← Book details A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 29

Sashe 27

A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai nima ka sallame ni
kawai,dan bazan zauna da mutumin dake
kyankyamin zuri'a ba,dole yau na barka,Allah ya
yafen baya,amma yanzu kam ta kau,ka sake ni
nima kawai...

"Bazan saki ba,amma dole ki fuce
min a gida,dan ba mai sa min hawan jini...

Kuka
Salman take tana jiyo sababin da Alhajin ke yi..

Hannu Miemie ta kai tana girgiza mata kai itama
tana kukan,gaba daya ta rungumo y'arta tana
kuka mai cin rai,ita kuma haka Allah yayi ta
marar sa'a a zaman aure,gashi yau a dalilinta
auren shekara sama da ashirin na neman
tsinkewa bayan ta t'sinke nata.

By Feenat
Ja'afar.
9/29/16, 9:39 AM - Queen Safiyyert
: *A BAKIN AURANKI* *
Feenat Ja'afar*.
42_Jugum Abba yai bayan jin bayanin Aunty
A'i,ita dai Salma sai kuka take,dan tasan yau
kam sai ta Allah,fad'a kam sai dai ta toshe
kunnenta.

Amma da mamakinta sai ji tai ya
sauke ajiyar zuciya tare da fadin "Allah ya
kyauta toh,dama tun farko ni mutumin nan ba
wai ya mun ba ne.

"Yadda naga kowa na yinshi a
gidan musamman Babar taku yasa nabi yarima
nasha kid'a, sai fatan Allah yasa haka shi yafi
alkairi..

Mama ce ta riga kowa saurin fad'in
"Amin,ni nasan naso shi,amma daga baya sam
mutumin ya fice min akai,dan daga gani ba wai
zaiyi wani mutunci bane,ga dankaran kulle,yanzu
kuma an kara da rashin son haihuwa..

Dame
yarinya zata ji?..

Kallon mamaki suke ma Maman
musamman Salma, yau mama ke fad'in aibun
Alhaji da bakinta?...

Lalle abu ya 6aci.

Da dare
suna kwance ta tasa Miemie a gaba tana
kallo,itama ido ta sa mata, tunaninta zancenta ya
tabbata.

A dalilin Miemie aure ya 6alle..

Murmushi tai kan ta gyara kwanciya.

"Miemie..

Kai ta daga tare da fad'in "Uhmm..

Sai ta
mirgino kusanta tai rub da ciki "Kina murna
kuwa?..

Baki ta yage mata ba dan ta fahimci
nufin Auntyn ba.

Sai ta kad'a kai,ta rasa wane
irin nishad'i ke shigarta da yamman nan zuwa
daren yanzu..

"A k'ya kam yi murna,wato kin
rabu da alakakai koh?

Kai ta daga mata tana
dariya..

Itama tana dariya ta fara mata chakulkuli
su na k'yak'yata dariya har su Abba dake waje
suna jiyo su.

Mama ya kallo,itama shi take kallo,
"kina jin mutananki koh?..

Kamar yau take
Sallah..

Murmushi tai tana sadda kai kasa, sai ya
girgiza kai yana tuna wani abu. ****** Tun daga
wannan lokacin hankalinta ya koma kan
makaranta, babban bakin cikinta bai wuce yadda
Alhaji yai burus da maganarta ba,a ganinta in har
da mutunci koh Abbanta ya samu da zancen..

Gashi a kalla yanzu ta kusa cinye kwanakin iddar
ta.

Duk suna waya da Maman su Nabila tace
yana zuwar musu,sai dai ita baya samun ganinta.

"Aunty!..

Aunty!!..

Da dan gudunta ta shigo gidan
tana k'wada mata kira rike da leda tana ja,bakin
nan har kusan kunnen Miemie.

Kamar a mafarki
taji kira ana ta6ata,a hankali ta bud'e ido dan
bata jima ba da bacci ya debeta sakamakon
ciwan period da take.

"Uhmm Miemie..

Ya akai?..

Ledar hannunta ta hau bud'e mata tana mata
magana duk a hard'e dan murna.

Riguna ne y'an
kanti masu kyau da tsada da takalma, sai teddy
guda biyu da y'ar tsana mai feeder a baki.

A
zabure ta mike tana duben Miemien,tasan ba mai
irin ma wa y'arta tsarabar nan sai Abbanta,yawu
ta had'iye kamin tace "Miemie,ina kika samo
kaya haka?..

