← Book details A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 29

Sashe 7

A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D'uk suna
d'aki, Ummi an hakimce a kujera ana d'anna
waya.

"Har kun rigani ashe d'uk saurin nan
nawa?..

K'allonta Ummi take ganin tana since
lifaya,ga flasks da jaka an ajiye.

"A ina zaki zo
da wuri,ke dad'i miji ce ai..

Banza tai da ita tana
gaida Mama, itama Maman a dan ciki ta amsa
mata.

D'uk sai taji ba dad'i, jikinta yai sanyi,da
murnar ta tazo amma sun dakushe mata.

"Sai ya
barki ki waiwayo mu?..

Maman ta k'alla, kan tai
kasa da kai, "ai na zata irin ta y'an da zai
miki,sai kin shekara koh kin fito yawan arba'in....

Baki Ummi ta ta6e,kan tace "d'uk mai irin halin
Ja'afar ai dole yai k'ulle Mama,in banda haka
wata biyu wai sai yau za kizo gidan ku,ni nazo
yafi a girga,wallahi tun wuri ki mawa tufkar
hanci..

Dan in kika sabar mishi da haka zai mike.

Dagowa tai da niyar yi wa Ummi magana Mama
ta tari numfashinta.

"Y'ar uwar ki ce,dole ta fad'a
miki gaskiya, ke zaki nema mana mutunci a gun
miji ki ma ji da k'yau.

Kasa tai da kai tana
murmushi, duk da a zuciyarta bataji dad'i ba
sam.

"Mama baza'a a sake ba inshaAllah.

Da
haka aka ware kuma zancen nawa ta tara a
banki.

"Ni fa ba'a ban kud'in cefane Mama, komai
yana kawo min har katin waya,sai dai in ina da
bukata yana cewa na mai magana...

Baki Ummin
ta ta6e,kan ta zuge jaka, sai ga nan kud'i tumi.

"Kinga kud'in cefane na,nima ai ba abinda na
rasa,ina ruwana da wani ni kud'in kati?

Kawai naji
dumus ni...

Gashi nan na banki ne dana sa Mama
ta sai min.

Kai Maman ta k'ada, tabbas Ummi
tasan ta kan maza,shi yasa take burgeta sosai.

Itade Salma an sata duhu,dan sun raba
hankalinta biyu.

T'saka mai wuya kenan.

By
Feenat Ja'afar.
9/29/16, 9:00 AM - Queen Safiyyert
: *A BAKIN AURANKI* *
Feenat Ja'afar*. 15_Sai
dare yazo a dalilin yadda take fad'in bata gama
ba,har cikin gidan ya shiga,kawai kuma sai yake
ma Mama k'warjini, dan fuska sake ta amsa
mishi,kan suka tattara suka tafi.

Koh da Salma
tazo k'wanciya maganganun su Ummi take ta
tunawa.

Ita babban haushinta ma yadda aka fa
fad'in koh tsoron Ja'afar take.

Washegari ma
haka ya yakaita gidan su Abban shi,nan ya wuni
suka biya gidan Garba.

Yau tun (7:30) ya fita,
sakamakon an fara jarabawa a makarantu.

Sha
d'aya ta gama aiki ta fara jiyo hayaniyar y'an
unguwa a makotanta,halamun sun hallara za'a
fara chapter.

D'uk yau sai hankalinta yai
gidan,duk da ba sabawa tai dasu ba.

Waya ta
d'auka,ta d'anna kiran Ja'afar _no answer_..

Ji
take kamar ta zaga in ya dawo ta fad'a mishi,sai
dai ta daure.

Da yamma kam kamar kullum yazo
fita shago tace zata leka makota.

Jim yai ba
amsa,sam tarbiyar matan unguwar bata mishi
ba,baya so Salma tai sabo dasu a samu
mishkila,amma kawai sai ya k'ada mata kai, "Sai
kin dawo.

Cike da murna ta rakoshi har bak'in
kofa ta koma d'aki.

Da sallamarta ta shiga,tun
daga bak'in kofar gidan zaka fara jiyo karad'in
matan.

Da fara'ar su suka amsa,d'uk sun baje a
tabarma, wasu ba koh dank'wali.

A dan kunyace
ta gaida su, dan ganin duk sun girme ta,sai wata
mai kamar shekarunta da D'a a goye.

Chan hira
taci gaba, zabiyar ciki sai karanta musu makamin
kama wuyan maza take.

