← Book details A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 29

Sashe 14

A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari har kofa ta rako shi zai fita tace zata
leka gidan Maman Ummi..

Yana fita yace mata
sai ta dawo kawai.

Da k'allo ta bishi,sai ta ga
kamar gat'se ya mata,dan haka ta koma ciki tai
k'wanciyarta.

Mukullin gidan da ake g'yara zai
fitar musu dashi sai ya dawo.

A k'wance ya
sameta ido rufe a parlour,sai yai jim,ganin bata
fita ba har ya dawo.

"Har kin dawo ne?..

Kai ta
girgiza mishi,sai yai d'aki yana tunaninta, haka ta
saba mishi kan gaba ta fand'are mishi,shi dai
yasan yai alkawarin mud'in ta tambaye shi fita
ya d'aina hana ta,yasan duniya makaranta,da
sannu zata gane abinda yake gujar mata.

Koh da
zai fita sai ya kara nanata mata kan taje kawai.

Bai jima da fita ba ta fito,tana dan jin hayaniyar
su kasa-kasa.

Har zatai Sallama sai ta ja ta
t'saya jin wata gulmar da suke.

"Ai yanzu ya
zamarta mai gadinshi, tunda ta dawo ba inda taje
tana d'aka,koh duk sururin zai kara auren ne?..

Tana jin Maman Ummi tace "oho mata,ba ita
areni muje biki ba,mijina baya fad'a..

Muryar
Maman Abba tajiyo tana fad'in ''ni tausayi ma
take bani wallahi, ranar chan dana shiga duk ta
rame tai baki,kana yaronka da kai an ma saki
2....

Baya tai cikin sanda danjin wani na shirin
fitowa.

Gida ta koma ta cire hijab tai dabar a
kujera, tun yaushe haka take faruwa da ita?..

Ashe ita k'allon mara wayo suke mata acikinsu?..

Kai ta daga sama, lalle ta gane mey Ja'afar yake
nufi da mutunci yake nemar mata..

Yau ta gane
ashe in an yi gulmar wani da kai yau gobe da kai
za'a kafa ai taka.

"Allah na gode maka daka sa
na ji na kuma gani.

Tabbas Ya Ja'afar babban
gata yai mata.

Toh a ina ma suka samu labarin
za ai mata kishiya?..har dare tana neman amsa.

Ranar har kukan bakin ciki tai na taraiyarta dasu
Maman Ummi.

Tuni ta tattare kowa ta wat'sar
shi,duk da ba duka aka taru aka zama daya ba.

Ranar Maman Waleeda da suke kira uwar tsoron
miji ita ta zo mata harda nasiha har gida,matar
da koh gidanta sai tai fita ashirin bata leka
ba,kuma makociya ta kusa,har misali tai mata da
Maman Ummi.

"A kaf unguwar nan bana tunanin
da matar da take cikin takura irin na Maman
Ummi Salma, ke shaida ce,in kinji gidan yai shiru
ba koh tarin yaro kasan uban na gida.

Sannan in
zai shekara ba taje ko'ina ba shine dai dai a
wajenshi,duk fita in zatai satar hanya take tasan
in ya fita da yamma sai dare,amma a gun kuri
tafi kowa iya dadin magana,da ina cikin su,daga
baya na gane taraiyyata baza tai dasu ba,sai na
zabi zaman gidana ya fiye min alkairi sama da
yawan gulma.

"Ka'rkara in abu ya faru in leka a
tsatssaye in dawo, dan Allah ki iya kafarki
Salma,dan zasu kai ki su baro ne kawai.

Kai ta
k'ada mata, "Na gode Maman Waleeda,Allah bar
zumunci,kuma InshaAllah naji bayanin ki,duk da
mun kusa tashi a unguwar ma duka InshaAllah.

Anan ta sanarta za ai mata kishiya,k'warai ta
jajanta mata kan ta kara da y'an shawarwari,tun
daga ranar mutunci da Maman Waleeda
suke,kusan duk yamma tana turo mata su
Waleeda taya fira,har lokacin tashinsu yazo.
***************************** Cikinta yana da
wata biyar lokacin auren Ja'afar saura sati.

Sam
bazaka zata Salma bace, dan tamkar bai dameta
ba haka tai a auren.

