← Book details Yaron Gidana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 17

Sashe 7

Yaron Gidana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

****
Kausar tana shiga office janyo wasu takardu tayi ta fara signing a jikinsu

El’ameen shigowa yayi
“My love”
Ɗagowa tayi ta harare sa
“kwuuiiiii my love🙄 wai meye kake bina ƙafa ƙafa?”

Matsowa gabanta yayi ya rankwafo da kansa kusa da fuskarta

“Wai naga tunda daga yau zamu rabu ya kamata in ɗauki mu girly for lunch”
Ɗagowa tayi tana hura hanci “Au dama Kanada budurwa?”

“Eh mana,inada budurwa saima kin ganta fine and gorgeous oh I can't Imagine halin da nike shiga In Bama tare da ita kewa kusan halakani yakeyi ”
.Damm gabanta ya fadi kardai kishi? Duk da tasan ba'a yake mata amma ba'a wasa da mace

“Wane sunanta kuma a ina take?” ta tambaya a sanyaye

“Aushh inajin nauyin kiran sunanta naked ,Amma dai chubby ce ma'abociyar ƙira tamkar an zanata,ga fara'a ga bossy attitude in tamun tsawa,daɗewa Nike cikin zullumi....”

“man zaka fadi sunanta ko A'ah in bazaka fada ba barmun office”

Tuntsirewa yayi da dariya “Babe kishi ,bayan kinsan kece ”

Harara ta banka masa
“Kana neman hawan ruwana yakai 360”

“Yanzu dai naji taso muje ,ko bazaki ci shawarma ba,uhm shawarma babe😂😂¿
_(Yau fa an turo mun kyautan kudi ta account wai in siya shawarma awwwn🤩🤩😂...gaskiya fans ɗina kuna kasheni da love na gode sosai)_

“Uhm uhm kaje kai kadai kuma kar ka sake ka dawo baka kawo mun nawa pack din ba”

Gyara tsayuwarsa yayi ya juya zai fita yina ƙobo

“Ok in kinje ki samu shawarma in bakizo ba kin rasa ”

Nunoshi tayi sa tsinin biro tana matse ido cikin tsananin barkwanci

“You wouldn't dare....amm zo nan kawai zo nan” dariya ya fashe dashi ya dawo inda take

“uhm uhm try me and see sai na siyo reserve dina inci gabanki in maki ƙwalele”

“da daga ranar mun fara gaban magana Ni dakai ,kuma ka kirani a waya kajika blocked”

Buɗe hannuwa yayi botherlessly
“Ba damuwa indai kina nan zanzo in ganki😏😁”

Cuna mashi biro tayi a wajen cikinsa kamar zata soka masa📌 da sauri yaja da baya yina dariya .

“Hahaha come and pack your self ,Tashi muje😄” ya miƙa hannu yana rufe files ɗin gabanta

Miƙewa tayi cikin nishadi tana gyara zaman veil dinta

Oum Aphnan
09065990265
[3/10, 3:08 PM] Chu_chu👻💩: Page N
My house boy

Fitowa daga cikin wajen kujerar ta tayi shikuma ya ɗauko mata hand bag dinta ,kamar yaron gidanta ɗin dai na gaske ,but this one is out of luv😉Suka fito daga office ɗin ta suna tafe,yina rike mata da jakan suna sakkowa ta stair case ɗin benen ,suna hira suna dararruku cikin tsokanar junansu .

A ƙasa kuwa Su July suna tsaka da hira saura su uku suka rage saiga wata hamshaƙiyar budurwa ta shigo reception din kamfanin.
Kana kallonta kasan wanka yabi jiki ,kyau ba'a magana ,kuɗi basai an ce maka ƴar gata bace ba

Tana shigowa ta fara yatsina tana ma su July Kallon uku saura kwata duk ganinsu take wasu tsamaye ,a zatonta ma receptionist ne don Basu kai matsayin ma'aikata masu office a idonta ba ,saboda ta saba da ganin officers ɗin ƙasar Hongkong en da take

“Hiii😎”

Ta kora attention ɗin wajen gabaɗaya suka waigo suka kalleta ,Juliana ce tace “Welcome miss”

Mere Baki tayi kafin tace “Nazo ganin Mr. El’ameen ” kallonta sukayi suka bushe da dariya ,tawani shigo da izzarta saboda zataga El’ameen.