Salma tai shiru tana jin
su,tabbas babban burinta shine Ja'afar ya so ta
har karshen rayuwa.

"Su amarya yanzu ai farin
take gani kan a juya mata bak'in bayan..

K'allo
matar tai,bata gane nufinta ba,sai dai bazata iya
tambaya ba.

Haka firar yau ta tashi kan makamin
rike miji har Salma ta fito.

Tunda ta zauna a gida
take tariyo firar sun.

Tabbas shawarar nan tayi ta
makamin rike miji, ta hakan kam ba yadda
Ja'afar zaiyi ya raina ta...

Toh amma Ja'afar
yana sonta,batajin zai mata dabi'a irinta mazajen
sauran Matan da ke fad'i.

Nan ta jefar da
dayawa a hudubar da taji a makota tai kitchen
dan k'unna ritio.

Sai d'ai Washegari ma da
yamma Salma ta sake tambayar shiga makota.

Karan nan kam kir ya fito yace mata a'a, da ido
kawai take binshi, "Ya Ja'afar yafi zaman kad'aici
ne,ba jimawa zanyi ba ka ji...

Ta langwa6e kai.

Ba dan yaso ba ya k'ada mata kai.

Minti biyar
bata kara ba tai makota,gidan chapter.

Yau kam
a sa'a taje,dan suna a kan firar rashin fitar matar
gidan,sai bata dabaru suke akan yadda zatai mijn
ya rika barinta fita.

"Kar ki fara tambayar
unguwa kina fara'a, sosai zaki dake mishi,mud'in
yaga 6acin rai toh jiki na bari zai barki.

Ni da
farko haka Salisu ya t'siro min da k'ulle,tun farko
nai ma tufkar hanci,da yace A'a yana fita zan
arce, gashi yanzu har ya saduda yana barina duk
inda na tambaya.

T'sam Salma tai,tana tariyo
maganar Ummi da Mama ta ranar,ga nan ta
makotanta.

Daga ganinsu sun san takan duniya.

Tabbas ta yarda itace tun yana d'anye ake
tank'wara shi.

Tun yanzu ya dace ta takawa
Ja'afar birki koh dan ta t'sira daga zargin wai
tana tsoron shi. *Wasa farin Girki.* Daga ranar
Salma ta tsiri dan hali,fita makota,tambayar fita
gida,ga wani t'sarewa da take in tana tambayar.

Kamar kullum tazo rakiya taja ta t'saya a gefe,
"Ya Ja'afar...

Jiyo wa yai shima rai ba dad'i,tare
da zuba mata ido,yasan abu daya zata tambaya.

"Zan leka gidan Maman Ummi gobe suna za ai
k'ulli...

K'allonta kawai yake, yadda tasha mur
tamkar wanda take bashi umarni.

"Anya Salma
wani abu bai shiga kanta ba kuwa?..

Gaba daya
ta sauya mishi hali k'wana biyu in dai akan fita
ne..

G'wara tun wuri ya taka mata burki dan yaki
jinin yawan fita sam shi.

"Kiyi hakuri Salma,ki
bari ki leka goben tunda suna ne...

Tuni ta
k'ank'ance ido, "gaskiya kar ka maidani saniyar
ware a unguwa ya Ja'afar, yau k'ulli kowa ya je
sai ni ce bazani ba?..

Ai sai a chake ni gobe
dama suna fad'in ni dad'i miji...

"Kuma ma ba
wannan ba,nima sai ina zuwa za'a zo min in
nawa yazo ai....

Shiru tai ganin yadda ya zuba
mata ido yana kallo, chan ya nisa "amma Salma
kin fuskanci kin fara sauya hali kuwa?...

Kin koyi
ja dani,kin koyi gantali k'arfi da yaji..

K'alloshi tai
a wani iri, "au gantali ma nake Ya Ja'afar?..

Fisabilillahi wace fita ce nake yi ba dalili?

A satin
nan sau biyu koh uku ne fa na fita kuma dubiyar
Ummi ne ba wani waje ba, koh shi ka ke nufi da
gantalin?

Kai ya k'ada,"kar mu rika ja in ja dake
Salma,kiyi hakuri kawai gobe ki je...

Juyawa yai
ganin tana neman wata maganar yai waje, baki
ta ta6e,kan tai cikin d'aki.

Tana jin tashin
machine d'inshi ta zaro hijabi ta k'ulle gida tai
cikin gidan k'ulli.

