← Book details A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 29

Sashe 18

A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tamkar ba kowa a gidan ka ke ji sai karar fankar
sama dake kadawa a parlourn wacce bata hana
gumi t'satsafo mata ba.

Rarrafo wa tai zuwa
kofa,iya karfinta ta kwalawa Bintun kira,ji take
tamkar zata mutu dan azabar ciwo,tuni ta fara
kuka tana ambatan Allah,tasan koh zata mutu
Bintu bazata taimake ta ba,fatan ta Allah ya
hankad'o mata Ja'afar koh wani ya ceceta.

"Wayyo Ya Ja'afar, Innalillahi..

Bintu..

A razane
ya karaso cikin gidan dan jin ta ambaci Bintu
cikin kuka.

"Subhanallah..

Salma..

Ina Bintun
toh?..

Da sauri ta dago,tana ganinshi ta kara
fashewa da kuka tana cije le6e. gaba daya ya
tallafota yana aikin sannu sannu.

Waya ya ciro
dan neman Garba ya kaisu asibiti, tana ta ringing
shiru..

Da rigarshi ya goge mata gomin dake
tsatsafo mata, "Bari na ga koh bacci waccan
take na taso ta.

Hannunshi ta rike gam tana
girgiza mai kai, Kanta ya shafa, "ki d'aure
Salma,bari na kirata kinji.

Dak'yar ta cika shi yai
dakin Bintun, dan ji take yana tafiya zata mutu.

Bata parlourn, sai ya bankad'a daki,tana mike a
kan gado taja rabin bargo tana dariya kasa-kasa
tana charting hankalinta yai gaba.

A sukwane yai
kanta,bai wata-wata ya sinketa da mari mai rai
da lafiya,a gigice ta mike tare da dafe
kunci,wayar ya warce, "Lalle haukar nan taki
karuwa take Bintu,yanzu dama kina cikin gidan
nan Salma take ta kakarin kiranki kamar zata
mutu?..

"Toh ki biyoni yanzun nan waje, tana turo
baki ta sakko kan gadon tana gunguni.

Nishi take
ta dafe d'ukkan hannunta a kasa, sannu yake
mata da tausayawa,da harara Bintu ta bita da jin
haushin akanta an mare ta.

"Ka kira min Iya
Shatu dan Allah Ya Ja'afar kar na mutu..

Bintu
ya kallo dake maka musu harara, "Kizo ki
kamamin ita na kira Iya Shatun, kamar bata so ta
matso kusa,yana fita ta mat'sa tana jan
tsuka,"aikin banza,dan kina wata shegiyar
nakudarki akan hakan kika ja aka mare ni, wallahi
za...

"Eh dan Allah kazo yanzu mukaita asibiti..

Shiru tai jin Ja'afar na kokarin shigowa tare da
matsawa gun Salman da sauri zata ta6ata tana
sannu.

A hankali ta janye daga hannun Bintun tai
dan ciki kad'an tana nishi, da sauri ya karaso
dakin yana mata sannu.

Nishi take iya karfinta
sukaji sallamar Iya shatu,tana dubata tace ai
haihuwa ce tazo gadan-gadan, ya basu waje, ya
siyo reza da sauran abin bukata.

Gam hannunta
na cikin nashi,ji yake tana cikawa in ya tafi zata
mutu.

Kanta ya tallafo yana ta d'aure, iya shatu
sai k'allon ikon Allah take.

"Kai hakuri
Jafaru,zata haihu lafiya dan ina jin kan D'a,
yanzu bazata ji komai naka ba sai adu'a.

Kai ya
kada harda guntun hawayenshi yai waje,yana fita
Bintu ta d'aura a bayanshi.

Iya shatu tsuhuwar
ingozoma ce mai ritaya, da guntun hand gulf din
zuwa awunta ta karbi haihuwar Salman.

Allah ya
taimake tazo mata da sauki inji Iyan,sai shigowa
yai shi da Garba yaji ihun jariri,baki wangale zai
dakin iya shatu ta fito k'ar6ar reza.

Ummanshi
ya fara mawa albishir sai Aunty A'i,tuni ya fesa
cikin gidan su,da ance mey ta samu?

Sai yace
bai gani ba.

Har aka kintsa komai basu kara
ganin keyar Bintu ba,sai da zasu asibiti ta fito,shi
kam bai
ya ma ta ita.