Har ranar Ja'afar yana fad'in
wai ta daina sonshi gaba daya,koh kishi bata yi
zai kara aure,murmushi kawai ta masa,dan tsaf
ta kula da rawar kan da yake k'wana biyu.

"Ba
k'ya shirye-shiyen komai gashi lokaci ya taho
fa...

Tamkar ya choka mata abu makogwaro taji
wani iri,kawai sai ta sa mishi ido tana k'allo.

Tabbas rawar kan Ja'afar karuwa take akan
auran nan,banda haka wani irin tambaya ce
wannan?...

Shikam tunani yake yadda Salman ta
g'yaru har kullum,a ganinahi halin ko'in kula da
yake nuna mata ne akan fita.

"In da hali zan fita
kar6o wasu kayana unguwar Ummi.

Kafad'a ya
daga mata,kan yace "sai kin dawo...

Yai waje.

Baki sake ta bishi,tun bayan dawowarta ta kasa
gane inda Ja'afar ya dosa,abu yake mata tamkar
ya kosa da zaman ta a gidan.

Gashi tun kamin
amarya ta tare har ya sallamata,wai ko'ina nan
gaba in zata kawai taje,dan yanzu bai son 6acin
rana irinta da.

Toh mey yake nufi?

By Feenat
Ja'afar.
9/29/16, 9:11 AM - Queen Safiyyert
: *A BAKIN AURANKI* *
Feenat Ja'afar*.
26_Kowa bin kofar dakinta yai da kallo, yana
murna ba'a rikicin mata biyu a gidanshi yau gashi
an fara,dole ne tun wuri yai ma tufkar hanci.

Har
yayi dakin Salman sai ya t'saya, dole ne ya nuna
mata kuranta, in da tai mishi fitsara ya k'yale toh
yanzu bazai d'auka ba,dan ba ita kadai bace a
gidan,kawai sai ya juya dakin Bintu.

Kuka take
yana ta fadanshi taki kulashi, chan kuma sai ya
sassauto, "Ni tashin hankali ne bana so a gidana
ne,tun wuri ma in zaku had'a kai ku had'a, dan
ba mai chazan hawan jini.

Kai ta dago tana mishi
k'allon tuhuma, "Au shine dalilin da yasa ka fad'a
wa matarka baka so na?..

Ni nace ina son ka
koh?..

A haka za ai zaman lafiyan?..

"Ke kinga
bana son iyayi,dawa nai wannan zancen?..

Da
sauri cikin kuka tace "da matarka man,wato
harda fad'a mata kwantai nayi nai ma tallan
kaina..

"Ban san anyi maganar nan ba Malama,ki
ma cire zargin ni na fad'a mata, bari na je zata
fad'a min yaushe muka fara y'ar sharri da ita...

Waje yayi zuwa dakin Salman.

Kai Bintu ta k'ada,
"ashe munafuka karya take dan ta had'ani fad'a
da Miji,toh karyarki taci karya,Allah sa ya k'wada
mata mari tukuicin sharri.

Ita kam tanajin bud'e
kofarshi ta mike tare kama k'ugu ta k'ank'ance
ido.

"Salma yaushe muka fara y'ar sharri dake a
gidan nan?..

Yaushe nace miki Bintu ce tai min
tallar kanta na aura?..

Harara ta sakar mishi da
k'allon kar ka rainan hankali.

"Ka nad'e taburmar
kunyar ka man ta haka,wato kayi amarya shine
ka zabi ka tuzartani agunta,karafkaf abinda ya
faru ta fad'a mini,toh da ka fad'a mata saura
igiya daya ta aurenka a kaina sai mey?..

Baki ya
saka cike da mamaki,lalle ya shiga tarkon kaidi
na mata, wato kowacce sharri take neman k'ulla
mishi a gun y'ar uwarta ashe?..

Bai da tace wa,
kawai sai ya juya zai fice, da sauri tace "a ka
fita man,dan nayi imani bazaka karyata cewar ba
kai ka fad'i ba...

"Idan kuma habaici da iyayi
kake neman matarka ta dinga min dan ka huce
haushinka na da toh bissmillah,dai dai nake dana
sa kafar wando daya da kowa a gidan nan
wallahi..

Juyowa yai yana kallonta, sai tai d'aki
ta barshi t'saye baki sake.

Titi ya fice ko ya
samu sa'ida, lalle yau ya jinjinawa sharrin
mata,amma kaf yafi jin haushin Salma,dan sam
yanzu ya fuskanci fitsararta tafi ta da yawa.

