← Book details Yaron Gidana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 17

Sashe 9

Yaron Gidana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Zarah yadai?”
“Lafiya kalou,kamar wani abu na damun ƙawata kwana biyun nan,what's d matter?”

Caɓe baki tayi “Babu komi me kika gani?”

“hmm bakomai kamar dai kin rage walwala ne...dama nazo maganar sir El'ameen ne” hakanan taji ras gabanta ya fadi .

Amma still Bata nuna ta girgiza ba “Ehem?” tayi mata alamar tambaya

“Ya daina zuwa aiki...” katseta tayi da sauri

“Kinsan mutum mai jama'a ”

“don yina mutum mai jama'a sai layukansa su daina shiga?”

“Zarah ki samu manajane da kokenki bani ba ,watakila ma ya bar aikin ne oho dai”

“haba bazaki bamu ɗan hint ba naga dai tare kuke”

“Zarah ... Zarah Plz mu bar hiransa”

Shikenan an barta .
Ta mike a sanyaye tabar office din cikin dan damuwa

Kausar tana ganin Zarah ta fita ta daura hannu aka zata fasa ihu sai kuma tai maza ta gintse bakinta ta sauke veil ɗin kanta zuwa saman kafada ta fara firfita goshinta da gumin wahala ya fara tsatsafo mata .
Cikin tashin hankali take nanata Innalillahi wainnailaihir rajiun ,ta zaro wayarta a jaka tana laluben wayarsa amma duk a kashe .

Tashin hankali wanda ba'a saka maki rana . Ada Sam bata damu da jinsa shiru da batayi ba ,sai yanzu da aka shaida mata kasa samunsa sannan taji a duniyarta babu mahalukin da takeson jin muryarsa sama da El'ameen.

A take taji ƙwalla sun fara cika mata ido ,ta sauke hannuwarta a table ta rafka tagumi cikin dogon tunani. .....a haka taji ana ƙwanƙwasa ƙofa ,a galabaice ta furzo kalmomin bakinta wajen bada umurnin a shigo
“Yes come innn ”

Cak ta mike ganinta cikin wasu crazy English wears sun dameta gam gam ,saman gwuiwar wandon jikinta a farfashe ,ta manne fuskarta da wani wawakeken tabarau

Ƙaƙalo dariyar yaƙe tayi tace “surayyya...your welcm ...ki zauna ga waje Allah dai yasa na canki sunan”

Wani wawiyar tsawa ta daka mata

“Kausar inakika kaimun mijina?”

“miji?” dama kina da miji?”

“ke dallah jacan rufe muna massai(tana nufin bakin Kausar ne massai)...karki mun irin na en duniya wallahi na yaga maki bariki ,ki fito mun da El'ameen dina ko kiga madarar tujara”

Tau ! Ta yanke ta da mari ,dafe wajen tayi a mamakance tace “Ni kika mara ?” daddagewa tayi ta kara ɗauketa da mari ta daya side din

“wannan marukan da na baki halsan damo gareshi ,zai iya daukn gyaran zama da sassaita tarbiyya wajen futsarrariyar yarinya irinki ....a gefe guda kuma zai iya daukan alo tsiya alo Danja ,El'ameen ɗin banza da wofi shi yaron goye ne da zaki zo ki na wani tambayata shi?

Fice mun daga office kafin in kakkaryaki in watsa ta window”

“Badai Ni kika mara ba?”
“ko in Kara maki ne shashasha fitsararriya ?”

Kwallane ya surnano mata “Wallahi yanzun nan zan kirawo wanda zai rama mun”

Biyoni ta tayi da gudu da wayan canjin Laptop tsaya in maki lilis sai wanda zai rama makin yazo da hujja.

