← Book details A Dalilin Da Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 20

Sashe 4

A Dalilin Da Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babban teburin cin abinci ne wanda yake zagaye da qana nan kujeru har guda ishirin manyan kulolin abinci ne har guda uku akai, gefe guda kuwa da qananan farantai guda goma sha biyu. Cokula da abin xiban abinci suma jeri a wani xan qaramin kwando, lemuka kala daban daban da Kofuna da ruwan gora ajiye a gefe daya.
muna zaune akan Dining xin mu takwas har da Baba mai dafa abinci. Bisimillah na fara yi sannan na sanya hannuna na buxe kulolin abincin, qamshin da ya bugi hancinmu nace, “Waw! Yau wani abin daxin aka shirya mana Baba?”
Tana dariya ta ce,
“Ya dai idon naki Aysha? Sa mai ganin da kyau kiga me yake badadeki da qamshi?”

Fried rice ne a babban kulan wanda ya sha kayan haxi kuma ya yi kyan dafuwa sai zabga qamshi yake, a kula ta biyu kuma farfesun kayan ciki ne shima sai tashin qamshi Citta da Curry da Thyme yake yi, a kula ta uku kuma farfesun kan rago ne shima sai fidda nashi kalar qamshin yake.
Murmushi na qawata fuskata dashi na ce, “Ubangiji Allah ka qarawa Baba lafiya mu ci gaba da sharvan lagwadan girke girke.” Dukkan su suka qyalqyale da dariya sannan suka amsa da amin.

“Indai har da gaske abincin ya qayatar da ke ina qaunar ganin duk abinda na dafa ki zuba a flet kin cinye…”
Baba ce ta faxi hakan tana kallona ido cikin ido don ta ji me zance, dariya nayi cikin salon basarwa sannan na xauki flet na zuba kayan ciki kaxan na ce,
“Kin san yau munada fita Baba bai kamata in cika cikina in kasa hassala komai ba.”

“Yan mata bisimillah ko wacce ta zuba abinda take bukata"
ina gama faxin haka nai bisimillah na fara cin abinda na zuba.

Murmushi kawai Baba tayi sannan ta zuba abinci ta fara ci, tsawon awa guda muna kan Dining xin duk da na gama cin kayan cikin tuni, bisa ga al’adata bana tashi akan Dining in bar ‘yan uwana, ko na gama nakan zauna inci gaba da danne dannen wayata har sai dukkan su sun gama sannan mu tashi gaba xaya.
Safiyya da Rahma ne suka fara tattara kwanukan da mukai amfani da su zuwa kiching sannan suka goge gurin.

muna zaune a tsakar falo dukkanmu Baba ce kawai akan kushin bisa ga al’adarmu idan akwai fitar da zamuyi a ranar ko T.V bama kunnawa. Yau ma hakan ta kasance, muna riqe da casbaha a hannayen mu muna jan “HASBUNALLAHU WANI’IMAL WAKIL” har lokacin da agogo ya buga qarfe goma sha biyu na dare.

“Qarfe goma sha biyu da rabi zamu fita, ya kamata mu je mu shirya.”
Ina gama faxin haka na shige cikin xakina, suma duk suka nufi xakunan su don shiryawa.

Wanka na fara yi wanda ya xaukeni tsawon minti goma sannan na xauro alwala sha biyu da kwata daidai na tada kabbara sallah. Tsawon minti goma ina roqon Allah nasara akan ceto rayuwar baiwar Allah Fatima da zamuje, saura minti biyar na fara saka kayana. Wando ne na jeans mai xauke da manyan aljihu har guda shida, abaya akwai biyu ta gaba gurin cinyoyina akwai guda biyu, gefe da gefe akwai guda biyu, ‘yar qaramar T.shit na xauko na sanya bayan na tamke kirjina a cikin brezian da ya yi matuqar kamani, powder kawai na shafa a fuskata na sanya man baki sannan na kama suman kaina na nannaxe shi na xaure da rebom. Drower gefen gadona na buxe sai ga bundigogi kala-kala a ciki.

Qanana na xauka guda huxu na saka biyu a aljihun wandona na baya, na saka biyu a aljihun gefe da gefe. Wata riga mai kama da leda dake ajiye akan gadona na xauka na wareta na sanya, rigar tana da xan tsawo don ta rufe quguna dana adana makamai na. a bayan rigar rubutu ne qanana anyisu da Golden Color idan ba kusa dakai na matsa ba bazaka iya gane abinda aka rubuta ba.
Hula ta na xauka asaman akwati na sanya a kaina, sai na xauki wani baqin gilashi na aje a gefena, takalmi na xauka na zura a qafafuna na xaure igiyar tamau yadda duk rintsi bazai tava kwancewa ba, gilashin na riqe a hannuna na fito da sauri zuwa falo idona kan agogo qarfe goma sha biyu da rabi da minti xaya.

“MATAN FAMA kenan”
Nai musu kirarin da ya sanya su sakin murmushi dukkan su suna sanye da riga da wando, da takalmi shigen na qafa ta kala ne kawai ya bambanta sun xora rigar mai kaman ta leda a jikinsu irin nawa, amma savanin nawa da akai rubutu da ruwan gwal su nasu farin rubutu aka yi, suna sanye da gilashi baqi wanda ya kusa mamaye rabin fuskarsu.