Suna fita su Aunty A'i suka
zo da Ummi,lokacin Bintun na t'sakar gida tana
yankar farce,ita dey Iya sai mamakin karfin hali
irin na Bintu take.

Sallama suke ta manna musu
bajon hauka,tuni Ummi taja dogon t'saki, taki
jinin Bintu a rayuwa.

"Banza y'ar bakin ciki
kawai,toh sai ki had'iyi zuciya ki mutu ai..

Hannu
Aunty A'i ta daga mata halamar tai shiru,ita k'wa
da harara tabi su har suka shige.

Sun dawo an
duba suna lafiya ita da babyn ta,Ja'afar baki har
kusan k'unne dan murna,yana makale da yarshi.

"Um,Baban baby ba koh dan karar nan ma ta
manyan yayu..

Kai ya sosa yana ma Aunty A'in
murmushi, ba dan yaso ba ya mika mata ita.

Kan
kace mey gida har ya cike da dangi yan barka da
yan unguwa.

Sai dare ta samu tasa hakarkarinta
dan hutu.

K'allon babyn take mey kama da
Abbanta, gashi kadai da dan _beauty points_
(dimples) tai gadonta.

Murmushi tayi tana kai
hannu kan kumatun babyn, Allah mai halitta.

Murmushi yake musu yayin da ya shigo d'akin,
sai ta daga kai ta k'alleshi, kai ta girgiza tana
dan murmushi.

Sallama ta uku yana musu kenan
yana dawo wa,ta rasa wani irin kulafuci yake
musu musamman babyn.

Zama yayi yana shafo
sumar babyn da farin ciki.

"Oh ni kam,koh zaka je
da ita in tai kuka sai ka kawo ta.

Murmushi yayi
yana kai baki kan dimple din babyn yana kissing.

"Ba kinki barina na k'wana anan ba?..

Da kalar
tausayi yace "yau dai daya naji dumin y'ata kinji?

Sai ya marairaice fuska.

Dariya ta dan mishi,kan
tai magana ta jiyo Babah mai zamar mata tana
ya fito zata zo ta k'wanta,taga sallamar bata
karewa.

Dariya suka sa kamin ya tashi yai waje.

"Maza ki rika biye mishi ki debo ma kanki
magana da kazamin goyo ai.

Da rashin fahimta ta
k'allota tana neman karin bayani. ***** ***** Yau
suna,baby taci sunan Mama tun ran huduba
amma ya 6oye mata.

Sosai yau daya Ja'afar ya
biya mama,harda mishi waya tana kwarara mishi
godiya ba iyaka.

Maijego tai ras abinta da Baby
Miemien ta,sun fito sunyi k'yau sosai.

By Feenat
Ja'afar.

Ai hakuri da wannan dan zani gidan
Suna Salma..

Zuwa yamma in na dawo zakujini
Lol..
9/29/16, 9:17 AM - Queen Safiyyert
: *A BAKIN AURANKI* *
Feenat Ja'afar*.
29_Suna ya wat'se kalau,maijego tai
goshi,ak'wati guda Mama ta mata na suna sai na
baba,ga Umman Ja'afar nata daban da tazo
suna,chan gidan su Ja'afar su ma sun mata
karamci,sai son barka.

Wankansu suke cikin
g'yara na musamman da Mama ta zage yi ma
y'arta, albarkacin Miemie mama ta sakko sosai.

Shirya Miemie take tare da taimakon Ja'afar din
suna ta nishad'in su yau za ai yawan arba'in.

Ta
chakare sosai kamar yau ne sunan ita da Miemie.

Baya ta juya mishi yana goya mata ita, "D'aure
ta dakyau,dan kinga machine zamu hau..

Kai ta
kad'a tana murmushi, Sai da ya zaga ko'ina yaga
yayi kan ya bata majanyi tana mishi dariya, "A'a
toh in baki iya ba ni sai na goya abata kawai...

Dariya tai kan tace "Da kwa kabar abin fad'i
agari kuwa.

Jakar ya d'au mata ta d'au mukulli
sukai waje,shima yasha sabuwar shadda abinshi.

Bintu na t'sakar gida tana d'anne-d'anne a wayar
da dak'yar ya bata.

Da harara ta bisu harda dan
t'saki a hankali.

"Toh mu zamu fita sarauniyar
charting..

Sai kisa mana mukulli a gida dan
gudun kar a dirko kina sana'ar taki koh..

