ammi da jan kunnen da take min a kullum a kan maza.
Zuciyata tana tuquqi ina yiwa mahaifina da mahfuz da duk wani namiji azzalumi “Allah ya isa.”

Anty Hassana ce ta ci gaba da cewa “Wadannan kwalaben magungunan da qwayoyin da yake baki da sunan maganin barci qarya yake yi, magungunan da yake gusar da hankali da tunanin dan adam ne, fitar dake yake daga cikin hankali da tunani irin na dan adam mai cikakken hankali, a taqaice dai kayan “maye” yake baki kina ta durawa cikin ki tsawon shekara da wasu watanni, don haka ya zama dole ki tattarosu gaba daya a zubar dasu, kuma ki dauki alqawarin daina shan komai daga rana mai kamar ta yau.”
Chapter 13 · 0% Book details