← Book details A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 29

Sashe 26

A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Chak ta tsaya jin daina kuka
Miemien,da sauri ta juyo taga Abba na jijjiga ta.

Ba shiri tai gun dai dai Miemien ta kawo wuta ta
kar6e ta.

Kuka na fitar hankali take tana bata
hakuri, ''Ni bansan mey yarinyar nan zata tsare
miki ba in ta zauna achan gunki ba,kullum sai da
kuka koh jinya za'a rabu?..

Ki bar y'arki a kusa
dake man tunda ita mai kulafuci ce...

Kai ta
daga tana share ma Miemien hawaye tana tai
shiru toh..

Dole tana ji tana gani ta koma da
Miemie, dan yau fir taki yadda tunda ta d'andana
zama da ita.

Kanta take shafawa,ita kam ta
tasata gaba tana ta kallo ba koh kiftawa.

A
hankali tace "Miemie..

Idonta a kan Salman tace
"Uhmm.

Kwanto wa tai a gefenta tana g'yara
mata kwanciya, kamar wata babba ta fara mata
fad'an ta zama mai ji dan Allah.

"Ban san
matsala Miemie, ki rufan asiri ki daina halin nan
naki na kumbura ma mijina baki,kinji?..

Kai ta
daga mata kamar gaske.

Sai tai murmushi tai
kan tace ta taso suje suyi girki a kitchen.

Shikam
Alhaji da murnar yau Miemie ta tafi ya shigo
gida,shi kanshi ya rasa mey yarinyar ta tsare
mishi a gidan,duba ga su Ja'afar na gidan.

Sai
dai tun daga bud'e kofar parlourn farin cikin ya
kau.

Dariyar Miemie ya fara cin karo yana
shigowa ta kitchen,dan haka da sababi ya isa.

"Mey ya zaunarki har bayan magriba baki dawo
ba?...

Mey kuma ya dawo da wannan?

Duk ido
suka zuba mishi,mai hali kuwa Miemie tuni ta
chunno baki gaba tana mishi wani irin kallo jin ya
fara sababin nashi.

"Wallahi har kusan suma tayi
dan kuka yau,tausayi ta bani shine na dawo da
ita,kai hakuri duk ita tasa muka kai magriba.

K'allon Miemien yayi da kamar harara kamin ya
kad'a kai dan takaici ya fice.

Ajiyar zuciya ta
saka,ta tsalake rijiya da baya da k'yar,kan ta
dawo kan Miemie ita tuni har ta cigaba da
sabgarta.

Sai dai ana zuwa kwanciya yace daga
yau Miemie zata bar kwana dakin su,koh ta koma
kasa.

Ya ta iya,dan a zauna lafiya ta sauke
Miemie kasan,dan ba yadda za ai ta luluka
yarinya chan wani waje ita tana wata jahar,a
ganintq Miemie nawa take. ******* Fur yanzu ta
daina ganin fuska gun Alhaji, in ya shigo ba
wanda ya isheshi kallo,asalima ya daina zama
bangarenta sai cin abinci koh bacci.

Yau dai ta
d'au damarar fara koyawa Miemie sabo da Alhaji.

"Abba ki ne kinji Miemie nah?..

Ki dinga mishi
oyoyo kina mishi dariya kinji?, banda
harara,banda turo baki,kina ji na?

Shiru tai tana
binta da kallo kawai,chan sai ta yak'e mata
hakori.

Cikin farin ciki Salman tace "yauwa,koh
ke fa,be a good girl ba? kai ta daga mata tana
dariya.

Alhaji yai wanka ya shirya yaje parlour
yana duba abu a system nashi su kuma suna
daki gun shirya Miemie.

Daga parlourn ya kwada
ma Salma kira wai ta fito mishi da agogon shi na
kan mirrior.

Murmushi tai ta k'alli Miemie,tasha
parking da ribbon sanye da gown ja da baka iya
g'wiwa, dake fara ce sai tai mata k'yau sosai.

Agogon ta d'akko ta kamo hannun Miemie, "Kai
ma Abba a maza yana parlour,ki nutsu dan Allah
kinji Miemie nah..

Kai ta daga tana dariya ta
karbi agogo tai parlour.

Bayanta ta biyo dan
ganin ya zata kaya, daga yau ne zata fara koya
musu kusanci da juna shi da Miemie.