Tuni ta
kara k'uluwa kuwa,ita dai an mayarta borar karfi
da yaji a cikin gida.

Hannu Salman ta dago mata
halamar sai sun dawo,da harara ta bisu har sukai
waje.

"Jishi kamar wani dan daudu rike da jakar
mata.

K'wafa tai tana tashi t'saye, "Ba dai kin
fara fita ba?..

K'wanan nan zaki yabawa Aya
zakinta wallahi. ** K'wana biyu yau tayi tana fita
yawan arba'in, yau ne na uku,yau kuma aka tafka
t'siya da maigidan,dan fur yace ba inda zata je.

"Bazaki k'waso ma yarinya rana ba fa,kiyi hakuri
kawai.

Iya wuya Salma ta kawo dan takaici, tayi
magiyar yaki kuma,kawai sai ta raya mata tunda
dama taki bari ta koma hagu.

"Amma gaskiya
baka min daidai ba Abban Miemie in har ka
hanani fita yau.

"A ka'ida sati ake fita yawan
arba'in fa,amma ni na yarda zanyi ukun shine har
na gama shiri amma kace bazani ba...

Gaskiya
da sake.

Gefe tai da kai tana kunkuni,tuni ta
kular dashi shi zuciya kusa.

"Toh ban hanaki ba
kije d'in, amma ki ajiye min y'ata ki tafi ke kad'ai.

Baki sake take k'allonshi,ganin yadda ya fidda
waya yasha kunu ya barta.

A zuciyarta tace "Eh
lalle,da gani abin Ya Ja'afar yazo da wulakanci...

"Kasan dai ba yadda za ai na tafi na bar Miemie
a gida,dan Allah in wasa ka ke ka bari,dan kam
nasa rai da fita yau..

A tunzure ya mike da niyar
magana cikin masifa,sai yai shiru yana k'allonta.

"Kiyi toh gaban kanki kawai..

Sai yai waje da
zummar barin gidan ma dan haushi.

Sai dai
mey?..

T'saye yayi yana binta da k'allo galala,
ganin yadda ta fara kame-kame dan ya kamata
tana musu la6e ta window.

"Ke kuma lafiya kike
abu kamar marar gaskiya?..

Dakewa tayi tai
ganin kamar bai ramfota ba.

"Dama zuwa nayi
ina son na leka nan na dawo ne...

"Ba mai fita
yau acikin gidan nan in dai ni ne mijin, wacce ban
isa ba ta fita nagani..

A fusace ya fice yabar
gidan,duk sai ta Salma tafi zafi.

Ita kam Bintu
dariya tasa harda shewa, "Yau karya ta kare,sai
a za6a zaman gidan miji koh fita yawan gantali
gard'i...

Tana jiyota tai banza da ita tana
hawayen bakin ciki.

Waya ta d'auka ta kira Aunty
A'i kan abinda Ya Ja'afar ya mata.

"Salma kiyi
biyayyar aurenki, dan Allah kiyi hakuri da fitar
kawai.

"K'wana biyu ai yayi ma,tunda kin zaga
ko'ina ai har gidan su...

"Aunty A'i ban fa wuni a
gida ba kullum a ziyara muke wuni.

"Ai duk fita
kina zuwa,dan Allah kar ki dawo muku da hannun
k'yauta baya man,kuna cikin zamanku abin
sha'awa.

Baki tai ta bata sai da ta tabbatar mata
da ta hakura kamin sukai sallama.

Haka tanaji
tana gani ta hakura da fitar tai zamanta a d'aki.

Koh abincin rana kin zuwa yai yaci a gidan sai
gidan Garba yaje.

Kawai zuciya ke raya mishi
Salma ta fita,bazai so yaje gida yaga tabbas ta
fitan ba,kawai sai yai zamanshi har yamma tukun
ya koma gida.

Dakin Bintu ya nufa har yanzu
baida walwala sai ya tabbatar da Salma bata fita
ba,yasan Bintu kat ce,bata t'sallaka doka akan
fita,in yace A'a, toh ta hakura.

Sannu da zuwa tai
mishi tana fara'a, a ranshi yana aiyana da Salma
ce yasan sai ta cika tai fa kan ta mishi sannu da
zuwa duk akan ya hanata unguwa,amma kullum
y'ar uwarta ko ajikinta.

"Yau bayan fita ta Salma
ta fita?..
Chapter 18 · 0% Book details