Dagowa tayi kamin tace "Abba ne...

Tsam tai tana kallon irin farin cikin da Miemien
take,wato in zai shekara bata ganshi ba tasan
Abbanta.

K'allota tayi tana mata yake ganin
yadda take cire feedern a bakin y'ar t'sanar tana
fad'in Inya..

Inya.

Da sauri ta tashi tare da zarar
gyale tai waje.

A kalla zataso ganinshi koh dan
ganin yadda yake a t'sawan shekara guda da
d'auri.

Sai dai har ta gama leke bata koh hango
mai kamar Ja'afar fa sai sawun mota.

Zaure ta
koma tana lumshe ido tare da dafe kirjinta.

Babu
makawa Ja'afar ya shigo zauren nan..

Dan ga
nan kamshin turarenshi ciki tana iya shakarshi.

Jiki a sanyaye ta juya ta koma cikin gida, a chan
d'akin Mama ta jiyo karad'in Miemie na ba ma
maman labari tana dariya.

Da murmushi ta samu
ta dan dosana tana kallonsu kamar ta sa kuka.

"Na fuskanci yarinyar nan in dai tai arangma da
Abbanta tana kwanan murna, haka kwanaki
dak'yar na ban6areta jikinshi ashe bata manta shi
ba tana kuka,shima harda y'ar kwalarshi yana
daga mata hannu...

Ido ta kurawa Maman ba koh
kiftawa..

Ba dai Mama na nufin Ja'afar yana
zuwa garin nan ba kuma har gidan nan?...

Mama
ce ta kat'se mata tunani da fad'in "Ban tunanin
yaron nan koh a hanya ya ganni zai gaidani ba
sam bayan aurenki, duba ga yadda na rika mishi
fatattakar arziki..

Zuwan shi biyu gidan nan ashe
makaranta ya koma kinji..

Murmushi tai Maman
da iyakar shi le6e tare da daga kai.

Tuni ta
zurfafa tunani,har bata jin mey Mama da Miemie
ke fad'a,kan ta farga har idonta ya cika da
kwalla,da sauri ta juyar da kai tare da goge wa
kamin su gani.

Sakkowa tai tana taya Miemie
rad'awa teddy suna suna dariya.

Kallonsu kawai
Mama take tana wani tunani, kai ta kad'a kamin
ta tashi ta basu gu dan tasan Abba yana gaf da
zuwa.

Washegari da yamma tana kokarin shiga
wanka akai mata sallama.

Hijab ta zira harda
shafa powder da zumudin Ja'afar ne ma,kila ya
samu labarin tana gida.

Turus tayi tare da
chunno baki kamar Miemie ganin Alhaji da
abokinshi.

Baki ya washe mata yana fad'in ta
karaso man kusa...

Murmushin mugunta tai kan
ta kalloshi "Dan bani minti biyar na fito a gida...

Kai ya daga yana mata murmushi, ashe bazai yi
wahalar shawo kan Salma ba kamar Halima.

Ruwan da ta zuba na wanka ta d'auka da wani a
buta dan tsarkake kai in tai wankan t'sarki.

Tana
yi tana murmushi har ta gama.

D'aki ta shiga ta
tsane kanta da towel kan ta dan shirya a
gaggauce ta fita.

Yadda take murmushi ne yasa
Mama tambayar waye yazo, a tunaninta koh
Ja'afar ne,tana cewa Alhaji ne ta 6ata rai.

"Ki dai
kama kanki ki saiwa kanki mutunci,dan sam
mutumin ba nagari bane,kinjini ai?

Kai ta kad'a
tana murmushi, lalle Mama, yau Alhajin guda?..

Sai ta kad'a kai, "adu'a bata fad'uwa kasa banza.

Bayan sun gaisa yake zungurar abokin nashi
sarkin iya t'sari, duk tana jinsu tana murmushi
dan feleke harda tambayar Miemie,sai da suka
gama tass tana jinsu tana kad'a kai.

"Ai yanzu na
fita sahun matarka Alhaji,sai dai kabi sahun
zawarawa na..dan nayi iddah ni...

Fuska ya
g'imtse yana kallonta, "haba kar muyi haka dake
man,ina fa lissafi,yau watanki biyu da kwana uku
rabonki da gida na, kinga ai bakiyi wata uku bare
ace kinyi iddah koh ba haka ba abokina?

Kai ya
jijjiga yana fad'in "kwarai kuwa,dan haka muka
sani a al'adan ce.