Ai a karce ta fice
[3/10, 3:08 PM] Chu_chu👻💩: Page S
My house boy

A gajiye ta shiga gidan su don ba'a fadin damuwa dake ranta ,tun fitar surayya office dinta har kawo tashinta office har shigowarta gida bata fasa kiran wayar El’ameen ba sai dai amsar dayane baya tafiya.... To wai me ya faru dashine? Kodai ya samu accident ne ya mutu ba'a sani ba? Ko dai anyi kidnapping dinsa ne.
Da sallama ta shigo falon gidan ,turus tayi ganin El’ameen turmushe a ƙasan carpet mamanta na kan kujera da alamu bai daɗe da shigowa ba . A fusace tace. “Me ya kawo ka gidanmu....El’ameen tashi ka fita!...ka gama kasheni da daɗin bakin ne ka dawo kan mahaifiyata?”

Momy ɗagowa tayi ta kalleta cikin fuskar ɓacin rai “Musulunci bai ba mace damar faɗan ma mijinta magana kowani kala ba ,so mind your tongue and be careful ” tana fadin hakan ta miƙe ta bar masu falon .

Kanta hautsinewa yayi da sauri ta dawo kujeran da Yike kallonsa “Tashi ka wani gurfana a ƙasa ,miƙe ka fadamun meke faruwa ina ka shige ake nemanka kasa surayya tazo za tayi mun tijara a office”

Cikin sanyin jiki ya mike ya zauna akan kujera “Ki yafe mun my Kausar ” he lamented .

“Ina ka shige all that long Kuma ina kabar wayoyinka...lastly me ya kawo ka gidanmu that's my q.”

“Kausar bana son fitina ,surayya matsala ce a rayuwata ,the very day da muka rabu baran baran dake a office naki ,ban sukuni ba ,nayi ta neman numberki ke kuma kin ƙi ɗagawa ,hakan yasan na rataya laifin komai na aza a wuyar surayya da ace batazo ba da bata hada mu fada ba,i then try to reconcile but how? Naje na samu babana da maganar auren mu Ni da ke ,and God so kind ya amince a ranar yazo ya samu dadynki sukayi maganar auren mu ,Dadynki yayi adressing ɗinsu garinku aje can a nemo mun auren ki ,saboda nisa yasa sukaje da sadaki da kayan na gani Inaso ,sunje da niyyar a saka muna rana sai kuma abinda ya faru ya faru....Tunda suka dawo da farincikinsu labari ya waɗe dangi sai kuma surayya sukayo hayan ƴan daba kan a nemoni a sabautani dake da ita kowa ya rasa...Dole In nema wajen ɓuya har zuwa sanda za'a fara programe of events ɗinmu ,to ashe kuma ta dawo wajen ki ,babe your life is in great jeopardy bazan iya jure rashinki ba ,shiyasa nazo in roƙi su momy su bani ke kawai mun fasa taron bikin mu gudu mu bar ƙasar kar ta kashe mun ke ,coz nasan taje office ɗinki kinji abunda ya faru”

Tunda yake maganar ta watsa masa ido ,sam ta kasa fahimtar mai yakeson isar mata

“El’ameen an turaku neman aurena garinmu batare da sani na ba? To naji da kukaje meye abinda ya farun?...kuma ita surayyar ƴar dabace da zakaji tsoronta ka ɓoye kanka saboda ita kadai ka sani hijira daga garina...wai me ka daukeni Ni ƴar iska ce zan bika wani waje kai ba mijina ba kuma ba muharramina ba? Wait kanajin ma zan iya aurenka El'ameen kayi mun ƙanƙanta”

Hankalinsa tashi ya sake yi “Babe kar kice mun Bakisan maganar auren mu ba?”

“How would I know tunda a munafurce kukeyin komai,saidai Alhamdulillah yanzu naji komai sai ka koma ka auri dodonka (surayya) ku ƙyaleni in samu salama...bazan aureka ba ”

“Babe bazan iya auren surayya ba ko mata sun ƙare a duniya ,and beside an Ɗaura auren mu fa ,wai su mama basu gaya maki Ba ?”