“Am i not talking to being?...mtseeww sound like foolishness”(bada mutane nake magana ba...taja tsaki)

Miƙewa July tayi cikin rashin kunya tayi maza ta riƙe kwankwaso tana jijjiga

“Miss ,bazaki samun ganin El’ameen ba sai in kin samu appointment ɗaga wajenshi ,in ya yarda ki gansa sai mu barki ki wuce”

Hassala ta daɗa yi ,ta fara hargagi tana masu masifa

“I said I called him and the picking call is not going....Bansan meye problem din numbobinsa na 9ja ba....aushhhh zafi” ta fara firfita da hannunta zufa na tsatsafo mata ,tana daddana wayarta da alamar dai son sake kiran layinsa takeson yi ,kuma zafin wajen ya ruɗata dukda yalwar Ac dasuke wajen

Kallon sheƙeƙe sukayi mata kawai suka kwashe da dariya “Heheehe Abuja babes with their fucking wahala...yen yen 9ja Numbers ƙaryar banza” july ta faɗi tana neman kujera ta zauna tana kallonta .

Ɗagowa ta sake yi looking so discomfort “Can you phone him by ur number? Ku kiramun shi...”

“Ma! an fada maki ba'a ganinsa saida appointment”
“shine nace his phone is not picking going ,dallah Malama in Zaki kira mun shi ki kirasa... Oh my God ,ku Wa'innan receptionist ɗin nan sam.........”

Ƙwalla ihun kiran “Babyyyyyyyyyy🏃‍♀️” tayi ,sannan ta ruga wajensa da gudu dayike sakkowa tareda kausar

Cikin matsananciyar mamaki yanufo inda take a sanyaye cikin mutuwar jiki ya kira sunanta da ɗinbin mamaki “Baby?!”

Buɗe masa hannu tayi irin ya rungumeta ɗin nan
“Whatsup baby? ....umuhhh💋”

Tayi maza ta kamo cheeks ɗin sa ta haɗe bakinsa da nata tana kissing ɗinsa ,sandarare ya tsaya a gabanta ,da sauri ta fara gyara masa zaman suit ɗin jikinsa ta kama gefe da gefen gaban suit ɗin da hannuwarta biyu ta tsaida idonta a kansa

“Baby jiya da dare na dawo daga Hongkong ko hutawa banyi ba naje gidanku baka nan,na kasa barci na ƙosa in ganka shine khalisat tace mun yau kana nan companyn nayi tracking address nazo....baby kayi duhu kaɗan😏But still adorable😘 Ina ka shige ne wayoyinka basa tafiya Hmm ,me ya hanaka kwana a gida? Where were you?”

Yanda ta tsinke tana zuba yanda kasan su kaɗai ne a falon babu kowa sai su ,kuma hakan ne A zuciyar surayya ta manta da duk wasu halitta dake wajen sai ita da hubbyn ta .

El’ameen ya kasa bata amsa kawai sai ma juyawa da yayi ya kalli Kausar da ta sagale hannu a ƙarfen benen tana kallonsu.

Sake waigawa yayi wajen surayya kafin ya fara inda inda

“Eh...am...Dama...?”

“Baby ynzu zakace na dameka da tambaya while i was worried about yhouuuu😢” ta maza ta sake faɗawa kafaɗarsa ta ƙanƙamesa kamar wani zai ƙwace shi a hannunta .

Bakinsa rawa ya kamayi a sanyaye yace “Kausar wannan itace surayya,ta matsayin causin ɗina...” da sauri surayya ta ɗago tana kallon halittar da yasa El’ameen laushi yina magana ba jin kan nan cikin ladabi ,ganinta babba ta girme mata fintinkau yasa tayi saurin miƙa mata hannu don su gaisa ,sannan ta washe mata baki tana ƙarashe ma el’ameen abunda ya manta bai faɗa ba

“Ni kwazin ɗin sane kuma fiancé ɗin sa (matar da zai aura bada jimawa ba)...”

Ƙyam Kausar ta tsaida idonta akan surayya firifirinta duk ya isheta ji take kamar ta ɗaga hannu ta kwaɗa mata mari kota Natsu don ta lura irin yaran gatan nan ne da basu taɓa sanin tsawa ba bare duka .