Tun
daga ranar ba jituwa t'sakanin matan, daya in
Bintu ta fad'awa Salma sai ta fad'a mata
dubu,daga karshe ta bige da kukan bakin ciki, har
mai gidan yazo ta kit'sa mai karya da
gaskiya,wani sai dai ya bata hakuri, dan a
ganinshi yanzu Salma tafi karfinshi,dan da ya
mata magana ita y'ar dika take,daga shi har
amaryar zata chake tass, sai dai yai abinda zaiyi.

Shi yasa shi kuma ya t'siri mata t'siya,in dai zata
kona mishi rai,toh shi kuma zai ta biyewa Bintu
suna ta mata feleke a t'sakar gida, daga karshe
kam sai yaci nasara,dan haka zata shiga d'aki tai
ta kukan bakin ciki,a nan zai ta mata dariyar
keta. ***** Sallama taji kamar ta Maman Ummi
da Maman Abba,lekawa tai ta window, sune
kuwa, "munafukan Allah ta'ala kawai...

Ta fada
tana kokarin ta fito rai 6ace,dan tai imani duk
abinda take fuskanta yanzu da sa hannun su
aciki...

Chak!

Taja ta t'saya rike da labule a
hannu ganin Bintu ta fito da gudu danjin sallamar
su.

"Sai yau Aunty Ladi zaki zo min?

Har nayi
fushi ai..

Baki sake Salma take k'allonsu,tana
k'allon suna nuno kofar dakin da baki suna ma
Bintun kuskus tai baya da sauri.

Ido ta rint'se
tare da cije le6e,lalle mutum mugun ice ne,yanzu
ta gane inda Bintu ta samo duk wasu
_information_ na zaman aure nata ba agun
Ja'afar ba,ido ta bud'e, ta d'au alhakin Ja'afar,
har rantsuwa yai mata amma taki yadda.

Karshe
har raba shimfida tai dashi akan maganar har sai
da ya gamo ta da Aunty A'i aka shirya.

Zama tai
tana jiyo shewarsu a dakin Bintun.

Har kullum
bazata daina nadama akan taraiyarta dasu
Maman Ummi ba,tasan duk fushin Ja'afar ne da
t'sinuwar mala'iku ke bibbiyarta.

Har hawayen
bakin ciki tayi yau,tai kuma alkawarin daina
sa6awa mijinta ko da taji haushin shi.

T'sakar
gida ta fito bayan ta g'yara fuskarta, tai sa'a
kuwa sun fito zasu tafi suna ta dariya.

Ganinta a
t'sakar gidan yai bala'in saita nutsuwar su,a
t'saye take k'yam tamkar wata soja ta had'e rai
tam,ido cikin ido take k'allonsu,tuni suka hau
inda-inda, "dama kina ciki?..

Sannun ku da gida..

Harara ta sakar musu,ba shiri sukai hanyar
waje,Bintu ce ta t'sayar su, "bari na raka ku
hanya Aunty,ina zuwa na kira mai gida izinin fita.

Duk tana k'allonsu,har tai ma Ja'afar waya wai
za tai rakiya waje ya bata izinin fita.

Bokiti ta
zaburo da sauri tai hanyar fita,da sauri sukai
waje sun zata kansu zata iyo,kawai sai ta ja
t'saki ta shige band'aki.

"A toh na zata koh rafka
mana zatayi ai,g'wara muyi ta kai ta kai,dan
wannan da gani zatai kishin hauka...

Dariya suka
sa tana jiyo su ta band'aki daga zauren sunki
tafiya.

Ruwanta na cika da ta tara ta bud'e
band'akin a hankali tai zaure, basu nufa ba sai jin
saukar ruwa sukai akansu har Bintun.

Bokitin ta
d'auka tai kansu dashi a sukwane, da ture ture
suka fita waje da gudu.

Tana haki ta leko kofar
gidan ''Ashe karyar munafurci kuke, da ku t'saya
na g'wada muku aikin mahaukaciya, shegu gadon
na aiya,a haka zaki kare Maman Ummi wallahi,
InshaAllah kema dubinki ta kusa cika.

"Ke kuma
yau mai rabani dake a gidan nan wallahi sai
Allah, yau zaki ga karyar iskanci.
Chapter 14 · 0% Book details