Kai ta kad'a tana murmushin
takaici, wato ga babyn roba,a hular a lokacin da
akaso a d'auka a randa aka ga dama.. 6aro-6aro
tai mishi dalla-dalla kan ita ai duk bayan sati uku
take period, kuma ya sani sai dai ya take.

A fafur
yace shi baisan zance ba,kawai ya maida ta
dakinta.

Juyawa tai ta koma gida,tana ji sai
kwad'a mata kira yake tai mishi banza.

Da farin
ciki ta shiga har baya misaltuwa, dan da yanzu
dabarar yin wanka ba tazo mata ba da tuni
ansha da ita an gama.

"Ba dai ya maidaki ba
naga kina murna tun yanzu Salma?..

Yanzu ke
bazakiyi kishin kanki ba har kin bada kai daga
fita bori ya hau?..

Ina laifin ya samo Abbanki da
maganar in dai da mutunci aciki...

"Au dariya ma
na baki koh Salma?..

Ga shash..

"Mama ni fa ba
aure a t'sakanin mu da Alhaji yanzu,dan tau nai
iddah ta....

Baki sake take kallonta,dariya tasa ta
bata labari,sai ga Mama na tikar dariya.

"Lalle
yarinyar nan da wayo ki ke,kwarai kinyi dabara,
dan sam mutumin ya sane min, dan ban fad'a
miki bane,ba'a fi sati da dawowarki gida ba muka
had'u da dan talikinnan,d'auke kai yai kamar bai
ganni ba fa,bayan sarai mun had'a ido..

"Shi yasa
yaron nan Ja'afar nake ganin kimarshi har
kullum,dan koh bayan rabuwarku yana daraja
mu,musamman zai sa azo har gida abokinshi yai
mana goma ta arziki in sun d'au Miemie...

Shiru
tayi tana sauraran maganar Mama, wai Ja'afar
take ma ya6o haka da kirari?..

Farin cikinta a yau
bai misaltuwa,ina Miemie na nan ta rad'a mata
itama suyi tare,tasan dai duk inda take yanzu
tana neman gida,dan tun dazu tai mata kwalliya
da kayan Abbanta kaninshi yazo ya d'auke ta.

Murmushi tai tana jijjiga kai.

Lalle ne *Duniya
Labari ce* By Feenat Ja'afar. feenat-jafar.my
wapblog.com
Feenat Jaafar's Mobile Blog
feenat-jafar.mywapblog.com
Like
Reply
Report
Aug 9
Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *
Feenat Ja'afar*.
43_Waya yake d'annawa a nitse yana duba sakon
waya kamar bayaso,kamili ne,da hasken
shi,sajenshi a yanzu shine sirrin 6oye kyanshi na
ainashi, sanye cikin kananan kaya da glass
manne a idonshi,da gani yana ji da ajinshi a dai-
dai lokacin nan,dan miskili ne yanzu na karfi da
yaji.

A yanzu ne yake tsone idon y'an mata
musamman na jami'a, dan ya iya t'sare kai da
tsare gida.

Rayuwarshi ta sauya,dan ya dawo
ainashin halaiyar shi ta da,koma yafi da din,
Ja'afar kenan,namijin duniya.

Dago kai yayi yana
duba yanayin garin da yadda kowanne shago
suke hadahadarsu,sai ya sauke kai kan Abdull
mai tahowa dauke da baby a kafad'a tana ta
washe baki tun kan ta karaso.

Tuni fara'a ta
maye g'urbin rashin walwalar shi,kashe wayar
yayi tare da ajiye ta gefe dan tarar gudan
jininshi,duk Abba dake gefe kad'an yana kallo.

"Abbaaa...

Miemien ta fad'a lokacin da yake
k'ar6ar ta,murmushi yayi mata tare da shafo
fuskarta "Na'am Miemien Abba..

Sai ta washe
baki.

Ciro changi ya mika ma Abdull, "Kan
magriba kazo ka maidata kaji?...

Kai ya kad'a
tare da amsa yayi godiya.

Zama yayi tare da
d'aura ta cinyarshi, Tasha kwalliya da rigar da ya
yo mata tsaraba cotton ja da pink,kan nan kamar
an mata shampoo sai kyalli yake yasha ribbons..

Hannu yakai kan dan beauty point nata ya latsa
sai ta sa mishi dariya.
Chapter 27 · 0% Book details