"Ai na zata bazaki zo ba,da har
zanyi aike naga machine din maigidan.

Hijab ta
cire ta jawo jarka, "bari ke dai Maman
Ummi,dak'yar na fito fa..

Murmushi tai kan ta
d'akko wani abu a bakar leda,"yanzu saratu ta
fita an kawo sabbin kaya dakakku wallahi,tai ta
jira baki zo ba zata tafi na dau miki wannan...

K'ar6a tai tana dubenshi kan ta kunce ledar,roba
ce karama da wani abu mai d'anko.

"Takalmin
Kaza ake fad'a miki,nasan yafi haka,kawai ta
mana sauki ne..

Amma abin ba magana,sai an
g'wada akan san na k'warai...

Dariya suka sa aka
tafa harda shewa.

"Wannan ne kawai makamin
wulakancin D'a namiji,tunda kuka d'aurani kan
_network_ nake son raina Allah.

"Dari biyu ai ma
yai araha...

Bari yazo dari biyar zan tat'sa, dan
asusu nake kan zuwa watan haihuwar Ummi na
tara da yawa...

Sai da aka gama k'ulli ana firar
duniya,a debo gulma har aka gama,ana kiran
magriba ta tuna Ja'afar, da sauri-sauri tai gida
dan yau abinci ta zarce tayi.

Kamar kullum ya
dawo bayan magriba ana kiran isha'i, sai dai sam
ranshi ba dad'i,nan tasha jinin jikinta,koh ya
dawo bata gida ne?

Har yaje masallaci akai isha'i
bai dawo ba har ta gaji da jiranshi ta k'unna inji.

Sai chan kusan tara ya shigo,har yanzu jiya
iyau,sam kuma sai taji ba dad'i, tun kan ya fad'i
lefin da tayi,amma de sai ta dake.

Komai
yayi,dan har abinci ya ci,sai dai fur yaki sakar
mata.

"Wai Ya Ja'afar mey nai ne ka ke ta shan
kanshi?..

K'allonta yake da mamakin anya
lman shi ce wannan?..

Bai da amsa,sai a
gunta kawai,saboda haka ya tashi yai hanyar
d'aki.

By Feenat Ja'afar.
9/29/16, 9:03 AM - Queen Safiyyert
: *A BAKIN AURANKI* *
Feenat Ja'afar*. 16-Ya
fito a band'aki ya ganta zaune a gad'o,kai ya
dauke yana goge jiki da _towel_,d'uk sai jikinta
yai sanyi,tabbas tasan Ja'afar kila zuciya
yayi,har ya gama shirin bacci uffan bai ce mata
ba,tuni ta fara kuluwa ganin ya ja filo bai bi
takanta ba.

"Wai mey in ma ina ta maka magana
tun dazun?..

Kai ya dago ya k'alleta da tuhuma,
"mey kika ce ban amsa miki ba?...

Baki ta turo
gaba kad'an, kai ya kada,tukun yace "Salma!...

Salma!!..

Dagowa tai ta bashi hankalinta dan jin
kiran da yawa.

"Na'am..

Ido ya tsura mata,sai tai
gefe da nata.

"Ina kika fita dazu har magriba?..

Jin tambayar tai ta bazata,hakan yasa ta kasa
K'allonshi, sai da ya maimaita tukun ta amsa a
hankali da "gidan k'ulli...

"Gidan k'ulli?..

Mey
mukai dake toh kan na fita?...

Duk t'siya ta ki
jinin kuma taga ran Ja'afar ya 6aci, sai dai an
rinjayi zuciyarta.

"Kai hakuri...

Itace Kalmar da ta
fad'i.

Tashi yai ya jingina da pillow,kan cikin
nut'suwa ya fara mata magana.

"Ba wannan ne
ba karon farko da ki ke fita ba'a son raina ba
Salma,nasha aiko yaro da sako yace gida a k'ulle
yake,amma nai ta daga miki kafa.

Duk gantalin
da take bada yardar shi ba sai da ya sanarta,ga
t'sinuwar mala'iku dake binta har ta dawo...

"Sam wannan ba Salman da nasani a wata 5 d'in
baya ba...

Wannan cikin wata d'aya ta sauya,bata
jin magana ta,duk abinda tasa kanta take ganin
shine d'ai dai shi take...

Sosai ya kasheta da
kalamai,har ta fara hawayen wai bata jin
magana.
Chapter 7 · 0% Book details