← Book details A Dalilin Da Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 20

Sashe 10

A Dalilin Da Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Abba wannan wane irin zalunci ne? baka da hankali ne? kana ganin yarinya ta shigo tana kukan hannunta don zalunci shine za ka qara mata da mari? Idan ba za ka rarrashe ta ba a matsayinta na qanwarka ai…”

“Shiiiiiii..."
Ya sanya yatsarshi a baki ya dakatar da mahaifiyar tashi yana gwalalo mata idanu, tamkar zai cinyeta d'anye
“Mummy kar ki min ihu, kina jin yarinyar tana neman haddasa min ciwon kai amma kun biye mata sai wani rarrashinta kuke yi, don ubanta idan ba za ta fadi abinda ya same ta ba me ya sa take mana ihu don ta kashen dodon kunne? Duk ku kuka lalata rayuwar ‘yar iskar yarinyar nan amma duk zan gyara muku zama.”
Ya karasa fadin haka yana nuna su da yatsarsa manuniya alamun zazzafar gargadi da Jan kunne.

"Abba mu ne za ka gyara wa zama?”
Mummy ta tambaye shi idanunta suna niyyar kawo hawaye kamar yadda ta saba idan ya tasa su a gaba da kwando-kwando na rashin mutunci.

“Mummy na ce ki yi min shiru ko...?”

“Tasss!”
Saukar zazzafar marin da ya jiyo a kumatunsa na dama ya hana shi ajiye numfashin maganarshi daidai, da jajayen idanunshi ya juya don ganin wanda yayi mishi wannan danyen wulaqancin, hada idanunsu keda wuya ya sunkuyar da nashi qwayoyin idanun yana qwafa a cikin zuciyarshi.
“Ashe har yanzu kana shuka wannan rashin mutuncin?”
Abdul’Ahad ya fadi hakan bayan ya cakumo wuyar rigar Abba hannu bibbiyu yana shakeshi.
“Iyayen naka kake ikirarin zaka gyara wa zama? Ina alqawarin da ka daukar min na daina wulaqanta su?” tunkudo shi gaban Mummy yayi ya duqar da shi kan gwiwoyinshi sannan cikin daga murya yace
“Ba su haquri.”

Zazzafar huci ya fesar, zuciyarsa cike da kuna, kamar bazai tanka ba sai can yace
“Allah ya huci zuciyarki, don Allah ki yi haquri.”

Soyayya irin ta d'a da uwa yasa har tana fadada fuskarta da murmushi gurin amsa yafiyarshi.

Shi ma Daddy bai ja da nisa ba yace ya yafe, dama duk tabarbarewar tarbiyar d'an nasu sune sila, Sun nuna mishi matsanancin gata kasancewar sun dad'e ba su samu haihuwa ba, kuma sunan mahaifinshi ke gare shi, shiyasa suke kiran shi da Abba.

Qwafa Abdul’Ahad ya yi, sannan ya cakumo wuyar rigarsa ya daga shi tsaye,
“Idan baka manta ba zuwana garin nan na qarshe na fada maka zan nemi transfer zuwa garinnan ko don saboda akai, don haka ina yi maka albishiri din dawowa garin nan da aiki, Duk inda ka sa qafa ina sane da kai, Ka san abin da zan iya aikatawa da wanda ba zan iya ba. idan kunne ya ji….”
Yana gama fadin haka ya nemi guri ya zauna, ya watsawa Yasmin da take tsiyayar hawaye harara, sannan ya fara mayar musu da bayanin duk abinda ya faru da Yasmin.