Ɗaura hannu tayi aka ta kwantsama ƙara ,da saida gabaɗaya gidan ya amsa

“Na shiga uku !!!” da gudu duk mutanen gidan suka fito ,da nufin son jin bahasi

“Da gaske an daura mun aure da wannan abar...👉🏾” ta nuna El'ameen cikin rainaswa

Turus kowa yayi Yina kallonta ,hakan ya tabbatar mata da hakan ne an ɗaura mata aure dashi a ɓoye . Wani irin gursheƙen kuka ta rushe dashi ta haye saman ta da gudu tana duddukan ƙafa.

Da sauri sisters dinta suka bi bayanta cikin tausayawa suma kansu sunsan ba'a yi mata adalci ba ,momy ne ta tsaya a wajen El’ameen tana bashi baki don shima hankalinsa a tashe yake ,Abunda suke ta ɓoyewane gashi ya fasu .

****
3 days later

Ƴan uwa da dangi sun fara taruwa ,saura kwana biyu a fara events din Biki ,Amma Kausar gaba take da kowa ,ko ƙofar ɗakintata daina fitowa sa'annan ƙanninta ma sun goyi da bayanta ,tamkar ma fushi suke da iyayensu da sukayi ma babbar yayansu auren dole.

Iyayen kaɗai suke hidimarsu da baƙinsu ,amma Kausar daidai da gyaran amaren nan bata yarda anyi mata ba ko lalle tace bata so.

El’ameen kullum sai yazo gidansu Kausar amma sam ta ƙi fitowa abun duk ya damesa .

Ranar da Dangin El’ameen suka kawo lefe da keys ɗin gidan Kausar ,a ranar momy ta fayyace masu halin da ango da amaryar suke ciki sanadiyyar wata surayya....Ai kuwa nan dangin ango suka rikice da salati ana ma surayya tofin Ala tsine ,Ana tausayawa El'ameen da zurfin cikinsa ,sannan sun ƙara raina wayonsa da wautansa da ya yarda mace tana masa barazana a rayuwarsa .

Suna komawa gida aka kira meeting din gaggawa aka fayyace ma kowa abinda ke faruwa harda kin amincewar amarya da auren saboda tsira da rayuwarta.
A nasu tunanin kenan.

Aikuwa baban surayya ransa in yayi dubu ya ɓaci ba'a bar taronba saida yasa aka nemowa surayya visa zata koma makaranta ,sannan ya ma dangi alkawarin maganar zata mutu inshaalh

***
Sai da El'ameen ya samu labarin barin surayya kasar sannan ya dawo sa karsashinsa ,now he's trying to face Kausar da nata matsalar ,ya rasa gane dalilin da yasa ta tsanesa,har text ya tura mata surayya ta koma makaranta bata ƙasar ma ,amma Kausar ta daina kulasa ,kullum damuwarta ta yaya zata nuna ma ƙawayenta ɗan mitsitsin yaron nan wai a matsayin Mijin ta?

A haka shagulgulan Biki sukayi ta gudana amarya dai ko make up taki yarda ayi mata kuma hoto daya batayi da angon ba ,kuma duk events din da zai hada amarya da ango shima bataje ba,don haka sam bikin yaki armashi haka dai da ƙarfin tsiya aka Tisa ƙeyar Kausar aka kaita gidan El'ameen gida har gida ,Ango ya Narka arnakun kuɗaɗe wajen tsara ginin zamani ,iyayen amarya sun ɓatar da dukiya wajen tsara ɗakunan amarya don ta fito ƴar gata,hakan yasa gidan ya hadu ya zama kamar Aljannar duniya saidai cikas ɗaya mutanen da zasu zauna a cikin gidan basu da fahimtar junansu ....wani irin zama za'ayi kenan ? Ga ango dai ya shigo da abokansa ,amarya batayi welcoming dinsu ba ,hakanan suka tafi da satattan gwuiwa .

What will happen next ? Yau dai shine first night din su ,daren da kowani ango sa amarya yikeso ganinsa amma banda amarya Kausar.
Chapter 9 · 0% Book details