A dunkume
ta isa gunshi yana duba abu a laptop, mika mishi
tayi ba koh magana, sai ya dago ganin itace,tai
mishi kyau sosai,ga sai kamshi take,ba abinda ta
bari na babanta a ganin shi har dacin ran,in baxai
manta ba yanzu ne zata shiga shekara uku,amma
duk ta tara dacin rai wai da fitsara.

Kai ya
d'auke ya cigaba da abinda yake, Salma har ta
fara murna ganin bai mata dan halin ba yau.

Ita
kwa Miemie sai ta ajiye agogo kan hannun kujera
ta juya tsautsayi agogo ya fad'o kasan tiles sai
glass din ya fashe.

Da azama ya juya,ganin
agogon akasa a fashe Miemie ta juya ta mike ya
fara sababi.

"Duk wani mugun hali irin na ubanta
yarinyar nan ta iya,agogon nawa zaki saka da
gangan ki fasa min?..

Waje Salma ta fito ganin
ya yo kan Miemien a sukwane, duk tana k'allon
abinda ya faru.

Kumatun Miemien ya ja tare da
kai mata rangwashi akai yana sababi,tuni ta hau
kuka jin zafin abin,da sauri Salman ta karaso dan
bashi hakuri.

"Shegiyar yarinya kawai,kin san
kud'in agogon da kika fasa kuwa?..

Ja Salman tai
ta tsaya tare da rintse ido.

Ga ihun Miemie tana
kiran Aunty,ga sai zagin y'arta yake harda
sheganta mata ita?

"Alhaji..

Cikin fusata ta kira
shi tare da bud'e, Rai 6ace shima ya dago da
niyar huce haushin shi kanta ta rigashi.

"A
gaskiya ka daina sheganta min yarinya, dan da
ubanta gaskiya,haka kawai, ina fa kallo tana mika
maka ka d'auke kai,ta ajiye ya fad'o kasa,toh
meye lefinta aciki har irin wannan zagi?..

A'a toh
gaskiya...

Kai ta kawar ranta 6ace.

Cika Miemien
yayi yana kallonta, wannan ne karo na farko da
ya fara ganin fitsarar Salma,shi zatai wa tsawa
akan Miemie?

By Feenat Ja'afar.
9/29/16, 9:37 AM - Queen Safiyyert
: *A BAKIN AURANKI* *
Feenat Ja'afar*. 41_Da
gudu ta karasa tana kama hannun
Salman,d'aukarta tayi a ta sa6a a baya, "Yi shiru
kinji..

Muje daki...

"Kar ki kuskura ki shigar min
d'aki da wannan yarinyar..

Chak taja ta tsaya
tare da juyowa tana kallonshi.

"Kema kar ki
shigar min d'aki,ni zakiyi wa rashin mutunci kan
y'arki?..

Toh baki isa ba,dan ba ayi macen da ta
isa daga min murya ba ki sani.

Cikin karfin hali
tace "Toh mey ka ke nufi da hakan?..

Daga fad'in
gaskiya?..

Haba Alhaji,Kullum ina fuskantar
yadda ka ke tsagwamar yarinyar nan,shi yasa
sam bata shiri da kai ai...

"Ba wani nan,bakin
halin yarki dai irin na tsohon mijinki dai,da kuma
shegen taurin kanta irin nashi,koh kin zata na
manta da waye shi zamanin neman aurenki?

Da
sauri ta tare mai numfashi harda sauke Miemie
kasa da sauri, "Ba ruwan Ja'afar cikin maganar
nan tamu,zai fi kyau in ka daina sakoshi
ciki..kuma na fad'a maka y'ata bata da wani
mugun hali,sai dai naka mugun halin rashin son
yara, da kuma..

Shiru tai tare da ja da baya ganin
ya zaburo kanta, "wallahi kar ma ka soma,dan ba
yadda za ai in zuba ido kullum kana aibanta min
yarinya wallahi, nawa Miemie take?

Amma k'arfi
da yaji so ake ta iya dan hali..

"Salma ni nake
fad'a kina fad'a?..

Ashe baki da mutunci?..

Kai
ta kad'a tare da juyar da kai, "Nikwa nake da
mutunci tunda a cikin gidan ubana ka auro ni
kuma...

"Subhanallah,haba ku k'wa..

Juyawa tayi
taga Maman su Nabila na shigowa dakin.

"Tun
ina shanya nake jiyo ihun Miemie da naku,bai
dace ba Allah,kuna abu a gaban yarinya..