Kafin qarfe goma na dare sun nemi mai daurin karaya na gargajiya ya duba mata hannun, ya kumbura suntum saboda jinkirin da aka dauka ba tare da an bi ta kanshi ba, Ashe wai karaya ta samu a hannun, Tasha tsananin azaba kuwa kafin a gama gyaran, don saida aka rirrike ta, duk da haushin da take ba shi yayi matuqar tausaya mata, ganin irin wahalar da ta sha gurin daura hannun.
Ya dauki tsawon lokaci yana rarrashin ta, daga bisani ya nufi bangarensu, zuciyarshi cike da tunani kala-kala
“Me yake faruwa da wannan yarinyar ne? anya kuwa ma mutum ce? Daga riqon hannun Yasmin sai kuma a ce ta karya ta?”
Da fari tun a Plaza ya zaci raki ne da shagwava irin na Yasmin, amma tunda mai dorin ya fadi ta sami karaya jikinshi ya yi matuqar sanyi, zuciyarshi ta cika da tunani da tambayoyi iri-iri.
***
Muna zauna a tsakar falo, misalin qarfe goma da rabi na dare, hira muke yi cikin wasa da dariya. Idan mutum ya kalle ni tamkar ba ni ce kwance magashiyan a dazu ba, hatta Fatima a wannan lokacin ta saki jikinta da mu, duk da dai ba ta cika tsoma bakinta a hirar da muke yi ba, amma idan mun yi abin ban dariya ta kan dara.

“Ya dai Fatima? Fadi abinda yake ranki mana.” Na wurga mata tambayar ba zato don tun dazu na lura akwai abinda take son furtawa.
Tsawon daqiqu tana kallon na da motsa bakinta alamun tana jinjina abinda zata fada ne.

Don in qara mata qwarin gwiwa yasa na ce
“Kar ki damu, fadi maganarki kawai”

“Ina neman alfarma a gareki.”
Ta yi qarfin halin fadin haka tana matsa yatsun hannayenta.

“Alafarmar me?” Na tambayeta da mamaki a fuskata.

“Don Allah ki bamu tarihin rayuwarki, don Allah.”

Dan murmushi nayi, sannan nace
“Kwantar da hankalinki fatima, ba sai kin hadani da Allah ba, da ma a yau na yi niyyar warware muku zare da abawa na tarihin rayuwata. Amma ku bani minti talatin in yi wanka….”

WACE CE AYSHA AZZAHARA’U??
Mahaifina Alhaji Sa’ad mutum ne mai matuqar son kudi, a rayuwarshi ba abin da yake so sama da kudi, tsabar son kudi irin na mahaifina yasa ya baro can garin iyaye da kakanninshi ya shiga duniya neman kudi.

Yana iya yin komai matuqar yasan zai sami kudi, shigarsa duniya ba inda bai zaga ba a manyan garuruwan arewacin Najeriya.
Babban matsalar mahaifina shi ne ya san ya nemi kudi ya tara, amma sam bai san yanda zai kashe su ba, baisan ya biyawa kanshi buqata ba, yana matuqar jin ciwon fitar da kudi ya kashe, idan zai kashe qwandala a cikin dukiyarshi yana jin tamkar naman jikinshi yake yanka.

A dole yake kashe naira dari biyu a rana, ko ciwo yake ya gwammace ya shiga daji ya sassaqo ganyayyaki ya dafa har Allah ya bashi lafiya, hatta abinci bai iya cire kudi ya siya mai tsada, sai dai ya sha garin kwaki da suga shi ma kadan saboda maleji.
A yawon neman arzikinshi ne Allah ya hada shi da wani ubangida mai matuqar dukiya a garin Kaduna, Ya tara arziki mai matuqar yawa a dalilin wannan ubangida nashi, shi kan shi ba zai ce ga inda Alhaji Buba (ubangidanshi) yake samun kudi ba, kuma bai san taqamaimai sana’ar ubangidanshi ba, kawai dai kudi yake kashewa bana wasa ba.

Sai da mahaifina ya shekara arba’in a duniya ba tare da ya yi aure ba, tsabar son kudi irin nashi yana jin matuqar ciwo ya kashe naira dubu dari biyar ya yi aure, Sai da Alhaji Buba ya yi masa alqawarin ya nemo matar zai bashi kudin auren sannan ya je gidan marayu ya zabo mahaifiyata ya aura, kudaden da Alhajin ya bashi kuma na hidimar auren ya zuba a account dinshi, yaci gaba da tara dukiya.