Surayya jikinta ɗan slanks yayi ganin ta mika mata hannu bata miƙo mata hannun ba sun gaisa ,a sanyaye ta waiga ta kalli El’ameen ɗin ta sake shigewa jikinsa

“Anan itama take aikin?”

Cikin ƙufula kamar ya rufe ta da duka yace “She’s my boss”
(Oga tace)

Washe baki tai “Babe like seriously ,wannan matan ta tara trillions of naira kenan? Tunda har tana da zarran zama oganka? Ai sannu mataaa ...aushhh oganmu🤭😆😆😆🤣”

Juyawa Kausar tayi ta tafi

“Laaa kamar tana kishi?🤣🤣🤣” ,cikin jin haushi El’ameen yace “Me yasa zakiyi ma ogata magana a haka?”

“Oh yi mun shiru😡😎 Na zaƙu inzo in ganka kayi mun Alƙawarin tokombo car ,idan na fita da first class a university ena ,kuma naci... amma kazo zaka ɓata mun rai ,bayan naga Khalisat da irin motar a gidanku ,kuma kai kamun alkawarin Ni zan fara hawanta a Nigeria?..shine karya alkawarin farko bai isheka ba sai ka haɗa ni da waccan hukuma halittar?(tana nufin kausar ce guzuma)

Oum Aphnan
[3/10, 3:08 PM] Chu_chu👻💩: “Me yasa kafin kizo baki faɗa mun ba”

“Sboda ina so in Surprising dinka ,and obviously it succeded😡”
Ƙunshe Baki su juliana sukayi suna dariya ganin yanda gabaɗaya El’ameen ya rude a gefe guda kuma suna mamakin kasancewarsa mai kuɗi ,amma yazo yina aiki a nan . Wani basaja ne wannan me yakeso yayi achieving?

“Calm down baby ok,listen to me ,you're not suppose to come to my office for Allah sake”

Zare ido tayi “Ina ne office din naka,? Yaushe akurkin wajen nan mai kamada plaza a turai ya zama work place din ka”?

Tsawa ya daka mata “Leave here...ki koma gida nayi magana”

Idonta cikowa yayi da ƙwalla “Kafana ƙafarka” ɗaure fuska yayi “Ok zamu gani” ya ɗaga ƙafa yayi hanyar wajen adana motocin wajen

“Ina motarka?”
“Karki sa in mareki ko In fada maki abunda zan dawo ina nadama leaveeeeee ...”

Meye halaƙarka da waccan guzumar?”

“Babyyyy...yaushe kika ƙaro Fitsara? Inacewa ki tafi kin tsaya kina mun ihu ,so kike kowa sai ya ji mu?”

Tsaki taja kawai ta nufi motarta da sauri ta mata key tabar wajen cikin ƙololuwan ɓacin rai

***
Kausar daga office ,wani near by restaurant ta shiga mai kyau ta zauna a daya daga cikin kujerun costomers ɗin

Ɗaya daga cikin yaran wajen ne tazo da list ɗin available foods da suke dashi ,tana nuna mata list ɗin tayi maza ta daga mata hannu cikin ɓacin rai . A sanyaye yarinyar ta juya ,can anjima sai gata ta dawo da list ɗin different varieties of snacks ,tsawa ta daka mata “Hey bar nan wajen” jikin ta a sanyaye ta wuce ta koma ,bayan kamar minti sha biyar sai ga wata yarinya ta nufota da list ɗin ganin tana zaune babu komai a gabanta .

A zuciye Kausar ta miƙe ta sungumi jakarta ta bar wajen ,ta rasa ma inda zataje don haka ta sake komawa office Tana shigowa a hargitse su zara suka hada kai suka fashe da dariya ,tsayawa tayi na seconds biyar tana kallonsu kana ta haye office dinta sa sauri saboda ƙwallam da ya ciko mata ido.....

Tana shiga ta goge idonta da bayan hannunta ,ta fiddo takardun da zatayi masu signing amma kawa saita zuba masu ido ta rafka tagumi.

Knocking taji saga waje a sanyaye tace “Come in”

El'ameen ne ya shigo aɗan firgice “Durling I'm very very sorry🙏🏻”

Saroro tayi da fuskarta da alamun fuskar shanu tamkar ba abunda ya dameta ta fara harhada takardun gabanta
Chapter 7 · 0% Book details