"Ba
ruwanki cikin zancen nan,in ba so ki ke ya taso
da kwantaccen naki ba ke ma..

Shiru taja
bakinta tayi tuni idonta ya fara zubar da kwalla,
ya cigaba "Yara nawa ma basa gabana bare ta
wani, saboda haka akan yaro ba mai sani ciwan
hawan jini,dole yau ki mayarta gun ubanta,koh ki
san nayi da ita.

Cikin kuka tace "Bazan iya
rabuwa da y'ata ba,kai hakuri raina ne ya 6aci..

Malalacin murmushi yayi,kan yace "Daga baya
kenan,amma dole ki za6a zaman dani koh da
yarinyar ki...

Maman Ja'afar ta kallo da itama ke
hawaye tana kallonta,sai ta cije le6e da takaici.

Juyawa tayi ta d'au Miemie, kan ta kalloshi ido
na fidda kwalla.

"Ni kam na kasance daga masu
taya annabinmu kishin Al'ummar shi,dan haka ina
son haihuwa,bi ma'ana zan iya rayuwa da Miemie
kad'ai mud'in Annabin mu zai alfahari dani...

Cikin zafin rai yace "Kimin hausar da zan gane
Malama ni..

"Annabinmu yace kuyi aure dan ku
hayaiyafa,domin go6e kiyama nai alfahari daku..

Kayi aure,amma baka fatan tara zuri'a, hakan
yana nufin kana tarjiya a bisa umarnin manzon
Allah..

A tunzure yai yo kanta, "Kimin shiru
fitsararriyar kawai,koh yayarki bata isa ja ina ja
ba wallahi, dole ne yau ki za6i d'aya..

Cigaba tai
da batun ta ido rufe, "Nai ma biyayya ta t'sawan
shekara guda ina bin yadda kaso,toh ka sani ni
Sunnah na dauki aurena,kuma zan cikashi ne ta
hanyar tara zuri'a, dan zanyi alfarhari idan na
kasance a daya daga wanda Annabi zai alfari da
ita...

Mari ya de6eta dashi jiki na 6ari,da sauri ta
dafe gun tare da bud'e ido,kuka Miemie tasa
ganin an daki Auntyn ta, "Mutuniyar banza
kawai,ni zaki mayar jahili?..

Murmushi tayi kan ta
kad'a kai.

"A'a,dan kuwa kafi jahili,danshi dama
bai sani ba bare take,kai kuwa ka sani amma
kana taya shedan rawa,dan baka kaunar..

Shiru
tayi ganin zai kara mata wani,da sauri ta rintse
ido tana hawaye,jin shiru bataji saukar mari ba
yasa ta bud'e ido.

Hannunshi rike a hannun
Maman su Ja'afar, "Lalle lokaci yayi da ya
kamata in tanka maka Alhaji,lokaci yayi da zan
daina bin umarnin ka ina 6ata..

Ashe har alfahari
ka ke cewar yaranka ma basa gabanka?..

Jiran
amsa take tana kallonshi, da borin kunya yace
"Cika min hannu...

Ba musu ta cika, Salma ya
nuno "Ke kuma ki tafi gidan ku,na sake ki saki
daya,na koyan hankali,in kin koyo kofa a bud'e
take ki dawo..

Ido ta rintse gabanta na fad'uwa,
wai ya saketa?..

Daga fad'in gaskiya.

Kan
Maman su Ja'afar ya dawo, "Wato zuwan
fitsararriyar yarinyar nan ta sa kin fara sauya hali
Halima koh..

Kai ta daga da sauri..

"Kwarai
kwa,dan yanzu na gane kuskuren dana tafka a
zaman baya da nayi da kai, nima ina son zuri'a,
ina son su Ja'afar sama da komai yanzu,kuma
zanso wanda duk yake son su,zan kuma yi fad'a
da duk mai kinsu, aciki kuwa harda kai usman...

Baki ya saka yana mata k'allon mamaki
"Usman?..

Babbar magana..

Halima yau ke kike
kama sunana ba ma Abban Ja'afar bare Alhaji?..

Shiru tayi tana kallonshi,sai sababi yake daga
karshe itama yace taje sai ya nemeta.

T'saki
sukai mai lokaci daya ita da Salma,duk da kallo
ya bisu Salma tai d'aki.
Chapter 26 · 0% Book details