Alhaji Buba ne ya bashi kyautar gida mai kyau a unguwar Rimi, kuma yayi masa kashaidi da tsoratarwar cewa matuqar ya sai da gidan nan to qarshen alaqarsu ta zo, wannan shi ne dalilin da yasa ya haqura suka zauna da amaryarsa Aisha (mahaifiyata) a wannan gida, amma kullum zuciyarshi quna take yi don yana ganin almubazzaranci ne.

Duk kyan gidan da suke ciki amma babu abinci mai kyau, sai mahaifiyata ta yi wata uku ba ta ga idon shinkafa ba, kullum girkinta daga tuwon masara miyar kuka ba nama ba kifi, sai jiqon garin kwaki da manejin sukari, ko kuma ta kwadanta shi da kuli-kuli.
Kuma abin da zai baku mamaki shi ne, shi kan shi mahaifina haka yake cin wannan abincin ba tare da wani damuwa ba.

Watan su biyu da aure mahaifita ta samu ciki mai matuqar wahala da laulayi, sam ba ta iya hassala aikin komai a gidan, kuma ba ta iya cin abincin da mahaifina ya bari a gidan, tana buqatar ababen marmari dana kwadayi, mahaifina yayi tsalle ya dire kan cewa ba ta isa ta sashi asarar kudinshi ba, duk yanda taso ta fahimtar da shi ya qi fahimta, daga qarshe ma cewa yayi saidai cikin nata ya zube matuqar sai ya barnatar da kudinshi a kanta.
Wani baqin hali da mahaifina ya ke da shi shi ne na hana mahaifiyata fita ko da maqwabta ne balle gidan marayu inda ya aurota, kuma ba ta da waya balle ta kira hukumar gidan marayun ta sanar da su halin da take ciki, idan zai fita sai ya kulle get din gidan ta waje yanda babu ta yadda za ta iya fita balle har ta sanarwa da wani halin da take ciki.

Cikinta yana girma jikinta yana kara bushewa, kallo daya za ka yi mata ka tabbatar tana fama da qarancin jini a jikinta, duk wannan bai sa mahaifina ya tausaya mata ba.

Idan yaga tayi kwana da kwanaki ba ta iya barci sai ya sami almajirai ya turasu daji su debo mata sassaqen madaci da ganyayyaki masu illah ga mace mai juna biyu ya dafa ya tilasta mata shan su, kuma tunda mahaifiyata ta samu ciki ba ta taba ziyartar asibiti ba, wannan shi ya kara haifar mata da mummunar matsala ba tare da saninta ba.

Cikinta har ya shiga wata na goma sha daya ba haihuwa ba alamarshi, lokacin ta koma tamkar kwarangwal saboda matuqar rama, sai tirtsentsen ciki a gaba wanda har rinjayarta yake wani lokacin.

A wannan lokacin da mahaifiyata take buqatar taimako daga mahaifina shi kuma sai ya tsiri tafiye-tafiye, sai yayi kwana biyu bashi a gida, Duk da hakan dai bai fasa kulle gidan ta waje ba idan zai fita.

Wata rana da daddare naquda ya tasowa mahaifiyata gadan-gadan, gashi kuma mahaifina baya gida, duk yanda taso zuwa ta bubbuga qofar get din gidan ta ciki ko Allah zai sa wani ya jiyota daga waje ya kawo mata dauki ina….!!! Allah bai bata ikon hakan ba, tayi matuqar galavaita yanda ko dan yatsanta ta kasa dagawa.

Abin da ya qara daga mata hankali shi ne yanda jini yake bin qafafuwanta, duk da dai ba ta taba haihuwa ba, kuma ba’a taba haihuwa a gabanta ba ta san akwai gagarumin matsala daga wannan jinin da taga yana biyowa daga qasanta.

Ciwo ya yi tsanani gareta, azaba tayi azaba, kuma haihuwar ta tsaya cak sai azabar ciwon mara da baya da duk wani sassa na jikinta, ta sadaqar da ci gaba da rayuwar duniya, don haka ta lumshe ido tana kalmar shahada a zuciyarta.
Chapter 10 · 0% Book details