Baba ta na zaune kan kushin jikinta sanye da babban hijabi, hannunta riqe da casbaha da alamu sallah ta idar.
“Baba za mu tafi.”
Na faxi hakan bayan na durqusa a gabanta. “Allah ya bada sa’a Ubangiji yasa ku dace da abinda zaku fita nema.”

“Amin summa Amin” muka amsa gaba xaya cikin qwarin gwiwa.

Babbar mota ce Jeep kirar sienna, duk sanda zamu yi irin wannan fitar na gaba xayan mu a ita muke fita. Sadiya, Nafisa Siyamah su suka zauna a kujerar baya na motar, Suhaila Rahma su suka zauna a kujerar tsakiya na motar, Safiyya ta zauna a mazaunin Driver ni kuma na zauna a gefenta sai da ta karanto addu’ar hawa abin hawa sannan tayi bisimillah ta tada motar.

Baba ce ta buxe mana get xin gidan muna ficewa ta maida get xin ta rufe ta kulle.

Tafiyar minti ashirin ta kawo mu hanyar da zamu sauka daga kan babban titin zuwa Prison xin, tun daga can nesa nai mata umarni ta yi Parking xin motar a gurin, muna fita ta kulle motar muka fara tafiya a qafa, hasken tocilan da muke hangowa acan nesa damu shi ya ba mu tabbacin masu gadin gidan ne su ke aikinsu.
Tsayawa na yi cak! Suma sauran ‘yan uwana sai suka tsaya a guri xaya, haxa kawunan mu mu ka yi nayi musu raxar abinda za mu yi sannan na xauki hanya na shige cikin daji da Tochlight a hannuna.
Su kuma suka fara sanxa suna qara kusantar gidan.

Gudu nake yi iya kacin qarfina ina taka busassun ganyayyaki da takalman qafata, idan da idan da sabo na rigada na saba da keta daji komai tsawon dare haka babu tsoro ko kaxan a tare dani, sai da nayi gudu mai yawa na zagaya gidan yarin ta can baya sannan na ciro bindiga ta na harba sama ta bada qara “Dam!” minti biyu tsakani na sake danna kunamar bindigar zuwa sararin samaniya. Harbin da nai na farko shi ya fara janye hankalin masu gadin suka fara waige waige suna qara dallara hasken tocilar su da gyara riqon bindiga qirar Single barrack xin da take hannun su.

“Kamar ta bayan gidan nan akai harbin nan ko? daya daga cikin masu gadin ya tambayi 'yan uwansa, Bai samu sararin a je numfashin maganar shi ba balle har dayan ya ba shi amsa suka qara ji yo wani qarar harbin, ba su qara tankawa junansu ba suka rabu zuwa inda suke da tabbacin harbin ya fito, daya ya bi hanyar dama, dayan kuma yabi hanyar hagu, da sauri na ajr tocilan hannuna a jikin wani dan itaciya yana haska gidan yarin yanda duk wanda ya biyo ta bayan gidan zai iya hango hasken. Daya ne ya fara qarasowa kafin ya ankara na lallaba ta bayan shi na buga masa kan bindiga a kunnenshi, shu…. Ya tafi zuwa qasa idanunshi suna rufewa suna budewa saboda azaba.
Kafin ya dawo hayyacinshi na shaqa mishi wata farar hoda wanda na karba a hannun Sadiya, daga can nesa na ji alamar tahowar daya mai gadin don haka na sulale na kwanta a cikin ganyayyaki.
Idanunshi da tocilan hannunshi can nesa suke haskawa don bayyi tsammanin wani zai kwanta a gurin ba, qafata na sanya na tade shi ya hantsila can gefe bindigar hannunshi ma tayi can gefe daya, kafin yayi yunqurin tashi na sanya qafata na buga mishi naushi a ciki, runtse ido yayi saboda tsananin zafi kafin ya bude na shaqa mishi hodar hannuna.
Tocilan na dauka na haska fuskar mai gadin da ya fara isowa gurin barci yake hankali kwance, amma wanda bai sani ba sai ya yi tsammanin mutuwa ya yi, ban saurari dayan ba don nasan shima yanzu barcin zai dauke shi, na qara matsawa jikin gidan yarin kadan, harbi na fara sakewa ina bada tazarar minti biyu tsakani sai da nai harbi hudu, qarar harbe-harben shi ya gigita hankalin jami’an tsaron da suke cikin gidan don sun tabbatar ba lafiya ba, duk tsammaninsu ya tafi kan cewa ‘yan fashi ne suka biyo wani da yake neman tserewa har kusa da gidan yarin, don hakan ya sha faruwa basau daya ba ba sau biyu ba.

Jin da sukayi harbin yakika qarewa ya sa suka fito da gudu dukkansu don ganin me yake faruwa. Su Rahma suma suna kwance a cikin ganyayyaki kamar yadda muka tsara, kafin jami’an tsaron su ankara aka ringa zarge qafafunsu da igiya ba tare da suna ganin masu musu wannan daurin talalar ba.
Sun samu nasarar zarge qafafun mutum tara, yayin da mutum shidda suka ankara da abinda yake faruwa.
Kin qarasawa gurin suka yi don gudun afkawa tarkon da sauran ‘yan’uwansu suka afka, Daga nesa suke haska gurin da tocilan hannunsu amma ba su ga komai ba sai ‘yan uwansu a kwance. Ga makamansu duk sun faxa gefe guda, a tsorace suka cigaba da haskawa suna harbe-harbe a iska.
Chapter 4 · 0% Book details